Showing 105001 words to 108000 words out of 117873 words
ba ta gani, motoci na ta kauce mata, wasu su bi ta da zagi, wasu su kunna mata fitilar zagi, amma ba ta ko san suna yi ba.
Ya sakar mata kakkarfan horn don ta sha gabansa, ta juya a firgice sai ya ga Saade. A hankali ya sauka a gefen titi, ya fito da sauri ya bi bayanta yana kiran sunanta.
Saadatu Hashim, Saadatu Askira ina za ki je haka?
Muryar Said abokinta, Saidu-Saidunta. Yau da shi ta aura wa zai yi mata wannan wulakancin da cin zarafin? Wani hawayen ya sake zubo mata, ta sa fuska cikin hijabinta tana kuka.
Said ya hau waiwaye cikin tsoro. Har zai ce ta shiga motarsa ya kai ta inda za ta je ya tuna gargadin Yareema Sageer.
Kada ka kara daukar matata a motarka ko da da niyyar taimako ne.
Said ya naushi hannun damansa da hannun hagu, ga shi kuma ba zai iya tafiya ya barta a kan titi ba, ko da kuwa supreme court Dr. Sageer Askira zai kai shi a dalilin hakan. Da ganin halin da ta ke ciki tana tsananin bukatar taimako, ba zai barta ta ragaita a babban birni irin Abuja ba.
Wane irin taimako zan iya ba ki?
Said ya fada cikin tsoro, yana tsaye nesa-nesa da Saade yana kuma waiwayawa dama da hauni kada Dr. Sageer ya zo ya same shi.
Kudin mota.
Ba ta san lokacin da ta furta ba.
Ina za ki je? Ya tambaya da sauri.
A hankali ta ce, Garinmu Askira.
In aka sauke ki a Maiduguri za ki iya zuwa har can Askiran?
Da sauri ta gyada kai.
Said ya ce, Zan sa ki a tasi zuwa airport, sai in bi bayanku, sai mu je in yankar miki ticket din Maiduguri.
Saade ta hau godiya, tana yi masa addua. Ji ta ke kamar ma ga ta ga Fulani a gabanta.
Hakan kuwa aka yi, Said bai bar airport din ba sai da ya tabbata jirgin Maiduguri ya daga da Saade. Ya kuma damka mata naira dubu goma, ya bar filin jirgin cike da tausayinta.
A ganinsa iyayensu sun cutar da ita da suka aura mata babban mutum kamar Dr. Sageer, ba zai ba ta kulawar da in shi ya aure ta zai ba ta ba, ban da kishin balaI bai san komai ba (a ganinsa).
Tunda jirgin Azman ya lulluka sararin samaniya ya doshi arewacin Nigeria, Saade ta kankame jikinta wuri guda tana kuka, ba ta san ya ya za ta iya rayuwa babu Sageer ba. Amma ta tabbata Ya Gumsu ta raba su kenan, ba za ta kara bari su rayu inuwa guda ba.
Ya taba cewa yana fuskantar barazana akan auren su, wanda ya sanya shi tabbatar da auren su a lokacin da bai shiryawa hakan ba, yanzu ta tabbatar ba komai bace barazanar, Ya Gumsu ce. Har gobe bata yi naam da zaman su tare ba.
Wannan tunanin kadai na matukar tayar da hankalin Saade, ta rasa inda za ta tsoma zuciyarta ta ji dadi. Wani irin sanyi ta ji yana shiga har cikin bargonta. Ba jimawa hakoranta suka soma karo da juna, kafin a yi haka zazzabi mai zafi da ciwon kan da ta kwana a ciki sun hadu sun rufe ta ruf.
Ta sauka a filin jirgin saman Maiduguri cikin mawuyacin hali. Ba ta gaya wa kowa tana tafe ba balle a san da zuwanta a zo a dauke ta, sannan ba wayarta a hannunta ta baro ta a kan gadonta. Duk da cewa ta haddace lambar Fulani, amma ta ga gara ta bi motar kasuwa ta karasa Askira, tunda akwai kudi isassu a hannunta.
A nan airport ta samu wani mai taxi yana faman binta da nacin tambayar ina zaa kai ta? Ta ga cewa, zuwa tasha da neman motar Askira karin wahala ne a gare ta, ga shi da ma ta yi matukar jigata, sai ta juya ta ce da shi,
Nawa zan ba ka ka kai ni har Askira?
Mai taxi ya yanko kudin da a tunaninsa ko rabinsu ba za ta biya ba. Amma sai ya ga babu musu ta amince. Ya bude mata kofa ta shiga ya rufe, ya ja mota suka naushi hanya.
