Showing 84001 words to 87000 words out of 89788 words
kawo yace a ba ki inji Malaminku". ta amsa ba tare da tace komai ba, ta miƙe cikin sauri zata wuce ɗaki gudun kar Mami ta tambayeta menene, aikuwa bata ida zance zuci ba Mami tace,"wait, weting be inside the leather?". shiru tayi tana tunanin abin cewa, ta doka ma ta tsawa da sake faɗin,""am i not asking you? bani nan na gani". ta faɗa tana miƙa hannu zata amsa ita kuma duk da haka taƙi bata, gashi har yanzu ta gagara sharto ƙarya da zata faɗa tunda bata saba ba. Mami ta kama ƙugu tana kallonta, kamin tayi kanta tana cewa,"ke dan ubanki what are you hiding from me da ba kya so na sa ni? mene aciki nace?". ganin zata duketa tace,"Mami magani ne". "Magani!". Mami ta faɗa da mamaki, kamin ta ƙara cewa,"wanne irin magani? ciki kika yi da Malamin makaranta zai kawo miki maganin zubarwa?, maganin mene? ko kuma da gasken ciki ki kai kamar yanda tunanina ke bani". ta tambayeta a tsawace, jikinta na kyarma ta hau girgiza kai tana cewa,"Mami ba ciki nayi ba. Maganin Brother Muhsin ne, na faɗawa Malaminmu matsalan ciwon ƙafarsa ne shine yace zai ke taimaka mana da tofi na adu'a a dinga bashi insha'Allahu zai warke". Mami ta hau jijjiga kai tace,"Allah zabiya, kice kin shahara da yawa. to shi dama Hassan ɗin ce miki yay yana biɗar taimako daga gareki? a'a ko dama duk cusa kan naki ne ya shura haka?". tana girgiza ma ta kai tace,"a'a kawai dai nce nasa ake masa". "to dama kin kai tsawon yaushe kina karɓar masa maganin?". "an kwana biyu, shine ma har yaji daɗi yanzu yana iya motsa ƙafan kaɗan...". ai bata ƙarasa ba Mami ta kunce ledar ruwan tofin adu'ar ta watsa ma ta shi tas a fuska. "shegiya uwar cusa kai da neman gindin zama. ina tambaya kuma kina bani amsa ko kunya, ke alallai sai kinyi suna a wurin ubanki ko, saboda kinga babu abinda yake ƙauna sama da ɗansa. to kije kici gaba da wahalar da kanki kina karɓo masa magani, wannan ɗa dai yanda kika taso ki ganshi a haka har abadan abadina ba zai taɓa takawa ba, a haka zai ƙare a wannan keken. kin ma ji na gaya miki, insha'Allahu ba zai warke ba, ni da ace ma ina da damar da zan ƙarasa ƙafafun ai saina ƙarasa su ko da kuwa da bin bokaye ne, dan haka sai kiyi ta wahalarki mu gani da adu'arku da tawa wacce amsashshiya". ta shige ɗaki ta barta anan, ita kuma ta durƙushe tana kuka cike da takaicin wannan hali na uwarta. Abid ya shigo ya sameta ahaka, ya nemi kujera ya zauna a hakimce yana ma ta wani mugun kallo, ƙafa ɗaya akan ɗaya yana girgizawa. "kin bar kukan nan ko saina tashi na zane miki jiki". yace da ita murya a ɗage. ta dube shi tace,"Bross dan Allah ka cewa Mami ta sauya halinta wannan ba hali ne mai kyau ba". shima murya a fusace yace,"ke ai jaka ce, ba ki san inda yake miki ciwo ba sam. taya za'a Mami ta ƙaunaci mutanen da suke sa ubanmu ya muzguna mana. tunda kike kin taɓa ganin Daddy ya ɗorani akan wani harkar business ɗinsa?, ya ɗau komai ya bawa wancan Muhsin ɗin, shege Allah ne ma yasan manufar jaki da bai bashi ƙaho ba, shi yasa aka riƙe masa ƙafafu". ta tashi zata wuce ɗaki tace,"ai mai gaskiya ake ɗorawa akan komai ba maha'inci ba. da kayo kyawun hali irin nasa da babu ta yanda Daddy zai nuna banbanci tsakaninku". tana ganin ya biyota