Showing 48001 words to 51000 words out of 89788 words

Chapter 17 - ALHUSSAIN Complete Hausa Novel

23 Aug 2025

402

ta duba abinda zata duba ta bani na wuce na fita. A ƙofar class na tsaya jiran Intisar, babu daɗewa itama ta fito, hangoni yasata ta fara dariyar dake ƙunshe da murna, tana ƙarasowa muka tafa da ita, exams dai tayi mana daɗi gaba ɗayanmu, muna tattaunawa akan wata question sai ga wata ƙawarmu ƴar carryover ta fito, muka jera muna tafiya. Intisar tace, " kallah wani bawan Allah, Allah ya bashi kyau sai dai babu ƙafa". Muka juyo ni da Rahinat don kallon mutumin da take magana akai, ana tura shi a kekensa na guragu, har sun wucemu, kamar ɗazu dai bayansa kawai na gani, da tausayawa nace,"Allah sarki wallahi nima ya bani tausayi, har ƙwalla sai dana masa ɗazu, kamar shine muka yi exams tare ko?". Na faɗa da muryar tausayawa ina daɗa bin bayansa da kallo. "ehh shine". Intisar ta faɗa. "baki ga akan stage aka ɗora shi ba daga shi sai halinsa, wannan exams idan baka yi karatu ba ai kana tsakiyar ruwa". ta ƙara faɗa. sai Rahina tace, "ke he is not a student, He is the Financial Accounting lecturer, baya ɗaukan ƴan Level one lectures until level two, Becouse he can't walk bare ya miƙe yay explaining a board, So at level two kuwa bayani ne zaizo yay maku verbally using projecter, ita Malama Muhsinah ƙanwarsa ce, ita ke karɓa masa a L1 nd also she is the one taking care of him at school". "eyyah Allah sarki, Allah ya bashi lafiya". Muka faɗa a tare ni da Intisar. "amma dai baida mugunta ko?". Na tambayi Rahina ina waro ido waje. "ehh to gaskiya bashi da mugunta, amma fa ya iya tsara questions, aima kun gani yanzu, kuma gashi da fara'a murmushi har tunbuɗinsa yake, kuma ba'a faɗuwa course nasa gaskiya saboda kunga yadda ake dagewa, nima ƙaddara ce ta dawo da ni". Muka ci gaba da tafiya muna hirarmu, daga bayanmu muka ji ana mana magana, muka dakata da tafiyar muka juyo. Saurayin yace da ni, "Beauty Malama Muhsina is calling you". Ya faɗa yana nuna ni. Na kallesa ina yamutsa fuska saboda ranar data haskemu. ina nuna kaina nace, "kuma ni tace ka kira, ai ba sunana Beauty ba, sai dai ko ƴan gabanmu ta ke nuna maka". Na faɗa ina maida kallona ga ƴan gabanmu dake tafiya. Murmushi naga yayi yana cewa, "na san ba ainihin sunanki bane, nima ce tayi min na kira mata beauty gata can tana tafiya with pink veil, ai farko dana kira ku Sisters kuka ji ina cewa ko?". Su Rahinat suka ce masa "ehh". Ya kuma cewa,"to da ku ka juyo na kalleki sai naga ehh lallai kin cancanta da a kira da suna Beauty, hakan yasa nima na ɗana. Allah ya tsare miki wannan kyawu naki". Ya faɗi hakan yana wucemu. Na kalla su Intisar da suke kallona suna murmushi, na sauke numfashi na ɓata rai sannan nace. "sarai kun san Malama Muhsina bata da kirki, maimakon ku tayani jimami ku abinma daɗi yay maku, ban san kiran akan mene ba Allah dai yasa ba laifi na mata ba". "amin dai". Suka amsa. Intisar tace, "amma ai ɗazu ta tuna maki baki rubuta suna ba, kiyi gaggawar zuwa may be kin kuma mantawa da rubuta wani abun". Na dafe ƙirji na furta, "na shiga uku na". "Beauty ki dai wuce ki tafi kiran Malama kar ki ƙarama kanki laifi". Rahinat ta faɗa da sigar tsokana. Na kalleta na mata harar wasa, ko mene abin tsokana anan oho. "na san zaman da zanyi dake". Na faɗa ina barinsu.
