Showing 18001 words to 21000 words out of 89788 words

Chapter 7 - ALHUSSAIN Complete Hausa Novel

23 Aug 2025

379

cinya tare da tura masa mazaunai tace masa, "karka fasa saki na ɗin, kaine zaka ji haushi. Saboda ina fita zan sami rangaɗeɗen saurayi mai rai da lafiya yayi wuff da ni, kai Abba kana raina wannan Sauran yarintar dake jikina ko, to Rabon kaji na aure shugaban ƙasarku ne". Ya Abba ya kaɗa kai kawai, idan ya biye tata abincin daya dawo ci ba zai sami cinsa ba. Ya dube ni yace, "ke tashi ki ɗauko min abinci na". Kamin na miƙe Gwaggo tace, "ke yi zamanki, yau kam sai dai ya nemi wani gidan yaci abinci. Abba ba dai ni zaka nunawa tsiya ba, zaka ganta iya ganin idonka, dama kowa ai da ranarsa. Idan kaji haushi ka koma can filin ball ɗin su dafa su baka, ko kuma kaje can gidan su budurwar taka daka saci ɗankwalina ka kai mata matsayin toshin sallah saita baka...kana faman ɓoɗara hanci kamar gajeran wando, da wasu idanuwanka ƙifi-ƙifi kamar na ƙaramar touchlight ɗin masu gadi, har na zaka nunawa fushi Abba". Haushi ya tuƙe Ya Abba, don haka ya juya kawai ya fice yana jijjiga kai. Gwaggo tabi bayansa da ido tana murmushi tayi ƙwafa tace, "ɗan ƙwal uba dani kake zancen ai". Muna haka muka jiyo sallaman Baba, da sauri na sakko a saman kafita na fita cikin hanzari ina amsa sallamar tasa, kamin Gwaggo da Farhana su mara min baya. Yana zama kan kujera na ƙaraso da fara'ata ta nuna jin daɗin ganin mahaifina nace, "Baba sannu da zuwa". Ya amsa min da, "yauwa Sabina". Farhana ta ƙaraso itama tana masa sannu da zuwa. Lokacin da Gwaggo ta ƙaraso ta zauna kan kujera, Baba ya sauko ya gaida ita, tana amsa masa tana sanya masa albarka. Baba yace, "Mama mene ya haɗaki da jikin naki, yace kinƙi bashi abinci". "auto kaga masu ɗa, ai ban san kana tuhuma ta ba sai naga ka sanya mini ankwa, sai naji daɗin maka jawabi...amma yanzu ban ganka da kakin ɗan sanda ba ina zan san kana yi Awwalu. Abinci ne na dafa bazan bashi ba, har ni yaron nan zai tsulawa tsiya na roƙe shi nace yazo ya siyo min kayan miya Sabina na makaranta, amma ya buɗi baki yace ai filin ball zaije, koma ba haka ba ai yayi girman a aike shi wurin me kayan miya, ƴan mata ai sai su raina shi. Ranar haka na zauna ban girka na rana ba sai da Ƴar arziƙi irin albarka ta dawo, wadda tayo gadon kirki a wajen mahaifiyarta". Baba yace, "to ayi masa afuwa Gwaggo ba zai ƙara ba. ba'a horo da yunwa ke kika faɗa mana hakan, kuma shi idan baici anan ba aina zaici". ta taɓe baki kamin tace, "ya tafi can wajen matan ubansa yaci, ko kuma tunda Allah ya kawoka ka ciri ashirin ka bashi ya sayo awara, abincina ne dai yau Abba ba zai ci ba". Baba baice komai ba, dan yasan tun da ta kafe kam bata sauya ra'ayinta. ya dai kalla Ya Abba da ido sukai magana, nan ya tashi ya fita bayan Baba ya bashi kuɗi a ɓoye, in ba haka ba Yanzu Gwaggo sai ta kuma sauke masa sababi idan ta gani. Baba ya kira ni yace nazo, na taso na dawo kusa da shi, kasa ɗauke idona nayi akansa duban yanda naga yana ta zabga murmushi da alamu yau ɗin yan cikin farin ciki, don tunda ya shigo na lura da hakan, ni kuma abunda yake min