tai hanyar ɗakinta ta gudu, tana faɗawa ciki tasa key ta rufe tana sauke nauyayyar ajiyar zuciya, dan da ace ya kamata sai taci ɗanyen kashinta yau. washe gari ƙarfe biyu na rana Daddy ya dawo daga Italy daya tafi. Muhsin na zaune kujera ɗaya da Daddy a kusa da shi, suna magana ƙasa-ƙasa da alama zancen sirrinsu ne, suma gefe ɗaya su Mom ke tasu hiran. Daddy ya lura tun ɗazun idon Muhsina na kansu, so kawai ta ke taji me suke cewa, yay murmushi cike da tsokanar ƴar tasa ya kuma yin ƙasa da kansa suna ci gaba da mgana. da ƙarfi Muhsin yace,"a'a Daddy ba ita ya kamata a bawa sabon company ba, Muhsina ai tayi yarinya da yawa, macece fa ita ba zata iya aiwatar da ayyukan company ba, a barta kawai da lecturing nata idan yaso sai a bawa Abid, shi zai iya lura da komai". ai kuwa tana jin haka ta miƙe ta fara dukan ƙafa tana kukan shagwaɓa har saida ya koma na gaske, tana cewa da Mom,"Mom kinji abinda Brother yake cewa ko, shi dama duk abinda yaga za'ayi min sai yace a'a, shi Abid ɗin ba ni ke gaba da shi ba. haka fa aka yimin wancan karon ma, ni dai gaskiya Daddy ban yarda ba". Daddy yana dariyar manyance yace,"to kwantar da hankalinki Daughter nah, we're just kidding you". sai ta fara dariya itama ta dawo kusa da Daddy ta zauna, yasa hannu ya kwanto da ita jikinsa yana faɗin, "wato dai sirikina zai sha fama, har yanzu kinƙi girma". kunya ya bata tai saurin rufe fuskarta. Muhsin na duban Mahaifiyarsa yace,"Mom kin manta ba ki faɗawa Daddy saƙona ba ko?". tana masa wani duba tace,"O'O! ba mantawa nayi ba, ina jira ne ya gama hutawa sai na sanar masa". Daddy yace,"hutun mene dama zan kuma yi?, good 3hours da dawowa na fa, hutawana yafi saƙon ɗana ne?". yay maganar da sigar faɗa. tace,"kayi haƙuri, dama cewa yay na sanar maka aure yake so domin ya samu mata, sauran bayani kuma kaji daga gare shi". Daddy ya dubi ɗansa cike da farinciki a fuskarsa yace,"are you serious? da gaske ne ka samu wadda ta yarda da aurenka a haka?". Ya ajiye file ɗin hannunsa gefe guda ya kamo hannun Muhsin yana daɗa kallonsa yace,"ina jinka son, ka sakani a farinciki, wace kake so kuma take sonka?". Shafa ƙeya Muhsin yay yana sunkuyar da kai ƙasa yace,"Daddy da gaske ne, Yarinyar ta aminta da ni". sai kuma ya marairaice fuska yace,"amma Daddy kar ayi westing time saboda ina gudun mahaifinta ya bawa wani ita, ba zan iya jurewa ba". Murmushi Dad yayi, ya shafa kan ɗan nasa shima kuma ya shafa gemunsa kafin yace, "Okay Son, Anything for you, ba zanyi sanya ba zaka sameta insha'Allahu. Uncle naka baya nan yana Cairo, but ending of this week zai dawo, so as soon daya dawo za muje mu gana da mahaifinta". Muhsin ji yake kamar zai mutu dan murna, ya kusa mallakar Beauty tasa, duk da ya yarda bata sonsa amma ya yarda zata so shi yayin daya mallaketa. Daddy yace,"Anan garin ta ke ko a wani state ɗin ka samo ta?". yace,"anan Abuja ta ke sai dai ban sa ni ba ko ƴan asalin ina ne". "Okay son, it shall be well, za muje ayi komai, worry not kaji. but can i get some information about her? like part of her education and her parents". yace,"Yeah Dad why not, her name is Sabina Auwla, she is one of my students yanzu haka L1 ta ke, she is well educated both arabic and boko, her father is