Showing 36001 words to 39000 words out of 89788 words
gama cika ni, idona ya taru da ƙwalla yana shirin zubar da hawaye, Dama ni Allah ya horen ruwan hawaye kamar ruwan famfo, sai na koma kamar wata taɓaɓɓa, kaina fa ko ɗankwali babu kuma ba a yanda nake ɗazu ba da rigar t-shirt a jikina, wannan riga ce doguwa aka zumbula min ta atamfa, bama ta ɓangarenmu bace, don ko Gwaggo rigar nan tayi mata yawa, sai dana ƙare ma ta kallo kana na tuna atamfar sallar bara da Baba yayi mana, kenan ta Umma ce ma, ƙofa na nufa gadan-gadan sai na jita a rufe da key. Zubewa nayi a wurin na ɗora hannu aka na kurma ihu ina faɗin, "innalilllahi wa'inna ilaihi raji'un, na shiga ukuna Gwaggo tah, wayyo Allah nah shikenan Yaya Haidar ya ɓata ni, Gwaggo kizo ki taimaka min, ya rufe ƙofar, kizo kar ya ƙarasa abinda bai cimma ba". Ihu nake sosai ina shure-shuren ƙafa kamar ƙan-ƙanuwar yarinyar da aka hana shan nono. Jin yadda nake kurma ihu ina buga salati cikin fizgar numfashi, shi ya farkar da Yaya Haidar, Ganinsa nayi a gabana a tsugune don ko tasowarsa ban sani ba, ƙoƙarin saita min yanayin da nake ciki yake, kallon da yake min sai naga kamar da tsoro a cikinsa, abinda yake kawowa a ransa daban, abinda nima nake kawowa a nawa ran daban. sai matsawa baya nake ina ƙanƙame jikina, shi kuma yana daɗa matsowa kamar zai shige jikina, amma fa gefe guda idan na gasgata abunda idanuwana ke gani cikin idonsa tausayi ne tsantsa, sai dana kai maƙura a mannuwa da jikin ƙofa kana na haƙura, jikina nata karkarwa, wallahi tsoronsa nake sosai, inda za'a auna jinina a wannan yanayin tabbas jinina ya hau, shima ɗin sai daya kawo gab dani numfashinmu na gauraya dana juna tukunna naji ya kamo hannu na guda ya damƙe, ya ɗaga kofin ruwan dake ɗayan hannunsa ya watsa min, ba shiri na rumtse idona tare da kurma wani sabon ihu ina roƙonsa. "wayyo Allah nah, Allahumma ajirni fi musibati waklifni kairan minha, don girman Allah Yaya Haidar karka kuma yimin komai, kaga dai ni ƙanwarka ce". Sakin hannuna da yayi shi ya dakatar da ni daga ihun da nake kwaɗawa, ban dai buɗe idon ba sai shashsheƙar kuka da nake ina daɗa faɗin, "Yaya Haidar babu kyau kaji tsoron Allah, duk wanda ya ɓata ƴar wani shima za'aiwa tasa bare ni da nake ƙanwarka, idan ka lalata min rayuwa kai kanka ba zaka sami kwanciyar hankali ba, ka saka rigarka bana son ganinka a haka, babu kyau kallon tsiraicin wani, ko riƙe hannuna da kayi haramunne...". Saukar marin da naji a kuncina ya katse sauran surutan da nake, a zabure kuma na miƙe tsaye ina rarraba ido ina neman hanayar fita, dan duk Yaya Haidar ya gama razana ni. kuma cikin abunda bai wuce sakan huɗu ba naji murya na fita da ɓacin rai yana faɗin,"wallahi idan ba ki rufe min wannan shegen bakin naki ba sai na zare belt na zane miki jiki a wurin nan, mahaukaciya kawai, an gaya maki kowa ɗan iska ne irinki". da ƙyar na iya saita idanuwana na tsayar dasu wuri ɗaya suka tsayar da kallonsu akansa, na gwame fuska zan sake fashewa da kuka, ina dukan ƙafana a ƙasa raina na sosuwa, naji haushin ƴar iska daya kirani, to amma babban baƙin cikina daya gama ganina, abunda ba nasa ba ya gama kallewa mai shi, kai Allah ya isan mai shi, nasa hannu na goge bakina kamar yace min yayi min kiss.
