Showing 54001 words to 57000 words out of 117873 words
ran ta ya bata gara ta tambayeshi don ya tantance mata wace Sa'adatun yake nufi? Don haka ta hadiye komai cikin laluma ta tambayeshi.
"Allah ya taimaki Giwan Askira, ko zan iya sanin wacece Sa'adatun?"
"'Yar ku Sa'adatu wadda yake riko a gidan sa ta wajen Fulani Bilkisu......".
Ai bai karasa ba sai ganin Ya Gumsu yayi tsaye a kansa, idanun ta a warwaje tana huci, yau da ba shi ne sarkin Askira ba, da ba shine uban 'ya'yan ta ba, furfurarsa ko wannan himilin rawanin nasa bai hanawa ta kwashe shi da mari.
"Idan wasa kuke..... Allah ya taimake ku ku bari, bana son irin wannan wasan....." cikin mamaki Askirama ke kallon ta baki a bude, ya dauka wannan karon farin ciki zata yi da zabin da yayiwa Yarima, shi da take fushin ya auri mai jajayen kunnuwa mara addini, ga wadda suka san asalin ta suka san addinin ta suka bata tarbiyya cikin gidan amma tana neman kawo masa zancen banza.
"Ni ne nake miki wasan? Zaki ga wasa kuwa ganin idon ki".
Mikewa yayi zai bar wajen Ya Gumsu ta sha gabansa idanunta tamkar an gumbuda musu barkono "Allah ya taimake ka ashe kuwa zaka bani takardar saki na.......kafin ranar da zaka aurawa Da na aure da tsintacciyar magen da har yau bamu san asalin ta ba, da 'yar data fito daga hannun makiyiyata don su hada kai su cuce ni su ga baya na nida zuri'ata a gidannan.....na tabbata ita ta kitsa maka wannan sharrin to insha Allahu a kanta zai kare!
Ba dai Yarima ba! Ba irin tsiya irin talauci ba, irin da babu cikakken asali don ni ban yarda ma BAGGARA ne su ba sun fi kama da bororon daji......".
Mai Askira ya hadiye tsananin bacin ransa bai nuna ba ko a fuska, babu wata mace data taba yi masa irin wannan tsaurin idon a rayuwar sa....amma Gumsun Askira zata ci albarka da yawa....albarkar 'ya'yan ta...albarkar kasancewar ta uwar 'ya'yan sa. Da albarkacin kasancewarta UWA ga duk wani mahaluki dake cikin Askira.
Kawai sai ya zagayeta zai wuce, bai taba sa'in sa da kowa ba, tsakanin sa da kowa dake karkashin sa biyayya ne ana so ko ba'a so. Shiyasa ba karamin yaki yayi da zuciyar sa yau akan Ya Gumsu ba, sabida babu saki a tarihin sarautar su, babu kaskanci ga uwar iyali.
Ya Gumsu bata daddara ba ta sake jawo Alkyabbar sa..."wallahi sai ka bani amsar inda kuka samo yarinyar nan....ba tun yanzu ba nasan watarana sai ta zame min jidali, na san sai an kakabawa 'ya'yana, yadda naga uwarta ta ci buri a kanta, dama dalilin kawota gidan kenan don ta samu ta auri dan sarki.....kamar yadda ta samu tsuntsu daga sama gasashshe....to ai ba ni kadai na haifi maza ba......don haka in har inada hakki akan Yarima na haihuwa da shayarwa to ban yarda ba ban amince ba.....".
Mai Askira yayi murmushi yace "sai kace dan wani na arziki ne da kike tada haqarqari akan sa ke mai da! Dan da tun yana karamin sa ya san dadin zina......girma da aure da martabar gidan su bata sa ya daina ya kama kansa ba. Zan rufa masa asiri da 'yar mutunci don ta taimaka mana ya kintsu shine kike wannan zubar da kimar? Gumsu ina jiye miki ranar jin kunyar ki.....ranar da duniya zata san dan da kike tinkahon dashi har yanzu bai bar zina ba, matar sa shan giya take, rayuwa suke kamar ta dabbobi, musuluncin nasu duka ba maraba.....gara ita nata babu tushe amma wanda bai ji tsoron Ubangiji ba kuma girman aure bai hana shi yin zina ba ba abun tutiya da shi a matsayin Da bane....
