Showing 84001 words to 87000 words out of 117873 words
kazar amarci?
Dariya Yareema Sageer ya yi, don yana son Yayarsa Murjanatu sosai, tana da son zumunci da hadin kansu, shi sai yanzu ma ya tuna wai ana kai wa amarya kaza, shi haka ya tafi hannun sa na dukan cinya, dan banzan Awaisun nan kuma bai tuna masa ba, amma babu komai bari lokacin ya zo su koma Abuja, zai yi komai don Saadatu. Ko dawisu ne zai sa a gasa mata ba kaza ba.
Ya ce, Mairam Murja, ba dai shirin tafiya ake ba? Na dauka za ku zauna har ku raka amarya Abuja?
Murjanatu ta ce, Na so hakan, amma Ambassador ya yi waya maza-maza in koma sabida yara sun koma makaranta, kada ka damu za mu zo suna next year in Allah ya yarda.
Yarima ya ji kamar ya nutse kasa don kunya, amma a zuciyarsa ya ji dadin wannan fatan nata, fata na gari lamiri in ji masu iya magana, kuma babu wanda zai so ta haifa masa Da a duniya irin Saadatu. Wani disappointment din is a blessing (Aisha Sultana da ta cire mahaifa) don an ce yaya suna tsotso dabiu da halaye na mahaifan su.
Ya ce, Wa zai kai ku Maiduguri (airport)?
Ta ce, Maimartaba ya bada mota da dogarai su kai mu, Humaira da Najaatu za su raka mu har su ga tashinmu sai su dawo.
Ya fiddo wayarsa daga aljihun gabansa yana fadin, Bari in kira Suhail da Ahmad duk su raka ku, tafiya da maza za ta fi dadi.
Ya yi magana da Ahmad da Suhail, sannan suka yi sallama da Murjanatu, suka karasa falon Yakirjinoma suka yi gaisuwa ta sa musu albarka. Ta kawo turaruka ta ce a kai wa Saadatu.
Daga nan sai Unguwar Fulani Hibbani. Najaatu da Humaira suka gaida yayyun nasu, Sageer da Awaisu. Humaira sai faman dauke kai ta ke don tsananin haushinsa da ta ke ji, ya rasa wadda zai aura sai yar Fulani Bilkisu don kawai a wulakanta iyayensu? Ita tun filazal ta tsani Saadatu sabida son da Askirama ke mata, balle yanzu da ta zama surukarsa kuma matar Yarima dungurugum.
Shi bai kula Humaira na ciccin magani da shi ba, ya dube ta da kulawa, ya ce,
Auta, sai yaushe za a shigo mana?
Ta yi wani dan murmushi na dole, ta ce, Matarka Yaya Yareema Junior ta ce fa, ya za a yi ni in je gaishe ta? Ai sai dai in ta zo nan mu gaisa.
Cikin mamaki ya ce, Junior? Don sam bai gane me ta ke nufi ba.
Ta ce, Kwarai, tare aka kai mu makaranta a El-Kanemi, ina aji uku tana aji daya, she has been washing my pants and undies, kai har gugar kaushi ta ke min, everything.
Yareema ya kufula iya kufula saura kadan ya kai mata mari Awaisu ya rike shi.
Ya ce, Saadatun? Wa ya ce miki baiwar gidanku ce? To yadda ki ke ya a gidan nan haka ita ma ta ke, idan watarana na ga kafarki a gidana sai na kakkarya ki, sakarai kawai.
Ya Hibbani ta fito daga dakinta tana daura dankwali, ta ce, Yareema mene ne? Ina barci na ke jin tashin fadanka.
Nan ya gaya mata a gajarce. Hibbani ta kyabe baki, ta ce, Kada ka ga laifin kanwarka Yareema, saboda da farko mu ba mu san yarta ba ce, boye mana ta yi. Cewa ta yi yar riko ce ta karbo, so don Humaira ta sa ta aikatau a makaranta ba ta yi laifi ba.
Kada ka manta Humaira yar sarki ce, jikar Sarki. Wannan kuwa ko asalin ubanta ba mu sani ba.
Idanun Yarima suka kada kamar gauta, ya bude dukkan idanunsa yana duban kishiyar mahaifiyarsa Fulani Hibbani, zai yi magana ya ce ita ma sun san nata asalin ba yar kowan ba ce, sadakarta aka kawo wa Askirama, Awaisu ya toshe masa baki, ya ja shi suka bar sassan gabadaya.
Humaira ta ce, Humm! Aka ce auren hadi ne na Askirama, ashe da ma can yana sonta, dubi yadda yake neman dukana.