Bani da tabbas ɗin abinda nake zargi, banda kuma wata hujjar kafawa akan hakan, kawai dai ganina da nai jikinsa nake jin kamar komai ya faru, dan haka kawai ba zai kawoni ɗakinsa ba, ɗakin ma kan gadonsa kuma ajikinsa. saina daɗa ƙanƙame ƙirjina wanda wuyar rigar yay min yawa, na zumɓuro baki gaba ina hararsa ta ƙasan ido, shi kuma ya saki wani munafikin murmushi daya tsaya iyaka leɓensa, ya juya yaci gaba da saka maɓallan rigarsa. "tsakani da Allah Yaya Haidar me kayi mini?". Na faɗa ina zubar hawaye. "ni me zanyi da wannan ƙazamin jikin naki?, Ki dai tambayi aljanun kanki dalilin da yasa suka zo min ɗaki". Na kalla jikina nace, "ni ba ƙazama bace, Kuma ba mai aljanu bace. Lafiyata ƙalau, kuma indai ba kaine ka kawo ni ɗakinka ba wane zai kawo ni". na faɗa ina hararan bayansa kamar yana gani na. rashin amsa min da yay naci gaba da cewa, "to ma babu abinda kayi min mene ya kawo ni ɗakinka? Bayan ni bana shiga ɗakin wanda ba muharramina ba, ɗakin naka ma wai a jikinka. Gaskiya ni dai ka gama cutata wallahi, duk tanadin dana gama yi sai daka kusa rusa min, kawai kasani a jikinka bayan jikina ba naka bane". Bakina ya matse min da ƙarfi cike da mugunta, na rasa yanda zanyi na ƙwaci kaina hakan yasa na bashi mintsini a bayan hannu, babu shiri ya sauke hannunsa yana yarfewa, yana ƙarewa jikina kallo ya taɓe baki yace. "iina abin yake da har kike wani banzan tunaninki, ni ko da kuɗi aka haɗani dake aina fi ƙarfin wannan ƙazamin jikin naki... kuma wanne dare ne jemage bai gani ba kike faman ɓoye-ɓoye, karki manta a gabana kika girma, hasalima ni na fara saya maki pad, to maye ne ma za ki ɓoye min wanda ban sanda da shi ba, to idan ba ki sani ba ki sani akan idona komai naki ya haɓɓaka Yarinya". Sai kuma yaja tsaki yana cewa, "mtswwww wani ne can dai zaiyi sha'awarki amma bani Aliyu Haidar ba, wata ƴar ƙanƙanuwa dake ma ni mai zanyi sha'awa to". Amma Yaya Haidar ɗan iska ne, wai a gaban idonsa komai nawa ya gama haɓɓaka, wayyo Allah nah anya kuwa bazan kurma ihu ba ko na sami sassauci, Wani sabon baƙin ciki ya kuma tsaya min a wuya, kai tasowar yarinta a gaban namijin da gida guda kuka tashi bai yi ba, ƙunƙuni na shiga yi wanda hakan yasa shi matse min fatar ciki a salo na mugunta. Ƙara na saki ina cire hannunsa daga wurin, ya bige hannun nawa yana faɗin. "maimata me kike cewa?". "ni fa ba abinda nace". "ƙarya kike yi, ki faɗa a fili mana idan kin cika mara kunya". "to ai kaine kana cewa babu abinda zaka yi da ni, kuma dai ni nasan ba haka bane sai dai idan baka da lafiya ne. Kana ganina ba ƙwaila ba, yanda nake ƴar duma-duma da ni ai duk wani mai cikakkiyar lafiya sai yayi sha'awata. Kaima dan na taso a gabanka ne shiyasa kake raina girmana". Na faɗa ina zumɓuro baki gaba, sai faman ƙifta idanu nake, kuma duk a tsora ce nake da shi, kallon yanda yake jan gemunsa nasan wani shirin salon muguntar yake haɗawa a ransa, domin wannan munafikin murmushin nasa ba na Allah bane. "ni dai ka matsa min na wuce tunda Allah ya kiyaye ni baka yi min komai ba. Amma fa kasani sai na kwashe komai na