the MD of PHCN. I recently went to their house, kuma da ganin gidansu gidan mutunci da karramawa ne duk da ban samu ganawa da wani a gidan ba, amma naga hakan daga wurin gate man nasu". "Okay Son, kamar an gama ne, karka wani damu kaji, kasa a ranka kama gama samunta". Cike da jin daɗi Muhsin ya rungume mahaifinsa, ya kuma buɗewa Mom hannu itama, ta taso daga inda take tazo ta rungume shi, Wadda kallo ɗaya za kai ma ta kasan tana farinciki da wannan maganar. Muhsin yace da Anie,"Anie ke ɗaya ne ba za ki tayani murna ba?". tana shafa makekiyar wayarta tace,"to Alhaji Hassan murnar me zan tayaka alhalin kana ƙoƙarin yimin kishiya. ai sai dai kawai na bika da adu'a Allah yasa yarinyar ƙwarai ce". Muhsina ta amsheta da cewa,"wallah kamar kin sa ni Anie, ga kyan hali gana fuska. wallahi duk kyauna dana ganta sai dana raina kaina, ai Brother nah yay dace, har na hangosu a lokacin biki". Daddy yana riƙe da hannunta yace,"kema Daughter ina roƙon Allah ya fito miki da miji kamin zuwan lokacin, na haɗaku gaba ɗayanku. ba ƙaramin farinciki zanyi da wannan rana ba". Haka dai suka ci gaba da harkokin su, Anie na cewa ta fasa tafiya har sai kishiyarta tazo ta gaisheta. da daddare kuwa Daddy ya shiga ɗakin Mom, ya sameta zaune a tsakiyar gado hannunta riƙe da wani medium enlargement tana kallo tana kuka. cikin hanzari ya ƙaraso gareta, ya amsa hoton daga hannunta ya ajiye sannan ya kwantar da kanta bisa kafaɗarsa yana lallashinta, sai da ƙyar ya samu ta tsagaita da kukan. yace,"yanzu Sweetheart har sai yaushe ne za ki bar wannan kukan umm? Mutasim fa ya tafi inda ba'a dawowa ya kamata ki haƙura ki fawwala Allah". tace,"Daddy a kullum ina ji ajikina wataran Mutasim zai dawo. ko a jiya nayi mafarki da shi, nafi tunanin yana raye bai mutu ba, kawai dai yana cikin wata rayuwar ne". Daddy ya sauke ajiyan zuciya yace,"but you know that dreams are not real. How can a person who has been missing for 27 years be back?, think of yourself. If he were alive ai da mun ganshi, dan Allah ki daina yawan sa shi a ranki kar wani ciwon ya kamaki". ta ɗago ta dube shi tana cewa,"Daddy karna ƙwallafa abinda na haifa a raina kenan? ni fa rashin ganin gawarsa ita tafi damuna, naso ace naga gawarsa nayi masa adu'a, yaron da bai jima da gama shan nono ba, rashin ganin gawarsa yasa har yanzu na kasa yarɗa da cewan ya mutu, Allah kaɗai yasan a wacce rayuwa yake ciki yanzu". kuka ta fashe da shi sosai, Daddy yaji tausayin matar tasa a ransa matuƙa, yana shafa bayanta yake bata haƙuri da lallashi har ta samu nutsuwa. daga nan ya kashe musu fitila suka kwanta yana manne da ita a jikinsa.
ɓangaren Muhsin kuwa tunda ya shiga ɗaki yake a fargaba, yanzu idan su Daddy suka je gidan su Beauty suma tace musu bata sonsa ya zaiyi? ya riga ya kamu da sonta wanda zai iya shiga wani hali a dalilin rashinta. wayarsa ya ɗauko yay dialling numba nata, domin ko kaɗan shi bai yi fushi da ita ba da abinda tayi masa, ya ma ta uzuri ne kasancewarta yarinya. haka wayan ya ƙaraci ringing nasa amma ba ta ɗaga ba, sai dai ya kwana da tunanin dole sai ya kama ƙafa da Yayanta da ta ke yawan masa zancensa, tunda ya lura tana sonsa tana kuma jin maganarsa, wataƙila idan yabi ta hanyarsa ta amincewa ƙudurinsa.
