Showing 75001 words to 78000 words out of 117873 words
shi yana kin auren ba.
Muryar Saade abin tausayi ta ce, Sai ma kin ji bakar maganar da ya gaya min da na ce ba zan koma Abuja ba zan gudu kauyenmu he was like (in yi ta gudu, in fi ruwa gudu, giya in shirya sha tare da matarsa) meaning bai dauki maganganun nawa da wani muhimmanci ba.
Raheema ta yi dariya sosai, ta ce.
I would like to see Yarima Sageer. Sister you are blessed for having him as a husband, ina son brave men, wadanda suka yarda da kansu, cika baki ko rikicin mace ba ya razana su su ja da baya a kan soyayyar su. Ni ma sai in ce,
Sai kin dawo, a gaida mutanen Tsanyawa.
Saade ta kai mata bugu ta goce tana mata dariya. Muryar ta abin tausayi tace.
Wato dai Raheema kema kina bayan in auri mai mata ko? Ta je bar ta dawo ta yi min dan karen duka?
Dariya sosai Raheema ta sake yi, ta ce, Tunda ki ka ce ga inda ya auro ta kuma ga asalinta me ye abun mamaki don ta sha giya? Su fa yadda muke shan soft drinks, haka suke shanta don baki taba fita ketare bane, canjin addininta ba zai sa ta iya dainawa farat daya ba, tunda dai ba shi yake sha ba shi kenan falillahil hamdu, ki yi mata addua Allah ya sa tana da rabon dainawa.
Sai kiran sallar asuba suka ji a kunnuwan su, dole suka mike don bada farali. Daga nan kuma suka kwanta, Hanne sai barcinta ta ke hankali kwance bisa katuwar katifa ita da danta Naziru.
*****
Washegari aka tashi da event na farko, wato sakun lalle. Masarautar ta cika ta batse da yan uwa da abokan arziki da baki da aka gayyato daga masarautu daban-daban, ga kuma alummar garin Askira wadanda ma ba a gayyata ba. Da ma in dai biki na gidan sarki ne ba sai an gayyace su ba, kwansu da kwarkwatarsu suke tahowa daga gidajensu zuwa gidan Sarki.
To balle auren Yareema Sageer kuma wanda Maimartaba da kanshi ya shelanta gayyatar ga kowa da ke Askira, bayan saukowa sallar jumaa a babban masallacin jumaa. Don haka ba a taba ganin taron bikin da ya hada jamaa irin na yau ba a masarautar gabadaya. Tun daga kan auren su Yaa Maira har zuwa kan na yar sarki ta karshe da aka aurar Najaatu.
An saka amarya a lalle lafiya, Raheema da Hanne da kanwar Raheema Sarina sune kawayen amarya. Washegari alhamis aka yi NIYA wato ranar yin royal snacks su nakiya, alkali, dubulan, bakilawa da sauransu daro-daro don raba wa mutane.
Ranar jumaa aka yi WUSHE-WUSHE. A babban filin dake cikin fada aka kira decorators suka tsara shi yayi kyau sosai. Wushe-wushe shine wuri daya da Yareema da Sa'ade Zasu hadu a duk tsawon bikin su, makada ne aka gaiyyato daban daban daga garuruwa daban-daban ciki har da HajjaGumsu da yaran ta da suka zo daga Maiduguri. Sai da aka taru ana kade-kade ango ya zo cikin manyan kaya da abokan shi karkashin rakiyar Awaisu Ibrahim Waziri da kuma sisters din shi mata su Mairam Murjanatu, Yaa Maira and co.zagaye da shi cikin laffaya mai hasken sararin samaniya suna rike da kaskon turaren wuta suna turara shi, makadan fada na biye da su,suna kide-kide da bushe-bushe suna wake Yarima da amarya Saadatu har su ka kai shi mazaunin da aka tanadar musu shi da Saadatun.
Abokanen shi kuma aka yi musu shimfidun kilishi na alfarma daga gefen sa, sannan su yan uwan shi mata su kuma suna zaune inda aka tanadar musu.
Sai aka cigaba da wasa da kide-kiden cikin zakuwar fitowar amarya, wanda yawanci sai an dan ja lokaci sosai kawai dan a ja wa ango rai, haka aladar bikin masarautar Askira ke gudana a kowanne bikin dan sarki.
Saade an shirya ta cikin laffaya an rufe ta ruf har kai. Sannan kawayen ta su Rahimah da Hanne sun saka ankon dongasho da su murjani sun rike kaskon turarukan wuta suka sako ta a tsakiya kamar yadda aka koyar dasu.Maman Rahimah da Innar Hanne na rike da ita cikin rakiyar kide-kide har aka kai ta aka zaunar a gefen Yarima Sageer, wanda a lokacin da Saade ta zauna a gefen sa sai da ya dauke numfashin sa na wucin-gadi. Kawayen ta kuma by her side akan shimfidundake kallon na abokan ango.
