Showing 24001 words to 27000 words out of 89788 words

Chapter 9 - ALHUSSAIN Complete Hausa Novel

23 Aug 2025

380

kurma ihu, idona ya ciko da hawaye, cikin zuciyata nake rayawa ko dai Yaya ya daina zaman wurin nan ne saboda ni, tunda yace na bar zuwa wurinsa naƙi, lokaci guda hawayen da nake ƙoƙarin dannewa suka sami nasarar gangarowa, nasa hannu na goge, shikenan yanzu yay min nisan da bazan kuma tozali dashi ba kenan, yanzu nasan yana can yana shan tabarsa, naji zuciyata kaman zata fito waje saboda ɗacin da take min.
Sai kuma nayi wani tunani, Yayana zai iya tsere min ne a iya lokutan daya san zan iya zuwa wurinsa, amma tunda ba shi da ko'ina jazaman dare yayi zai dawo wurinsa domin kwanciya, Da sauri na buɗe jakana na ɗauko wata takarda da nai rubutu tun a gida mai ɗauke da taƙaitattun bayani kaman haka.
_ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya Yayana, don Allah idan kazo ka nemi waya ka kira ni, zamu bar garin kano mu koma abuja da zama, ina maka fatan alkhairi. Ƙanwarka Sabina._ sai daga can ƙasa na zuba numbobin wayana guda biyu, wayar da a daren jiya Baba ya bamu ni da Yaya Abba. Kangon na shiga na sami inda zai iya katari da ita daya shigo na soke a wurin. Tukunna na fito na koma cikin napep ɗin muka juya, damuwar duniya ta tarar min aka, gefe guda rashin sanin taƙamaimai halin da Yayana ke ciki, ɗayan gefen fargabr zamanmu da Matan Babana, daga Anty har Umma babu mai sona a cikinsu, ko me na tare musu oho, sai dai nafi alaƙanta hakan da irin son da Baba yake min shine yasa Anty ta tsaneni, ita kuwa Umma haushinta da ni sunyi zaman kishi da Mamana. har ƙofar gida ya ajeni, lokacin da naje driver'n mu har ya iso a cikin mota ƙirar Sienna mai azababben kyau, ta burgeni sose sai dai yanayin damuwan da nake ciki ba zai barni nuna jin daɗina ba a fili, amma mamaki na cewar motar mallakinmu ce bai barni ba. Ina shiga Gwaggo na cewa, "yauwa kin dawo". "ehh". Shine nace da ita a taƙaice ina goge hawayen gefen fuskana. Na wuce zuwa ɗaki tabi bayana da kallo tana karantar yanayin nawa. "ke lafiya kuwa, ko wani abun ya faru a makarantar ne na ganki a haka?". Gudun kar ta hauni da tarin tambaya sai nai maza na ɗau buta na faɗa toilet. Na wanko fuskana kana na fito ina ƙaƙalo murmushi, ina kallonta nace,
"Gwaggo wai har an fito". "ehh ke kaɗaima muke jira. ina tambayanki kin mani shiru baki bani amsa ba, nace lafiya naga kin dawo kamar wadda aka yowa akaina uwa da uba sun mutu lokaci ɗaya". "Gwaggo na biya ne munyi sallama da Farhana". tana taɓe baki tace, "uhmm shine idonki yay wannan jawur ɗin haka. to naga dai kashin awakai ma suna rabewa bare ku da zaku iya ziyartar juna a duk sanda kuka so...kai Wannan lokacin aurenku kwai lusin". Ƙarshen furucinta ya bani dariya wai looking zata ce shine lusin. Mu uku muka ɗunguma