[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*
_By Oum Ramadhan✍🏼_
*(29)*
"ka cire soyayyarta daga zuciyarka, ka cire burin aurenta a ranka...ka barta a wannan matsayin da kuka fara bawa juna tun farko". "saboda me?". "saboda ba zaka sameta ba, Hussain ba zaka aureta ba muddin ina numfashi a doron ƙasar nan". wannan furucin shi yasaka Alhussain saurin zuro ƙafafunsa ya sauko daga kan gadon, ya miƙe tsaye akan ƙafafunsa yana ƙarewa bayan matar da baya iya kallon fuskarta kallo, kallonta yake da saƙawar mabanbanta abubuwa acikin ransa. sai dai a duk abunda ya saƙa ɗin baya iya warware shi, saboda haka yayi tattaki zuwa inda ta ke a tsaye jikinta naɗe da lafaya brown colour, tana fuskantar kusurwar ɗakin nasa ta ɓarin hagu, daga tazarar da ba zata wuce inchi 2 ba a tsakaninsu ya dakata. sannan ya tattaro yawun bakinsa da yaji kamar yana neman ƙafewa yace da ita,"wace ke?". shiru tayi masa bata bashi amsa ba, ya rufe ido ya zuƙi numfashi, gami da sanya hannu ya shafo sumar kansa yana kaiwa cinyarsa duka. "Wace ke? kuma me yasa kike min waɗannan maganganun?". ya ƙara tambayarta amon muryarsa na cika ɗakin gaba ɗaya. maimakon amsar daya tsammaci ji daga gareta sai yaji sautin murmushinta ya fita a hankali, wanda ya tabbata murmushin ya tsaya mata iyaka leɓe ne kawai duk da cewar bai ga fuskarta ba. zuciyarsa tayi wani zafi dan haka bai san lokacin daya ɗora hannu a saman kafaɗar matar ba dan juyo da ita, amma abu biyu ya hana hakan, farko wani azababben shock daya ji ya ratsa gaba ɗaya jininsa har yay saurin ɗauke hannunsa yana yarfewa, sai na biyu kuma da matar taƙi juyowa tana me ƙara sunkuyar da kanta ƙasa tare da matsawa, kuma bakinta na furta masa,"ba yanzu ba Hussain, ba yanzu zaka sami waɗannan amsoshin ba, da sauran lokaci". tsaye yayi yana tsare bayanta da ido, dan ya tabbata in har ya ƙara taku ɗaya to zsta iya guduwa. "ban sanki ba, kuma kema nasan baki sanni ba, dan haka ki fita acikin rayuwata da kike ƙoƙarin shiga...ba ruwanki da lamarin soyayyata balle aurena". wannan karon a zafafe yake maganar, yana mai yin ƙoƙari wajen ganin ya wata dabarar da zata sa matar ta juyo yaga fuskarta. "tukunnama! me kike nema a wurina?". kai tsaye kuma ya ji muryarta fa fito da cewa,"kai nake nema Hussain, kai nake nema na faɗa maka muddin baka cire soyayyar yarinyar nan tunda wuri a ranka ba to la shakka zata zame maka guba, Hussain karka Ƙwalla soyayyarka akanta domin hakan zai illataka...kuma abu na ƙarshe da nake so na faɗa maka shine, Alƙalamin ƙaddara bai rubuta abunda ku ka tsarawa kanku ba Hussain". da gama faɗar hakan ɓat sai matar ta ɓace. wanda hakan ya zama dalilin farkawar Alhussain a gigice yana ambaton sunan Allah. ya shiga murza idanuwansa yana daɗa ƙarewa ɗakin nasa kallo dan tabbatar da mafarkin da yay ba gaskiya bane. ya sauke ajiyar zuciya yana mai duban agogo dake saƙale ajikin bango. "10:00am". ƙarfe goma na safe haka agogon ya nuna, sai ya mayar da kansa ya jingina ajikin gado yana me haɗe murfayen idonsa ya rufe. lokaci ɗaya mafarkin da yake yi tsawon kwanaki uku a jere ya shiga tariyo masa acikin kansa, kwana uku kenan wannan matar tana zuwar masa da magana ɗaya. _"wace ita?, kuma me yasa take waɗannan maganganun?, wanne irin saƙo take so ta bar masa? me alƙalamin ƙaddarar ya rubuta? sunan Hussain da ta ke kiransa da shi daga ina ya samo asali?"._ sai kawai ya shiga sauke nunfashi da sauri-sauri. _"ba zaka aureta ba, ka cireta a ranka muddin ina nunfashi."_ wannan maganar ta kuma haskawa acikin idonsa, a wani zabure ya buɗe idonsa yana fitar da huci yayin da yake damƙar zanen gadon da kyau yana jin kamar zai jijjige ɗakin baki ɗaya.
