Showing 54001 words to 57000 words out of 89788 words
ya bani ba. Yaya Haidar yace,“Gwaggo wai yaran nan idan ba’a basu aiki dame zasu horu idan sunje gidan miji, ki riƙa kawar dakai akan Sabina mana bafa ita ɗaya ne ƴa ba”. “au tou, haba sai ka ce min kai kayi ƴaƴan ai har daka san horo, tunda har ka iya tsayawa tsegege ina faɗa kana faɗa, Aliyu ka shiga hankalinka dani, wai bance ma ka daina zuwa gefe na ba har ka ganta ka saka min ita aiki ba, Aliyu ka fita idona na rufe billahillazi tun kafin nayi maka abinda har ka koma ga ubangiji bazaka manta ba wallah”. tana ida zancenta, ta ƙwala min kira, ni kuwa dama ƙiris nake jira na fito muna haɗa ido tace,“jakar uban can, kar kace min kuka ka bata, don wallah mai barinka ka ƙara kwana gidan nan sai ikon Allah”. da sauri na girgiza kai ina tuna sharaɗin daya gindaya min nace,"a’a fa Gwaggo, ina wanki ne ƙwaro ya faɗa min a ido, shine kika kalla yayi ja haka, amma na fitar sai dai bai daina min zafi ba, muje”. naja hannun ta muka wuce don nasan zata iya fahimtar abinda ya faru.
[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*
_By Oum Ramadhan✍🏼_
*(20)*
*Kano.*
"idan ka gama ka kulle masallacin". limamin masallacin da ke tsaye akan Alhussain yace da shi. Alhussain da kansa ke ƙasa kan ƙur'anin dake hannunsa yana karantawa bai ɗago ba sai daya kai aya tukunna. sannan ya ɗago da kansa dake masa nauyi ya kalli Liman ya amsa mishi da,"tom Malam". har Liman ya kai bakin ƙofa sai ya dawo ya duƙa ya ajiyewa Alhussain naira 200 a kusa da shi.
tsawon wucewar mintuna talatin sannan ya kammala karatun ƙur'anin, ya shafa adu'ar da yay sannan ya mayar da ƙur'anin ya kai cikin drower ya aje. ya dawo ya tsuguna ya ɗauki kuɗin da Liman ya aje masa yana tayi masa adu'a cikin ransa. sannan ya fita ya rufe duka ƙofofin masallacin ya ɗora mukullin a inda ake ajiyewa. bayan sallar isha'i ne lokacin, dan haka unguwar ta daɗa yin shiru sai haushin karnuka da kake shi, haka kowanne layi duhu saboda rashin wutar nepa. tafiya yake yana takawa a hankali saboda yanda ƙafafunsa ke yi masa tsananin ciwo, haka har ya fito bakin titi, anan ya hangi wata ƴar tsohuwa mai siyar da tuwa ya ƙarasa wurinta ya siyi tuwo da miya na hamsin, a wurin ya zauna yaci sannan ya tashi ya koma bakin masallaci inda yake kwana anan yanzu tun bayan fitowarsa daga cell. kuma a wannan zaman da yay ne gyangyaɗi ya fara ɗaukarsa, cikin baccin dake neman ɗibarsa yaji kamar hayaniya, dan haka ya buɗe idonsa da sauri, dai-dai lokacin da motar ƴan sanda ta tsaya a wurin, a gabansa, dan haka ƙwayar idonsa akansu ta sauka. bakinsa da zuciyarsa suka shiga furta kalmar innalillahi wa'inna ilaihi raji'un a sanda yaga Ƴan Sanda na tunkaro shi, wasu matasa kuma a tare dasu na faɗa musu cewar,"ehh shine, wallahi shine". kalmar shine ta bada tartsatsin tsawa acikin kansa, yaja numfashi ya sauke tare da lumshe ido. a cikin duhun idonsa abunda ya faru da shi kwanakin baya da suka shuɗe ya shiga haska masa, ko kaɗan baya fatan hakan ta ƙara maimaituwa masa, ko da a mafarki baya fatan ƙaddara ta ƙara kaishi hannun ƴan sanda. zuciyarsa a yanzu faɗa masa ta ke akan ya tashi ya gudu, ya tashi gudu tun kamin su cimmasa su kama