Showing 15001 words to 18000 words out of 89788 words
shan sha ka fashe”. Yadda ta ke sababinta ni kuma yana saka ni nishaɗi, ita kuma idan duniya akwai abinda ta tsana tana faɗa ina dariya, duk da kasancewar ta itama Kaka ce a gare ni, Gwaggo tayi murmushi ta dube ni tace, “Karima wannan kuma ai gaki gata, yo me zan bata ni kuwa, abin ma da ba wani ci take yi ba, gaba ɗaya makaranta ta saka ta gaba, ko baki kula ba yanzu ma daga can ta ke”. Adda Karima ta gwame baki tace, “kuma fa haka, ita wai huda-huda, gara dai ayi aure duk sa’anni sunyi sun dire ku kuma kunce karatu to ayi dai mugani, lafiya ƙalau”. Saboda tsabar gulma nacin ta bata samu damar amsa gaisuwar da nai mata ba sai da ta gama habaicinta. ni kuwa ina dariya nace, "7Adda Karima kenan, ke dai ba’a raba ki da abin faɗa, to abinda kema kina da iko akaina, miji ai sai kimin wannan abu ɗan sauƙi..”. Kafin na ƙarasa tuni Adda Karima tace,"abu ɗan sauƙi fidda wando ta ka, Sabina ai shikenan tunda haka kika ce”. ina jinta na shiga ciki, duk bakin Gwaggo idan Adda Karima tana wuri tofa nata mutuwa yake yi muɗus. Napep ɗin dana sauka shi ya ɗauke su, ita kuma Gwaggo ta dawo ciki daga rakiyarsu. ina ɗaki ina canja kaya Gwaggo tayi sallama ta shigo ɗakin, gefen gado ta zauna tana faɗin, “ina raba ki da mayarwa Karima martani idan tana maki magana, kinsan dai kaf dangi babu wanda ya kaita shiga abinda babu ruwanta, saboda haka ki kiyaye ta wallah”. Ina gyaran zaman rigata, na miƙa hannu na ɗakko hula na sanya akaina sannan na dubi Gwaggo nayi mata kallon tsaf nace, “to karki damu Gwaggo zan kiyaye, wai da naga itama matsayin Kaka take a wuri na shisa ma nake yi da ita, baki ga ita wancan ko kallo bata ishe ni ba”. Gwaggo tace, “au yo to ni ai nazaci baki ganta ba, kinga fa bana son iya shege, sai kace baku san juna ba, kai ku dai ko miji kuka haɗa iya ka abin da zakuyi kenan, Allah ya shirye ku to”. Miƙewa tayi tana faɗin bari nayi alwala, har ta kai bakin ƙofa ta ɗaga labule ta dawo tana faɗin, “au ke la ɗazu kuwa Farhana tazo zaku tafi, nace mata baki dawo ba, ƙila ko kin tsaya bada hadda ne”. saboda kar taja zancen da sauri nace, “eh, hadda na bayar saboda jiya ban bayar ba, kuma bana son tayi min yawa shisa”. “au to madalla, ai na zaci ko wurin ɗan iskan yaron can kika koma, dan ta kawon ƙorafin hakan”. Sai da zuciyata ta buga, bugun da ban taɓa jin tayi ba, zuciyata bata son ana zagin bawan Allah'n nan ko kaɗan. Rumtse ido nayi ta dubi Gwaggo da wani irin kallo, da ƙyar leɓena na ƙasa ya samu nasarar motsawa kana na sama ya motsa suka haɗu suka samu nasarar furtar kalmar a’a ga Gwaggo. Bata kuma yinƙurin cewa komi ba ta saki labulen ta fita. ni kuwa na dafe kaina saboda yanda naji yana sara min na furta,“Ya Salam!”.*AL-HUSSAIN*
_By Oum Ramadhan✍🏼_
*(7)*
"kinga farar singlet ɗina?". muryar Yaya Abba ta amsa a cikin kunnena. "ban ganta ba, bani na kwashe kayan ba sai dai ka tambayi Gwaggo". na ƙaraso wajensa ina ƙara faɗin,"Yaya Abba dan Allah zuge min". ya kama zip ɗin rigata ya zuge min sannan yasa kai ya fice ya zabga mitar da baya rabo da ita. ban dai ji Gwaggo ta tanka masa ba kuma nasan saboda karta yi magana suyi da shine shiyasa ta share shi, ni kuwa da ina gyara naga singlet ɗin amma na manta inda na ajeta shi yasa nace masa ban gani ba, dan ina cewa ban san inda na aje ba na shigesu da jaraba yau.