A da, na sanya kwanaki uku auren Yarima da Sa'adatu, don in samu inyi gayyata, to na fasa yanzu, nida Waziri zamu daura auren yau Juma'ah bayan sakkowa masallaci. Don in nuna miki ni ke da iko daku daga ke har dan naki. Gara ke na baki hakkin ki na uwa na sanar miki... shikuwa saidai ya ji labari......".
Yana gama fadin haka yasa kai ya fice fadar da bai yi niyyar fita yau ba.
Waziri sai ganin maimartaba yayi yana shigowa fada a matukar fusace, shikadai yake iya gane fushin mai Askira. Kyawun fuskarsa da kamalarsa kan boye fushin sa a yawancin lokuta.
Yana zama fadawa suka yi kirari suka kuma basu wuri, don sun lura ya shigo fada ne kawai sabida Wazirin sa Ibrahim.
"Ka fadawa 'King-makers' akwai daurin auren Yarima bayan sakkowa daga masallaci yau".
Waziri yayi kabbara a fili, don ya dade yana jiran ranar da Askirama zai zo masa da zancen karin auren Yarima, yana daga wasu daga cikin labaran halin da rayuwar auren Yarima ke ciki daga abakin Awaisu, hatta zancen cire mahaifa da Aisha -Sultana ta yi ya sani, bai gayawa mai Askira bane don ya san in rashin jikoki ya ishe shi da kan shi zai magantu.
"Amma Allah ya taimakeka baka ganin gara a hada masa guda uku a wanke su rana daya a kai masa? Hakan taimako ne babba gare shi a bisa nazari na na halin da yake ciki, kamar guda daya ta yi masa kadan".
Askirama yayi murmushi ya dubi Waziri Ibrahim, "wannan daya ce tamkar da goma! Kuma itace maganin matsalolin Yarima insha Allahu. Tun farko ita naso ya aura ya kawo min zancen baturiyar nan, idan har ta fito daga cikin Bilkisu ina tabbatar maka karamar Bilkisu ce.....da ace Bilkisu na fara aure a rayuwata babu macen da zan kara aure".
Waziri Ibrahim bai san sanda yayi dariya ba, yau mai Askira ya saki layi sabida soyayyar Fulani Bilkisu, ya manta ko da wa yake magana....
A take ya dau waya ya fara aiwatar da umarnin sarki.
Kafin karfe 2 na rana duk wani da ya kwana ya tashi a garin Askira mace ko namiji ya samu gayyatar daurin auren Yarima Sageer da Sa'adatu, banda Sa'aden da uwarta dake kule kowacce a dakin ta zuciya babu dadi, ita Sa'ade halin da ta ga Fulani a ciki ne ya hanata kwanciyar hankali, tun jiya data shige daki ta rufe bata kara fitowa ba, sannnan daga ita har Fanna da Zarah tace bata bukatar ganin kowa. Abinci ma tace bata bukata tanada cake da friuts a firjin gefen gadon ta.
Duk tunanin Sa'ade yafi bata matsala suka samu tsakanin ta da Askirama.