daɗi kenan a rayuwata, naga mahaifina acikin farinciki da kwanciyar hankali. Baƙar jakar hannunsa ta laptop ya buɗe ya zaro wasu takardu ya miƙon yace na karanta. Habawa ai ina karanta layi biyun farko na miƙe tsaye nai wani tsalle nai juyi ina ihun murna, Farhana na fizgo na nuna ma ta itama, tsabar farinciki mun kasa ƙarasa karanta sauran rubutun. baki ɗayanmu tsalle muke muna murna, kamin daga baya na koma na zauna ina hamdala ga Allah, maimaitawa nake, "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Allah mun gode maka abisa ni'imar da kayi mana. Ya Allah kaci gaba da bawa mahaifina nasara a rayuwarsa". Gwaggo tace, "wai meke faruwa ne, ni duk kun barni a duhu, ko abin farincikin banda ni ya sama. An baki aba kin wani ƙwaƙwame ke kaɗai, ina ce dai ɗa nawa ne tunda sai dana haifa kika sa me shi a uba". nace, "oh Allah na! nikam yau gwaggo ban san me na maki ba. to gashi nan".Na faɗa ina tasowa na bata takardar. Sai da ta gama mani kallon sama da ƙasa kana ta karɓi takardar, hannu ta miƙa saman abun tv namu ta ɗauko akwatin glass ɗina, ta buɗe shi ta ɗauko glass ɗin ta ƙwaƙwuma a fuska sannan ta wani harɗe ƙafafu ta hau kallon takarda kace gaske karantawar take. Dariya muke so muyi daga ni har Baba amma gudun sababinta yasa muka gimtse kayarmu. ta ɗau kusan mintina biyu sannan ta sauke takardar daga kallonta, ta cire glass ɗin, tana faman juya takardar ta kalla Baba tace, "Kai Auwalu, tunda ta gama nata zagin kai sai ka sami damar min bayanin abinda ke ƙunshe aciki. Sarai ai kasan babu abinda na iya karantawar amma ka barta ta miƙo min saboda cin fuska, dama ranar nan tace min ni ai bana ganewa, kamar Addagana haka nake. Yo Allah na tuba duk lalacewa ai nafi wannan lukutar matar tunda ni nayi makaranar Allo. Ita yarinya ce har yanzu bata san mene kishi ba shi yasa take haɗani da waɗanda suka kusa rabani da mijina". O'o, niko na riƙe baki ina kallonta har tagama magana. Gwaggo ba dai mita ba, wannan zancen anyi wata da yinsa amma duk sanda ta tashi sai tace ai nace bata ganewa Addagana tafi ta jaa, kuma ba komai bane saboda na haɗata da kishiyarta. Baba ya numfasa yace, "Mama wannan takarda ce daga wurin aikinmu...". Ai tun Baba bai ƙarasa ba ta dafe ƙirji cikin tashin hankali tace, "na shiga uku na Auwalu ba dai sun kuma korarka bane, wannan ƙaddara da me tayi kama". tana faɗa tana shirin yin kuka. Ina dubanta ina gwame fuska nace, "kai Gwaggo hakanne zaisa kiga ina murna kuma. Abuja fa zamu koma". Tayi min wani kallon sheƙeƙe na ban gane nufinki ba, "me kuma zai maida mu Baba Ja?". Gwaggo bata taɓa cewa Abuja sai dai tace Babaja, saboda acewarta ai cin mutunci ne yasa aka lanƙwaya sunan ubanta aka maida shi Abuja daga Abubakar. Baba yaci gaba da mata bayani, "ehh Gwaggo zamu koma Abuja ne da zama saboda ƙarin matsayi da ma'aikata ta bani". "kai don manzan Allah??". ta faɗa har tana zamowa daga wurin zamanta. "wallahi kuwa Gwaggo, an bani muƙamin MD na ma'aikatar wutar lantarki. Sun bani gidaje biyu acan Abuja, da motoci uku, da kuma miliyan uku, ta buƙaci na ɗauki iyalaina mu koma can da zama gaba ɗaya nan da sati guda".