Hibbani ta ce, Tabdijan! Ya Gumsu ta ga ta kanta, ai zama bai gan ni ba, bari in je in gaya mata Yareema ya gama afkawa har fiye da ubansa sai ta yi da gaske, kin ga yadda jijiyar kansa da ta wuyansa ke tashi?
Humaira ta ce, Ni tunda nake ban taba ganin makiran mutane irin wadannan Baggaran ba, kyawunsu ke rudarSarakuna, amma wallahi kyawun da babu asali aikin banza ne.
Hibbani ba ta saurare ta ba ta figi mayafi ta nufi Unguwar Ya Gumsu.
Karya da gaskiya duk ta gaya mata, Ya Gumsu mai neman kuka an jefe ta da kashin awaki ba ta san sanda ta fashe da kuka ba tana fadin,
Tawa ta same ni, ni Gumsu. To ba inda za ta bi shi a nan za ta zauna a Askira, ya je can wajen baturiyar ya zauna, ko ba komai su ba sa mugun abu, zuciyarsu ba muguwa ba ce.
Bangaren Fulani suka nufa, Awaisu na ta cooling dinsa yana cewa ya yi hakuri, mata ne haka suke, sun gaji kananan maganganu wadanda bai kamata a biye musu ba.
Sabida yadda ransa ke bace, duk tsokanar da Fulani Bilkisu ke masa ya kasa tankawa sai murmushi kawai yake. A karshe ta yi musu addua da fatan alkhairi. Ya sunkuyar da kai da ganinshi ka ga wanda ke gaban surukar da yake matukar girmamawa, ya ce,
Allah ya taimaki Fulani, ina ganin fa gobe za mu wuce Abuja, nan hayaniya ta yi yawa ba ta barin mutum ya huta.
Fulani ta ce, Haba Yareema, ka yi hakuri ku cika sati daya a gama miskero sai ku tafin.
Ba da son ransa ba ya amince, don ba zai iya yi mata musu ba, amma kwarai maganganun Hibbani da yarta sun sa so yake ya dauke Saade su bar Askira. Ba zai lamunci kowa nasa ya taba mutuncinta ko na mahaifiyarta ba.
Daga nan sai gidan su Awaisu wato gidan Wazirin gari Ibrahim, nan ma suka kai gaisuwa, sai gidan Galadima, Zanna, Shettima, Wali da dukkan king makers daya bayan daya sai da suka bi su suka kai gaisuwa, suka kuma yi musu godiya da ban gajiya.
Sai goshin magriba ya dawo gida, Awaisu da ya sauke shi bai tsaya ba ya wuce gidansa. Awaisu na da matarsa Asiya har da albarkar yara biyu.
Sanda Yarima Sageer ya shigo gidansa koina tsaf-tsaf sai tashin kamshin turaren wuta yake kuma koina shiru. Kuyangi da hadimai sun kulle koina sun wuce bangarensu. Saadatu ta gaya musu daga karfe shidda na yamma ta sallami kowa.
Ita da za a raba ta da wannan tarin yammatan masu jini a jika daga gidanta da sai ta fi jin dadi, to ta san ba ta isa ta zauna babu kuyangi ba a matsayinta na matar Yariman Askira mai jiran gado, ba ta isa ta karya aladar masarauta ba.
Zai wuce ke nan zuwa upstairsdin sa da zummar yayi wanka sannan ya zo ya duba Saade, sai ya ji motsin mutum, da sauri ya juya, wata siririyar kuyanga ce ta sha hoda da jambaki ta zube a gabansa.
Allah ya taimake ka dan zakin duniya, sunana Sadiya ko da ana bukatar kwarkwara (sa-daka).
Kamar daga sama sai ga Saadatu ta bullo daga kitchen din falon za ta wuce, ta yi wannan kyakkyawan gani ta kuma ji abin da Sadiya ta ce. Kofin tangaran na (mug) da ta hado zazzafan shayi mai kauri ta saki ya fadi kasa ba da saninta ba, ji-ka ke tush! Kofin ya tarwatse, gilashin da ruwan zafin duka a kan kafarta.
Da sauri ta durkushe ta kama kafar wadda har ta soma fidda jini.
Sadiya da Yarima suka yi kanta a tare. Wata irin tsawa da ta daka wa Sadiya sai da hantar cikinta ta kada, Dont touch me, get out! Ki hada kayanki duka ki koma cikin gida, kada in kara ganinki a sassana.
Da gudu Sadiya ta fice ta san yau kashinta ya bushe, ta yi shuka a idon makwarwa. Babu bayani ga sauran bayi yan uwanta ta hada kayanta ta koma gidan Sarki a daren.