bayan na gama shirina na fita parlonmu da yake madaidaici, na zauna naci sauran ɗumamen tuwon da Gwaggo tace ta rage min, ina gamawa kuma na dawo ɗaki na ɗauki littafin da nayi renting shekaranjiya na shiga karatu, tun a daren jiya na gama karanta book 1 ɗin, Sumayya Abdulƙadir ce ta rubuta shi ina masifar son littafanfa.
sai wajen sha biyo na miƙe, na fito falon ina gyaran ɗaurin ture kaga tsiyana sai ga Farhana ta shigo bakinta ɗauke da sallama. fuskarta na washewa da siririyar dariya ta ƙaraso inda nake, wanda ni kuma ganinta yasa na cukule fuska, na dakata da waƙar da nakeyi, ina faman cika ina batsewa, saita hannu tasa da nufin ture ɗaurin nawa tana faɗin, "bari na ture sai naga tsiyar". Na wani bankama mata uwar harara sannan nace, "da kuwa kinga tsiya ganin idonki". Tayi dariya tana kama hannuna da nufin mu zauna kan kujera, na turje ina daɗa nuna mata nifa ban bar fushi da ita ba. cikin daɗin baki ta kama cewa, "haba mana Sabina wai mene kike hakan...wai so kike sai duniya ta jimu ts mana dariya". ta faɗa tana duba na tare da manno min kiss a goshi. ganin dai kamar ba zan sauko daga kan dokin fushin dana hau ba sai fuskarta ta sauya zuwa damuwa, nan fara'arta ta ɗauke gaba ɗaya, ni kaina na sa ni Farhana na tsananin so na, haka nima, bama iya faɗan minti biyar bamu shirya ba, kai hasalima bama yin faɗan, mukan yi ƙoƙarin kiyaye duk wani abu na ɓacin ranmu, duk da cewar wani lokacin ni na kan kasa haƙuri amma ita ko menene haƙuri takeyi. sai dai a wannan karon ina mamaki da silar abunda yasa nake faɗa da ita har nake irin wannan fushin haka, fushi da ita akan mutumin da ban sa ni ba, na tsince shi ne kawai a hanya, har kuma nake jin zan iya rabuwa da ita akansa, bama ita kaɗai ba, kowanene gani nake zan iya rabuwa da shi muddin bai samawa Yaya lafiya ba. Na kauda fuskana gefe guda domin bama zan tankawa maganar da tai ba. tana ƙara riƙe hannuna da nake son ƙwacewa tace, "kinga indai akan Yaya'nki ne kwantar da hankalinki, daga yau ba zaki ƙara jin bakina akansa ba. Wannan alƙawari ne na maki". jin hakan yasa na juyo ina dubanta, idan na kalla shin maganartata da gaske ne, ganin na zuba mata ido ina karantar fuskartata yasa tace, "wallahi da gaske nake miki, ni bazan yarda wani ya lalata mana zumuncinmu ba. Tsakanina da shi Allah ya shirye shi kawai, ko ba hakan kike so ba?". na saki fuskata ina murmushi, kamar yanda muke yi ada yanzu ma haka mukai, domin kuwa tafin hannuna ɗaga na bata muka tafa ina faɗin, "yauwa ko kefa, yanzu naga haskenki". sai tamin harar wasa da cewa, "ji min walaƙanci, duk wannan uban hasken nawa baƙi kike ganinsa dama?". Ina dariya nace, "yo da kike wani kaurara hasken naki, ai na bogi ne tunda na bature ne". Ina faɗa cike da tsokana, ina kaucewa biyo ni da tayi. Har ɗaki ta biyo ni muna dariya, Gwaggo na linke kaya ta bimu da ido. Sai dana ɓuya a bayanta ta sami damar yin magana tana duban Farhana.