Wajejen karfe daya Fanna ta shigo ta samu Sa'ade dake kwance a gado tun safe, waya take da Sa'id yana gaya mata yadda garin Abuja ya zame masa boring saboda rashin ta, maimakon tayi dariya ta bashi amsa cikin raha yadda suka saba sai tace "Sa'id, ina cikin damuwa, mamana ta shige daki ta kulle tun jiya tace kada wani daga cikinmu ya je inda take" Sa'id yace "manya kanyi irin wannan a lokacin da suke so su kebe don su samu suyi tunani ko neman mafita kan wani mhimmin al'amari da ya shafe su, so karki damu tunda kinsan lafiyar ta kalau, ita da kanta in ta samu saukin al'amuranta zata neme ku......." Fanna ta ce "ranki ya dade....ranki ya dade!" Ta cire wayar daga kunnen ta ta dubi Fanna, Fanna ta ce "lokacin sallah ya yi, ga kuma abincin ki". Sa'ade ta yamutsa fuska ta ce "maida abincin nan" "me yasa bazaki ci ba?" Inji Fanna cikin damuwa, uwa ta ki ci, 'yar ma tun safe ta ki cin komai duk sun sa ta a damuwa....Lokacin yayi daidai da bugawar dakikar agogo karfe biyu da rabi na rana, ya tafi tare da bugun zuciyar SA'ADE.... ba tareda ta sani ba, ta zama karkashin igiyoyin Yareema Sageer har guda uku.
"An daura auren Yarima Sageer Yusuf Askira da Sa'adatu Hashim Askira akan sadaki lakadan ba ajalan ba.....". Abinda Fanna ta ji kenan data sako kafarta a kitchen don dawo da kayan abincin da Sa'ade ta ki ci, amma bata yarda tasu Sa'adatun bace don wani abu makamancin wannan bai taba zuwa mata a rai ba, Yarima mijin baturiya wacece zata yi gigin shiga gidan sa? Ai sai mai tsautsayi, matar da aka ce har kwalba take dagawa. Don haka ta tausayawa koma wacece wannan Sa'adatun da aka aurawa Yarima. Don daula zata samu zata shigeta iya shiga....amma tabbas ta hadu da gamon ta.
Abinda Fanna ke ta fada a ranta kenan tana cigaba da ayyukan ta a kicin.
Yarima yana dakin Awaisu na gidan Waziri a wannan lokacin, shima Awaisun ya zo sakamakon kiran gaggawa da Waziri yayi masa. Ya kuma gaya masa ko me kenan amma yace kada ya bari Yarima ya sani har sai an gama daurin aure, mai martaba zai gaya masa da kansa.
Awaisu, kamar zai suma don dadi da farin cikin jin wadda aka zabawa Yarima, once or twice, Yarima ya taba yi masa maganar Sa'ade, yace ta iya girki sannan ga ta da hankali. Daga wannan bai kara cewa komai akan ta ba. Ya tabbata ko baya son ta zai karbeta tunda har yana yabon ta, sannan uwarta mutuniyar sa ce (Fulani Bilkisu). Bazai bada mata kasa a ido ya ce baya son 'yar data fito daga hannun ta ba. Yarinyar kawai yake tausayawa zama da Sultana amma zai nemi Yarima da ya raba musu gida don a zauna lafiya.
Shi dai Yarima ya ga Awaisu sai shiri yake cikin farar shadda excelcior, yana yi yana bin waka a radio da alama cikin nishadi yake, ya ce Asiya tana jirana a cikin gida don haka na sallameka inada daurin aure a fada inna gama da ita". Yarima ya kulu da wannan kora da Awaisu yayi masa yace "ni kake kora? Daurin auren wa?" ALLAH ya taimaki Yarima wane ni in kore ku! Amma don Allah ka kara gaba ko in bar maka mukullin dakin in ka gama hirar ka rufe, inada daurin aure muhimmi". Daga haka ya sanya hularsa da takalmi ya fesa turare, ya dubi Yarima yana murmushi ganin kallon takaicin da yake masa.... dariya yayi a rans yace ka kuma zama namiji malam, a da muna maza ne tunda mai jan kunne kake aure, yanzu ne zaka san ka yi aure da matan usli da suka amsa sunan mata....
