Showing 81001 words to 84000 words out of 117873 words
ke sauke ajiyar zuciya tana tambayar kanta, wannan shi ake nufi da auren ke nan? Su dunkule su zama abu guda in every aspect kuma marufar sirrin juna? Sirrin da yafi karfin kwatance ko fadar sa ga wani. As a university student ba za ta ce kwata-kwata ba ta san manufar aure ba duk da babu wanda ya taba zaunar da ita ya gaya mata, duk sakewar da ke tsakaninta da Fulani magana irin wannan ba ta taba hada su ba. Baggara akwai kunya tamkar Fulani suke, sai dai kuma sun fi Fulani ilmin addini.
Sai goshin asubahi ta samu barci, kuma ko na minti daya Yarima bai yarda ya raba ta da jikinsa ba. In ma ta yi kokarin zamewa tsaf cikin barcin zai kara kanainaye ta. Tun tana jin kunya har ta gaji ta yi barcin ta a jikin sa. Ko don wannan turaren nasa mai dadin kamshi da sanyaya zuciya za ta so su wayi gari a haka.
Daren yau bakidayansa wani yanayi ne da ba za ta taba mantawa ba a tarihin rayuwarta. Ba ta maraba da auren Yareema Sageer, ba ta kuma taba mafarkin faruwarsa ba, amma daga daren jiya zuwa yau sai ta ji dama su dauwama a haka! Ba tareda wani dan adam ya kara ratsa tsakanin su ba.
The moment is awesome because its strange but pleasant ga Saade, don haka image din ya tsaya a kwakwalwarta. Hoton ta makalkale cikin jikin Yarima Sagir, ya kasa bacewa dagascreen na zuciyarta. A haka aka yi kiran assalatu.
Da yake ba ta dade da samun barcin ba, ko motsi ba ta yi ba. Har Yarima ya mike ya je toilet din da ke makale da dakin ya kammala abin da zai yi ya fito Saade ba ta da alamar farkawa. Duk da bahagon halin Ya Gumsu, a baya na gaya muku cewa yayanta akwai sallah.
Sai ya tsaya a daidai fuskar Saade yana taje jikakkiyar sumar kanshi. Yarfin ruwan a fuskarta ya sa ta bude ido kadan, sai idonta cikin na Yarima. Da fari ta dauka a dakinta ta ke na Abuja, amma ta san Uncle Yarima bai taba shigar mata daki a irin wannan lokacin ba.
Ta sha ganinshi da pajamas ko a gidanshi, amma ya kan daure tsakiyarta da igiyar jikinta, amma yau bai daure ba, physique chest dinsa dauke yake da suma a kwance luf, wanda hakan ya sa ta saurin kauda kanta. Sai kuma ta tuna wai fa ashe su din yanzu miji da mata ne.
Ajiyar zuciya ta kwace wa Saade daga kwancen da ta ke. Har sai yaushe kwakwalwarta da zuciyarta zasu karbi reality na kasancewar ta matar Yarima Sagir ne?
Yareema ya mika mata hannu da nufin ta kama ya taimaka mata ta tashi, amma sai ta juya daya barin ta rabu da shi.
Ya ce, Tashi Saadahtou mu yi jamin sallah kina makarar da ni.
Saadatu ta yi shiru, ta ya ya za ta iya gaya masa cewa, period ta ke yi?
Ba za ki tashi ba?
Ya fada for the second time yana mamakin abin da zai hana ta yin sallah, sai kuma ya tuna mace ce, don haka ya juya ya tada sallarsa.
Har gari ya soma haske Yarima na sallah, ita kuma ta kasa komawa barci. Tunanin rayuwar da za ta riske ta a gaba ta ke yi. Tunda yanzu rayuwarta ta zama dependent upon Yareema. Sai yadda yayi da ita.
A baya shi din guardian ne, amma a yanzu matsayinsa ya zarta na kowa kenan including iyayenta. Wannan ba karamin nauyi ba ne aka dora mata, wanda ba ta san ya ya za ta yi da shi ba.
Ta duba ta laluba cikin tsokar zuciyarta ko za ta ga SO ko akasin sa a kan Yareema Sageer? Amma sai ba ta samu ko guda dayan su ba, babu soyayya haka babu kiyayya tsakanin ta da Yarima, sannan daga daren jiya zuwa yau alamuran Yareema Sageer masu ban mamaki ne da suka soma rikita hankali da nutsuwarta.
Tana nan kwance har Yareema ya gama sallolinsa, ya sunce ya shiga wanka. Da ya fito ya tambayi Saade,
Manyan kaya zan sa ko kanana?