zuwa mota, Yaya Abba a gaba ya zauna, mu kuma muka shiga baya. Da la'asar muka isa Abuja, gidanmu a wani estate yake na manyan mutane, cikinsa baki ɗaya gidaje ne na alfarma, kai daka shiga kaga estate ɗin masu muƙami, a gida na tsakiya mai lamba uku mukai horn, aka buɗe mana tangamemen gate ɗin gidanmu, ya ilahil alamina, Aljannar duniya kenan, mai karatu karka so kaga haɗuwa da tsaruwar gidanmu, wai tun bamu shiga cikinsa ba kenan, ta ko'ina fitilu ne ke haskawa, yayin da wasu haɗaɗɗun flowers ke mana maraba. Part part na gidan ya kai kusan 7, nan Baba ya fara mana lissafi, part ɗaya nasa, ɗaya ni da Gwaggo, ɗaya na Anty da ƴaƴanta, ɗaya na Umma da nata yaran itama, sai na Yaya Abba, sai kuma na masu aiki, sai ɗayan da babu kowa. Nan ya kuma zagayawa damu zuwa wajen parking lot, wayyo Allah nah, wasu tsadaddun motoci ne cikin wata rumfa kamar a ƙasar turai, in taƙaice muku dai ginin gidan kamar a saudiya. Baba ya nuna min wata arniyar mota fara mai tintend glass ƙirar lambogini, ya juyo ya dube mu ƴaƴansa mu shida, yace" ina kike Sabina". Na matso kusa ina faɗin, "Gani Baba". Maƙullin mota ya miƙo min, nasa hannu na amsa, abinda nake rayawa a raina shi kuwa ya tabbata. Domin buɗar bakin Baba cewa yay dani, "wannan farar motar taki ce Sabina". Kan ubancan, ai ban san lokacin dana buga tsalle nai sama na dire ƙasa ba, na kaiwa Gwaggo wata muƙura na ƙanƙameta, saura kaɗan ya rage ta zube ƙasa na riƙo kayata, daɗiɗin duniya ya gama baibayeni, ihun murna nake ina kwaranyowa Allah godiya daya mana wannan arziƙi, na sake ta na dawo wurin Baba, a kunyace naje jikinsa na rungume shi, adu'a nake masa da kuma tarin godiya, shima yasa nasa hannu ɗaya ya rungume ni yana sanya min albarka.
Hmm wani abun dariya sai kunga matan gidanmu, yanda suka kumbura kamar an hura baloon tana jiran fashewa, kowacce sai faman aika min da saƙon harara take, baƙin cikinsu na daɗa fitowa ƙarara, har Umma ta kasa danne zuciyarta tace. "to amma Alhaji ga sauran yara a gabanka sai ita ɗaya ne zaka ma kyauta daga zuwanmu, kuma kyauta ma harta irin mota mai shegen tsada, motar da sai a ƙasar turai ake ido huɗu da ita". cikin rashin nuna gane lissafin nata yace,"banda abinki Hajara ai cikinsu itace Babba, suma za'a basu amma ba yanzu ba". Baba na shiru Gwaggo tace, "to shi mai sunan Sahibina ba zaka bashi bane?". Baba yace, "shi da yake magajin gida Gwaggo, ai ragamar komai na hannunsa, da kansa zaizo ya zaɓa". tai wani murnushi na ƙulawar sannan tace,"auto yanzu naji bayani. Tunda ka gama da marayun ƴaƴana, can ta matsewa sauran, su samu ko kar su samu ko a katarina". Ta dubi Yaya Abba, cikin mutunci yau ake masa magana tace, "mai sunan Sahibina zo ka zaɓa ka dirje, kamin ƴan baƙin ciki su haɗiya zuciya su mutu ba suga arziƙinka ba. Hakan ba zai min daɗi ba sam".


