Showing 51001 words to 54000 words out of 117873 words

Chapter 18 - Masarautar Mu 1 to 4 Complete

ta ne? Bata cika son magana tayi tsayi a tsakanin su ba, karatun ma da yace zai koya mata bayan dawowarsa daga tafiyar da yayi saida ta san yadda tayi ta kaucewa hakan ta roki Sa'idu ya koya mata lokacin jarrabawar kwas din, yana da effect mai karfi kanta wanda shi bai sani ba itama bata sani ba, abinda ta sani kawai shine bata son mu'amala mai zurfi a tsakanin su.
"Ki shirya gobe da asubah zamu kama hanyar Askira, maimartaba yace a kai ki kiyi hutu" bata san lokacin da ta dago zaune ba tana ta faman blushing, bai tsaya kallon ta ba yasa kai ya fita.
Tun a daren ta hada duk abinda take bukatar tafiya da shi. Baccin ta ma ragagge ne sabida doki. Tayi kewar Fulani da Zarah.....Shi kansa Askirama ta yi kewarsa.
Washegari data yi sallahr asubah bata koma barci ba, wanka tayi, tayi ssaukar shiga ta bakar abaya mai santsi da adon stones sosai a jikin ta. Bata shafa komai a fuskarta ba sai wet-lips ta kuma fesa sassanyan turare. Ta zauna bakin gadonta da trolley dinta a gaba tana jiran Yarima.
Bai fito ba sai wajen karfe shidda na safe, kallo daya tayi masa da ya murda kofar dakin ya shigo bayan tayi masa izni, taji bazata iya jure kallon ba, kwayar idanunta ta zamo mai rauni sabida yau ya fito Prince dinsa.
Ta taba ganin maimartaba da irin kayan jikin sa, yakan saka kayan in zai zauna cikin iyalinsa, kaya ne kufta da wando na sarautar Askira wadanda basu cika nauyi ba. Amma kuma sun sha aikin zare na silver da hula zanna bukar a kansa. Kasancewar kusan kullum cikin shigar suit take ganin sa yau sai ya zamo mata wani daban, classique and elegant kai kace Askirama ne ya zama yaro.
"Lets go!"
Inji Yarima, ganin ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, bayan a badini kirjinta ne ke wani irin harbawa da sabbabin emotions da bata san daga ina suke fitowa daga karkashin zuciyarta ba.
Hannu yasa ya ja trolley dinta. Ya fita ta bishi a baya bayan ta dau handbag dinta tana mamaki a cikin ranta; Yarima ya dau kayanta da kansa. Sai taji har tsigar jikin ta na tashi da wani irin feelings mai sanyi a zuciyar ta. Hakan kuma bai janye bakin fentin data ke kallon shi dashi ba.
A falo suka ci karo da Aisha - Sultana, kayan barci ne a jikin ta, ta tsaya jingine da kofar dakin ta tana kallon su, ta gabanta Yarima ya wuce dauke da jakar Sa'ade, Sa'aden na gaisheta da safiya, wata harara ta zabga mata ba tareda ta amsa ba. "Mun tafi Askira Aunty, sai na dawo" jin bata amsa mata ba ta wuce ta, ta tadda Yarima a mota, Salis ne ya ja su. Ta dauka a motar zasu tafi har Askira amma sai ta gansu a filin jirgin saman Abuja.
For the first time Sa'ade a jirgi, in ka gansu itada Yarima tsammani zakayi sababbin couples ne sabon aure duk da babu hira a tsakanin su. A cikin jirgin Azman ne mai zuwa Maiduguri a first-class seats, ga kujerar ta ga ta Yarima, Lokacin da waitress ta kawo abin motsa baki kasa cin komai tayi sabida uneasiness din da take ciki na zama a gefen Yarima. Ga kamshin Paco Rabbanne dinsa dake kara hargitsa ta. Shikuwa yayi amfani da wannan damar wajen kare mata kallo, kallon da bai taba yi mata ba, har ya zarta ka'idar muslunci domin kallo ne na kurullah. A zuciyar sa ba abinda bai fada ba, wanda daga shi sai Ubangijinsa suka sani, a zahirin sa kamar ba ita yake kallo ba.
Bai fi minti goma ya rage suyi landing ba Sa'adatu ta soma jin amai na taso mata sakamakon wani Igbo da ya gifta ta gabanta yana warin qashi irin na maza, ai kuwa tana yunkurawa domin ta tashi sai amai ya kelayo a jikin Yarima Sageer, basu da yawa a first class seats din don haka hankalin sauran mutanen ya dawo gare su, Sa'ade ta hau zazzare ido cike da tsoro bakin ta na rawa tana son furta ban hakuri kalaman sun ki fitowa. Amma ga mamakin ta ko a fuska bai nuna kyama ba, wani irin kallo yayi mata yace "sai kin goge min shi tas!"