Yarima ya sunkuya ya kama kafar, ta ture hannun sa tana kokarin janye kafarta. Azaba ba yar kadan ta ke ji a cikin tsokarta ba amma ta fi jin zafin tayin da Sadiya ta yiwa Yareema fiye da ciwon, kawai sai ya sunkuce ta ya yi saman benen da ita, duk inda suka wuce sai jini ya disa.
Shi ba likita ba, amma ba ya rabo da first aid box a gidansa, toilet ya kai ta cikin jacuzzi ya wanke jinin ya cire kwalbar da ta makale tana kuka tana kankame shi, sannan ya sa mata iodine don azaba ba ta san sanda ta rungume shi ba.
Ya dauko ta suka dawo daki bisa sofa ya shimfidar da ita yana ta faman jera mata sannu. He looked worried and disturbed kamar a jikinsa ciwon yake. Ya dauko pain reliever da gorar ruwan Faro ya ba ta ta sha. Ya kwantar da kanta bisa cinyoyinsa yana shafa kanta hankali.
Saade sai ajiyar zuciya ta ke, amma bacin ran Sadiya bai gushe daga zuciyarta ba.
Kamar Yareema ya fahimci hakan sai ya ce, Me ya sa ki ka kori yarinyar can?
Da jajayen idanunta ta harare shi.
Ba ka ji me ta ce ba ne? She wantto be your concubine bayan na ce kada in kara ganinsu daga karfe shidda, amma shi ne don ta raina ni ta dawo da ta ji dawowarka.
Wani murmushi ya subuce wa Yareema, mace ba ta kishi sai a kan mijin da ta ke so, ko ta fara so.
Ya ce, To me ye abun damuwa anan? Za ta taimaka miki ne ta dauke dukkan lalurorina har zuwa lokacin da za ki karbe ni a matsayin miji, tunda ba ki sona Saadatu ba laifi ba ne don sauran mata sun so ni, beside ba haramci ta fada ba.
A hankali Saade ta janye kanta daga jikin Yareema Sageer, ta kwanta daya barin akan pillow, sabida yadda zuciyarta ke tafarfasa. A wannan lokacin ta tabbata da za ta ga Sadiya sai ta yi mata mummunan lahani.
Yareema Sageer ya je ya kwanta a barin da ta maida fuskarta, ya yi mamaki da ya ga cewa kuka ta ke yi.
Im sorry idan maganata ta bata ranki Saadatu. Gaskiyar magana ita ce, ba kya sona, ban san dai wa ki ke so din ba. Amma jikina yana ba ni wannan siririn yaron fari da na ke yawan ganinku tare nemai wuya uwa marikin lema.
Ni na gaya maka?
Ta tambaya cikin rishin kuka.
Ban taba ce maka bana sonka ba Yaya Sageer, kuma ni ban taba son kowa ba. Karatu kawai nake so in yi. Auren ya yi min wuri, ka ga fa duka shekaruna sha tara, level 2 nake.
Akwai sauran shekaru biyu a gaba kafin in yi nutsuwar da zan iya daukan marriage responsiblities, sannan baa nemi amincewa ta ba aka daura mana aure, ba mu fahimci juna ba in this aspect ta ya ya ka ke tunanin hankalina zai karbi wannan auren?
Sosai Yareema ya fahimce ta, ya sanya hannu cikin jelunan kitsonta yana murzawa a hankali, ya ce, Na fahimce ki Saadatu. Ni kuma na ba ki dama ki ci gaba da yin rayuwarki yadda ki ka saba gudanar da ita a Abuja banda kula wannan yaron. Ni bazan takura miki ba. Insha Allahu ba abin da zai canza har sai lokacin da ki ka ji cewa you are ready to accept me as a husband, kafin nan ina so ki ba ni dama in zama malamin ki kuma aminin ki, mai koya miki karatu kuma abokin shawarar ki mai kula da dukkan alamuranki.
Alfarma daya za ki yi mun, duk lokacin da zan sumbace ki kada ki ce min aa, ina matukar son in sumbace ki, na yi miki alkawarin ba zan wuce hakan ba.
Da sauri Saade ta wara ido cikin jin kunya ta dube shi. A hankali ta ce,
Yaya Sageer ina jin kunya!.