******
ASKIRA EMIRATE
Lokacin da suka shiga garin Askira magriba ta kawo kai. Ita ta dinga nuna masa hanya har kofar fada. Ya ajiye ta ta mika masa duka dubu goman, sannan ba tare da ta kara cewa uffan ba bayan godiya, ta durfafi cikin gida.
Amma me? Tana saka kafa a soro na farko hajijiya ta soma dibarta, ga yunwa ga wahalar zaman mota. Ga wani irin masifaffen ciwon kai da ke sakadarta, taku biyu ta yi a soron farko Fadawa na zazzaune sai gani suka yi mace ta fadi a wajen, sakamakon kafafunta da suka kasa daukarta, duhun yunwa da na hajijiya kuma suka mamayi ganinta.
Taimakon Allah ne kadai ya kawo ta Askira lafiya.
Fadawa biyu sun shaida ko wace ce, kasancewar cikinsu akwai direban fada da ya ke kai su El-Kanemi. Cikin kidima suka kira bayi mata, su uku suka dauke ta ranga-ranga sai Unguwar Fulani Bilkisu.
Ba aladar Askirama ba ce bin dakunan matansa, amma Fulani Hibbani wadda ita ce mai girki, sarkin gulma da daukar zance ta shigo yanzun nan ta same shi yana cin abinci, kamar ta manta shi din ne ta ke magana da shi, tsabar gulma da ke cinta.
Mai Askira ashe abin da Yareema ya yi ke nan? Ya sako yar Bilkisu bayan ya yi mata shegen duka? Ta dawo rai a hannun Allah Anya shi ma ba giyar yake sha ba kamar matar.
Sauran maganar makalewa ta yi a bakinta ganin wata irin zabura da Askirama ya yi. Kafin ta ankara kuma ta tsinto shi a bakin kofa bayan ya saka takalminsa na gashin dawisu.
Fanna tare da dukkan kuyangin Fulani suna kan Saade, sai firfita suke mata bayan an samu ta farfado, tana kwance shame-shame bisa cinyar Fulani, tambayar duniyar nan Fulani ta yi mata, amma ta ki cewa komai. Fulani ta soma fusata, amma ta yi kokarin hadiye fushinta.
Ba za ki gaya min ina Yareeman ba? Ya san kin taho? Ke da wa ki ka zo? In sakinki ya yi ki yi mana bayani.
Kallo daya Fanna ta yi wa sauran kuyangin suka hau darewa suna barin falon, ta yi hakan ne ganin irin rikicewar da Fulani ta yi har ta manta cewa suna tsaye. Ko sakin Saade aka yi ba za su so a ji ba, a wannan gidan na gulma da jiran kiris a kan duk wani abu da ya shafi uwargijyarta.
Gyara kimtsi kimtsi gyara Zakin Askira.
Suka jiyo kuyangi na fadi daga waje, tabbacin Alanguburo ya durfafo unguwar da kansa. Kamar kiftawar ido kuma sai ga shi a kansu, sabida saurin da ya shigo da shi ba irin tafiyar sarauta da yake yi ba.
Lafiya Bilkisu? Me ya faru?
Ya tambaya cikin matukar kidima yana kallon kumburarriyar fuskar Saade da ta hade ta cakude ta yi jajir.
Wa ya kawo ta? Ina Yareeman? Dukanta ya yi?
Muryarsa ta karye gabadaya cikin debe tsammanin abin da Hibbani ta gaya masa.
Fulani Bilkisu ta yarfar da hannu, ta ce, Wallahi Allah ban san komai ba. Yadda ka ganta ni ma haka na ganta. Na kuma yi tambayar duniya ta ki ce min komai.
Jikinsa har rawa yake ya ce, Bari in kira shi a waya, amma in ya tabbata abin da aka gaya min ne zan sa kafar wando daya da Yareema.
Yana kokarin kiransa ne sai ga kiran Yareeman ya shigo. Ya amsa wayar ba tare da ya ce uffan ba.
Daga can bangaren Yareema ya ce cikin wata irin murya da Askirama ya kasa gaskatawa ta Sagirunsa ce.
Alanguburo, Allah Kawun jo (Allah ya kara maka yawan rai) a taimake ni a gaya min ko Saadatu ta zo Askira???
Kamar ba zai yi magana ba, amma tabbas yana son amsa guda daya kwakkwara daga bakin Yareema.
Ka fara gaya min abin da nake son sani, sakinta ka yi?