Tayi narai-narai da ido kamar zata yi kuka don damuwar abinda tayi masa "...don Allah kayi hakuri Uncle Yarima....ban yi da sani ba" a ginshire ya ce "na ce kin yi da sani ne?" "To kayi hakuri don Allah bazan iya goge maka ba" suna wannan jayayyar sai ga waitress tazo don ta gyara wajen tana ta yiwa Sa'ade sannu don a zaton ta ciki gareta.
Kasancewar kayan rubi biyu ne ta saman kamar jabba take mara nauyi akwai jamfa daga ciki yasa ya cire ta saman. Sa'ade tayi maza ta dauko turarenta a jakarta ta mika masa. Karba yayi yana jujjuya shi a hannun sa 'sapphire' itama Fulani ce ta bata, a tunanin ta zai bukaci turare tunda tayi masa kayan karni.
"Me zan yi da turaren mata?"
"Ka fesa saboda karni"
Ta fada kamar zata saki kuka don damuwa, ta rasa da bakin da zata bashi hakuri. Mika mata turarenta yayi yana dubanta ta kasan ido yace a hankali "idan matata taji kamshin turaren ki a jiki na what do you expect?" Sa'ade ta runtse ido tace "ni fa ban bayar da wata manufa ba, don ya kashe smell din aman ne" "idan kuma ni son smell din aman nake fa?" Kallon sa tayi da budaddun idanuwa.... mamakin ta ya bayyana karara cikin idanun ta
Ba jimawa jirgin su yayi landing a Maiduguri.
Motocin ASKIRA EMIRATE har guda biyar manya da kanana suka zo tafiya dasu, da fadawa da dogarai cikin uniform din su na bayin masarautar. Mota guda suka yi amfani amma da yake babba ce sosai kirar (4matic) mai kujeru takwas ba kujera daya suka zauna ba, Sa'ade na daga kujerar baya Yarima na owner side. Suka dauki hanya. Ji take kamar tayi fiffike ta ganta a dakin mahaifiyar ta. Har suka zo Askira barci take wanda a jirgi takuruwar zama kusa da Yarima bai barta ta yi ba.
Ana bude musu motar ta fice da azama bata jira fitowar Yarima ba, wanda tun shigowar su Askira taga kamar komai nasa ya canza, simplicity din da annurin ya tafi, ya juye ya rikide ya zama cikakken Prince din sa.
Da gudu ta karasa unguwar Fulani Bilkisu ko jakarta bata dauko ba sai biyota aka yi da ita. Da Zarah ta fara tozali, suka ruga da gudu suka makalkale juna. Zarah na tambayar me ta taho mata dashi daga Abuja? Tace "everything, sweetheart". Fulani ta fito daga shigifarta cikin wata irin kyakkyawar shiga ta alfarma, ta tsaya daga bakin kofa tana kallon su da murmushi, kamshin ta ne yasa Sa'ade ta lura da ita, ta ajiye Zarah ta kwasa da gudu ta rungume Fulani, kawai kuma sai ta fara hawaye.
Fulani tace "yau nake ganin sakarci, me aka yi na kuka? Ko suna miki wani abu ne?" Ta girgiza kai "babu komai, kukan farin cikin sake ganin ki nake yi, watanni shidda ba kwana shidda ba". Fulani ta hau tureta daga jikin ta jin takun ana shigowa, Fanna ce ta taho dauke da abinci a makeken tray ta ajiye a dining. Tana murmushi tace da Fulani "Allah ya taimakeki yau tare na hada muku abinci da uwar daki na, don Allah ku ci tare" Sa'ade ta sa dariya cikin dadi tana kallon uwartata. Fulani ta gimtse fuska tace "Fanna yaushe na koma abokiyar wasan ki?" Fanna tayi nara-narai da ido tana murmushi tace "Allah ya ja da ranki Alfarma ce muke nema, wata shidda cif bamu ganki ba".
Babu wanda ya gayawa Fanna Sa'ade 'yar Fulani ce ta cikin ta amma ta dade da fahimtar hakan. Yadda aka yi ta samu 'yar ne bata sani ba.