faɗawa Gwaggo". Na faɗa ina mai ƙoƙarin ɗauke hannunsa daya tokare ni a jikin bango. Ƙwafa naji yayi wadda tasa na ɗago ido ina kallonsa, ban ankare ba kawai naji saukar bakinsa cikin nawa yana kissing ena da salo na mugunta, ture shi nake ina dukansa a kafaɗa amma yaƙi sakina saima cizo daya bani a leɓe, kuka na fashe da shi ina buga masa Allah ya isa acikin zuciyata, Zare bakinsa yayi ya ɗago yana kallona fuska a ɗaure yana aika min harara. ni ko na kai masa duka nace, "Allah ya isa ban yafe ba". Na faɗa ina ture hannunsa zan wuce, Raina a matuƙar ɓace, tunda uwata ta tsuguna ta haifeni Gwaggo ta raineni babu wani namiji daya taɓa riƙen ko da hannu, sai Yayana kawai dana taɓa riƙe nasa, shima kuma wallahi bana sanin lokacin da nake riƙe masa hannu, amma yau wani ƙaton banza ya haɗa bakinsa da nawa, bayan naci burin mallakin zuciyata ne kaɗai yake da wannan damar. Allah ya isa dana ja ita ta bashi haushi, ya fizgoni ya haɗani da jikin bango, sai daya ɗalɗalle min baki kana ya kuma manna bakinsa da nawa, Yanzu kam harshena ya kamo yana dannewa da haƙorinsa yana cizawa, sosai nake jin zafi amma bai ƙyale ni ba sai daya tabbatar jikina yayi laushi kana ya rabu da ni. "kinga yanzu sai kiji daɗin yima Gwaggo bayani, mara kunyar banza kawai". Ya faɗa hakan yana nufar ƙofa yasa key ya buɗe, bai ko kalli inda nake ba yace da ni, "zo ki fice min a ɗaki, ko na ƙara maki wanda yafi wannan". Yo baima kuma wani yunƙurin magana ba nai wufff na fice da guduna har ina waiwayan bayana kar ya biyoni. "mugu azzalumi ɗan iska kawai, kuma na rantse sai na faɗawa Gwaggo". Shine abinda nake faɗa har na iso side ɗinmu, Haka kawai ban iya rashin kunya ba yau yasa na farata, ina zuwa bakin ƙofa na saita kaina sannan na buɗe ƙofa na shiga, a parlo na sami Gwaggo zaune tana sauraren karatun ƙur'ani suratul baƙara, ta taso da sauri tana min magana ni kam nayi mata shiru na wuce ɗakina. Ina shiga na faɗa toilet na ɗauka brush da macline na shiga goge bakina kamar zan ɗaye fatar jiki. Sai dana tabbatar na goge ƙazantar bakinsa kaf sannan nai wanka na fito, ina fitowa naji wani warin turare mara daɗi ya daki hancina nayi saurin toshe hancina da bakina da towel ɗin da nake goge ruwan kaina. _"to wannan hayaƙin fa na mene?"_
Na tambayi kaina, sai naji Gwaggo ta shigo tana faɗin, "Sabina kin fito?". Ni dai ban mata magana ba saboda duk warin turaren nan ya isheni, makunnan AC naje na ware haɗe da fanka, sannan na ɗauko air freshner na feshe ɗakin, sai dana juye kwalbar duka amma fitar warin nan ko gezau, naji ba zan iya ba na buɗe closet na ɗau hijab na fice da gudu a ɗakin ina tari, ina sauke numfashi kamar wadda taci gudu, ga amai dake taso min. "sannu". Gwaggo kawai ke jaramin duk bata cikin natsuwarta, sai firfita take min. "Gwaggo wannan wane irin turare ne aka saka min a ɗaki, nafa aljanu ne ma, kinji kuwa kamar kayan cikina zasu fito". Na faɗa ina jera tari, maƙogarona har yaji yake min. Tausayina ya cika Gwaggo, bata iya amsa min ba sai ji nayi ta kirani, "Sabina". Muryarta a hankali kuma cikin damuwa.