Yareema ya wani irin girgiza kai, tamkar Askirama na ganinsa, gumi ya wanke masa fuska, muryarsa na hardewa ya ce, Babu saki tsakani na da Saadatu har abada! Babu wulakanci tsakanina da amanarka har abada. Sai kauna da soyayya mara yankewa domin na samu fiye da abin da ka kwadaita min samu cikin aurena da Saadatu
Na je in kai resignation letter ga V.C in cike takardu in dawo mu taho tare sabida wata yar matsala da na samu wajen aikin nawa, kafin in dawo sai sai sai.
Ya kasa karasawa. Ambatar sunan mahaifiyarsa a wannan gabar ya san daidai yake da raurawar igiyar aurenta kamar yadda ya tabbata nasa auren yana rawa a halin yanzu, in har komawar Saade gida ya tabbata kuma ya je kunnen Askirama.
Wata tsawa da Maimartaba ya daka masa sai da ta hautsina gabadaya kayan cikinsa, Ba za ka gaya min abin da nake son sani ba? Sakinta ka yi ko aah?
Yareema ya kifa kai jikin kujera ya saka kuka kamar Mai Askira na gabansa.
Ban sake ta ba wallahi ban sake ta ba Ya Gumsu ce ta kore ta, kuma Uche ya gaya min har dukanta sun yi. Im on my way nowto Askiratunda alhamdulillahi ta iso gida.
Waye ya gaya maka ta iso gidan? Ka fada wa Babarka ta share dakin Saadatu ta zauna, don nata dakin na rufe shi daga yau.
Kai kuma bana bukatar ganinka gabana ka je ta aura maka duk yar uban da ta ke so.
Yareema kadan ya rage ya zauce, bai iya sauraron bakaken maganganun Askirama ba ya ji sallamar Ya Gumsu da Aunty Daja.
Ya Gumsu ta dube shi ta kyabe baki, ta ce, Yanzu sabida na raba ka da wannan jarabar shi ne ka ke yanka wannan uban gumin? Sannu tattabara sarkin soyayya. Ai da ma waadin watanni uku muka yi da kai za ka mayar wa uwarta yarta yadda ka karbe ta. To na ji shiru, shi ne na zo ni da kaina na sake ta, ka gaya min hadisin da ya ce ba ta saku ba.
Aunty Daja ta karbe, Ban da abinka Yareema, uwarka gata ta ke maka, yanzu aure na neman ci gaba ake yi ba na komawa baya ba. Kamar ka Yareeman Askira mai jiran gado ka rasa matar aure sai agolar gidanku? Ban da uwarka tsayayya ce ai da yanzu labari ya sha bambam.
Bai san sanda ya kai mata kutufo ba, ta yi maza ta kauce ya naushi iska. Ya daga ragaitattun idanunsa ya dube ta.
Aunty Daja ki ke ko wa? In uwata za ta shiga hurumina in kyale ta ban da ke wallahi. Na auri agolar tunda ke kin auri Minista ina ruwanki? Agolar na ga ta fi dacewa da rayuwata, sai ki zuba ruwa a kasa ki sha kun kore ta kamar yadda Askirama ya kori uwata.
Bai ankara ba ya ji hawaye na son zubo masa, don haka ya tashi ya bar wajen. Ko a jikin Ya Gumsu, ta ce, Ya dade bai kore ni ba, tunda ya auri uwarta na kara gane kansa? Sau dubu gara min tubabbiyar nan a kan diyar Bilkisu. Dadin abun ina da inda zan zauna ko ba gidanka ba. Kuma ba zan bar gidan nan ba sai ka rubuta takardarta ka ba ni
Yareema bai tsaya ba ya nufi motarsa. Yana ji Aunty Daja na lallashin Ya Gumsu, ta yi hakuri tunda dai sun kore ta ba sai ya yi saki ba, ko ba komai sun kunsawa Bilkisu bakin ciki, kuma in tana son yarta ba za ta barta ta dawo ba a yadda suka ci zarafinta.
Yanzu abin da ya kamata ki maida hankali a kai shi ne, nema masa auren Hajjaju.
Ya Gumsu ta balla mata harara tana zama cikin royal chairs din Saade, ta ce, Ke ma kina wasa ne, wa zai karba masa auren a halin yanzu na taba yar mowa? Da na sani ma ban kore ta ba, dagewa na fara yi aka auri Hajjajun, bayan ta shigo sannan mu san yadda zamu yi da ta gidan, amma yanzu na tabbata na bata goma ne daya ba ta gyaru ba. Tunda ki ka ji ya ce ubansa ya kore ni.
Ya Gumsu ta fada cikin damuwa, wadda ba ta karasa har kasan ranta ba.
