Showing 9001 words to 12000 words out of 89788 words
mani adu'a". Ya dubeni cike da soyayyar uba ga ƴarsa sannan ya ɗora hannunsa saman kaina yace, "Sabina Adu'a ta zama dole, kije Allah yay maki albarka, ya baki masara a rayuwarki. Allah ya kaiki lafiya ya dawo dake lapia ya kareku a duk inda kuke". ina murmushi nake amsa mishi da,"amin Baba nah na gode sosai, Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana". Gwaggo ma tayo tata adu'a sannan na fita, Har naje soro sai kuma na dawo, saboda tunawa da nai akwai inda nake son zuwa kuma banda kuɗin mota, satina guda kenan rabon dana fita waje, dama inda makarantar boko ne nake ɗan samun canji a hannuna, to anyi hutu, itama kuma islamiyar sai yaune muke komawa. to yanda na ƙwallafa rai da zuwa inda nake so naje yau ai yacce Baba ya shigo dole na nemi kuɗi. ganin na dawo Baba ya shiga tambayana me ya dawo dani, ni kuma kai tsaye nai masa ƙaryar zan siya littafi ne na manta ban karɓi kuɗin ba. na faɗa masa ina tsoron kar yace babu kuɗin a hannunsa amma naje zai shigo makarantar anjima yaywa Malam Saminu magana su bada bashi kaman yanda aka saba. Allah ya taimakeni sai naji kawai yana tambayana nawa ne kuɗin, da yake ban saba da ƙarya irin haka ba sai na rasa nawa zance, na tsaya ina kame-kamen kamar 200 kamar 150, sai kawai ya zaro 500 ya bani yace na riƙe canjin idan yayi saura, na kuwa amsa murna fal raina inata zabga masa adu'a. shima kuma ya shiga yi min adu'ar Allah ya jiƙan mahaifiyata ya haɗani da miji na gari.
ko da naje islamiya bayan an gama yi mana ƙarin karatun ƙur'ani mu ƴan manyan aji, sai aka kiramu aka rarraba mu zuwa sauran ajujuwa domin kula da yara sakamakon Malamai zasu shiga meeting. Sai biyar da rabi kana Malamai suka gama meeting, kuma a ciki ne har aka tattauna akan cewar za'a ɗauke ni gasar musabaƙar qur'ani ta ƙasa domin na wakilci makaranta kasancewata gwarzuwa. A lokacin da Malamai suka dawo daga meeting muka koma zuwa ajinmu, ina zaune Malam Hussain ya kira ni, nan ya sanar min abinda hukumar makaranta ta tattauna akaina na ga me da zuwa musabaqa, saboda haka saina sanar da iyayena idan zasu bani damar zuwa, kuma duk da hakan suna da buƙatar ganin mahaifina ko kuma wani babba a gidanmu. ina ta murna da farinciki na miƙe daɗi duk ya isheni, dan ni kaina ina alfahari da baiwar ilimin da Allah ya ban. Ƙarfe shida aka tashemu, a bakin gate ɗin makaranta na sami Farhana tsaye tana jirana, ƙirjina rungume da qur'ani na ƙaraso inda take, nan muka jera muka fara tafiya. shiru shiru babu wanda yay magana acikinmu tsawon tafiyar da mukai, kamar bamu ɗin nan da bama rabo da abin faɗa ba idan muka haɗu, hasalima idan aka tashi muka taho bamu da aikinyi sai gulmar Malam wane da wane. can dai Farhana da bata iya haƙura da yin shiru ta nisa cikin ƴar murya tace,"Ƙawata wai lafiya naga kwana biyu kina sha re ni, laifin me nayi miki ban sani ba ƙawalli?". ta faɗa tana dafa kafaɗa ni kuma ina zamewa, fuskar nan tawa na ƙara cukuleta dan sarai na san