Yayi ficewar sa ya barshi kwance a gadon sa da baki sake, yana mamakin Awaisu ne yau yayi masa wannan wulakancin? Daurin auren da zai je ya fi shi Sageer muhimmanci???
****
Bayan daurin aure aka zarce da bushe-bushen algaita da kalankuwa, masu goge da masu ganguna kowa na baje kolin nasa. Gabadaya garin ya rude da hayaniya anata labarin Yarima ne aka daurawa aure da 'yar da kishiyar mahaifiyar sa ke riko, wasu na fadin 'yar ta ce data yi shegen ta kafin tayi aure (wa'iyazu billah) Allah ka kare harshenmu daga fadin gaibu, da abinda bamu da tabbas a kan shi.
Wannan zance ya kai kunnen Ya Gumsu ta hanyar 'yan kanzagin ta da 'yan hana ruwa gudu, cewa ashe Sa'aden 'yar Bilkisu ce data yi shegenta kafin tayi aure aka kuma biyota da ita har gidan auren ta.
Saura kadan Ya Gumsu ta haukace, ga Askirama yana fada bazai shigo ba sai bayan isha balle taje ta huce akansa.
Me ya dace ta yi? Ban da ta je su yi wacce zasu yi itada Fulani Bilkisu? Shegiya a cikin iyalinta! Ai gara mata mara addinin!
Yau babu ko mayafi haka ta ratsa ta tafi unguwar Fulani Bilkisu, ta wuce bayin ta da hadimai fuuuuuu! Ko gaisuwar da suke mata bata karba ba.... yau ko ita ko Bilkisu, koda hakan shine zaiyi sanadin igiyar aurenta.
Fanna na kokarin fitowa da tsintsiya a hannun ta Ya Gumsu tayi ciki da ita, saura kadan ta fadi, sai wara ido take tana neman Fulani amma bata ganta ba, ta daga murya kamar zata tsaga gidan tace.
"Bilkisu! Fito wajen ki na zo!" Wannan kira har cikin kwanyar Fulani Bilkisu, gabanta ya fadi ta dafe kirjin ta, Ya Gumsu ta soma dukan kofar dakin ta tun karfin ta, tana cewa "Da na ya fi karfin auren SHEGIYA kurwar mu kurr. Yadda kika lashe mai Askira shine kika kawo shegiya ta lashe Yarima? Wallahi sai bayan raina wannan auren zai tabbata...." dukan kofar take kamar zata ballata. Bilkisu jikin ta sai rawa yake hawaye na zubo mata, tana so ta fito ta fuskanci Gumsu ta fada mata 'yar ta ba shegiya bace da ubanta kuma itama bada son ranta bane amma ta san halin Ya Gumsu, zata tara mata mutanene aka, ta wulakantata gaban bayin ta, su taru su zubar da mutuncin mai Askira don ta tabbata Gumsu dambe take so su yi ba wani abu ba, ta samu hanyar lalata maganar auren, to ko za'a lalata zancen auren nan ba daga gareta ba, da Gumsu ta san halin da ta ke ciki akan auren da ta tausaya mata, itama bata so, ko kadan bata so. Saidai ta zabi farin cikin Askirama akan nata da na Sa'ade.
Don haka ta daure ta cije bata fito ba, ta bar Ya Gumsu ita kadai tana ta zage-zage, bakaken maganganu ba irin wadanda bata fada akan Bilkisu ba, har da cewa da ganin ta dama an ga tsohuwar karuwa ta zo ta hargitsa musu miji bakidaya ya daina ganin kowa da gashi sai ita, duk wannan bai isheta ba ta zo ta hada auren masifa da bala'i a cikin zuri'arta, to ko zata yi yawo tsirara sai Yarima ya sakar mata 'yar ta.
Kuyangi da bayin Fulani duk sun sunkuyar da kai ko motsi sun kasa, sai yanzu suka fahimci dawa aka daurawa Yarima aure, jikin su yayi matukar sanyi musamman Fanna, hawaye ta soma na tausayin Sa'ade don bata cancanci aure na rashin kwanciyar hankali irin wannan ba ko shekaru ashirin bata yi ba.
