Showing 12001 words to 15000 words out of 117873 words
yi zaton tana da hankalin sanin an yi mata alkhairi ta bi da kyakkayawar addua irin haka ba.
Cikin daren Fulani ta kasa barci, ba kewar Sa'ade ta ke ba, damuwar ta na hada Humaira da Sa'ade da za'ayi ne waje daya, ta san Humaira da shegen kinibibi kamar na uwar ta zata iya jan Sa'ade a jiki ta ji sirrin su ta fesawa uwarta. Don haka ta mike daga kwanciyar ta ta sanya hijab kan rigar barcin ta ta nufi dakin Sa'ade.
Ta yi dai-dai sai sharar barci take abinta, santala-santalan fararen cinyoyin ta a waje, rigar barcin ta yaye can sama, gashin kanta da Fanna ta wanke mata dazu da shampoo sai sheki yake ga santsi, sai ta ganta exactly like herself when she was twelve years of age, a perfect replica of Bilkisu! Bata taba yi mata cikakken kallo irin na yau ba, kauyancin duk ya fara barin jikin ta, a maganarta kawai zaka ji shi.
Ta daddage ta daka mata duka a cinya, Sa'ade ta zabura ta tashi tana sosa wajen tana mutstsikar ido. "Haka kike kwana tsakiyar kwan lantarki sabida baki da hankali ko? Me yasa baki kashe ba?" Sa'ade ta zumburo baki "ni ban san ana kashewa ba" "daga yau duk sanda zaki kwanta ki kashe fitila mai haske ki bar dim, na ga alama ke kidahuma ce" Sa'ade ta kumburo kumatu bata amsa ba. Ta dora kafarta daya bisa gadon ta tsaya akan daya, sannan ta kama kunnenta na dama da kyau ta murde, Sa'ade ta saki tsuwwa don zafi, Fulani tace "idan kika gayawa wani a makarantar ku ko wadda zaku tafi tare ke 'ya ta ce sai na kabari ya fi ki jin dadi a gidannan, kowa ya tambayeki wacece ni a wurin ki ki ce ke 'yar kanwata ce, babar ki ta mutu, kin ji ni ko baki ji ni ba?"
Hawaye na fitowa daga idon Sa'ade ta ce "na ji!".
Fulani ta sakar mata kunnen, ta juya zata bar dakin. Sai ta tsinkayo muryar Sa'ade cikin rishin kuka.
"Amma me yasa kika tsaneni haka? Da har ba kya so a ce ni 'yar ki ce? Kawai saboda ni Babana talakane ba sarki bane?"
Wuta ta daukewa Fulani Bilkisu, ta kasa gaba, ta kasa baya. Bata taba zaton yarinyar zata iya yi mata wannan tambayar ba. Sa'ade tayi murmushi mai ciwo ta share hawayen ta da bayan hannun ta.....
"Ki nemo min dan uwan mahaifina na Damaturu, tunda kinsan inda ya ke, insha Allahu zan nesanta kaina dake kamar yadda kike so, zan koma wajen sa".
Bata bata amsa ba ta fita daga dakin, jikin ta yai matukar sanyi, bata zaci yarinyar nada hankalin gane abubuwa har haka ba, a shekarun ta goma sha biyu, ko ta yi mata bayani bazata gane ba, bata kin mahaifin ta don talaucinsa sai don rashin SO da zafin AUREN DOLE. Tunda itama 'yar talakawa ce futuk! Gaba da baya, inda halacci ashe kuwa bazata manta talauci sabida arzikin gidan aure ba.
Da maganganun da Sa'ade ta gasa mata ta kwana a ranar suna gasa mata zuciya. Shi yasa da safe ta ki fitowa balle ta ga tafiyar ta, bata so ta karasa karya mata zuciya, bata shirya karbar ta matsayin 'ya anan kusa ba kuma har abada bata jin zata iya idan ta tuna Hashimu ne Baban ta.
Fanna ce ta zo ta tashi Sa'ade ta taimaka mata tayi wanka, ta bata kayan makarantarta ta sanya, tuni an fidda kayan ta zuwa mota. Tun shigar ta gidan kwana ashirin da daya sai yau ta fito ta shaqi fresh air, daga iskar fanka sai ta A/C. Ta na ta wurga ido ko zata ga Fulani, amma ko motsin ta bata ji ba, ta san kuma bata isa ta shigar mata daki ba bisa umarni ba. Duk ta ji ba dadi da abinda bacin rai ya kwashe ta ta gaya mata jiya. Ta san a matsayin ta na uwa, ko me zata yi mata bata cancanci wadannan kalaman daga gare ta ba.