Tsaye na sameta a bakin admin block, dama bamu da nisa da wurin a tafiyan da mukai, ta harɗe hannaye a ƙirji tana jiran isowata, gabana ya faɗi da irin kallon da ta ke mani, na kuma sadda kaina ƙasa na ƙarasa gabanta, ina rissinawa nace. "Maa Someone said you were calling me". Na faɗa har muryata na rawa. Da alama dai tana da izza, tana jijji da kai tace min, "and now you have the opportunity to come After you finish westing my time, right?". Shiru nayi ban ce mata komai ba sai tsilli-tsilli da idanu da nake. ina kallo ta taɓe baki haɗi da maƙe kafaɗa cikin ɗagin murya tace min, "Comon jor my friend, ki wuce Proff want to see you". "Maa waye proff?". Na tambayeta da son ƙarin bayani. ai kamar na zageta saita ɗaga murya a zafafe tana faɗin,"wane proff kike tambayana? Duk faɗin waƴanda ke maku lectures akwai Malami Proff ne sama da mutum ɗaya, mtswww this girl you don't have manner of etiquette at all". Taja tsaki tana kamo kunnena ta bani ranƙwashi,"to daga yau ki san wane Proff, daƙiƙiya kawai, comon to write your name on script ɗazu ma kika kasa, and that is how you got in to university, kamata yay ace kina primary school. Ana magana kina zumɓurowa mutane baki, maida shi ko na bige miki laɓɓa". Nai saurin maida bakina, na ɓata rai ina jin kamar nayi mata mene, ta gallan harara tace,"ki same shi a office nasa". "aina office ɗin yake?". Bata ce min komi ba tai juwarta ta shiga admin block ɗin, na bi bayanta, muna zuwa office na huɗu tai min nuni da yatsanta sannan tai gaba abinta, nabi bayanta da murguɗa baki kana nayi knocking door. "Yes, come in". Aka ce dani, hakan yasa na buɗe na shiga ƙafafuna na rawa saboda duk a tsorace nake ban san laifin da nayi ba, ni da ko wani Proff ma ban taɓa sani ba. Ina wurga idanu nake taka ƙafata, ƙaton hotonsa na gani an rubuta Proffessor Muhsin Muhammad Na kowa, _"fatabarakallahu ahsanal khaliƙin"._ na faɗa a zuciyata. sai dai kuma kan na kai ga ɗauke idona akan hoton ƙirjina ya buga dummm, hakan yasa na murza idanu ina ƙara kallon hoton da kyau kamin wata faɗuwar gaba ta musamman ta riskeni. na sauke idona daga kan hoton kamin su ƙara tsayawa akan ƙatuwar calender ɗin dake gefena, ina daɗa kallon fuskar hoton na tsawon wasu daƙiƙu kamin na tsayar da tunanina akan abunda ke wucewa ta cikin kaina. ƙwarai na san wannan fuskar, na santa farin sani, nayi mata sanin da zanenta ba zai taɓa ɗaukewa a idona ba, to amma mene alaƙarta da mamallakin wannan ofishin?, tukunna ma wannan sunan da muƙamin daga ina ya samo su? a yaushe?. mamaki ya kamani zuwa nisan da ba zai kwatantu ba, wani abu ya daki ƙwaƙwalwata a lokaci guda, Yaya! Yaya dai!, dama waye shi?. dukkan tunanin dake cikin kaina da ma abinda zuciyata ke rayawa ya tsaya acak a sanda idona ya sauka akansa, lokacin daya juyo ya fuskanceni, dan sanda na shigo ya juya min baya. sai na zama kamar wadda aka dasa a wurin, idanuwana na gaza ko da ƙiftawa daga kallonsa, kallon fuskarsa dake ɗauke da ƙayataccen murmushi da yake, irin murmushin nan daya taɓa yi a waccen ranar da yace zaiyi koyi da ni. kuma a take dukkan faruwar wani abu ya shiga haskawa cikin idona, tun daga ranar dana fara ganinsa zuwa ranar ƙarshe da naje wurinsa, da ma sauran ranakun dana ɗiba ina zuwa ban same shi ba. waccan rayuwar dana sansa ba irin wannan bace, haka zalika wancan yanayin da na sansa da shi ba irin wannan yanayin ba ne. yanayin da yake ɗauke da shi a yanzu yanayi ne na nuna yana cikin nishaɗi da jin daɗin rayuwa. kuma da dukkan wata alama wayar da yake ne yasa shi hakan. _ko dai mafarki nake?