ta san dalilin ɗauke mata wutar da nai, amma saboda rainin wayo da neman magana take tambayana. dan haka nima saina raina mata nawa wayon da cewa, "ba komai, me kika kalla dama?". nayi mata tambayar kaina na gaba ina tafiya cikin sauri-sauri. ta ƙara cewa,"aikam dai da wani abu, domin ba haka muke da ke ba, amma a ƴan kwanakin nan duk kin wani sauya min". kaman zance mata a'a ko nayi mata shiru, sai na tuna da maganar malaminmu da yake cewa mutumin daya fi kowa shine wanda idan mutum yay masa ba zai ƙullace shi ba, zai samesa ya faɗa masa wane kayi min abu kaza da banji daɗinsa dan Allah karka sake, amma duk wanda zai ƙullaci mutum akan yay masa laifi ya riƙe abin a ransa yaƙi faɗa maka, ko kun haɗu a zuciyarsa zai gaisa da kaine ta dole yay maka yaƙe to wannan mugun mutum ne, ni kuwa bana so na kasance cikin mugwayen mutane. dan haka na ɗan waigo nai mata kallo ɗaya sannan na ɗauke kaina nace,"Farhana ba magana ta wasa ba, da gaske nake faɗa miki bana jin daɗin aibanta min Yaya da kike ko kaɗan, bana so kike faɗan mummunar kalma akansa, ki daina walaƙanta min shi a wajen mutane, idan kene na yiwa Yayanki haka zaki ji daɗi ne?". nayi maganar raina a matuƙar ɓace, sai tayi saurin dafe ƙirji tana faɗin, "ni ko ina na isa na yiwa Yaya Abba haka, rufa ni ki saya". ta faɗa tana nuna kamar bata gane inda maganata ta dosa ba. na jijjiga kai nace, "nasan kin san akan wanda nake magana, amma saboda kina so ki mayar dani ƙaramar ƴar iska shine zaki nuna wani waskewa ko". nai maganar dai-dai lokacin da muka ƙaraso inda motarta ke ajiye, kuma kamin ta buɗi baki tace wani abu sai kawai gani tai na wuce gaba abina, ina jinta tana jera min kira nai mata shiru ban tsaya sauraronta ba, dan banda lokacinta. sai gata ta tsaya da motar a gabana tare da zuge glass ta min magana. "Sabina wai mene kike yi haka don Allah, ya wani banza can zai ƙoƙarin rusa abotar mu tun ta yarinta...". Maganarta ta katse a lokacin dana juya ina cewa da ita cikin masifa,"Malama shi ba banza ba ne, ki fito kai tsaye ni ki kirani da banza tunda ni na shiga rayuwarsa. Kuma karki damu da tafiyata a cikin motarki domin nima ina da ƙafa, dama ban saba da ita ba saboda ban ganta a gidanmu ba. Kije kawai abinki". Daga haka na wuce nayi tafiyata, raina duk a dagule na shiga gida, saboda na gama tsara bayan an tashi makaranta zanje wurin Yaya domin ganin lafiyarsa, tun wancan ranar da yay min gargaɗin kar na ƙara zuwa ban koma ba yau gashi kwana takwas kenan, sai dai hankalina da tunanina duka na kansa, ga yau ɗin dana ƙwallafa rai da zuwa lokaci yay halinsa dan magriba tayi, ga itama Farhana ta ƙara ɓata mani rai, shi yasa duk kaina ya cunkushe. ina ɗaga labule nayi sallama cikin parlo, lokacin Gwaggo na zaman tahiyar ƙarshe na sallar magriba da ake, bayan ta idar da adu'ointa ta juyo tana kallona da yanda nake ta faman ɗacin rai. ta gefen ido na kalla Gwaggo na girgiza kai alamu na Allah ya kyauta kana tace min, "saboda kina fushi ba za ki yi sallar ba kenan ko