Kawai sai ta kama kuka. Jikin ta a sanyaye ta bi bayan Fanna suka fita daga shiyyar Fulani, kuyangin Fulani na ta kallon ta don su har sun manta tana cikin gidan. Da yake safiya ce basu hadu da mutane sosai a hanya ba sai bayi jefi-jefi amma matan gidan da 'ya'yan su ko jikokin su babu ko daya, kowa yana sashen sa.
Har suka shiga dalleliyar motar da direba da dogarai biyu ke ciki, daya na tuki, daya na gefen sa. Sa'ade bata bar kuka ba. A jikin motar an rubuta da ruwan gwal "ASKIRA EMIRATE". Gefen hagu dogarawa suka bude mata ta shiga, kafin su rufe kofar ta kamo hannun Fanna, idanunta narai-narai da hawaye tace.
"ki ce ma Fulani don Allah don Annabi ta yi hakuri".
Fanna bata san akan me ake aiken ta bada hakurin ba, ta dai lura akwai wani babban al'amari tsakanin uwargijiyarta da wannan bakauyiyar yarinyar. An raineta ne kawai a bisa bin umarni, babu tambaya, don haka tace "insha Allahu zan gayawa Fulani sakon ki".
Fanna na barin wajen ba da jimawa ba Sa'ade ta hango wata kyakkyawar budurwa na tahowa karkashin rakiyar bayi 'yammata tsararrakin ta, tafiyar ta kawai data banbanta da tasu ya sa ta gane itace Humaira da Alanguburo yace zasu tafi tare wato 'yar autar sarki. Duk da kayan makaranta ne a jikin ta irin wadanda ke jikin ta amma an dora farar alkyabba wadda ta sha aiki da zare ruwan gold mai matukar walwali akai.
Tun kafin ta karaso dogarawan nan suka bude kofar da azama suna yi mata kirari irin wanda 'ya'yan gidan kawai ake yi wa. Ta shiga barin dama, yayin da Sa'ade ke barin hagu. Da ta zo bakin motar sai kuyangar dake bayanta ta zare mata alkyabbar ta shiga daga ita sai kayan makaranta. Daga haka aka ja sullubebiyar motar a hankali suka soma tafiya, kuyangin nata basu bar wajen ba har motar su Sa'ade ta hau kwalta.
Tunda suka mika hanya sosai yarinyar take ma Sa'ade kallo na kurilla, ita kuwa tun gaisuwar farko data yi mata bata kara ce mata komai ba. Ta maida hankalin ta ga kallon hanya suna wuce bishiyu da dazuzzuka kamar walkiya. Sanda suka cimma garin Chibok ta ce da Sa'ade cikin ginshira.
"Me ye hadin ki da Fulani?"
Sa'ade ta tuna gargadin Fulani don haka nan da nan tace "ni 'yar kanwar ta ce, mahaifiyata ta mutu". Gimbiya Humaira ta yi mata kallon shakka don ita dai bata taba ganin irin wannan kamar ta kwabo da kwabo ba irin wadda ke tsakanin Fulani Bilkisu da yarinyar da ke gefen ta. Kamar kamannin sun zarta na matsayin data ambata din na kasancewar ta 'yar kanwa a gareta. To amma wace hujja gareta na karyatawa? Tunda ta san bata haifi 'yar a gidan su ba?
Sai ta dauke kai itama ta koma kallon gefen titi. A ranta tana fadin ita sam bazata yi mu'amala da 'yar kalen dangi ba mai maganar kauyawa.
****
EL-KANEMI COLLEGE OF ISLAMIC
THEOLOGY
Makarantar kwalejin kimiyya ce ta addinin muslunci wadda Larabawan Yemen dana Sudan suka bude a Maiduguri da hadin gwiwar manyan masu kudin jihar Borno. Itace makarantar da sarki Yusufu ke kai 'ya'yan sa maza da mata, tun daga kan babbar 'yar sa (Ya Maira) sunan sarautar ta kenan a matsayin ta na babbar 'ya, har zuwa kan auta Humairah.
A tsarin makarantar daga Lahadi zuwa Alhamis sune renakun karatu, Juma'ah da Asabar renakun hutu.
Malamin maths na fita na Qur'an na shiga, na English na fita na Nahawu ko Fiqh zai shiga, na chemistry na fita na Adab ko Tarikh ko Mutala'a zai shiga haka dai tsarin karantarwar su yake. Wato kimiyya cakude da ilmin addini tsantsa.
Sannan ana gama lessons karfe uku ake fara Islamiyya ga mai son haddan Qur'an zalla ake yi har zuwa biyar na yamma.
Malaman makarantar kuma yawanci larabawan Sudan da Yemen ne, sai kuma Yarabawa
Maza da mata basa haduwa sam, dan katanga ce makekiya a tsakanin su sannan kowane bangare da gate din shi.