Na ansa mata ina ɗagowa na gyara ɗaurin towel ɗina, ajiyar zuciya ta sauke tana faɗin, "to masha'Allahu, Allah ya ƙara miki lafiya ya yaye miki lalurar dake damunki". "amin". Na amsa saboda adu'a ce tayi min me kyau ba tare da sanin inda adu'ar tata ta dosa ba. sai dai dubanta nake da rashin fahimta, saboda yanda damuwa ta bayyana ƙururu a fuskarta, cikin wani yanayi na tashin hankali da ban taɓa gani a ƙwayar idonta ba. "Gwaggo menene? ko kina tunanin banda lafiya? Allah lafiyana ƙalau ki daina tada hankalinki kinji, kinga zuciyata zata shiga damuwa da wannan sabon yanayin naki...ko kuma wani abu ya faru ne?". na faɗa a sanda na taso daga mazaunina na dawo kusa da ita, na dafa hannayenta dake kan cinyarta, ina tsareta da idanuwa. sai tace da ni,"a'a ba abinda ya faru, kuma ai ko ƙalau kike abune mai kyau nayi miki adu'ar samun lafiya Sabina". Ta ansa min tana miƙewa daga kusa da ni ta isa friedge ta ɗauko wani jarka da ruwa a ciki, a cup ta tsiyaya min ruwan ta miƙo min tace,"ungo nan shanye". ni dai kallonta nake da sauyin da nake gani a tare da ita, na amsa na kafa kai zan kurɓe, ɗacin maganin yasa nai saurin ɗauke kofin zan miƙe naje na zubar dana bakina saboda ruwan ba daɗi wanda sai yanzu na fahimci na magani ne. murya a ɗage tace, "dawo ko na saɓa miki, ruwan magani ne maza haɗiye shi, idan ba so kike ranki ya ɓaci ba to karki dawo min da shi". Fuskar Gwaggo babu wasa ta ke min wannan maganar, gaddama na saka mata sai da naga da gaske ta ke kana na haɗiye don dole, kuka ne kawai ban sanya ba. Ina faman yatsine fuska ne nace, "to ni wai don Allah Gwaggo taya ma za ki haɗani da magani bayan lafiya lau nake, ai ba haka ake rayuwa ba, ni dai gaskiya karki kuma min haka domin wannan cuta da cutarwa ne". "ai ban san kina min faɗa ba sai kin rufe ni da duka Sabina". "ni fa ba faɗa nake miki ba Gwaggo, ina gaya miki gaskiyar abinda bana so ne". Na faɗa ina yin narai-narai da idanu. "hmm nayi miki uzuri ƙila har yanzu ba ke bace, da kika taho Haidar yana ɗakin nasa ne?". Baki na turo gaba bance mata komai ba, ta doka min tsawa, "ba tambayar ki nake bane ki ka wani turo min baki gaba kamar zumɓutu, za ki maida shi ko saina bige miki laɓɓa". "to ni ina zan sa ni ne?". "ke kr ki maida ni sha uku, ba daga ɗakinsa kike ba?". "ni mene zai kaini ɗakinsa to, ni tun ɗazu da muka dawo ban kuma ganinsa ba, ƙila yaji faɗanki yaji haushi ya tafi gidansu". Ƙaramar dariya kawai naga Gwaggo tayi ta miƙe tana magana ita ɗaya,
"wato da mai aljanu da mahaukaci dai basu da maraba, ni dama tunda naga kin shigo kin wuce fuuu kamar tashin iska nayi tunanin bake ɗaya bace, ile kuwa haka yake, to Allah ya sauƙa amma ni wannan abu naki da mamaki da kuma tsoro. Bari dai Haidar ɗin ya shigo naji sauran bayani daga bakinsa". "au wai Gwaggo kinma san ya sace ni ya kaini ɗakinsa kenan, bayan sarai kin san shi ɗin mugu ne. Kuma fa kene kike min faɗan ko ɗakin Yaya Abba baki yarda na dinga zuwa ba". "hmmm ba za ki gane bane, ni dai yau na gode masa saboda ya taimakemu. Ɗan ƙwal uba ashe yaron nan kwanyarsa cike ta ke da baiwar ilimi. Ai naga ranar Haidar yau, kuma na gode masa, dan da ace Abba ne kawai a gidan nan abin ba zai yi kyau ba tunda shi wannan bayan karatun sallah babu abinda ya iya sai buga