"ƙalau kuke kuwa?". Farhana na riƙe da ƙugu take ce mata, "wai Gwaggo saboda kuturun walaƙanci ni yarinyar nan zata cewa fari na bature ne". "ai ba ƙarya nayi ba, uban tulin robobin mayukan ɗakinki na mene?". Ina dariyar ina magana kuma cike da tsokana. Gwaggo ce ta juyo ta dube ni, ta wani yatsine fuska kana tace, "kema ai banda Allah ya rufa maki asiri gyatuminki ya ɗauko hasken Sahibina da ba'a san kalar da zaki kwaso ba, da har kike tsokanar wata, ki bar ganin Samari na aikin sunturi akanki duk tabarakin Sahibina kika ci. Ah tou". tai maganar dan ta ramawa Farahana, amma sai taji ba ki ɗayanmu mun sheƙe da dariya, Na buɗi baki nace, "Wai naci tabarakin Sahibinki, Abunda tarihi ma ya nuna shi Sahibin naki Kawu Baffa Sule ma ya fishi kyau, kinga kuwa in haka ne ai da an gani ajikin sauran Ƴaƴan nasa. Kawai dai shi Babana Allah ya zaɓe shi ne, gashi nan santalele kamar balarabe, Shi yasa ake kishi da shi, don ko Sahibin naki da kike koɗawa albarka". Na faɗa ina ƙunshe dariya ta saboda yanda naga Gwaggo na aika min wani kallo mai kama da harara. Gajeran tsaki ta saki tace, "Ki kiyayi ramata Sabina, shi gyatumin naki har kishin mene zanyi da shi, banda aikin wofi na haife shi kuma na kama kishi da shi". sai kuma ta ɗauko mifici ta shiga dukansa a ƙasa tana faɗin, "Kuma In faɗa miki ƙaryar tarihi ya faɗi abin kushewa akan Sahibina Allah ya jiƙansa da gafara. Ke idan a wannan zamanin naku ne ma ai sai na dinga tofe shi da li'ilafi ƙuraishin, ko da yake a wancan zamanin ma me aka fasa, yanda ƴan mata ke tururuwa akansa kamar ƙuda ya sami zaƙi tsabagen tsantsar kyawunsa da farin jini. Amma haka ya miƙe ya dire yace sai ni, haka ya dinƙa bani tabara ana aika min da yasin a gidanmu, Ɗan baiwa kenan wallahi shima Zaɓin Allah ne domin kuwa Allah ya bashi. Ai naga zallar soyayya a wurinsa, Allah sarki Allah yay maka rahma abin ƙaunata". Kawai sai ganin Gwaggo mukai ta fashe da kuka tana matse ido. Niko mai zanyi banda dariya da tafawa harda ƙwalla. "Allah ya jiƙansa, kice Dai Gwaggo kunsha ƙauna ke da Kakanmu". Farhana ke mata wannan tambayar tana ƙunshe dariyarta. "Hmmm". Gwaggo tace tana juyowa ta fuskanci Farhana."amin ƴar aljannah, ai ke kam mutunci ba daga nan ba, ki godewa Allah da baki ɗauko halin ƙawarki ba na rashin kirki". Farhana na daɗa riƙe dariyarta tace,"Gwaggo yau kuma Sabinan taki guda".