Tunda aka kai Sa'ade da Humairah dormitory dalibai 'yan uwan su ke kallon su, ba don komai ba sai don irin tsadaddun kayan abincin da ake shigo dasu katan-katan ana loda musu a lokokin su, a karshe lokokin nasu ma sun yi kadan su kwashe kayan, sai Humaira ta ce da metron da masu jerawar su je da sauran ta bar musu. Ko kallon Sa'ade bata yi kada a ce tare suke, amma kayan abincin su ba banbanci haka takalmi da jakar makarantar su, wanda ya tabbatarwa 'yan dakin cewa tare suke din.
Gadon Humaira na gefen na Sa'ade, don haka ta yi amfani da wannan damar ta maida ita baiwar ta, komai tana daga kwance take sa ta ta yi mata, dauko wannan miko wancan, ko kofi zata yi amfani da shi sai ta sa Sa'ade ta wanke mata shi, kuma da yake Sa'aden ta iya kitso ita ke yi mata duk sati, basa yin wanki iyayensu ke biya a wanke musu shiyasa Sa'ade ta samu sauki, da har wanki da guga ita zata ce ta yi mata.
Girman kai irin na Humaira ya hanata alaqa da mutanen dakin, ita kadai take rayuwar ta ko a class don bata ga wanda ya isa tayi mu'amala da shi ba duk da cewa duk 'ya'yan masu kudi ne a makarantar amma a wurin Humaira in ba ka da jinin sarauta cikin jikin ka to baka isa mutum ba. Kuma duk makarantar ita kadai ce 'yar Sarki.
Sabanin Sa'ade wadda ta maida kanta abokiyar kowa a dakin nasu, in har bata hidimar Humaira to zaka sameta cikin jama'ar dakin suna hira da harkar arziki, ga ta da kyauta, haka take ta rabar da kayan abincin nata musamman ga wanda ta lura yana da bukata, cakuduwar ta da dalibai 'yan uwan ta wadanda suka fita experience da exposure ya sa ta fara samun wayewar kai. A aji kuwa duk ita ce koma baya a kowane darasi daga na boko har na addini, amma bata barin hakan ya kashe mata gwiwa, ya cire mata hope na cewa da sannu zata iya idan ta sanya jajircewa da bada himma.
Haka monitar ajin nasu Raheema Kyari ke yawan gaya mata, wadda tasu ta zo daya, sakamakon yawan tambayar ta abubuwa da Sa'ade ke yi idan bata gane ba ba tareda nuna jin kunya ko girman kai ba. Ba ajin su daya da Humairah ba ita 'yar JSS 3 ce yayin da Sa'ade ke JS 1. Don haka tafi jin dadin rayuwa a class fiye da a dormitory (dakin barcin dalibai) sabida babu Humaira mai takura mata, a nitse take karatun ta tare da likewa monita Raheema tana daukar ilmi daga wajen ta.
Malaman ko sun so yin korafi akan rashin kokarin Sa'ade sai su fahimci abin nata daga tushe ne wato bata samu foundation a makaranta mai kyau ba kamar sauran daliban makarantar, don in sun tambayeta wace makaranta tayi tana gaya musu a kauyen Tsanyawa ne, makarantar da maigari yasa aka bude, don a koyawa yara A BA CA DA sai su daga mata kafa musamman in suka lura da yadda take da kishin abun a zuciyarta, in aka koya abu bata gane ba har kuka take yi. Duk kokarin Raheemah na koyar da ita ba komai take ganewa din ba musamman darasin lissafi, da yawa a makarantar sun dauka Sa'ade baiwar Humairah ce, irin 'ya'yan bayi da ake hado 'ya'yan sarakai dasu su zo makaranta tare don su dinga hidimta musu, sabida haka Humairan ke nunawa.
Sannu-sannu bata hana zuwa, saidai a dade ba'a je ba, a hankali Kwakwalwar Sa'ade ta soma budewa, musamman a haddar Al'qurani da Ingilishi. Raheema ta taka rawar gani akan hakan don fisabilillah take kaunar Sa'ade sabida saukin kanta, baban Raheema babban dan kasuwa ne a jihar Maiduguri wanda sunan sa yayi fice akan sana'arsa ta fata.
Watarana Raheema ta kawo wa Sa'ade ziyara dakin su, sai ta same ta durkushe gaban Humaira ta sunkuyar da kai tana hawaye, Humairan na ta zazzzaga mata fada har tana fadin dama 'yan kalen dangi basu iya cin arziki ba, banda haka tun safe ta sa ta gyaran sittirunta amma tasa kafa ta fice yawon neman suna bata gyara mata ba, su ko Fulani Bilkisu ba wata tsiya bace a wurin su tunda sun san asalin ta balle su ya-ku-bayin data kawo musu gida suna cinye arzikin Babansu.