Ta yi masa shiru.
Ya ce, Alright. Bari kawai in sa kanana, ban sani ba ko saboda tsufana ne ba kya so na.
Ta juya masa baya bata ba shi amsa ba. Ya gama sanya kayansa riga da wandon BALANCIAGA ruwan goro masu ratsin black. Sai ya fito a Georgeous Prince dinsa. Kai bazaka ce ya taba aure ba.
Ya hawo bisa gadon daidai inda ta juya fuskarta yau zaki sha tea irin wanda baki taba shan irin sa ba.
Sai ta rufe idanun ta gabadaya daga barin kallon sa, don ji ta yi zuciyar ta na racing.
A cikin dakinsa akwai karamar butar dafa shayi, ya jona kettle din bayan ya yi hade-haden shayinsa na naa-naa da girfa, yadda Saadatu ta juya masa baya ta ki juyowa yana taba ransa, sabida shi dai ba haka matarshi ta sabar mishi ba. Da sun wayi gari da ta soma haba-haba da shi har sai ya ce ta dame shi.
Ya zuba kakkamsan shayinsa a dan karamin farin kofin shayi na karau, ya zauna a gefen gadon daga daidai kafafunta yana sipping a hankali.
Kamshin shayin da yake sha duk ya cika ta, ya kuma tayar mata da appetite na abinci, sai lokacin ta tuna rabonta da abinci. Tun na safiyar jiya da Hanne ta matsa mata ta ci lomar sinasir guda biyu. Akuyar cikinta har wani irin kugi ta ke yi cikinta na murdawa da yake tana da ulcer kadan tun a El-Kanemi. Dole ta mike ta nufi toilet ta yi brush, ta yi wanka ta kuma nemi pad din da za ta canza ta rasa.
Kayan jikinta ta maida, wato doguwar riga mai bin jiki ta roba wadda ake sa wa a kasan laffaya (underwear), ba ta nada laffayar ba ta fito gashin kanta da ya sha kitson nan jelunan sun kwanta lambam a wuyanta. Kai tsaye ta nufi kofa don ta tuna Raheema ta gaya mata ta sa mata pad din a lokar jikin gadon dakinta da suka kai ta jiya.
Amma me? Kofar a kulle gam, kuma ya zare mukullin jiki.
Ta juya a sanyaye ta dube shi suka hada ido yana kurbar shayi, ya ga damuwa karara a tare da ita. Ya ajiye kofin hannunsa a kan lokar gadon ya taso a hankali ya iso gabanta.
Hannayensa duka biyu ya zuba a cikin aljihun wandonsa, ya dube ta keenly, murya raunane ya ce,
Me ya sa ki ke guduna ne Saadatu?
Ta sadda kanta kasa.
Ya ce, Ki kwantar da hankalinki kin ji, za mu zauna mu yi magana ta fahimta kafin mu tafi Abuja, yanzu nan da awa guda za ki ga gidan nan ya cika, don haka ki yi hakuri ki ba ni one hour in yi ta tare da ke, kada ki bar ni ni kadai.
Murya can kasa kamar an shake ta ta ce,
Zan dawo, abu zan dauko.
Gaya min ko mene ne in dauko miki, amma ba za ki bar dakin nan ba sai na miki umarni.
Kamar ta fashe da kuka, ta ce, Ba ka san inda yake ba, besides abin na mata ne.
Yarima ya ce,
Okey. I can relate. To mu je tare, kada ki yi min wayo ki shige daki ki rufe.
Ta turo baki, ta ce,
Na yarda. Sannan ya bude kofar suka sauka zuwa downstairs.
Bayin da aka ba su suna ta hidimar tsaftace gidan suka wuce su bayan sun gurfana sun yi gaisuwa, yana kallo ta bude lokar ta dauko ledar sanitary pad ya sa ta a gaba suka koma upstairs dinsa.
Suna shiga dakin ta wuce toilet, kafin ta fito Yarima ya zuba mata shayin da ya sha yana firfita mata between two cups. Ta fito tana taku a hankali kamar mara gaskiya ta zauna a kan sofa bed can nesa da shi ta zuba uban tagumi da hannaye bibbiyu.
Yareema ya taso zuwa inda ta ke, ya rusuna ya mika mata shayin, sannan ya zauna daidai kafafunta, kai ka ce ita ce Yariman ba shi ba. Ta sa hannu ta karbi shayin don ba ta yi wa yunwa fulako.