_ zancen da zuciyata keyi kenan, dan haka saina sadda kaina ƙasa na rufe ido, sannan na buɗe da dukkan yaƙinin zanga saɓanin abunda nake gani. sai dai wannan muryar tasa da ba zan taɓa mancewa da ita ba ta shigo cikin kunnuwana ta sami mahalli acikin ƙoƙon kaina. "Beauty bismillah come have a sit". Ya faɗa har zuwa wannan lokacin bai bar wayar da yake ba, na ɗago ina duban kujeran da yake min nuni da shi, sannan na ƙara masa wani kallon, kallon dana kasa fassara shi da irin yacce zuciyata ke lissafi. abu guda ɗaya kawai da na sani shine a lokacin da ma guda ɗaya nake nema da zanyi masa wulaƙancin da har mutuwa ba zai manta da shi ba. a rayuwata na tsani mutane guda uku, munafuki! maƙaryaci da kuma mayaudari. dan haka na ɗaga ƙafafuna na ƙarasa na zauna akan kujerar, gaba ɗaya ma zuciyata ta kasa lissafa abunda zanyiwa wannan bawan na Allah, duk da a gefe guda zuciyar tawa ta kasa gasgata shi ɗinne. dan wancan da na sani, ko kusa bashi da wata alama da ke nunin yana da wata rayuwar ta daban bayan wacce yake acikinta.
sai dai har yanzu tunanin guda biyu ne acikin kaina. idan wancan dana sani ne to wanene shi?, haka idan ba shi bane to wannan wanene?. sai dai a irin alamomin da nake gani kamar ba mutumin da nake tsammani ba ne, dan shi wannan nunawa yake kamar bai taɓa sanina ba?, beside ma Yaushe ya zama gurgu? ko kuma hakan duk na cikin takun basajarsa?. na ɗago ina ƙare masa kallo, me yasa nake jin bugun zuciyata na tsananta ne idan ina kallonsa, alhalin shi wancan bana tsintar kaina a irin hakan. gaba ɗaya yay shiru yana sauraren maganar da ake masa ta cikin waya, ya ɗago karaf muka haɗa ido da shi, ya sakar min sanyayyan murmushi, hakan yasa na ɗauke nawa idon daga kansa cikin ɗaurewar fuska. zuciyata gaya min ta ke Wannan ba wanda na sani bane, domin ba zan taɓa manta duk wasu abubuwa da suka danganci Yayana ba, sai dai tsananin kamarsu da wancan ya ɓaci, tamkar an tsaga kara, ba su da wata maraba daga kamannin fuskar har surar jikin, hatta muryarsu iri guda ce, kawai shi wannan gurgu ne kuma yana da fara'a, to amma shima wancan ai halin rayuwan daya tsinci kansa ne yasa baida abubuwan da wannan yake da su. ban san lokacin dana miƙe tsaye ba, na tsaya akan ƙafafuna, fuskata a turɓune babu wani ɗigon annuri na zagayo gabansa, don in samu in tabbatar da zargina, yazo nan yana musu basaja kamar yanda yake yi a garin Kano. Ina tsayawa gabansa na kama ƙugu da duka hannu biyu ina faman jijjjige-jijjige, ƙiyasto abinda zan masa nake idan har na tabbatar da shi ɗin ne. sai dai nayi istigfari sannan na kamo hannunsa, saboda na san hakan da zanyi haramunne ya saɓa da shari'an musulunci, sai dai bani da yanda na iya, fatana kawai na fita daga duhun da nake ciki, links ɗin hannun rigarsa na ɓalle na yaye hannun rigar tasa. shi dai bina da ido kawai yake yana kallon ikon Allah, saboda farko dana riƙe ya janye saina kuma janyo shi na damƙe, na kuma tsorata da yawan gargasar da na gani a hannunsa, wanda wannan gargasar ita ta ƙara tsoratani har na ɗan ja da baya, babu shakka wancan mutumin da nake kira da Yayana ne. amma me yasa yaywa rayuwar masu saurin yarda irina haka? Yaudara!. sai dai har yanzu ina cikin shakku, ban gama yarda shi ba ne, haka kuma ban yarda ba shi bane. sai kuma na ƙara kamo ɗayan hannun nasa daya ke riƙe da waya, na amshe wayan na aza masa a ɗayan hannun yaci gaba da wayarsa, kuma a wannan hannun ne na sauke a jiyar zuciya, saboda hannun hagun wancan mutumin da nake kira da Yaya