Ya janyo ta gabadaya zuwa jikinsa, ya ce, I will take care of that daga yau, a hankali zan cire kunyar dukkanta har watarana da kanki za ki zo ki ce, Yareema Sageer.. Saade ta yi maza ta rufe idon ta. Ta cusa kai kasan filo. Shikuma ya yi amfani da wannan damar ya dauke filon ya kuma hade bakinsu wuri guda yana kissing din nata gently, softly, affectionately. Tun Saade na kokarin janyewa har ta soma lumshe yan idanunta. A zuciyarta tambayar kanta ta ke, wato bayan kissing din akwai abin da ya fi shi kenan anan gaba,tunda gashi Yareema yana cewa, ba zai wuce sumbar ba? To ko mene ne? Ko wace rana ce Yarima zai nemi hakan? Wannan din kadai sai ta rufe ido ta kuma kai zuciya nesa sabida nauyin sa..Idan akwai abin da ya fi shi a nan gaba ba ta san ya ya za ta yi da ranta ba.
Sauran kwanakin su a Askira sai suka zamo na jinyar kafa da sassanyar soyayya, wadda Yareema Sageer yake matukar kokari wajen ganin bai wuce gona da iri ba. He is not going far beyond what he begged for. He is only kissing her, sumba mai sunan sumba in dai ga Saadatu ne ba ya taba gajiya, baya taba koshi. Rannan ya ce mata,
“theres charisma in kissing You.
Kwanansu shidda a gidan su na Askira kafarta ta kame, ya ce ta hada duk abin da ta ke bukata gobe za su bi jirgi tare da Maimartaba da Fulani zuwa Abuja. Alkawarin da Askirama ya yi na kaita Abuja gidan mijinta da kan sa ya ce zai cika shi da yardar Ubangiji.
Washegari tunda asubahi an shirya motocin da za su kai su Maiduguri (filin jirgi) sannan an zabi wadanda za su yi wa Maimartaba da Fulani rakiya, cikin masu rakiyar Fulani har da Fanna wanda hakan ya faranta ran Saadatu sosai, fargabarta ta komawa Abuja ta ragu kashi sabain cikin dari ganin irin wannan rakiyar gata da zaa yi mata.
******
Jirgin Azman ya sauke su a Abuja da yamma lis. Direban Dr. Sageer da na abokinsa Dr. Ziyad su suka zo suka kwashe su a manyan motoci zuwa gidajen malamai na NTNU. Tunda suka sauko daga jirgi yake ta gwada kiran lambar Sultana tana ta ringing amma ba ta dauka ba. Ya san duk inda ta ke zuwa yanzu ta dawo gida. So yake ya gaya mata tahowarsu tare da su Maimartaba don ta sa Uche ya tanadi abinci na musamman, amma ga wayar tana ta ringing ba ta daga ba.
Ya yi tsaki, sannan ya kira Uche, wanda ke Baskwata a lokacin yana wanka, ita ya kamata ta bai wa Uche umarni ba shi ba, amma da bai same ta ba dole ya kira shi.
Uche, Im already on the way with his Royal Highness, cook to your best, deliciously. Madam ta dawo?
Uche ya yi shiru da waya a kunne, ta ya ya zai ce masa ta dawo, amma tun shigowarta tana main falo tana drinking kada ya zo da iyayensa yanzu? Kafin ya hada amsar da zai bai wa ogan nasa Sageer ya kashe wayarsa. Da sauri Uche ya hau sake kiran shi a waya amma rashin kyawunnetworkyasa yakasa samun shi. Kuma kafin ya sanya suttura a jikin shi ya wanke kumfar jikin shi ya baro baskwata (boys quarters) zuwa cikin gidan ya ji saukar dirin motocinsu suna shigowa get din gidan.
Duk da yake arne ya san drinking alcohol is very bad to Muslims more especially women in marital homes, its against their religion, tradition and culture. Sai ya ji tausayin ubangidansa ya kama shi, don yana son Sultana. Allah ya sa kada father din ya ce ya sake ta.
Yana daga kitchen wanda ya bi ya shigo ta kofar baya cikin mutuwar jiki yana lekensu ta window suna ta shigowa cikin nadi da amawali da kaya na sarauta a jikin kowannensu. Ga wata mace kuma an lullube a cikin alkyabba wata baiwa ta riko ta. Yarima ya bude kofar falon wadda sakayota kawai aka yi. Maimartaba shi ne farkon shiga don Yareema ya dan ja baya ya bashi hanya cikin girmamawa sannan Fulani ta mara masa baya. Suka kuwa yi kyakkyawan gani, wanda ba su jin za su taba mantawa a rayuwar su.
Aisha-Sultana ce daga ita sai half vest da wando three quarter baki, tana kwance magashiyyan cikin manya-manyan kwalaben whiskey. Ba barci ta ke ba, kuma tana jin shigowarsu amma ko yatsarta ba ta iya motsawa, idanunta a lumshe.