Ganin yadda ta ke shan shayin da sauri duk da zafinsa ya sa shi tambayarta.
Tun yaushe rabonki da abinci?
Saade ba ta ce komai ba, sai shan shayinta ta ke yi, kan ka ce me ye wannan ta zuke shi. Da gaskiyar sa bata taba shan shayi mai dadin nasa ba da wartsake makoshi. Ya mike zuwa ga bed side fridge dinsa, ya dauko danyar madarar oldenburger mara sanyi, ya zo ya bude ya tsiyaya mata a tambulan ya zauna dab da ita ya kai kofin bakinta.
Da farko kunya ta ji, amma kuma an ce mata suna son kulawa irin wannan daga mazajensu, kulawar da ba duk maza ke iyawa ba sabida girman kan su. Sai ta ji ta kasa tankwabe wannan kulawartasa, ta bude baki tana shan madarar sosai daga hannun Yareema, sai da ta shanye madarar tas, zai kara mata ta ce a hankali,
Ya isa.
Sai ya ajiye kofin ya juya ya kwantar da kai a cinyoyinta. Hannayensa zagaye da kugun ta.
Now, tell me Saadatu, why dont you love Sageer?
Ta rasa inda za ta sa kanta, sabida Uncle Sageer ya yi kwanciyarsa akan cinyoyinta, ya mike kafafunsa bisa sofa din.
Uncle Ta fada a hankali very upset and unease. So take ta ce ya daga ta kada wani ya shigo, amma kunya ta hana ta.
Kada ki kara ce min Uncle, ban san ta ina na zama Uncle dinki ba. Ni ba kanin Fulani ba, ni ba kanin Baban ki ba...
Ni, (ya nuna kan sa) ni ne SAGEER kawai, Sageer Askira, ba ni da wani lakabi bayan wannan.
Ya sa tafukan hannunsa a fuskarta.
Very smooth and supple. In ji dai ba shafe-shafen zamani ki ke ba? I love natural skin shi ya sa nake son Sultana.
Ai ba ta san lokacin da ta ture kansa daga cinyarta ba ta mike. Allah ya so ta bai cire mukullin daga jiki ba, ta bude kofar ta yi ficewarta.
An ce ko babu SOYAYYA kishin cikin AURE daban yake. Haka ta wuni ranta a bacea kan yar maganar da Dr. Sageer ya fada akan Sultana, yayin da Dr. Sageer ya wuni cikin matsanancin nishadi da bai taba tsintar kansa a ciki ba.
A yadda ya fahimta insha Allahu ba zai sha wahalar samun soyayyar Saadatu ba, tunda har ta fara kishin matarsa. Dama ya fada ne don ya ga reaction din ta.
Ya canza kayan jikinsa zuwa Jabba da hular data dace da kalar kayan wato deep-brown, ya fesa turarensa ya fito. Tuni bayi sun cika tebir da abinci naui-naui. wanda aka kawo daga unguwar Fulani Bilkisu.
A cikin bayin da Maimartaba ya ba su akwai wata kuyanga Sadiya, burinta kawai Yarima ya yi kwarkwara da ita ba tun yau ba, don haka ba karamin dadi ta ji ba da aka hado da ita cikin hadiman gidansa.
Yanzun ma yana fitowa ta fadi gabansa,
Gyara kimtsi da kyau, lafiya dan zakin Duniya lafiya dan malafar duniya, lafiya dan mai fada da cikawa lafiya dan mashasha lafiyarka dama da hauni mai nasara zauna daidai dan bawan Allah zauna daidai dan masu alheri.
Yana zama bisa dining table ba tare da ya dago ido ya dube ta ba, ta hau yi masa firfita da maficin gashin Dawisu tana ci gaba da zubo kirarin. Daidai lokacin da Saade ta bude kofar dakin ta fito cikin wata irin sassaukar kwalliya ta riga da zane dark blue na yadin karen miski wanda ba a samunshi koina sai gidan sarauta.
Wani kallo da ta sakar wa Sadiya ya sa ba shiri ta juya tana mata nata kirarin.
An fito lafiya uwar masu gida, zauna daidai uwar alheri taka lafiya matar Zakin duniya.
Saade ta kira sunanta a hankali kafin ta wuce ta ce,
Sadiya!
Kada ku kara zuwa nan in ba ni na kira ku ba. Lokacin aikinku daga karfe shidda ne zuwa bakwai na safe, da kun gama jera abincin karin kumallo shi ke nan na sallame ku.
Sadiya ta amsa a matukar ladabce, sannan ta fice.