**
yau sati guda kenan ina fama da ciwo, zazzaɓi yay min wani irin kamu duk na rame na fita a hayyacina. yaune kawai na samu ɗan dama-dama na fito parlo, shima a kujera na kwanta dan bana iya zama saboda rashin ƙwarin jikina, ko school ban je ba tunda aka koma yau sati biyu kenan. kuma ba komai ya haifar min da wannan ciwon ba sai mafarkin da nayi, mafarkin wani dattijo da nayi yana min nuni da wani mutum dake zaune kan kujera kamar wani sarki, yayin da yake faɗa min cewa wannan mutumin shine mafarin ƙaddarata, kuma akansa ne alƙalamin ƙaddarata yay rubutu. a yayin da ƙaddara ta ɗauremu ni da shi a wannan lokacin zan tsunduma a duniyar farinciki, sai dai kuma abu biyu zai haɗe min a lokacin, wannan lokaci gudan da nake cikin farinciki zai haɗe min da kuka mara iyaka. a duk lokacin da nai ƙoƙarin ganin naga fuskar na kan kujerar sai na gagara, a jiya ne dana tunkare shi ina taɓa kafaɗarsa sai naga ya faɗo daga kan kujerar, kuma ta ke iska ta ɗauko wani farin ƙyalle wanda yayi kama da linkafani ta rufeshi gaba ɗaya, ban san ta yanda zan kwatanta tashin hankalin da na shiga ba, amma dai nayi dakiyar tsugunawa gaban gawar na kai hannu zan buɗe fuskar dan ganin waye, kuma a daidai lokacin dana kama likafanin zan ɗaga lokacinne Gwaggo ta shigo ta tasheni daga barci. dalilin daya sa gabana yake ta faɗuwa kenan har zuwa yanzu, na kuma gagara gane fassarar mafarkin, tashin hankalina ɗaya kar ace silar taɓa shi ne na zama ajalinsa, gashi ban san ta inda zan yiwa Gwaggo bayani ba tunda ance ba'a faɗar mummunan mafarki.
"ya jikin naki". muryar Anty ta faɗa a sanda ta ke shigowa parlon, na ɗaga kai na kalleta ina amsa sallamarta har ta ƙaraso inda nake ta zauna. masu karatu kunji abun kamar almara ko, haka dai muka wayi gari Allah ya shiryar da Anty, hakan kuma yay ma kowa daɗi musamman ma ni, dan yanda ta ke lura dani babu ha'inci sai nake jin kamar ƙanwar uwata. "kinci abinci?". ta tambaye ni cike da kulawa, na girgiza ma ta kai ina cewa,"komai naci ɗaci Anty, bakina ba daɗi". ta kamani tana miƙar dani zaune ta ke cewa,"to haka za'ayi mutum dan Allah babu cin abinci babu shan magani, Sabina sauƙi fa muke nema dole sai kinyi haƙuri". ta taɓa kaina taji zafi rau, pillow'n kujera ta samun ta bayana ta jinginar dani, ta miƙe ta shiga ɗakin Gwaggo, tana sallah ta sameta, sanin sallar Gwaggo ba mai ƙarewa bace da wuri yasa ta tambayeta ina maganina, tayi ma ta nuni da drower, ta ɗauko ta fito. curstard ta dama, duk sona da shi kasa sha nayi, har Gwaggo ma ta fito suna ta fama da ni amma naƙi shan ko da spoon ɗaya bare nasha maganin, kowa sai roƙona yake akan na daure nasha maganin amma naƙi sai ƙara narkewa nake inawa Gwaggo kuka. ita dai duk hankalinta tashe yake, sam bata so ta rasani, ana haka Yayana ya dawo daga school, shima duk yanda ya lallaɓa ni ƙememe naƙi shan maganin, Yaya Abba kuwa dama shi ko ta kaina baya bi, ga jikina ƙara tsananta yake zafi rau kamar wuta, ga uban amai da nake kyalawa. Gwaggo kuka ta saka tana cewa,"wannan yarinya kwai muguwa, kawai dan