_Hmm Ya kuke ganin zaman wannan gida zai kasance?_
_Ina Alhussain ya shiga?._
_shin ko zaiga takardar da Sabina ta bar masa?._
_Ko zasu ƙara haɗuwa?. idan da rabon zasu ƙara haɗuwa to aina?_

*Please Comment, Vote and Share.**AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(10)*
baba ya girgiza kai, a yanayin yanda Gwaggo tai magana fuskarsa ta nuna rashin jin daɗi, to amma babu damar yayi magana, dan yanzu zata dire masa tace dama shike ɗaure musu gindin zaluntar marayu, duk wani abu da suke da sanya hannunsa a ciki, shima dama ba ƙaunarmu yake ba, kuji fa, wai mu da ubanmu amma abu kaɗan zaiyi za tace baya sonmu. Ni dai da har yanzu daɗi bai gama saki na ba tuni na nufi motana na buɗe na shige ciki ina dubawa, shi kuwa Yaya Abba na daga zaune kan wata kujera ya zuba ido yana kallon abinda ake. Anty da ta ƙware wajen iya kissa nan da nan ta kawar da baƙincikinta ta hau borin tayani murna, Anty macece da ta tsanemu sosai ni da Yaya Abba, don da tana da ikon kawar damu da tuni ta aikata hakan, amma kuma fa duk wannan ƙiyayyar ta ƙware wajen iya kissa da makirci, domin bata taɓa nunawa tana ƙinmu a gaban Baba, Ta inda tafi Umma wayo kenan, domin ita Umma agaban kowa nunawa take bata son ƴaƴan mijinta. Shi yasa Baba idan zaka kwana dubu kana ce masa Anty tayi Laifi baya yarda, Ita kanta Gwaggo da ba ta yarda da laifinta, saboda Anty makirar macece, Kuma ko laifi tayi to tasan hanyar da zata wanke kanta, amma itama tun a inda Gwaggo ta rafkowa lamarinta, ranar da tace Ya Abba ya shigar Mata ɗaki. Anty ta taho inda nake tana ta fara'a tana ce min, "Masha'Allahu mota tayi kyau sosai, inye su Sabina an zama ƴan gayu, lallai arziƙi mai daɗi, gaskiya na tayaki murna wallahi, Babanki ya gwangwajeki ƙwarai matuƙa, duk randa aka fara driving ni za'a fara ɗanawa, sai ki masa adu'an Allah ya ƙara wadata arziƙinsa ya kuma kare shi daga sharrin maƙiya mahassada, kema kuma Allah ya rabaki da sharrin ƙarfe". Duk tana faɗaɗa fara'arta take tayani murnar, wanda sam bai kai har ƙasan zuciyrta ba. hmmm amma kunsan me? saboda baƙar mugunta kunsan kuma abin ba don Allah take ba, hannunta na kan wuyana tana bani wani mugun mintsini, da naga tana neman raunana min wuya sai na fito a motar ina yaƙe domin shegen mintsininta ya shigeni, na sauke hannunta daga wuyana na riƙe a hannuna, inama ta murmushi nake cewa, "ameen Anty na gode sosai". Na faɗi hakanne saboda Baba dake tsaye a wurin, nima kuma cike da mugunta na ganyarata ma ta mintsini a hannunta dake cikin nawa, ba shiri ta janye hannunta tana yaƙe da dukkan alama ya shigeta kamar yanda nata ya shige ni. Na juya wurin ƙannena nace su zo su ga motar, dan suna tsaye ne kamar gumaka, to dake kowacce ta ɗauko halin uwarta haka suka zo suna leƙa motan suna tayani murna, fuska babu yabo babu fallasa, ni dai a raina nace oho muku, ni bana riƙo da irin yanda kuke min, kuma Allah ya ganar daku. Sai da Baba ya gama nuna mana komai na gidan sannan kowa ya wuce part nasa. Ina shiga side namu na raka Gwaggo ɗakinta, na nuna mata yanda ake amfani da duk wasu abubuwa musamman ma na banɗaki, ni ɗin ma ba kowanne abu na san ta kansa ba sai dai na jarraba musamman Ac. Duk wannan abun gwananintar da nayi ma ta ban burgeta ba, Sai da tayi min tsiyarta da ta saba. Harda cewa ai ruwan zafin hita da akasa yake zuba a famfo da gangan aka saka don ya salluɓe ma ta fata ne saboda an san ba iya amfani zata yi da shi ba, to ita a cire shi kawai. ni dai bance ma ta komai ba, ita kanta dariyar ƙeta take min harna gama na