Aunty Daja ta yi tsaki, ta ce, Haba Gumsun Askira, ke ce fa uwar Yareema, uwar Ya Maira, masarautar Askira taki ce ke da yayanki, kin taba jin an saki Gumsun gari uwar iyali?
Ai sai dai ya yi fushinsa ya gama ya sauka, amma ba sa saki, shi ya sa na tabbatar miki yaron nan ba zai saki yar Bilkisu ba, mu dai yi kokari ya yi aure na shiga tsara ki manta da wata yar Bilkisu. Kishiya kadai ta ishe ta.
Hum! In ji Ya Gumsu. Ba ta san irin bayanin da za ta yi wa yar uwarta ba, ta gane cewa, kishi da BAGGARA ba abu ne mai sauki ba, sai dai ita kishiyar ta yi ta jin jiki tana kunsar bakin ciki har karshen rayuwar ta.
Ta yadda Mai Askira zai yarda ya karba wa Yarima auren yar sarkin Bauchi yanzu shi ne ba ta sani ba. Babu ubansa Sarkin Askira kuma wa zai bashi auren? Ko ita za ta je ta nemo masa waliccin auren yar sarkin Bauchin da kan ta?
Ta fahimci ta lalata chance dinta ne kawai na kara auren Yarima da korar Saade da dukan ta. Da ta sani ma kafewa ta yi the other way kan cewa, tunda ta bada dama ya auri zabin ransa da zabin ran mahaifinsa, to ita ma ya auri zabinta. Amma yanzu ta tabbata kwabarta ta gama yin ruwa.
Don haka ta kasa zama gidan Yarima kamar yadda ta yi niyya, ta bi Aunty Daja gidanta tunda shi ma ya fice ya bar musu gidan, ta kuma tabbata Askira ya nufa.
Uche dake shigowa a lokacin yana ganin fitar su ya je ya kulle koina na gidan.
Tana kallon kiran Maimartaba yana ta shigowa wayar ta, amma ta yi funfurus ta ki dagawa sabida tsoro. Ta san ba zai taba sakinta ba, amma in ka tabo shi hukuncinsa ba shi da dadi.
Suna tafe a hanyarsu ta komawa gidan Daja, ta gaya mata Maimartaba yana ta kiranta, Daja ta ce,
Ki dauka a yi ta ta kare.
Ta kuwa daga ta hanyar cewa,
Allah Kawun jo (Allah ya kara maka yawan rai). Ina kan layi.
Muryar Askirama mai zurfi da kauri (husky) ta bakunci kunnuwanta.
Bana zaton Yareema ya gaya miki sakona. Cewa na yi ki share dakin Saadatu ki zauna, don ba ki da daki yanzu a gidana.
Cikin gatsali ta ce, Allah ya kara yawan rai wani abu aka ce na yi? Ziyara fa kawai na kawo musu. Ta fashe da kuka, kukan da daga ji za ka san bana gaskiya ba ne. Don takaici Mai Askira sai ya kashe wayarsa, kada ya yi abin da zai zo daga baya yana nadama.
Ya Gumsu ta shiga bandaki a washegarin ranar za ta yi wanka. Ta sa kafa a cikin bahon wanka ba ta lura da jikakken sabulun da ke ciki ba, kafarta ta sauka a kan sabulun ta zame ta tafi gabadaya ta yi wata irin mummunar faduwa. Faduwar da sai daukanta aka yi ranga-ranga zuwa asibiti baki ya karkace yana ta fidda kumfa.
Idan Ubangiji ya nufi alamari, bawa ya nuna ja da hukuncin Ubangiji, sai Ubangiji ya barshi da dabararsa, amma idan Ya ga dama talalar da zai maka ta dare daya ce. Wani rabon sai ya kawar da kai dagadoron duniya gabadaya. A ci gaba da rayuwar babu kai, babu mai tuna ka da kyakkyawar zuciya balle ya yi maka addua.
Don haka Gumsun Askirais lucky that shes alive a daidai lokacin da Saade ke jikin mahaifiyarta tana ta kelaya amai kamar da bakin kwarya.
Tunda ta iso ta ke zazzabi da ciwon kai, kafin wayewar gari kuma sai haraswa, ta kasa cin komai, gabadaya ta fige ta yi zuru-zuru. Fulani da Fanna suna tsaye a kanta tun jiya. Shi ma Maimartaba ba ya rufa awa guda bai kira Fulani ya ji me Saade ta ke ciki ba.
A karshe ya turo likitar matan gidan don ta zo ta duba ta a san takamaimai