Ba fadan data ke mata ne yasa ta kuka ba, domin in da sabo ta saba, ambaton sunan Fulani data yi ta zaga ne ya tsaya mata a zucci. Ya kona mata zuciya. Fulanin da has never been nice to her in any way amma zuciyar ta na mata wani irin so, da bata taba jin sa akan kowa ba including Baban ta.
Rahima ta kama hannun ta ta cira ta tsaye suka bar dakin, Humaira ta sakar musu tsaki tana fadin "ya'yan mutsiyata, gayyar tsiya".
Can bayan dormitory suka zaga suka zauna akan duwarwatsun da ke wajen, Raheema ta ce "wai don Allah Humaira ke baiwar ta ce? Ko iyayen ki bayi ne a gidan su?" Bata san me yasa ta yarda da Raheema ba, tun sanda ta fahimci Raheemar na tausaya mata tsakani da Allah. Ta girgiza kai tare da share hawayen idon ta "ni ba baiwar ta bace, ana riko na ne a gidan su, kishiyar mamanta ce yar mahaifiyata a hannun ta nake".
Raheema tace "tabdi! Amma shine kike mata bauta tana miki wannan wulakancin? Ke ba baiwar ta ba iyayenki ba bayin su ba? To wallahi ki kama kan ki, ki nuna mata zaman kan ki ke yi ba zaman ta ba in ba haka ba watarana sai ta kai ga taba lafiyar jikin ki" da sauri Sa'ade ta girgiza kai.
"Zan yi mata komai saboda Baban ta!".
Raheema ta rasa abinda zata ce, sabida a amon muryar ta kadai ta fahimci akwai wani girmamawa da kauna na musamman data ke yi wa Baban Humaira, abinda ta fada har zuciyar ta ya ke. Wannan ya tabbatar mata Sa'adatu irin mutanen nan ne da basa manta alkhairin da wani yayi musu komai kankantar sa.
****
An yi jarrabawar karshen zango, as expected Sa'ade ta dauko na biyun karshe, ta yi kuka har ta gode Allah, amma a islamiyya ta yi dan kokari ba laifi musamman a hadda.
Damuwar ta yadda zata dauki wannan mummunan sakamako ta kaiwa Alanguburo, bayan ta yi masa alkawarin yin kokari iyakar iyawar ta.
Raheema ta ce ta bata lambar wayar wani a gidan su zata kira ta in ta koma gida, Sa'ade tace banda Fulani babu mai waya a sassan su, ita kuma bata san lambar ta ba, ko ta sani bazata yi karambanin bayarwa ba Fulani ta tsinke mata kunne haka kawai.
A daren ta hada musu kayan su da zasu tafi dasu gida a kananan trollies din su, sauran kayan abincin da suka rage Humaira tace ta fitar duka ta kaiwa metrons.
Ta yi sallama da 'yan dakin su cike da kewa suna fadi a ransu ai gara ta je gida ta huta da wannan bautar data sha ta gimbiya Humaira, wasu kuma suka ce a ran su watakila har a gidan ma irin bautar data ke mata kenan.
Kusan su ne na farko da aka zo dauka a washegari. Suna tsaye ita da Raheema a jikin bishiya suna hira, Humaira na daga zaune a gefe akan jijiyar bishiya tana ta harare-harare irin wanda ta saba da kallon kowa a wulakance. Zungureriyar mota kirar 4matic baka wuluk ta yi parking a gefe, da rubutu baro-baro cikin ruwan gwal "ASKIRA EMIRATE".
"Ma'assalam Raheema, an zo daukar mu"
Ta fada tana jan trollies din biyu dake gaban ta, nata da na Humairah, Raheemah ta daga ido tana kallon inda ta nufa, tun kafin ta karasa dogarawa biyu suka yi wuf suka fito daga motar suka karbi kayan hannun ta. Ta karanta rubutun ta sake karantawa "ASKIRA EMIRATE" Ashe daga masarautar Askira suke, no wonder Humairah take mulkin data ga dama. Baban ta ya sha basu labarin masarautar Askira da irin dimbin arzikin ta da shaharar ta a yankin Borno.
Ta karasa da gudu ta cimma Sa'ade, ta rike hanayen ta, tana murmushi ta ce "ki gaida mun Fulani, i will give you a giant surprise insha Allah" Sa'ade ta yi dariya ta ce "Fulani zata ji, ki gaida Mama dasu Sarina (kannen ta)".
Raheema na juyawa ta kusa karo da Humairah, da sauri ta bata hanya sabida mugun kallon data sakar mata. Ta shiga gefen dama data saba zama dogarin ya rufe kofar. Ya zaga