Gwaggo ta harari gefena da cewar,"Wannan ai ƙaunar da take min a baki ne kawai... kina ganin ta haka sam bata ƙaunata. Yo banda rashin ƙauna ana zancen marigayi kina dariya saboda ɗibar albarka, ai yau Sabina ta nuna min matsayina a zuciyarta". Ni dai dariya nake kawai bance mata komai ba, dan yanzu ina ƙara yin magana zata kuma hawa. dama Gwaggo sarkin zuba zance, sai dai idan baku zauna da ita ba, Nan ta hau bawa Farhana Labarin Kakanmu wato mijinta kenan. "ina faɗa miki Farhana ai naga zallar soyayya daga wurin Sahibina, soyayya ba irin ta ƴan yanzu ba irin ta aljanu. Babu irin kalar walaƙancin da ban masa ba amma bawan Allah'n nan haka ya nace yace idan babu ni sai rijiya. ke abokansa har ce masa suke babu zuciya a ƙirjinsa saboda irin wulaƙancin da nake masa. ni kuwa abunda ma yake ƙara ƙona min rai nake ci masa fuska idan naji yana faɗin wai in bani rijiya zai faɗa ko kuma ya rungumi tiransufo ma. idan ya faɗi hakan raina yana sosuwa, saboda lokacin ina jin tashen ƴan matanci, gani kyakykyawa gashina har gadon baya, idan ba kiyi min farin sani a matsayina na buzuwa ba to zaki rantse kice baƙar balarabiya ce, gidanmu fa Maza dandazo suke a ƙwar gida sai akai asuba ana jiran fitowata, ni kuwa dama ta samu nayi ta juya su kamar waina a tanda, tunms layi yazo kan Sahibina Allah ya jiƙan rai, shi dama ya kwashi buhunhunan rashin mutunci a wurina, amma don tsiya da tusa min takaici duk sanda nayi masa sai yace ai indai ba ƙona shi zanyi ba ya zama toka, to ba zai daina zuwa inda nake ba kuma ba zai fasa furta min soyayya ba. Watarana dana shirya masa mugunta, Ina jin ance yana sallama da ni Na kaɗa karkashi na fita ta bayan gida na sami dakalin ƙofar wani gida na sheƙa a wurin, Sannan na dawo naci gayu na yafa gyale, na fito waje ina tafiyan rangwaɗa sai faman yauƙi nake kyace tarwaɗa kin san mu buzaye bada ganan ba. Shi ko yallaɓai tunda ya ganni yake faman murmushi yana nuna jin daɗi, Ji yake kamar ya sure ni mu shilla sama, ina isa wurinsa na wani kashe masa ido ɗaya sannan nayi masa sigina da hannu ina masa nuni da ƙofar gidan da zamu yi zancen. Hmmm haka ya biyo ni sai wani nishaɗi yake a tunaninsa yau ya taki sa'a ya mallaki zuciyata ne bai san mugunta na shirya masa ba, ɗan Fillo'nka na hawa saman dakali jinsa kike timmjim ya zame ya faɗo cikin kwalbati, salati yake yana neman ɗauki ni kuwa sheƙa masa dariya nake kamar zararriya saboda mugunta, nayita iya kuɗina na kaɗa masa mazaune nace gobe ka ƙara dawowa inda nake". duk yanda naso dariya a wannan lokacin sai ya gagara, saboda yanda Gwaggo ta saito faranti a fuskata, jira take na ƙyalƙyale ta kwaɗo min. Farahana da biye ta dakakke sai ce ma ta tayi, "ohhh Allah sarki Kakanmu, amma dai daga ranar bai kuma zuwa wurinki ba ko Gwaggo?". Gwaggo ta jawo robar goro ta ɓalla ta Kai baki, tana tauna tana cewa, "ai ɗiyar Aljannah ina kai ki bana baroki, daga inda na sallamawa mutumin nan a faɗuwar da yayi sai da yay karaya biyu targaɗe ɗaya amma yana warkewa sai gashi ya dawo yana kuma zayyana min irin soyayyar da yake min, Kuma fa ko da yana kwance kullum sai ya aiko azo duba mishi ni, in taƙaice miki dai ƙarshe ai sara mishi kawai nayi nace Sahibina ai kai bai kamata a kiraka da masoyin zuciya ba, da masheƙin rai da zuciya ya kamata a kiraka". "to fa! garin ya ya cancanci wannan sunan Gwaggo?". Farhana ta faɗa tana waro ido, tana ƙara tunzura Gwaggo. Ina duban Gwaggo ina dariya na miƙo mata hannu ta sammin goron sai ta make hannun nawa, yau harda su murguɗa min baki bayan harar da ake watsa min. Nan taci gaba da bawa Farhana labari, "ai ɗiyar Aljannah ya cancanci wannan sunan shi yasa na raɗa masa. Akaina fa yay faɗa da ƴan daba talatin saboda sun kawon hari, duk wuƙaƙen da