A ranta tana fadin, Ta Allah ba taki ba. Insha Allahu ni ce Sa-dakarsa ta farko duk boyon da za ki yi masa, me ya kai ki auren Basarake in kin san kishi gare ki?
Yarima yana jinsu kansa a duke yana danna wayarsa, sai ya ji murmushi ya kwace masa. Ya dauka zuba masa abincin ta fito ta yi, amma tunda ta kori Sadiya sai ta juya ta koma daki abinta ta barshi a nan zaune.
Sai ya ji ya kasa ci. Ya zuba abincin daidai misali a kan plate, ya dauka ya bi bayanta.
Ta zauna kenan a bakin gado ta yi tagumi, wadannan yammata da aka cika mata gida da su kullum suna sintiri a gaban Yareema yaya zata yi da su? Ta isa ta ce zata zauna babu kuyanga? Ko cewa zata yi a kwashe su a kawo mata tsoffi? Kowa ya ji hakan a take zai fassara ta da kishi. Ita kuma ta san ba kishi take ba tsoro ta ke ji, tunda ta san wa aka aura mata. Tana wannan sake-saken sai gani ta yi tattausan hannun Yarima mai daure da agogon ‘Swatch Blustery’ ya miko mata plate cike da soyayyen dankali da sauce din koda da hanta.
Saade ta dago ido a hankali ta dube shi. Ya daga mata gira, ya ce,
Karbi.
Sai ta kasa tankwabe wannan kulawar a karo na biyu. Ta sa hannu ta karba cike da jin nauyi, ita ba ta ba shi ba shi ya dauko da kansa ya kawo mata, ta tuna wane ne Yareema Sageer a masarautar Askira gabadaya da yadda kannensa da yayyensa duka ke sonshi da girmama shi. In ta ce ba ta ji wani iri a ranta ba kan rashin kyautawar ta ta yi karya, sai ta ji somehowkamar abin da ta ke yi ba daidai ba ne. Don haka ta motsa dan bakinta a hankali yana shirin ficewa daga dakin tace.
Uncle kai ba za ka ci ba?
Ya juyo gabadaya ya fuskance ta sabida ya tsani wannan Uncle din da ta ke ce masa.
Ya ce, This will be the last time da za ki sake kirana Uncle tunda dai ni ba kanin Fulani ba ne, idan ba za ki fadi sunana ba ki sa ma min wani. Amma ki ka sake ce min Uncle Allah zan cire hijabin da ke tsakaninmu Saadatu, wanda ke sa ki yi min kallon kanin Babanki.
Maganar ta bata dariya amma bata yi ba.
Ya juya ya fice yana cewa, Mun tafi Ta-Sani ni da Awaisu.
Murmushi ya subuce wa Saade, kowanne irin hijabi ne tsakanin nasu? Oho! Ta maida hankali ga cin abincinta, kunnenta har motsi yake sabida yunwa da dadin abincin wanda daga jin kamshin sa ta san daga unguwar Fulani Bilkisu yake.
Yareema da Awaisu sun je sun gaida Alhaji Kyari, bayan sun gaida Maimartaba, sannan suka wuce cikin gida, unguwar Ya Gumsu suka fara zuwa suka kwashi gaisuwa, ta amsa musu kadaran-kadahan sai kallon Yareema ta ke da wutsiyar idanu kamar mai son gane cewa ya bi umarnin ta ne ko aah? Ya maida Saadatu cikakkiyar matar sa?
Tsoronta Allah tsoronta ranar da Sageer zai hada shimfida da Saadatu, don ta san daga ranar ba za ta sake gane kansa ba,kamar yadda ba ta kara gane na ubansa ba tunda ya auri uwarta, kai ba ita kadai mahaifiyarsa ba, har waccan baturiyar tata ta kare. Ita ta san sirrin matan BAGGARA, ta san ta inda Fulani Bilkisu ta bi ta birkice musu kan miji kenan. Allah kadai ya san iya abubuwan da ta koya wa yarta, da sirrin mallakar da ta dankara wa Saaden(Allah Sarki ZATO. Mu kasance masu kyautata zato ga yan uwanmu musulmi, in ba haka ba za mu kare ne da daukar nauyin zunubansu. TAKORI).
Daga wajen Ya Gumsu suka nufi unguwar Yaakirjiloma, Mairam Murjanatu na shirin tafiya tare da yayanta, tana ganin Yarima faraarta ta fadada, ta ce,
Ka ga ango sha kamshi. Angon Saa da Aisha-Sultana. In ce ko an rago min