Daga nan sai aka cigaba da kide-kide da wasanni.Saade bata yarda sun hada ido da Yarima ba duk kokarin sa ga son faruwar hakan, bata ma bude fuskarta daga cikin laffaya ba, duk kokarin Yarima Sageer na son gano halin da kwayar idon ta ke ciki a wannan lokacin hakan bai yiwu ba.
Tana jin sanda Uncle Sageer da yan uwan sa mata da maza da abokai suka yi ta yi mataruwan liki. Har tsakar dare ana wannan shagalin kafin taron wushe-wushe ya tashi. Kuma Yarima bai samu damar ganin Saadeprivately ba har su Maman Rahimah suka kama ta suka koma cikin gida.
Ranar asabar kuma aka yi KELATUL wato aka wanke wa amarya gashi aka yarfa mata kitson bare-bari kanana-kanana sun kai guda dari uku. Da yammacin ranar kuma aka yi biji-ginata inda aka shimfida manyan tabarmi aka ajiye amarya a tsakiya ana kida ana wakoki irin na barebarin Askira. Bayan an yi mata kwalliyar masarauta.
Ranar lahadi aka yi kaulu na amarya da na ango da safe. Kaulu shi ne za a ajiye miyar yauki a gaban amarya bayan an mata kitso da kwalliya. Baaba suka goya amarya suka kai ta filin da ake yin kaulu. Yan uwan Yareema na ciki daya da na sauran dakunan suka dinga dibar wannan miyar yaukin suna shafa mata, sannan daya bayan daya suka zo suna ajiye mata kyaututtuka na bajinta haka sauran matan Maimartaba.
Da yammacin ranar aka yi dubdo, wato wunin biki a harshen Hausa. Biki ya yi biki ba ka jin komai a masarautar Askira sai kade-kade da bushe-bushen algaita. Duk wadannan events din da ake yi ango bai ga fuskar amarya ba, kuma Fulani Bilkisu ita ke da alhakin yin miskero, wato abincin da ake kai wa gidan amarya. Kuma ita ke ciyar da ango da amarya dadadan girke-girke masu kara lafiya da kuzari.
In ta girka sai kuyanginta su kai sassan Yareema su ci shi da Awaisu. Korafi kam Awaisu ya sha shi gurin Yareema, kan cewa shi fa bikin nan ya ishe shi hayaniya ta yi masa yawa. A ba shi amaryarshi kawai su kama hanya. Shi ba auren fari ba to wadannan aladun duk na menene?
Awaisu sai dai ya yi murmushi don ya gama gane Yareema Sageer ya karbi auren nan da hannu bibbiyu. Har fiye da auren sa da baturiyar sa mai kananan ido. Auren da yake kira na soyayya kuma babu ya shi. Abin da bai sani ba, kuma yake matukar son sani shi ne, da ma can Yareema yana son Saade ne ko sai da aka ce an aura masa ita ya fara son ta??
Sai da Baaba (kannen Maimartaba mata) da kannen Ya Gumsu suka shigo tafiya da amarya ne idonta ya karasa raina fata. Domin a baya kallon komai take matsayin almara ko mafarki. Saadatu ta kankame Fulani tana ihu sosai ita ba inda za ta je ta bar Fulani.
Sai yanzu ne ta tabbatar da gaske an yi mata aure, kuma ba da kowa ba da Yariman Askira, Uncle Yareeman da ta ke girmamawa fiye da kowa in ka dauke iyayenta, Dr. Sageer a NTNU, kuma mijin Aisha-Sultana.
A karshe Baaba sai goya amarya suka yi tana kuka tana komai, kannen Yareema mata su Houdda sai tsiya suke mata, ko irin nasihar nan ta uwa Fulani ba ta samu damar yi mata ba sabida kukan da ta ke tun safe ya daga mata hankali. Su Mama (Babar Raheema) da su Raheeman suna gidan amarya tun safe inda ake aikin jere da kafi.
Duk wasu furnitures da aka zuba a sassan Saade dake gidan Yarima Alhaji Kyari ne ya taho da su tafiyayyu daga kasar Italiya, wadanda Maimartaba ya yi mata an wuce mata da su Abuja.