suke tare dasu haka yay masu fata-fata, Ya kamo hannuna cikin kulawar so ya dawo dani gida, kamar zai yi kuka yake roƙona don Allah Sahiba karKi sake fitowa waje bare wani banza ya kuma kalle mani Ke, take a wajen naji wani ƙahon sonsa ya huda zuciyata ƙaunarsa ta nemi waje tai malemale, naja da baya na matso kusa da shi na yi masa kirarin so mai jijjiga ruhin masoyi, sannan na koma gida. Ina shiga na cewa mahaifiyata Adi, nifa Fillo zan aura, kowa daya ji haka sai da yayi mamakin abun saboda ada nace akan me zan auri wani matsolon rake, ai ƙwamma na sami ɗan'uwana usulin buzu kakkaura mai ƙwarin ƙashi na aura. Farhana ai banga so da ƙauna ba sai dana je gidan Sahibi na Sahibarsa, Kishiyoyi suka sanyo ni gaba amma sam Sahibina baya bi takansu, ni kuwa haka na dinga tsula tsiyata a gidannan ina gasa su son raina da tawa salon kissar, kuma fa gani ƴar figigiya amma haka na zame musu ciwon idanu. sanda na sami ciki na fara laulayi ai Kamar na zazzagawa kishiyoyina wuta a jiki saboda yanda Sahibina ke Tattalina kyace wata ƙwai". Gwaggo ta numfasa tana kuma fashewa da kuka tace, "Allah ya jiƙan Sahibina, ya mutu yana cikin mayen so na". Wayyo Allah cikina ni Sabina, yau nayi dariya na godewa Allah saboda dramar Gwaggo, na ƙara tsokanota da cewa, "to amma kuma Gwaggo ai tarihi ya nuna Kakanmu kamar yafi son Uwar gidansa Addagana, akace ma yana kan cinyarta ya mutu". Ba shiri naja bakina nai shiru saboda kallon da Gwaggo ta wurgo min haɗe da jefo min murfin bokiti. "to duk wanda ya faɗa miki wannan zancen ƙarya yake munafikin Allah ta'ala. Ke Sabina zanfa iya haɗa ki da D.P.O yau ɗin nan, saboda haka ki fita a idona, ke kiji wata makirar ƙarya, a gidan ubanwa ya mutu akan cinyarta, wanne shegen ne ya faɗa miki haka?". ni dama ba don komai yasa na faɗi hakan ba sai dan kunnata, saboda nasan yanda take tsakaninta da kishiyoyi, gashi dai shekaru da dama amma kamar waɗanda mijin ke aurensu yanzu. Gwaggo dai kamar nai mata me, haushin maganata da dariyata suka tsaya mata a rai. alhalin ita kanta wadda ake bawa labarin dariya ta ke, amma tawa dariyar ita ta zama laifi, na buɗi baki zanyi magana kenan ta dakatar dani cikin kwazazzafa. "ke kin san Allah zan miki adu'a bakinki ya tsaya a haka na tsawon shekara guda, sarai kin san na gada a wurin Kakana na biyu na ɓangaren kishiyar Babata Adi, kasancewar sunyi zaman mutunci sai muka zama kamar ƴan uwa, don haka ahir ɗinki da ni a yau ɗin nan. Ki tambayi kishiyata Hussaina kisha labari, da tayi min ba dai-dai ba sai da ta kwan talatin da bakwai ba tayi kashi ba, shima banda ta bani haƙuri sai dai ta shura a haka". Nai shiru ban kuma magana ba, ina latsa wayar Farhana. Ina jinsu Suna ta shan hirarsu. Ya Abba ne ya shigo ɗakin ɗauke da sallama a bakinsa, muka amsa masa ya shigo ɗakin ya tsaya yana zuba hannayensa a aljihu. Sannan ya shiga buɗe kwanuka da alama abinci yake nema, ya ɗago yana kallon Gwaggo yace, "ina abinci na?". a hasale tace da shi,"Ka kawo ka aje ne, ko kuma aure na kake da zaka shigo min gida har cikin ɗakina kake tambayana abinci". Ya kama ƙugu ya riƙe yana dubanta babu alamar wasa a fuskarsa kamar wani mijin gaske, yay gyaran murya yace, "naji koma mine kice, ni dai ina abinci na, yasin yau na kwaso yunwa baki ga yanda nai wani laushi ba kamar lagwani". Ta harare shi tace, "To ai kai dama lagwanin ne, saboda kullum a yamushe kake Kamar lawashi. Ni wannan yaro don dai Allah yay maka halittar maza ne amma da sai nace mace ne kai". Ya Abba ya ɓata fuska yace,"nifa sai na rubuta miki takarda akan irin wannan cin fuskar da kike mani. Kuma idan kina wasa ki kuma cewa tak ki kalla idan ban sake ki ba...ya zaai a gaban ƙannena kike faɗa min irin wannan maganar". Gwaggo tayi tsaki ta doki