akwai lamɓaceciyar ƙunuwa a wurin, wannan kuma babu wata alama ta hakan. Na rufe ido ina aikin sauke numfashi, sai kuma kunya ta baibayeni nasa hannu na rufe fuskana, na ma kasa ɗaga ƙafa na koma mazauni na. sai naji ya kamo hannuna, nai saurin buɗe fuska ina kallonsa, sai naga yana ƙoƙarin miƙewa amma ya kasa, ta ke naji ruwan hawaye sun cika min ido saboda tsantsar tausayinsa, shima kuma yanayinsa ya koma zuwa na damuwa. "mene? Me kake so?". Na tambaye shi cikin sanyin murya da tausayawa. a wannan lokacin na manta da tunanin ruɗanin dana shiga cikin wucewar wasu daƙiƙu. baiyi magana ba sai nuni da yay min da kansa, saboda haka dana fahimci me yake nufi saina duƙa, ina tsugunawa gabansa naji yana faɗa acikin wayar. "Mom ga Beauty zaku gaisa". Ya faɗi hakan yana kara min waya a kunne, kenan da mahaifiyarsa ne yake waya tun a ɗazu, dole ya kasance cikin nishaɗi, _me mahaifiya a raye shike jin daɗin rayuwa,_ na faɗa a zuciyata ina sanya hannu na goge ƙwallar idona. Na maida hankali kan maganar da Mom ke yimin. "Beauty nah". Itama naji ta kirani da wannan sunan, duk da mamakin daya kamani sai na kawar, ban san lokacin da muryana ya koma na shagwaɓaɓɓu nace, "Mom ba sunana Beauty ba". tai murmushin manyance tace, "to ya sunan ɗiyar tawa?". nace, "Sabina, Sabina'n Gwaggo". maganar tawa ta sakata yin murmushin mai sauti, sannan tace da ni. "Allah ya albarkaci rayuwanki Sabina tah, ya kuma dawwamar dake a farinciki". na amsa da,"ameen Mom, na gode sosai. Kema Allah ya ƙara maki lafiya da nisan kwana". Ta amsa min da, "amin ɗiyar kirki". Sai yanzu na tuna ban gaidata ba, nai saurin rufe bakina ina zaro ido na kalla Proff dake aikin kallona, a hankali nace, "Mom ina yini. Kiyi haƙuri don Allah tun farko ban gaida ki ba". tace, "dont worry my daughter, jin muryanki ya fiye min gaisuwan, tabbas yau ɗin nayi farinciki da jinki. Ina Yayan naki?". Tana faɗar haka na ɗago na dube shi, zuciyata na kuma tsinkewa da lamarin, dan da Mom tace Yayana sai naji kamar wancan Yayan nawa ne da gaske. "Daughter". Nai firgigit daga gajeran tunanin dana tafi, "na'am Mom". "ina Yayan naki?". ta kuma tambayana. "Mom gashi nan". "oak bashi wayar, Idan kinje gida ki gaida min da Gwaggo sosai kinji". nai knodding kaina kamar a gabanta nace, "tom Mom zataji". lokaci ɗaya saina sami kaina da yin wasu abubuwa da ban san lokacin da nake yin su ba, shi kansa abunda nace mata a yanzu sai daga baya na san na faɗa. "Mom ki cewa Yaya ya daina ƙarya ba kyau, shi dai babban mutum ne". Nai maganar ina masa kallo mai harara. murmushi naji ta sa ki kana tace, "shikenan zanyi masa faɗa, daga yau ba zai ƙara ba Beauty nah, oak Bye bye". "aha Bye Mom". Na faɗa ina miƙa masa wayar, yana ansa kuma na miƙe daga tsugunen da nake da zummar barin wajen ya maidoni na zauna. Ina faman cin magani nake kiciniyar ƙwace hannuna daga nasa amma yaƙi bani damar hakan, su kai sallama da Mom, cikin ɗaurewar fuska yace dani, "ba ki da kunya dama? Sa'anki ne ni da kike hararana? Ko dan kinji nace a kira min ke, yanzun nan sai na baki carryover, kuma idan aka faɗi course ɗina har spilling". Wayyo Allah nah ni Sabina, a wannan lokacin ji nayi kamar na ɗora hannu akaina na kurma ihu, domin maganar da yake a cikin tamkewar muryar nan sai ya kuma rikeɗe min zuwa Yayana. to ni maganar carryover ma bata bani tsoro ba kamar yanda shi yake bani tsoro, babu maganar da na tuna sai ranar da Yayana yace karna kuma zuwa inda yake idan ba haka ba sai ya mani fyaɗe, sak da irin wannan sautin muryar ne.