******
SAADE A GIDAN YAREEMAN ASKIRA
Daga ita sai Hanne da Raheema a bedroom din da aka zaba aka shigar da ita, wanda shi yafi kowanne kayatuwa, sai kuyangi da bayin Fulani da ke ta kintsa duk inda aka bata. Fadin dukiyar da Askirama ya dankara a gidan Yareema Sageer bata baki ne, ki sa a ranki gidan Yariman Askira mai jiran gado, shi ke nan zance ya kare.
Gida ne ginin sarauta (royal mansion) wanda aka yiwa zubi na zamani,turawa suka zana shi suka kuma zo suka gina daga Amsterdam, da aka yi wa sassan matan aure har hudu, komai da ke cikin wannan sashe shi ne a wancan sai bambancin kalar fenti. A sashen kowacce mace manyan faluka ne bi-da-bi har guda Uku da dakunan barci Uku. Babun ce kawai babu a gidan Yarima Sageer Yusuf Askira.
Sassan Aisha Sultana shi ne na farko, sai na Saade sannan wasu guda biyu a rufe. An ware bangaren bayi da hadimai daga can karshen gidan.
Sassan Yarima kuma yana upstairs wanda girmansa ya yi a hada sassan matan nasa guda biyu. Komai da ke cikin sassan Yarima ya zo da shi ne daga Amsterdam kuma duk bayan shekaru biyu ake fidda komai na gidan a sake, a yo odar wasu. A raba wa talakawan gari, ko bayi da hadimai.
A can gidan Wazirin gari Ibrahim a dakin Awaisu Yarima Sageer ne tsaye jikin mudubin dogon yaro yana sanya links din hannun farar shadda kal da ya saka, sai tashin kamshin invictus dakin Awaisu ke yi. Awaisu ya kasa danne dariyarsa ganin irin kwalliyar da Yareema ke yi wadda ko ranar da zai raka shi dakin Aisha-Sultana bai yi irinta ba, ya karkata hula ya sake karkatawa yafi sau biyar, ya ga bata yi kyau ba ya cire ya sake canza wata, [to wancan aure ne da aka riga aka kwashe albarkarsa tun a waje]. A ransa Awaisu godiya yake wa Allah yana kuma adduar Allah ya sa auren nan ya zamo karshen duk wasu matsaloli na dan uwansa Sageer.
Amma dai sai gobe za mu je sayen baki ko? Ka ga yanzu dare ya yi sosai, na san duk sun yi barci bai kamata mu tada amarya ba tana barcin gajiyar biki irin wannan.
Inji Awaisu cikin seriousness.
Wata harara da Yarima ya juyo ya zuba masa sai da ta sa Awaisu durkushewa a inda yake yana dariya. Kafin ya dago daga dariyarsa Yarima ya gama saka takalmansa ya fice yana fadin.
In ka ga dama kada ka je, da ma ba ni na gayyace ka ba, aure dai ka sani ba yau na fara ba balle ka ce rawar kafa na ke yi.
Awaisu bai bar dariya ba da ma gwanin ta ne, ya saka takalmansa ya bi bayan Yareema Sageer yana cewa,
Ko don in bata maka lokaci kafin ka shiga dakin Sa'adatu dole in bi ka.
Yarima ya girgiza kai jin abinda Awaisu ya ce, ya ce, Awaisu! Mind your language. Saadatu is my step-sister rainon ta na yi wa uwarta alkawarin zan yi, kuma shi zan yi din. Zan ba ka mamaki, jibi-jibin nan zan koma wurin mata ta.
Awaisu don dariya har da hawaye, ya ce, Aah Yarima, kada wata tara ta cika kuma mu zo bikin radin suna, wannan rainon in dai kai za ka yi shi Saadatu ba za ta taba girma ba.
Suna ta barkwancinsu na aminai har suka karaso gidan sarki, don Yareema ya ce sai ya je ya yi wa Ya Gumsu sai da safe, ya kuma nemi albarka kafin ya karasa wajen Saadatu.
[Da ya san abinda zai tarar, da ya yi wucewar sa kai tsaye dakin amaryar sa, in ya so da safe ya zo tasani].
Dazu da yamma Yaa Maira ta kira shi cikin sirri sun yi magana, inda ta ce ya bi Ya Gumsu a hankali da duk abin da ta ke so, don ba karamin yaki ta yi da ita kafin ta amince a yi bikinnan cikin dadin rai ba.
Yarima ya yi sallama a hamshakiyar turakar mahaifiyarsa Ya Gumsu, Awaisu bai biyo shi ba ya zauna a mota don ya ba shi dama ya gana da Ya Gumsu. Tana hakimce bisa kujerar mulkinta sai karkada kafa take yi cikin izza lokacin da Yarima ya yi sallama. Ta hadiye wani malolon abu da ya tokare ta a makoshi ganin irin kwalliyar da ya caba da bata taba ganin sa cikin irin ta ba, wanda ke nuna yana farin ciki da auren diyar Fulani Bilkisu.