shi, bai san dame suka zo ba wannan karan, idan har ya ƙara shiga hannun hukuna taya za'ai ya fito?. ya buɗe idanuwansa ya suke kan ƙafafunsa biyu, ɗaya ta kumbura suntum ɗayar kuma ta ɗan sace ba kamar da ba. ya ƙara maimaita kalmar innalillahi a cikin ransa, ko daya miƙe tsaye, ko da yace zai gudu, la shakka babu inda zai kai ga ɗora ƙafarsa zasu cimma masa, da ƙyar ya takawa, irin takun da ko kusa ko kaɗan ba zai iya yin gudu ba. maimaituwar kalmar innalillahi a bakinsa ta haɗe da damƙwar kwalarsa da ɗan sanda yayi, ya fizgo shi ya miƙe tsaye, sannan ɗayan ɗan sandan daya ƙaraso shi da wasu mutane ukun da bai sansu ba ya kama hannunsa ya saka masa ankwa. sannan suka tasa ƙeyarsa zuwa cikin mota suka tafi. _"gani nan Yaya. Yaya gani nan, karka bari ƙwallar ta zubo dan Allah"._ maganar daya ji na shiga kunnensa kenan, muryar Sabina ce, daga ina?, tana ina?, ya rumtse ido da ƙarfi ya kuma buɗesu, acikin motar dai yake, cikin motar dai daya ji ana faɗar direct gidan gyara hali za'a kai shi. bai san lokacin daya daki kansa da jikin motar ba, inda tasan abunda ta ke haifar masa, da ta hana ganinta da jinta suna yi masa gizo, da ta hana sunanta ambatuwa acikin zuciyarsa. kuma buguwar da yay a wannan lokacin shi yay sanadiyar ɓallewar jini daga kansa, saukar jinin da yay sanadiyar tsayar komai acikin kansa, ya daina ji da ganin komai.
*Abuja.*
"haka za ki fita ba ki ci komai ba?".
"ina tsoron layi ne shiyasa, idan naje can ɗin na sami resturant a kusa saina saya na ci". "hakan yayi, a dawo lafiya. Idan kinga mutane ba sauƙi a wurin ki dawo ya ba ki kuɗi a hannu kawai saiki amfani da shi". "ameen..tom Gwaggo". Na amsa ina gyara yafa mayafina. Da sauri na fito compound, ina zuwa na tarar motana babu mai, na daki kai ina jan tsaki, ni yanzu ya zanyi? Shine tambayar da nayi ma kaina, ga Yaya Abba baya nan, ni kuma bana son kula Yaya Haidar bare nace ya ara min tasa, to ya zanyi dole haka zan haƙura neje wurin nasa tunda dai babu wata motar a ajiye sai ta matan gidan, su kuwa ba shiri muke ba bare nace zan ari tasu, shi yasa nacewa Baba a ɗaukar mana driver a aje, yace a'a baida amfani tunda dai kowa ya iya motar nan kuma ga Yaya Abba da Yaya Haidar ma. Har na nufi part ɗin su Yaya Haidar na hango Anty na shirin fita, na dawo da sauri na ƙarasa wurinta lokacin harma ta shiga mota tana ƙoƙarin fita, na tsayar da ita, ta zage glass tana jiran cewata sai faman haɗe rai ta ke tana min gani-gani. cikin ƴar murya nace,"Anty please bari na biki ki ajeni a bank, motana babu mai aciki, jiya su Yaya sunyi tafiya ina tunanin basu san ya ƙare ba basu tsaya sunsha ba, idan nace zan bari aje a sayo zan ƙara yin late". Nace da ita ina maganar da sigar roƙo na lallami. "tunda ubanki ya saya min motar ai dole ne na zame miki driver, to ko na rasa abar ɗauka a motana bana yayibi mai aljanu ba na kwasarwa kaina matsala". Ta faɗi hakan tana ɗauke kanta akaina taja motar ta fice a gidan. Oh ni Sabina, yanzu har ta kai ake min gorin mai aljanu, na goge guntun hawayen daya sakkomin, _Allah ka yaye min da ni da sauran ƴan'uwana ba ki ɗaya._ nayi adu'an a zuciyana ina nufar hanyar gate, saboda na san idan na koma Gwaggo cewa zata yi na fasa