Tana gama fadin hakan ta juya ta fita, Sa'ade tayi wata irin super ta dane jikin Fulani saura kadan ta kada ita, Zarah sai dariya take yi. A haka suka ci abincin cike da begen juna su uku. Tana gamawa tayi wanka ta sauya kayan jikin ta zuwa marasa nauyi ta dauko waya ta kira Sa'id. Yace "Sa'adatu, yaya kwana biyu kuma ya hutu? Ina fatan kina bitar Physiology textbook dinnan?" Sa'ade tace "ni yanzu ina garin mu bana Abuja ka kyale ni in huta da wani karatu, ina tare da uwata rabin raina" Sa'id yayi murmushi yace "sai na zo Askira kawo gaisuwar neman iri" Sa'ade tayi tsaki tace "Allah ya sawwake inyi saurayi da classmate dina, wani dan yaro da kai, ni dinnan da kake gani matar manya ce inji Fanna" dariya sosai Sa'id yayi, ya ce "me yafi ka auri yaro sabon jini kamar ka? Ya sa ka dariya kaima ka saka shi? In yaga dama ya goyaki ya yi ta zagaye gida dake?" Sai ganin Fulani tayi tsaye a kanta. Ba karamin firgita tayi ba ganin expression na fuskarta. Tayi maza ta kashe wayar ba tareda ta yiwa Sa'idu sallama ba.
Tana zazzare ido na rashin gaskiya.
"Keda wa kike waya?"
Fulani ta tambaya fuskarta babu annuri.
A tsorace tace "dan ajin mu ne kawai"
Fulani ta juya bata ce komai ba. Saidai kwarai ta so ta magantu din, but she don't want to be too strict har Sa'ade ta koyi boye mata sirrikan ta. Saida ta kai bakin kofa sannan tace mata ta tafi wajen Askirama kada ta nemeta.....
****












Rami ne mai tsananin zurfi, wanda har baya iya hango karshen sa sabida zurfin sa, ya leka ciki sabida ya ji kamar muryar Yarima yana kuka yana neman taimako. Bai ga ta inda ta bullo ba kawai ya ganta ne a bakin ramin, tana rike da igiya mai tsayi, tana zuwa bakin ramin ta jefa masa igiyar tace "Kama ka fito da iznin Ubangiji".
Bai ga fuskarta ba sabida ta sunkuya ne akan ramin, gashin kanta ya sakko ya rufe fuskar tata gabadaya, saida tayi magana sannan ya shaida muryar ta.
Ba jimawa ya ga ta kama igiyar nan tana janyo wanda ke ciki har ta fiddo shi tsaf, yana fitowa suka rungume juna suna hawaye. A lokacin ne ya samu damar ganin fuskokin su gabadaya; Sa'adatu ce da dan lelen sa YARIMA SAGEER.
Tamkar an warware masa dukkan baccin da ke kansa ya farka firgigit misalin karfe biyu na sulusin dare, lokaci ne da aka tabbatar mafarki yana iya zama reality. To ko me wannan mafarkin da yayi yake nufi? Sa'adatu as saviour of Sageer? Ba don babu kyau bayyana mafarki ga wani ba, da ya nemi Limamin Askira ya gaya masa mafarkin da yayi. Duk da haka a nasa hankalin, ya fahimci tamkar wani hannun ka mai sanda ne Ubangiji yayi masa, mai nufin akwai wani babban al'amari tsakanin Sageer da Sa'adatu kamar yadda ya so hakan ta kasance a baya.
Bai san sanda ya sa hannu ya soma tashin Fulani Bilkisu wadda ke barci sadidan a gefen sa. Ta tashi tana yamutsa fuska tana mutstsikar ido. Ya ce "Bilkisu bude idon ki ki dube ni". A yanayin da Askirama yayi maganar cikin rauni yasa ta dole watstsakewa.
"Lafiya Askirama? Lafiya gatan mara gata? Lafiya giwan ASKIRA?"
Ta fada cikin tausasa murya, mai Askira ya kama hannayenta duka biyu ya rike cikin nasa. "Alfarma nake nema wajen ki irin wadda ban taba nema ba...... ki bani Sa'adatu in aurawa Yarima a gobe".
Fulani Bilkisu ta ji maganar ne tamkar saukar aradu a kunnen ta, kwakwalwarta ta kasa digesting maganar yadda ya kamata sabida wani abu ne da bata tsammani ba a rayuwar ta. Bata kin Yarima don tamkar dan cikin ta ta dauke shi. To amma neman matan da ake cewa yana yi fa tun bai san kansa ba har girman sa har ita Sa'adatun ma ta shaida da bakin ta? Shin Sa'ade ta cancanci hada rayuwa da wayayyen mutum irin Yarima? Ina Sa'aden ta ina hada kishi da Aisha-Sultana?
Don haka Fulani ta rasa amsar da zata baiwa mijinta mai Askira, sai bin shi da ido, a zaton ta makuwa yayi cikin barcin sa. Amma da ya girgiza kafadun ta ya sake maimaitawa sai ta tabbatarwa kanta mai Askira yana nufin abinda yake fada ne.