Saida Ya Gumsu ta tabbatar ta gayawa Bilkisu maganganun da har ta mutu bazata manta ba, in kuma tana da zuciya to zata karbi 'yar ta daga auren Yarima sannan ta bar falon, duk wannan bai isheta ba ta so ne Bilkisu ta fito tayi mata dukan da Askirama zai kasa ganeta.
Ita kuwa Sa'ade tana daki a kwance, tun shigowar Ya Gumsu data soma dukan kofar Fulani ta taka aguje ta shige toilet ta rufe kanta, a zaton ta Ya Gumsu ta samu tabin hankali ne, so yawancin duk abubuwan da take fada bata ji su ba kasancewar kofar sound proof ce.
Bayan fitar Ya Gumsu data ji shirun yayi yawa sai ta fito, a guje ta nufi kofar Fulani tana kuka tana rokon ta ta bude. Kome Fulani tayi tunani? Sai kawai ta taso ta bude kofar.
Halin da Sa'ade ta ganta a ciki ya matukar tada hankalinta, fuskarta ta kumbura tayi jazur idanun ta sun yi luhu-luhu. Sa'ade ta fada jikin Fulani ta wani irin rungumeta tana tambayarta "dukan ki ta yi? Is she lunatic?"
Duk da halin da Fulani ke ciki sai da Sa'ade ta sanyata murmushi. Ta ja ta suka shige ciki bayan tasa mukulli ta rufe kofar. Suka zauna a tare a gefen gadon ta.
"Ba duka na tayi ba, zagi na dai kawai tayi saboda an aurawa dan ta 'ya ta".
Innocently Sa'ade tace "to ke ina ruwanki don an yiwa dan ta aure? Ko ke kika ce ayi masa?"
Fulani tayi murmushi ta murza tausasan hannun Sa'ade cikin nata sannan tace.
"Laifi na gareta shine ni na haifi 'yar da Askirama ya aurawa dan nata, bayan wannan bani da hannu a ciki".
Sa'ade ta yamutse fuska tace "ban gane ba? Zarah ta isa aure ne?"
Kwatakwata ta manta itama 'yar Fulani ce tsabar rudun da kalaman Fulani suka jefa ta".
"Zarah kadai na haifa? Kafun in samu Zarah wa na fara samu?"
Sa'ade ta luluka a duniyar a tunani, ita lallai so take ta canko wa Fulani ta haifa wanda ya isa aure amma tunanin ta ya kasa bata, domin bata ga marabarta da Zarah ba.
Murmushi Fulani ta sake yi sannan ta rungume Sa'ade, "ki yi hakuri Sa'adatu kin ji? Mun yi miki laifi daga ni har Askirama, ya nemi alfarmar in bashi ke ya aurawa Yarima nikuma kinsan bazan iya juya masa baya ba. Tunda daga ni har ke zamansa muke yi cikin gidannan mu abin ikon sa ne, sannan in da halarci ko mahaukaci Askirama ya kawo yace ki aura daga ni har ke mun isa mu ce a'ah? Balle dan cikin sa mafi soyuwa a gareshi?"
Sa'ade sauraron ta take absent-mindedly tana hada daya da biyu domin ya bata ma'ana. Aure.... ita da Yarima......Yarima wanne? YARIMA! Yarima!! Yarima!!! Shikadai ne mai wannan sunan duk masarautar Askira.
"Don Allah Fulani ki fiddani duhun da kalamanki suka sanya ni.." ta fada cikin karkarwar jiki data murya. Ta kama hannuwan Fulani biyu ta rike tamau a cikin nata.
Fulani ta ga wannan shine lokaci mafi dacewa da zata gayawa Sa'adatu komai, tunda bakin alkalami