mene uwar ƴan nurƙufanci". "ina hutu ne". na bata amsa a taƙaice. "to tashi ki ɗauko mana tourchlight a ɗaki, ga battery can kan abun tv ki saka na ciki yayi sanyi". na miƙe naje na ɗauko na kunna haske, sannan na koma kan kujera na zauna, ko uniform ban iya cirewa ba kuma banda niyyar zan cire, sai faman kumbure-kumbure kawai nake. Gwaggo dake ankare dani tai min banza bata bi ta kaina ba, Taci gaba da harkar abinda ke gabanta, can data gaji da ƙwafar da nake jerawa babu ƙaƙƙautawa ta juyo ta wurgo min harara da cewar,"ke wai ƙalau ki ke kuwa, kinzo kin sani gaba kina ta aikin ƙwafa, ko sallama ma fa ina jinki a ciki kika yi ta. Sabina bafa zan ɗauki wannan sabon halin naki ba, ke da waye a makarantar?". ina aikin tsuke baki nace, "ba Farhana ba ce". Gwaggo tayi tsaki tace, "Allah ya gyara ki idan kina da rabon gyaruwa, tun kuna cin ƙasa rabonku da yin faɗa ke da ita amma saboda mahaukacin yaron nan kina son zama fitinanniya ko Sabina. To wallah tun wuri ki shiga hankalinki, ki fita a sabgarsa tunda kinji dai yanda yake, amma zan gyara miki zama ne karki dawo kan layi ki gani". sai kawai na hau bori ina dukan ƙafa a ƙasa kamar zan fashe da kuka. "na rantse da Allah Gwaggo shi ba mahaukaci ba ne kuma ba ɗan iska bane, wallahi da gaske nake miki da kin kalle shi kinga mutumin kirki, sam bai ma yi kama da ƴan daba ba, kawai tsintar kansa a cikin ƙangi na rayuwa yasa ya jefa kansa cikin wannan yanayi, shine ita kuma Farhana saboda rashin sanin daraja ta ɗan Adam ta ke cewa mahaukaci ne. Amma wallah ba shi ba ne, kallo ɗaya zaki yiwa yanayinsa ki gane, kuma ma ai yace min ba zai kuma shan taba ba". baki buɗe tace, "au ya tabbata lahu dai ɗan daba ne kenan, to ai gwara da kika faɗa da kanki na ji. To bari kiji ko ki fita harkarsa ki manta da shi ko kuma na haɗaki da ubanki, tunda ni yanzu ban isa na faɗa kiji ba, zamanin na faɗa miki kiji ya jima da shuɗewa tun ba ki balaga ba". na sakko daga kan kujerar na dawo kusa da Gwaggo na zauna, na kamo hannunta ina cewa,"kiyi haƙuri Gwaggo nah, ba wai bana jin maganarki ba ne. Allah Gwaggo kika kalla bawan Allah'n nan sai kin tausaya masa, har kuka sai kin yi mishi wallahi, kuma ke da kanki za kiji kina son taimaka mishi". "mtswwww". Gwaggo taja tsaki tana watsa min harara tare da ƙwace hannunta. "tashi ki ɓace min anan wurin ko ranki ya ɓaci...insha'Allahu zan kaiki masallaci ai miki sauka". saina miƙe ina faman yarfar da hannu na wuce ɗaki, na kwanta kan katifa nai shiru ina mai jin raina duk babu daɗi, ni kaina na rasa dalilin damuwa da mutumin da ban san wane shi ba, haka kawai nake jin tsananin tausayinsa da son taimaka mishi, har sanda bacci ya fara ɗaukana, sai dai wani abu na ban mamaki dana rufe ido saina dinga ganin hoton fuskarsa na bayyanar min.
Washegari ya kasance Asabar, ƙarfe 9 na shirya domin tafiya Tahfeez, ina yiwa Gwaggo Sallama sai ga sallamar Farhana, ɗauke kai nayi daga kallonta a lokacin data ke shigowa, itama bata kula ba ta duƙa tana gaida Gwaggo.