zuwa, ni kuma nafi so nayi abuna yau na huta, don akwai terming ɗin da nayi. Har na kai gate zan buɗe ƙofa na jiyo Gwaggo na ƙwala min kira, na juyo na ganta tsaye tana jan kwandon shara, ko ina zata da shi oho, rigima dai irin tata kawai, Baba yace su Zainab suna zuwa suna mata aiki tace bata son marasa mutunci suke zuwar mata inda take, Inna Karima zata kawo mata mai aiki. daga inda ta ke tsayen tace, "idan kin gama ƙare min kallon, nace har yanzu ba ki tafi ba dama?". "ummm motan nawa ne babu mai, zanje na hau ta haya sai na tafi". "to zuwan yau dama dole ne ko ƙaƙa?". ina ɗan marairaice fuska nace, "nafi so ne nayi yau ɗin, please Gwaggo ki barni na tafi". Ina kallo ta taɓe baki, "wai please, dole dai idan za'a maka magana sai an haɗa da ɗan iskan yaran da ba jinsa kake ba, yare bana uwa ba bana uba ba, shegen bature duk ya lalatawa ƴaƴan musulmi harshe, banda kece ma da sai nace zagi na akai". Ina nesa da ita banji mai tace ba, na juya zan tafiyata tace, "riga Malam masallaci ai ban gama maganar da ke ba, ina Abba ko wannan yaron Haidar?". Tana rufe baki Yaya Haidar na fitowa daga ɓangarenta, yana gyara maɓallin hannun rigarsa fuska a haɗe yace, "ni fa ba yaro bane karki kuma ce min yaro". "to ubana". Tace da shi tana hararsa. Sai kuma tayi masa kallon tsab kamin tace, "fita zaka yi ne?". "umm". Yace da ita yana tafiya. "yauwa to ga Sabina nan zata je banki, sai ka ajeta a can motarta ce babu mai". "ni ba driver bane, taje ta nemi nepep ta hau mana". Tace da shi, "yanzu Haidar ni zance kayi abu kai tsaye kace min ba zaka yi ba saboda banda girma a idanunka. Wannan yarinyar fa ƙanwarka ce, me yasa kake nuna mata tsana da yawa har haka ne, idan baka ɗauketa ba ai kaje ka ɗauki wata ƙatuwar banza. Kuma motar nan dai naga ai Babanta ne ya saya maka ita, amma saboda kai mutunci bai gama ratsa jininka ba shine zaka ce ba zaka kaita inda take so ba". cikin jin haushi yace da ita,"da nayi magana sai kice bana ganin girmanki, shi yasa idan kina magana nake miki shiru. Kuma shi Baban daya saya min motar ai ba cewa yayi gata nan ka zama driver'n Sabina ba. And again motana bata ɗaukan marar kunya ne". "idan bata ɗauka mara kunya ba ai ta ɗauka fitsararru". Gwaggo ta sa ki wani guntun murmushi kamin tayi ƙwafa tace, "hmmm ina jiye maka ranar ƙin dillanci. Ina roƙon Allah kar ya jarabce ka da son wannan yarinyar kayi tunanin zan baka ita Aliyu, ko da zanga ledar jini gefe, ledar ruwa gefe babu zancen mallaka maka Sabina, atoh ka jini da kyau". "nima kar Allah ya nuna min wannan ranar, dan babu abinda zanyi da wannan mummunar jikar taki. Da za ki ce mata ma ta daina kwalliya idan zata fita may be ta ke yin samari, wannan kwalliyar babu abinda ke ƙara mata sai girman ƙwailancinta, ƙwaila kamarta ace babu mai so, ki miƙe tsaye ki samu ki haɗata ta farfaɗo don tayi tsala da yawa". "akwai babban tsala ma irinka, kai wacce asararriyar macen ma zata iya aurenka, cikakkiyar mace dai cewa zata yi baka girma ba, tunda gaba ɗayanka yaushe ne ma aka cire maka shayi". Wani shu'umin murmushi naga yanayi yana cizon leɓe, yayi ƙwafa murya can ƙasa yace, "to Gwaggo koma wace a bamu ɗaki ɗaya da ita a jira wata tara a gani. Anan za'a