_Please Share, Vote and Comment let me know what you think._*AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(8)*
Gwaggo ta rangaɗa wata uwar guɗa data amsa a gaba ɗaya cikin gidan, hamdala take ta jerawa ga Allah, har da miƙewa ta taka rawa irin tasu ta tsofaffi. "Allah maji kukan bayinsa...kai gaba ɗaya ma na rasa wacce iriyar murna zanyi". Yaya Abba daya shigo yace da ita,"tsohuwa kina ta ihu fa dare ne, maganarki har soro, dama ke muryar kamar cakwaikwaiwa". tace da shi,"umm Abba ai yau sai dai kayi da wata bada ni ba kam...dan lokacinka dai ban da shi". Murna nake yi sosai kamar babu gobe, amma ɓangare guda na zuciyata yana tunanin halin da zan shiga zai kasance. wannan mutumin, wannan bawan Allah'n da Allah ya haɗani da shi ta ayar da ban san fassararta ba, wannan mutumin da nake jin kamar ina da wata babbar alaƙa da shi, mutumin da babu ƙarya tun a ranar farko nake jin tasirinsa a tare dani a kullu yaumin, mutumin da tunanins akaɗai a sanda bana tare da shi yake sakani zubar hawaye saboda rashin sanin dalilin wanne hali yake ciki.
Gaba ɗaya murnar da nake yi tsayawa tayi cak, saboda tunawa da nai zan tafi na bar Yaya, tunanin daya haifar da wani ɗan ƙaramin tashin hankali a zuciyata, ta fara bugu kamar zata fito waje. dai-dai ta nutsuwata nayi saboda ina gaban wanda bana son ya fahimci yanayin da nake ciki. dan duk wanda ya kallen a yanzu dole sai ya ɓazgo wani abun, Ina kallon Farhana ma yadda ta kafe ni da idanunta, tana son gano sirrin dake zuciyata, amma sam na kafa na tsare saboda yanzu sai ta ruguza min tsari, dan ita bata iya sirri ba. Ganin hakan yasa ni furta, “Yauwa Baba barin zuba maka ruwan alwala, na kalla magriba ta gaba to”. ina gama faɗar haka na miƙe na nufi hanyar fita, idon Farhana na kaina har a lokacin, yayin da Gwaggo take ta faman zuba kamar kanyar da ta samu jeje da iska. Ina fita na samu damar dai-dai ta nutsuwata, amma fa sam hakan ya gagara, don tuni hawaye sun fara zubo min, dama ni Allah ya hore min kamar famfo, hawayena a wajen tausayi da rauni basu da wahalar sauka. ina zuba ruwan na dawo, na samu gefen Gwaggo na zauna ina sauraron hirar ta su, ba wani fuskantar hirar nake ba, tunanina da neman mafita bai wuce yadda za'ayi tafiyar nan tare da Yaya ba. kallon Farhana nai, nayi mata sigina da ido, saboda mu fita mu samu abin faɗa, amma sai naga ta basar kamar bata ganni ba. Ganin haka yasa na miƙe na kama hannunta ina faɗin, “tashi mu shiga ciki”. Hannuna ta kama muka nufi hanyar ɗaki, muna shiga ta dube ni sheƙeƙe tace, “ya dai uwar ɗorawa kai damuwa”. harara na watsa mata ina faɗin. “ke fa ƴar rainin hankali ce Farhana, meye nufinki dama?”. ta ɗan harare ni tace, “Oh oh jimin rainin tunani, ke zan tambaya dai meye ke damunki, naganki sukuku, don tun ɗazu na fuskanci damuwar da kika shiga bayan kin gama murna”. na ɗan ja ƙaramin tsaki kaɗan na miƙe tsaye ina safa da marwa kana na kama ƙugu na tsaya nace, “ba zaki gane ba Farhana, kin san halina sarai, ina da saka damuwa akan abinda nasa a raina but..”. ban ƙarasa faɗin abinda zance ba Gwaggo ta bankaɗo labule tana faɗin, “an kira sallah ko baku ji ne wai, ko kuwa ba zaku yi ba ku duka?”. nace, “kaii Gwaggo mai baiwa, yo waye yace maki bamu ji ne wai, banda abinki Gwaggo kuma anyi ta rashin sallar kenan?”