Gwaggo tace da ita, "ya haƙuri da halin ƙawarki duk da nasan kina yi. amma yanzu lamarinta ƙara ta'azzara yake sai an kai zuciya nesa zama da ita...kin ganta nan tun jiya rabonta da min magana, gaisuwarma yau ko samu banyi ba, ni kuwa tunda Ubanta dai yazo ya gaisheni tata ba abar damuwa bace". Farhana tayi murmushi Kawai ta miƙe a tsugune tana dubana tace, "mu tafi ko". na ɗan harare ta gami da murguɗa mata baki kana nace, "ni ai bance ki biyo min ba. Kiyi tafiyanki kawai". Gwaggo ta rarumi mafici zata ƙwalo min nai saurin miƙewa na fice. "ƴar ƙwal uba da ki zauna mana. Farhana indai tayi wani shirmen ki faɗa min dai-dai nke da ita". Farhana na dariya ta amsa da, "to". tunda muka shiga mota babu wanda ya kula ɗan'uwansa, sai da muka kusa zuwa makaranta ta kama ce min. "wai ke don Allah mene na damuwa da wannan mahaukacin, ɗan daba kawai, ɗan iska wanda bakin uwa yay tasiri akansa, haka kawai yazo zai sanya min ƙawa a damuwa, ni Allah da ace nasan haka zata faru da bamu je amso ɗinkin ba a ranar". na juyo na harareta ace, "ni ina mamakin rashin imaninki Farhana. Duk wanda yaga wannan bawan Allah'n sai yaji tausayinsa, amma ke na rasa dalilin bushewar zuciyarki akansa. kuma kina ta bada shaidar zirrr akansa kina ganin kaman burgewa kike, to tunda Allah yasa islamiya za kije kya tambayi Malami makomar irinku". "irinmu? makomarmu ta me?". "kice Malam Ali mene makomar masu shaidar zirr zai baki amsa". "Sabina zirr fa shaidar ƙarya kenan". "to me kike yi banda ita?". sai tai guntun murmushi tana cewa, "To ni dai tausayinsa ne ba zanji ba, kuma abunda na gani da shi zanyi shaida, mutumin da baya jin tausayin kansa kan me kuma kai zaka tausaya masa. Ai sarai yasan shaye-shayen da yake cutarwa ne a gare shi amma yake yi. Shege ɗan iskan banza kawai". ban san lokacin dana kai hannu na daki stearing motar ba har ina ƙoƙarin ƙwace shi daga hannunta, tai ƙarfin riƙewa da kyau tana tureni. na ɗaga murya cikin masifa nake ce mata, "Farhana na faɗa miki babu kyau aibata musulmi ko da ya kasance yana aikata mummunan halaye bai kamata aibata shi ba. Farhana na roƙe ki karki ƙara furta mummunar kalma akan Yaya, idan ba za ki iya masa adu'ar shiriya ba don Allah kiyi shiru da bakinki akansa...karki ga ina roƙonki, na rantse miki gaba ba zata mana daɗi dake ba". na ƙara maganar ina jan ƙwafa. ita dai ta min shiru bata ce komai ba, domin ta lura akan wannan banzan mutumin zamu iya ɓaɓewa ta har abada. kuma har muka isa makaranta ban bar surfa mata masifa da bala'i ba. kuma ci kanki bata ce min ba sai ma earpice data maƙala a kunne naci gaba da haushina ni ɗaya, aiko sai dana tsinka shi. Ƙarfe 2 aka tashemu a makaranta, maimakon nai gida saina tari napep nace ya kaina sharaɗa, ban ko bari mun haɗu da Farhana ba dan Malam na fita na fito kasancewar bamu zauna sit guda da ita ba. Dai-dai kan layi nace mai nepep ɗin ya saukeni, na ciro kuɗinsa a jaka na bashi, ina yankowa wajen bolar kuwa na hange shi a bakin wani tanki ya kunna famfo ya duƙa yana shan ruwa, yauma dai jikinsa fes yana sanye da yadin dana ganshi tun a ranar farko, da alama dai siturarsa ɗaya ce, sai Allah masanin lokacin da yake cirewa ya wanke su. yana gama shan ruwan kuma ya koma can inda ya ke zama ya zauna, da zamansa ya zaro taba sigari cikin aljihu ya kunna ya fara zuƙa. haka kawai sai naji zuciyata tayi matsewar da bata taɓa yi ba, sam-sam bana ƙaunar ganinsa da wannan sigarin ban san me yasa ba, sai naji ƙafafuna na saurin tafiyar da zance basu taɓa yi ba har na ƙarasa gare shi. kansa na duƙe kamar yanda ya saba idan zai sha, ina isa na zare sigarin daga hannunsa a hankali na jefar, fuskana a haɗe.