tantance darajar kaciyar tawa". ni kaina kalmarsa ta ƙarshe ba kaɗan ɗin kunya ta bani ba. Gwaggo kam sheƙeƙe tayi tana kallonsa kafin tace,"kai dama ai ba kunya gareka ba, Allah dai ya shiryeka idan na shiryuwa ne, idan kuma bana shiryuwa bane yay mana maganinka". Murmushi kawai yay mata baice komai ba, yasa key ya buɗe motar, tana dubana tace, "to ki taso ku tafi". Yay saurin waigowa ya kalleni ya kalleta, "ni fa babu yarinyar da zata shigar min mota, tunma wannan jikar taki mara kunya. Yarinyar da gaba ɗaya kayan jikinta suka girma a gabanka amma ji take kamar ita ta baka nono". kawai saina Durƙushe a wajan na fashe da kuka, idan da kalmar dana tsana naji yana cewa na girma gabansa, ranar nan haka yace min tun twins ɗina na ƙifil-ƙifil ya sansu amma saboda yanzu sun cika min ƙirji shine nake ganinmu kai guda da shi. masifa naji Gwaggo na masa na ɗago ina dukan ƙafa a ƙasa ina ƙara sautin kukana. "ni dai Gwaggo Allah na gaji da ganin Yaya Haidar da Anty a gidan nan, duk su biyun sun tsaneni". "ita kuma guntuwar me tayi miki?". "ɗazu itama fa daga nace ta rage min hanya take cewa ba zata yayibi mai aljanu ba...". Ban ƙarasa ba ta tareni da cewar, "ita Guntuwar ta gaya miki wannan kalmar mai ɗacin saurare?". Na ɗaga kaina ina ƙara cewa, "kuma ai duk ke kika jawo min koma wacce magana ce, ina zaman zamana kin tashi kina yaɗawa mutane wai ina da aljanu". Jikinta naga yay sanyi, sai kuma ta duba Yaya Haidar tace, "kira min Auwalu a waya kace yazo ya sameni cikin gaggawa, ke kuma tashi muje ciki". Ta ƙarasa maganar tana dubana. Na miƙe zan bita sai ga Baba ya ƙaraso wurin, ta zuba masa ido tana faɗin, "yauwa Ashe kana cikin gidan?". "ehh inan ban fita ba. Daga wurinki nake naga duk baku nan, ina fitowa kuma na hangoku anan". Ta shiga goge hawaye, a cikin muryar ƙonewar zuciya take faɗa masa. "yanzu tsakani da Allah abinda matanka suke a cikin gidan nan suna kyautawa, kwata-kwata basu san hakkin maraya ba, kai kuma gaka sun gama shanyeka babu abinda kake iya tsinanawa, ni kuma gaba ɗaya baka tausayina, nasha wuyar kishiyoyi zan kuma sha ta matanka, to wannan a baya ne akayi baza a kuma ba. Babu shegiyar da zan zubawa ido acikin gidan nan tana cin zarafin marayun yaran nan, wanda suka yi a baya ma su da Allah.
Ƴar nan ko ɗumin hannun uwarta bata ji ba da ta zo duniya amma hakan baisa aji tausayinta ba, Yanzu har ta kai da su dinƙa goranta mata akan tana da aljanu, to ita ta ɗorawa kanta ne? shi dai ciwon nan bai wuce kan uban kowa ba, to Kaja musu kunne su shiga hankalinsu da taɓa yarinyar nan idan ba haka ba kuma billahillazi zan ajiye sanyin da nayi a gefe na zazzage musu buhun rashin mutunci, na zama kalar uwar mijin da ba'a so. Wannan ƙiyayya da ake nuna mata haka tun ina da rai, to randa babu ni kuma fa? to ni wallahi da a taɓa min Sabina ƙwamma a fito fili ace min Hannatu na tsaneki, in yaso ayimin zagin ƙare dangi zanfi jin daɗin hakan, ɓacin ranta yana damuna haka kukanta yana ɗaga min hankali, ka gayawa wannan guntuwar karta ƙara yin abunda tayi saboda hukuncin da zan ɗauka akanta ba zaiyi mata daɗi ba". Baba dake tsaye yana sauraronta ya ɗago ya kalleta yace, "ni dai don Allah Gwaggo ki bar wannan kukan