ƙwallo". Ni dai taɓe baki nayi na gyara zamana ban ce mata komai ba. "aike Yau ki manta da duk wani rashin kyautawa da Haidar yay miki a rayuwa, ki gode masa saboda ya taimakeki". "a tsotse min bakin nawa da yay shine ya taimake ni?". A zabure naga ta yar da tsumman dake hannunta wanda ta ke goge ruwan daya zube. ta tsare ni da tambayan, "ban gama gane ya tsotse miki baki ba, bakinki dana sa ya haɗa yana tsotsa ko me?". "ehh mana, kawai ya kamani ya haɗani da bango yay ta totse min baki kamar ya sami alawa, ina ta ihu ina kiran sunanki ba ki kawo min ɗauki ba, har da cizar min leɓe yayi saboda mugunta gashi nan wurin har jini sai da yayi". Na faɗa ina kaurarra maganar yanda Gwaggo zata fusata. tsumman ta ɗauka taci gaba da goge ruwa tana cewa, "to ya zaiyi dole ce ta saka, sai yayi hakan za ki sami kanki". sai nace, "Gwaggo idan na fahimceki haɗa baki ku ka yi dai da shi kenan, shi yasa da nace zan faɗa miki ya ƙara totse min baki yace sai na faɗa miki da hujja...". sai tai saurin Katse min maganata da cewan, "keee ni fa ki daina ambatar min tsotsar bakin nan haka. Ki dinƙa cewa yayi miki tofi shine kawai, amma kya dinƙa cewa ya tsotse miki baki kamar wani ɗan iska". Ban ƙara ce mata komai ba na miƙe na bar wurin cikin fushi ina faɗin, "kuma sai dai idan Baba bai dawo ba, sai na zayyane masa komai. Ai Allah ya hana ko da riƙe hannun mace ne wanda ba muharraminta ba yayi, amma shi kaɗan ne ya rage bai min ciki ba". Ashe ta jiyo ni, tace, "kamin ki zayyane masa ni zayyane masa, ai dama dole muyi zama da shi akan wannan baƙon lamarin naki. Gaɓuwa kawai". Da daddare bayan mun kammala cin abinci, muka zauna kallo a parlo, Yaya Abba ne da Yaya Haidar suka shigo, kowanne kujera ya nema ya zauna, nayi mamakin ganinsa, amma sai na bar mamaki duk yanda akayi sun shirya da Gwaggo ne. Yaya Abba na zama yace da Gwaggo, "ina abincina?" tace, "acici mala'ikun tauna, kai daka shigo gida ina abincin ka an dafa ko ba'a dafa ba, to jeka kitchen ka ɗauka, Matarka dai ta shiga uku da ɗora sanwa dan ba zaka sassauta mata ba". Ya miƙe yana dariya ya wuce. Shi kuwa goga uban ƴan ji da kai tunda ya shigo ya zauna bai magana ba, sai faman latsa waya da yake yana wani harhaɗe rai, ni duk haushi ma yake bani, saboda bana son mutum mai faɗin rai, ni yanzu ma bana ganin girmansa tun abin ɗazu daya mani, a hakansa kamar salihin bawa nan kuwa iskanci ne fal a cikinsa. Naji Gwaggo tace da shi, "Haidar ina fa daɗa godiya a gare ka kaji". "ba komai, ki godewa Allah kawai".Ya faɗa a taƙaice, still kansa na kan wayarsa. tace,"uhm ai dama godiyar Allah ta zama dole bare ka gayamin magana. Kaine dai da nake mamaki ya kamata na maka godiya, saboda yau ka shayar dani ruwan mamaki, yanda naji kana rera ƙira'ar nan kamar Sudais". Sannan ta juyo kaina tace, "Sabina ki masa godiya kinji ko". Sai yanzu na ɗago kaina dake kan waya, ina faman murguɗe-murguɗe da harare-hare na ɗaga idona na kalle shi, karaf muka haɗa ido, sai dana tsuke fuska na taƙarƙare na murguɗa masa baki, hakan yasa shi sakin ƙwafa mai ƙarfi yana jijjiga kai. Gwaggo ta sake cewa da ni, "ke wai yanzu ba'a isa ace kiyi abu a lokacin ba kiyi ne?". yace da ita, "ba ki kalla murguɗan baki ta ke yi ba saboda bata da kunya, to wallahi ni tashi zanyi