abunda ban sani ba tun ɗazu ya hangeni sai dai baiyi tunanin ni bace kasancewar niƙab ne lulluɓe a fuskata, sai yanzu dana zo na ƙwace masa sigari ya gane ni ɗince shi yasa ya kawar da kansa. yanzu na riga na saba da wajen da yake rayuwarsa, bana jin ƙyanƙyami ko kaɗan, warin sigarin ma yanzu na saba da shi, na naɗe hijab ɗina na durƙusa a gabansa dai-dai saitin inda fuskarsa take. sai ya sake ɗauke kansa ya maida ɗayan gefen, nai murmushi na ɗaga niƙab ɗina ina sunkuyar da kai na leƙa fukarsa nace, "Yaya ni ce fa, fushin na menene? ƙanwarka ce fa Sabina ka juyo ka kalleni". bakinsa ya motsa a hankali kamar ba maganar zaiyi ba yace,"na san kece ai". sai na ɗan shagwaɓe murya ina faɗin,"to amma shine kake ɗauke kai daga gare ni". Yace,"bana kula mara jin magana ne". "Yaya rashin jin maganan me nayi kuma?". na faɗa ina ɗan marairaicewa. ya ɗago ya duben sau ɗaya wanda ya sanya shi jin faɗuwar gaba yace, "bana hanaki zuwa wurina ba, kina so na yi miki fyaɗe ko?". Da mamakin dake haskawa cikin ƙwayar idonsa na rashin tsorota da irin wannan furucina yasa ya tsareni da ido. sai nai siririyar dariyar data bayyanar da fafaren haƙorana kamin nan nace. "Yaya ba zaka fasa tsorata ni da wannan kalman na fyaɗe ba, haka ba zan fasa faɗa maka kai ɗin baka yi kama da macuci ba, kowa ya ganka yaga mutumin kirki, dan haka ka aje barazanarka a gefe". sai yace,"shi dama mugu yana da kama ne?". saina girgiza masa,"ko kusa, hasalima sai kake rayuwa da mugun mutum tare da kai ba tare daka sa ni ba...amma ko menene dai kai ba mugu bane". da ƙaramar murya naji ya kirayi sunana, "Sabina". na amsa, "na'am Yaya nah". "don Allah ki daina zuwa wurina, kar mutane suyi miki mummunar shaida irina, kinga ke ɗin halinki mai kyau ne". Na gyara zamana ina dubansa nace, "Yaya nah ni macece da bana mu'amala da wanda baya jin kunyar Allah, wanda yake saɓon Allah, amma yau gaka kai kuma ka tsaya min a rai, irin tsayawar da har na fara tsorata, ina tsananin tausayinka, hakan yasa na kasa barinka domin kai ɗin ina jinka ne tamkar jinina". Yace, "na gode da har kika iya fahimtata saɓanin mutane da yawa. Amma ni dai ina roƙonki da ki bar rayuwata". "Yaya bazan iya barinka ba a halin da kake ciki". Na faɗa ina zura hannuna cikin aljihunsa ba tare daya sani ba, sai a lokacin dana ɗauko kwalin sigari na nuna mishi ina cewa. "Yaya wannan hatsari ce ga rayuwarka. Kaji tsoron Allah ka daina shanta, Hakan da kake yi yana nuna cewar baka tsoron Allah ne, nasan cewar halin rayuwar daka tsinci kanka shi ya jefa ka cikin wannan halin, amma me yasa ba zaka amshi ƙaddarar da Allah ya jarabce ka da ita da hannu biyu ba? Bayan kasan cewar yarda da ƙaddara Mai kyau ko mara kyau suna cikin shika-shikan imani. Manzon Allah S.W.A yana cewa da ace zaka ciyar da kwatankwacin dutsen uhudu na zinare cikin ɗaukaka Addinin Allah, lallai ba zai karɓa daga gare ka ba har sai kayi imani da ƙaddara. Yaya nah don darajar Allah ina so daga yau kaji tsoron Allah ka daina saɓa mishi, ka nisanta kanka ga waccen abar mai cutarwa". sanda nai shiru na ɗago ina kallonsa, wanda idanunsa suka cika da ruwan hawaye a dai-dai lokacin kuma suka sami nasar zuba. Tausayinsa ya ƙara damƙar zuciyata, Allah kaɗai yasan wanne hali wannan bawa nasa ya shiga a rayuwa, a raina nayi adu'ar _Allah ka kawo mishi mafita._ Tunda ta fara magana ya kasa ɗauke idanunsa akanta, wani abu a ga me da ita na shiga zuciyarsa, tunaninsa ya katse sanda naci gaba da cewa,"Yaya nah zaka iya