fito. Ɗakina na wuce kai tsaye, ina shiga na hau cire kayana domin yin wanka saboda duk a gajiye nake. Wanka nayi da ruwa mai ɗumi sirke da turaruka masu ƙamshin gaske, da aka jere su a toilet ɗin, ban wani jima a ciki ba na fito, ina fitowa na shafa mai da kuma faran powder. closet na nufa na zage domin ciro kaya, cak na tsaya ina riƙe da baki na saboda mamaki, kamin na buga tsalle na kurma ihu saboda daɗi, ashe shiyasa Baba yace babu buƙatar mu taho da kaya, mu bada duk waɗanda muke da su, kayan na shiga dubawa ɗaya bayan ɗaya, shegun kaya ne na alfarma kamar wata amarya aka zuba min a ciki sunfi set 30, Kuma duk abayas sunfi yawa dama sune favorite nawa, ban san lokacin dana zube kan gado ba ina hawayen farinciki ina kuma kwaranyo Baba adu'a, oh ni Sabina ban taɓa mafarkin tsintar kaina a irin wannan daular ba, ko da kuwa a gidan miji duk kuwa da ina fatan samun miji mai yalwar arziƙi na halal, sai gashi ashe zanyi katari da shi tun a gidan ubana, lallai arziƙi na ubangiji ne, shike badawa da hanawa a duk lokacin daya so. Wata dark blue abaya na ciro mara nauyi na saka, sannan nabi lafiyayyan gadona na kwanta, nan take kuwa bacci yayi awon gaba dani. Bani na farka ba sai da ana sallan isha'i, da sauri na diro akan gadon tunawa da nayi banyi sallar magrib ba, ina toilet ina ta ma kaina dariya, Ƴar ƙauye an haye gado anji laushin katifa, naji daɗin baccin da ban saba yinsa ba. Ina zaune bisa sallaya ina karatun qur'ani sai naji landline ɗin dake aje a drowern gefen gado na ƙara, banma lura da zamanta ba sai ayanzu, na miƙe da sauri na ƙarasa don ɗauka domin nasan kiran baya rasa nasaba da Baba tunda dai shine yay mana connecting baici ace kowa na da numban kowa ba. Ina ɗagawa naji Baba yace, "ki fito parlo ki same mu". Na amsa masa da, "to Baba". Daga haka shi kuma ya kashe wayan. ina gyara zaman veil na fita zuwa parlo, yanda na sami duk ƴan gidan kowa a zaune kan kujera yaran kuma a ƙasa, na san magana ce mai muhimmanci Baba ke so yayi damu. wuri na samu na zauna nan ƙasa da gefen ƙafar Gwaggona, sannan na ɗago da kaina na gaida su Umma. Anty na washe min haƙora ta amsa min gaisuwar tawa, saɓanin Umma data amsa min a ciki-ciki kuma fuska a turɓune. Baba yay gyaran murya yace da Yaya Abba yayi adu'a. Bayan gama adu'a Baba ya fara magana akan abinda yasa ya tara mu, maganar duka akan nasiha ce da kuma faɗa akan zaman lafiya,. Ƙwalla na taruwa a idona nace, "insha'Allahu Baba zaka same mu da yin abinda kake so, ko domin farincikinka da kuma kwanciyar hankalinka". Yace da ni, "Yauwa Sabina haka nake son ji, Allah yayi miki albarka. Dama nasan ke baki da hayaniya". na amsa da, "amin". Cikin farincikin adu'ar da yayi min. kishin wannan adu'ar yasa ƙannena suma suka ce, "insha'Allahu Baba, ba zamu yi abinda zai ɓata maka rai ba". Amma ba wai don sunyi niyya ba saboda da yayi maganar babu wadda tayi yunƙurin magana. Anty ma tace, "karka damu Baban Abba, adu'an kawai da zamu yi shine Allah ya bamu zaman lafiya. Amma ni ta ɓangarena babu wata matsala". "nima haka". Umma ta faɗa murya can ƙasa fuskarta na nunawa da abinda ke cikin ranta. Sai da kowa ya gama magana sannan Gwaggo ta gyara zamanta, ta taɓa kafaɗata tace, "ke hayo nan". Na miƙe na hau kujera kusa da ita na zauna, ta kuma dubana tace, "kinji daɗin zaman?". Nace ma ta, "ehh Gwaggo". ta dubi Yaya Abba tace, "kai Abba tashi ka kashe min wannan na'urar sanyin, kasan ina da mara lafiya, ba zai yiwu ni a ruɓar dani ba, ita kuma Albarkar tawa da nake ji da ita a bar min ita da