a yanzu cikin ɗaurewar fuska yace da ni, "binciken me kika mani ɗazu a jikina?". nace, "na duba ne naga ko kai ɗan yankan kaine". Na faɗa cike da jin haushinsa. sai Yay siririyar dariya yana cewa, "shine sai kika zo kina bincike ni right?, ta yanda Koda ni ɗin ne kamin na gama waya da Mom kin arce ba? Ke gaki me wayo ko, to yanda kika shigo office ɗin nan kin shigo kenan har busa ƙaho kina nan". na nuna masa ko kaɗan ban kaɗu da maganarsa ba, dan na lura irin Malamn nanne watsatstsu da idan mace ta biye musu zasu kaita su barota. dan haka kai tsaye na jefa masa tambayan,"kiran nawa na menene?". na faɗa ina miƙe da ƙoƙarin ƙwace hannuna daga riƙon da yay min. kuma muryarsa ta fito kai tsaye zuwa kunnena da cewan,"zamu je gidanku ne na faɗawa Daddy'nki, daga shiganki exams hall kika yi min sata, hakanne ma yasa na binciko files naki na duba address na gidanku, ko da idan na tambayeki za ki min ƙarya".


*Please Comment, Vote & Share.*
[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(17)*
a lokaci guda furucinsa ya daki tsakiyar kaina. Na zaro ido a tsorace ina dubansa nace,"na shiga ukuna, ni ɗin na maka sata?". Ya ɗaga min gira ɗaya alaman ehh, a ruɗe na shiga ce masa,"wallahi ko Gwaggona tasan bana sata, Kuma ban taɓa yunƙurin yi ba. kuma don Allah karka je kace ma Baba na maka sata, ba zai tsaya jin komai ba zai ɗauka tsatstsauran mataki akaina. Ni dai nasan ban maka sata ba amma ka faɗa min ko mene indai kuɗin account ɗina ya kai zan biyaka ta ke anan". Ina faɗa duk na rikirkice, tsorona Allah tsorona Baba ya kuma korata daga gida. a wannan duniyar tashin hankain da Proff ya jefani naji maganarsa na shiga kunnuwana da cewa,"kuɗi ko kuma wata kadara ba zata iya biyana abinda kika satar min ba, dole Baba da kike tsoro shi zansa Daddy nah yaje ya sama ya faɗa masa, ta yanda Baba da Daddy nah zasu yi saurin yanke hukunci dai-dai da buƙatata". kawai saina fashe da ina faɗin, "wallahi tunda uwata ta haifo ni duniyar nan ban taɓa yiwa kowa sata ba. ko wancan karanma sharri Umma tayi min. dan Gwaggo nah ta bani tarbiya mai kyau wanda ko kallon abinda ba nawa ba bana iya tsayawa yi". Sosai nake kukan har sai dana kifa kaina a gwiwata, wannan wacce iriyar ƙaddara ce. Naji ya cika bakinsa da iska ya furzar, a cikin siga ta lallashi yake ce min, "ohhh Beauty please stop crying mana, am just kidding you ba zan faɗawa Baba satar da kika mani

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login