Har kasan kafafunta ya isa ya gurfana yadda suke gaida iyayensu, ya yi gaisuwa ta amsa cikin dacin rai. Daga nan duk suka yi shiru. Yarima ya kasa ce mata ya zo neman albarkarta ne zai shiga dakin amaryarsa, aka ce wargi ma wuri shika samu. Ita kuma tana ta kitsa abubuwan da ta shirya fada masa ba tare da tunanin me zai je ya zo ba.
Ya Gumsu ta dubi dan ta Dr. Sageer wanda kansa ke sunkuye a gabanta. Ji yake kamar ya yi fiffike ya fice ya tadda Saadatu. Shi kansa ya rasa ko wane irin excitement yake ciki mai neman karar da numfashinsa. Zuciyarsa har wani irin bugawa ta ke yi in ya tuna Saadatu zai je ya tadda a matsayin matarsa yau, ba yar amanar da yake riko a gidansa ba kullum yana fama da zuciyarsa a kanta.
Sai jin muryar Ya Gumsu ya yi a tsakiyar kansa.
An yi aure na gani, kuma na sa albarka kamar yadda Yaa Maira ke so. Maimartaba ma yake so, amma Yareema ban yarda ka taba yar Bilkisu ba.
Ina nufin ban yarda ka hada shimfida da ita ba, don kuwa jinina ba zai gogi jinin Bilkisun Askirama ba. Balle in hada zuria da ita. Na ba ka watanni uku ka zo ka kara aure, aure na mutunci na gidan mutunci, duk wadannan matan naka tarkace ne, tunda babu jinin sarauta ko daya a cikinsu.
Na samo maka mata yar Sarkin Bauchi, sunanta Hajjaju, mun gama magana da mahaifiyarta ta ce kana iya zuwa ku fara fahimtar juna, in dai da gaske ni na haife ka Yarima wannan shi ne umarnina.
Ta mike ta shige turakar barcinta ta rufo kofa ta bar Yarima sai tsiyayar zufa yake daga tsugunne, ya rasa inda zai sa kansa. Don kwata-kwata bai fahimci inda zancen Ya Gumsu ya dosa ba, ko kuma ya ce ya fahimta, kwakwalwarsa ce ta kasa fassarawa.
Ya Gumsu na da masaniyar cewa weakness dinsa shi ne Mace. Macen ma ta aurensa wadda zuciya da ruhinsa ya dade yana so da kwadaituwa akan ta, to in ta ce ba zai tabbatar da aurensa da Saade ba, neman matan ta ke so ya koma wanda ya yi wa Maimartaba alkawarin ya daina? Ya yi wa Ubangijinsa alkawarin daga ranar da ya mallaki Saadatu ya daina? Wane irin aure sai ka ce namamajo, aure wata uku ya zo ya kara aure wai Hajjaju? Yo shi ko sunanta Makkah ina zai kai ta duk son matansa?
Guda biyun sun ishe shi sabida shi ba wai mata yake so ya tara ba, in ya samu abunda yake bukata a guda daya zai iya kama kan sa. Abin da ya rasa daga matarsa Aisha-Sultana (sai jar fata da yalolon gashi) wanda ya kai shi ga bin son zuciyarsa da zugar aboki Ziyad maimakon ya nemi karin aure.
Rana daya Mai Askira ya hutar da shi da yake shi uba ne mai tsinkaye, mai son gyara rayuwar yayansa ba ya dagula ta ba irin Ya Gumsu. Shi bai dauki wannan auren da ta ke son yi masa gata ba, sai hanyar huce haushinta a kan auren diyar kishiyarta Fulani Bilkisun Askirama.
Amma ya sani a yadda Ya Gumsu ta ke kan dokin zuciya irin wannan, ba wasu kalaman lallashi da zai yi amfani da su da za su sa ta saurare shi. Mafi aala ya nisance ta har sai ta huce, tunda dama ga alfarmar da ita ma Fulani Bilkisun ta nema daga gare shi, na cewa zai bar Saadatu ta gama makaranta kafin ya dora mata nauyin aure.
Jiki a salube Yareema Sageer ya baro turakar Ya Gumsu, ya tadda Awaisu a mota, bayan dogarai sun bude masa ya shiga, Awaisu ya ja motar ta kofar shiga gidan Yareema ta baya suka bi, duk da cewa ba wata tafiya ce mai nisa ba, trackable distance ne daga masarautar.
Hanne, Raheema da Saadatu ne kadai a dakin, Hanne da Raheema hirar tsaruwar