jinya". Yayi kamar bai jita ba yaci gaba da danna wayarsa, domin yasan sarai rigima ce irin tata yasa tace a kashe, gari dai bana damuna bane babu sanyi ko kaɗan, Yanzu haka zafi-zafi ake, to amma ni kuma jikina baya son sanyi ko kaɗan, idan kowa zaice yana jin zafi ni kuma zance sanyi, ita kuma Umma jikinta irin shirgegen nan ne, bata shiri da zafi ko kaɗan, duk sanyin da ake zaka same ta tace a kunna mata fanka ko kuma ta fito shan iska, Ko bini-bini kaga ta yayi mi mafici ta hau firfita, yanzu haka ma saboda yanda ta ɓaɓɓashe iska na shigarta ta ko'ina yasa Gwaggo tace a kashe Ac. ta haɗe rai ta kuma cewa, "Abba dan ubanka Auwalu dake gabana a yanzu, nace ka miƙe ka kashe min na'urar bada sanyi ko". Baba yace, "kai Abba ba magana ake maka bane". Sai a sannan ya miƙe yaje ya kashe Ac'n ya dawo ya zauna, Gwaggo kuwa ta fusata ta hau masifa tana faɗin, "yo ni idan na faɗa maka Abba baya ganin girmana ai baka yarda. Amma yanzu da yayi a gabanka sai ka tabbatar". Yaya Abba yace, "nifl fa ba ƙin tashi nayi ba Gwaggo, ba kiga ina ƙoƙarin miƙewa bane, kuma tunda nake dake kin taɓa sa ni abu naƙi yi ne". "yo Abba na nawa kuma, kuma ai ba yau ka saba ƙaryatani ba. Kaci mutunci na agaban waɗannan marasa kirkin kaji ko, in yaso kai da su sai ku haɗu kuyi min fitsarar san ranku". jan baki yayi yay shiru bai tankata ba. Gwaggo tabi kowa da kallo ta taɓe baki sannan ta juya ta dubi Baba tace, "to Auwalu ni magana ce nake son nayi, wadda gaba ɗayanta kashedi ce da kuma jan kunne. A tou; ƙwamma a buɗe kunne da kyau a saurareni". "to Gwaggo muna jinki ai". Ya faɗa cikin rissinawa da girmamawa. "a'a ni fa kai tsaye bada kai nake ba, su wancananka ai sun san kansu, uwayen kilibibi da iya kisisina". ya sake cewa "Gwaggo a dai yi haƙuri, shi yasama na taramu anan ɗin gaba ɗaya". "oho dai, ni ka tara ko karka tara dama ina da niyyar isar da wannan saƙon tunda Allah ya haɗamu zama wuri ɗaya. gida dai arziƙin ɗana ne dole na zauna a cikinsa tunda bana uban kowa bane, gida kuma na uban Sabina ne zamanta cikinsa daram dam-dam ehe, babu shege daya isa ya raba inuwarta da ubanta". Anty da ta san dasu ake ta kwantar da murya tace, "Hajiya Gwaggo kiyi haƙuri, duk abunda ya faru a baya ya wuce...". Ai bata kai aya ba Gwaggo ta dakatar da ita tana faɗin, "munafuka ke kika kaini Hajji dana zama Hajiya, kina wani kwantar da murya da sadda kai kamar ta Allah, baƙar makira Allah a fuska Fir'auna a zuci, Yo Zara'u ni ai sai dai ki gayawa wani baƙin halinki, domin farin sanin dana yi miki ko uwar data haife ki bata sanki ba, saboda haka ki daina wani ƙumbiya² ki fito sak a mutum ki faɗa musu sabon tuggun da kike shiryawa a zuciyarki, saboda ni bana karantar fuskar Mutum sai dai na karanci zuciyarsa, wannan baiwar tawa ce ni ɗaya da Allah ya bani. ki sa ni da kyau saboda ki kiyaye gaba, domin kina ƙara aikata abunda ban gamsu da shi ba zan sanya Auwalu ya yanka miki Jan kati, akan Sabina babu abinda ba zan iya ba". Kuka Anty ta saka tana faɗin, "wallahi Gwaggo ba sanin da kika yi min da bane, ki bar yimin wannan mummunar fahimtar a yanzu". Gwaggo ta taɓe baki tace, "ki bar ɓarnatar da hawayenki a banza kina kukan munafurci, Kina yaudarata kina yaudarar kanki, da kika ganni nan na zauna cikin kishiyoyi babu kalar kissa da makircin da ban sa ni ba, don haka kisan a inda za kiyi". Baba yace, "Gwaggo ke fa uwace, faɗa ya kamata kiyi musu da nasiha, amma duk wannan ƙananun maganganun basu taso ba". Ta kalle shi ta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login