"Kin amince ko Bilkisu? Hankalina bazai kara kwanciya ba batare da na tabbatar da sunnah tsakanin Sageer da Sa'adatu ba, jikina na bani itace zata zamo maganin dukkan matsalolin sa, don ban taba yin mafarkin da bai zama gaskiya ba".
Ya kwashe mafarkin da yayi duka yanzun nan ya fada mata.
Fulani Bilkisu ta rasa abinda zata ce, she's mute for some minutes, tana mai tariyo tarin alkhairin Sarki Yusufu ga Sa'ade tun zuwanta Askira, shin bazata manta da komi ba ta bisu da addu'a ta zama mai rama khairan da khairan?
Ta lumshe idon ta cikin na Askirama, wanda ke tabbatar masa da ta karbi alfarmar sa, bata da abin cewa. Itada Sa'adatu duka abin ikon sa ne sai abinda ya hukunta a gare su.
****

Koda ta koma dakin ta a washegari bata ce da Sa'adatu komai ba, cikin dimuwa da zullumi take, sabida Mai Askira ya ce kafin su koma hutun nan da suka zo sai da igiyar aure a tsakanin su.
Sa'ade ta lura a wunin ranar bakidaya Fulani ta zama sukuku! Bata umh bata umh umh. Abinci wannan a wunin yau bata ci shi ba kuma tace ba azumi take ba. Ta lura tunda ta dawo daga turakar maigidanta take cikin wannan halin, to ko ita da Mai Askira ne suka samu sabani? Saidai hakan mawuyaci ne don bata taba ganin ma'aurata masu fahimtar juna kamar su ba.
Sai itama ta shiga damuwa, damuwar uwarka ai yana nufin taka damuwar. Damuwar Fulani shine bata san ta ina zata farawa Sa'ade zancen aure ba, she's too young and innocent, auren ma kuma da Yarima Sageer, wanda ta riga ta gama sanin sirrin su shi da matar sa, ta kuma dauke shi matsayin guardian dinta. Sama da komai bata taba tunanin yiwa Sa'ade aure nan kusa ba, ta so sai ta gama karatun ta, to kana naka Allah na nasa kuma nasan shine gaskiya.
Sa'ade sai zarya take tsakanin dakin ta dana Fulani very disturbed, ko Fulani zata kira ta tace zo kiji damuwata, amma Fulani ko kallon ta ta kasa yi, ji take kamar ta yi ba daidai ba ta kuma yi mata laifi data karba mata zancen aure bada sanin ta ba. Ba jimawa jikin ta ya dau dumi, data tuno me ake yi a gidan Yarima Sageer "Zina da Shan giya". Ba ga matar ba ba ga mijin ba kowanne shegen kansa ne, ta dauki innocent 'yar ta ta kai musu, matar ta sha giya ta rotsa mata kai, ko mijin yayo zinarsa ya goga mata cuta?
Amma kuma wanene Yarima? Dan Askirama mafi soyuwa a gare shi. Askiraman da ya maida Sa'aden mutum a lokacin da ita ta kasa karbar ta. Wannan damuwa a take ta kwantar da Fulani Bilkisu, amma sai ta mike tana rangaji ta sawa kofar ta mukulli kada Sa'ade ko Fanna su zo su dameta.
****
Ya Gumsu na tareda mai Askira a washegari, itace tayi turaka kuma itace zata wuni tare da shi a wunin yau da baya fita fada, duk ranar Jumaah daga ya dawo masallaci sallahr jumaah baya kara fita, yana zama ne ya ribaci yammacin da ibada musamman karatun Suratul-Kahfi da suratul Mulk, Yaasin da Waqi'ah. Sannan yana karanta Suratul Nouh kafa 41 a kowanne yammacin Juma'ah.
Tana hada masa shayi a cikin kofi (mug) ya dubeta da murmushi. Ya ce "Gumsun Askira, Uwargidan mai Askira....inada wani kyakkyawan albishir dauke a bakin nan nawa". Ya Gumsu ta karkace ta gyara zama bisa tattausar dardumar da maimartaba ke zaune har da tattara dukkan nutsuwar ta ta bashi, a zaton ta albishir zai mata da tafiyar su wata kasar su huta.
Amma abinda mai Askira ya fada bata taba jin abinda ya girgiza zuciyarta da rayuwarta bakidaya irin sa ba. Ya jirkita kwanyarta, ya gusar da annurin fuskarta nan take ya mayeshi da wani mummunan bacin rai da Askirama ko wani mahaluki bai taba gani a kan fuskarta ba.
"Kwanaki uku masu zuwa zan daura auren Yarima da Sa'adatu!"
Amma Ya Gumsu sai

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login