bana so, ki kuma yi haƙuri zanyi musu faɗa hakan ba zai kuma faruwa ba". "karka kuma bani haƙuri akan laifin matanka domin cutata kake, kai da ubanka marigayi babu abinda kuka iya idan an cuce ni sai bani haƙuri, to ni wannan mugun kalmar na gaji da jinta, tun ina zaman gidanka wancan Zamanin na zaman Halima da Hajara kake zaluntata da wannan kalmar, karka ƙara idan ba haka nayi maka irin yanda nama Sulaimanu. Maganar ƙarshe da zanyi wallahi wallahi kaji na rantse ko, duk ƴar wofin da ta kuma shiga harkar Sabina a gidannan sai ka saketa ta koma gidan koko da wainar gero". Ya buɗe baki zai ƙara bata haƙuri sai kuma yay shiru. Ya kuma kalleni yace, "ke acikinsu wace ta gaya miki haka?". "Anty". Nace da shi. Wani kallo yay min wanda na lura da alamar bai yarda da maganar ba, domin baya taɓa yarda da laifinta. Na miƙe ina gyara ratayen jakata nace, "Gwaggo zan tafi". "kin bari sai gobe ko kuwa?". ta faɗa tana min wani kallo. Na zumɓuri baki ina kallon Yaya Haidar da shima ya ɗago a lokacin yana kallona. Baba har zai wuce kuma sai ya dakata da faɗin, "Gwaggo ina ce na hanaki shara, me tsintsiya keyi a hannunki da safiyar nan?". ya faɗa yana ƙoƙarin ƙarɓar tsintsiyar hannunta. tace da shi, "ban son shishshigi da ƙwala kai a faranti, bada tsintsiyar hannuna zaka ji ba da wannan abin zaka ji". ta faɗa tana nuna masa Yaya Haidar dake kusa da ita. kamin ta ɗora da faɗin,"Tun ɗazu nake fama da yaron nan akan ya ajiye Sabina a banki, yaƙi ya tsaya sai karta min maganganun banza yake, ka san jinsa yake kamar sa'nni muke". Kamin Baba yay magana da sauri Yaya Haidar ya kalleni yace,"kin fasa tafiyar ne?". Yay maganar kamar bashi ba, ni kuwa nayi kamar ban jisa ba, na ɗauke kai gefe ina hare-hare, shima kuma sai hararata yake ta ƙasan ido. Baba yace, "ita ina motar tata?". nayi saurin cewa, "Baba ciwo fa naji a ƙafana, bazan iya driving ɗin ba nace ya kaini don Allah tunda Yaya Abba baya nan, shine yace aishi ba driver bane, naje na hau napep, har Gwaggo ma sai da tayi masa magana yace shi ba zai ɗau mara kunya ba". Ina yin shiru shima yace, "Baba ƙarya ta ke yi babu wani ciwo da taji, Gwaggo tazo ta samemu ne muna maganan zanje na sayo petrol a zuba mata a motan nata tunda ni ina sauri ne". Gwaggo ta riƙe haɓa tana faɗin, "iko sai lillahi, au yau kuma ni zaka ƙaryata Aliyu, yau naga makirci a wurin ɗa namiji. To Auwalu ai ka gani da idonka, shi da Abba don suyi min rashin kunya su ƙaryata ni wannan ba komai bane a wurinsu, yau gashi harda su kissa. wannan yara dai ai albasa batayi halin ruwa ba musamman Aliyu, dan ba haka uwarka da ubanka suke ba, Allah zai kawo Sulaimanu gidan nan zanji idan shine ya ɗaure maka gindin yimin fitsara". ta numfasa da ƙara cewar, "to koma menene dai kaje dan kanka. ni ba wannan ne buƙatata ba, kawai Auwalu kace ya ɗauketa ya kaita inda ta ke son zuwa, ya jira har sai ta gama kana ya dawo da ita, don na tabbata maka babu inda za shi bacin shegen yawonsa da ba ƙararre bane". Baba ya dube shi yace, "wurin aiki zaka ne?...". Gwaggo tai saurin cewa,"ai kaji tsiya, shi har ƴaƴansa ma tsoronsu yake, kai da zaka balbale shi kamar wuta amma kana masa magana a ruwan sanyi". Baba baice mata komai ba, Yaya