. tace, “oho maki marar kunya, na sani ko ba zaku yi ba, tunda ku ko yaushe a cikin jini kuke. abu da a zamaninmu iwar haka ma yara kamar ku basu fara abin mata ba sai an wuce haka...amma ku yaran yanzu nan da nan sai ku nemi kufi ƙarfin kan mutum”. “gaskiya Gwaggo Allah ya baki baiwa, baiwa ba ta faɗe ba, ina ruwanki ne ke kam, don Allah kije, na san abin da kike nufi gamu nan kije abinki”. na faɗa sanda nake ƙara riƙe ƙugu. Farhana kam dariya kawai take tana faɗin, “ni kam dramar ku tana burge ni, muje muyi alwala kafin ta dawo”. muna idar da Sallah Farhana tace zata tafi, Gwaggo ta zuba mata tuwon shinkafa da miyar kuɓewa tace ta kaima Hajiyarsu. Ta karɓa tana godiya, har mun kai soro naja na tsaya ina faɗin,“muje kice ma Baba zan kwana a gidanku in yaso sai mu tattauna abinda zamu tattauna kinji”. Farhana ta ɗanyi jim kafin tace, “Gwaggo dai nasan zata yarda amma kina ganin Baba fa?”. “ke kam muje zai amince insha'Allah”. na faɗa da ƙosawa, da wani abu dake bin jikina wanda ban san menene shi ba. muka koma ciki, Gwaggo bata gama lazimin da take yi ba, sai da ta gama sannan ta juyo da kallonta kanmu tace, “oh yau naga abinda ya ishe ni, yo bakwa iya zama sai dai ku tsaya min haka aka ƙi ƙam sai kace kunzo ɗaukar fansa”. Farhana tayi dariya ta zauna kan kujera, ni kuma na tsugunna a lokacin da nake jin kamar nai fiffike na isa ga Yaya. Farhana tace da ita, “Allah ya huci zuciyar Gwaggo, ina abin ɗaukar fansa anan, sauri muke yi shisa muka ga ba sai mun zauna ba”. Gwaggo ta ajiye carbin dake hannunta tace, “to naji sarakan iya tsari, meye ne dama?”. tana tambayar ga Farhana ne a lokacin da take kafeni da ido. na ɗan ɓata fuska gudun karta harbo jirgina nace,"bafa ni kika tambaya ba da kike jiran amsa daga bakina". ta watsa min Harara kana ta juya inda Farhana take tana faɗin, “ina jinki Farhana meye ne?". “Gwaggo dama tare da Sabina zamu je gida gobe insha'Allah sai mu dawo, ina so zata rakani taron get together da zamu yi ne a school”. Gwaggo ta gwame baki tana kauda kai, sannan ta samu damar furta,“ta jira ubanta ya shigo in yaso sai taji daga gare shi”. nasan sarai ta faɗa ne dan bata so naje, kuma ba zata iya cewa Farhana a'a ba, domin a rayuwarta in akwai abunda bata so shine na kwana ba kusa da ita ba. na yamutse fuska nace, “Gwaggo dan Allah”. na rufe ido ina ƙara faɗin,"Gwaggo, Gwaggo, Gwaggo wai ce nake kece ke da iko da ni, to kuma why zaki ce sai Baba ya amince". tayi ƙwafa bata ce min komai ba, ta ɗau carbi taci gaba da lazimi. duk na ƙosa ta bani attension ɗinta na fara yi mata magiyar dana saba, amma gaba ɗaya sai naga ta sauya fuska, har Farhana ta miƙe tace ita kam tafiya zata yi, nai saurin riƙo hannunta ina roƙonta sai ga Baba yayi sallama muka amsa mashi, ya samu wuri ya zauna, yadda ya ganmu ya sashi faɗin, “duk yadda aka yi akwai abin da kuke buƙata ko...ko kuma wata matsalar ce?". ni dai nayi ƙasa da kaina, Farhana kuma tace,“Baba dama..dama muna son zuwa..”. Baba yana murmushin manyance yace, “ina jinku meye ne dama?”. tana sosa gira tace,"Baba dama ina so mu tafi gidanmu ne tare da Sabina tunda kun kusa tafiya ku barni". ina kallon yanda Gwaggo tai saurin juyowa tana kallon Farhana da ɗumbin mamaki, tama kasa rufe baki, saboda jin furucin daya banbanta da wanda ta faɗa mata a ɗazu, fuskarta kuma na haskawa da rashin yarda damu, dan yanda maganar Farhana ta banbanta tasan dole kwai wani abu da muke ɓoyewa. laɓɓanta suna motsawa da son faɗin wani abu amma sai bata faɗa ba, ta ɗauke kai ta kama ƴan waƙoƙinta na ɗan ƙwairo. "mai zai hana ni ƙin amince miki Farhana, ba ke ɗaya da kuke aminan juna da Sabina ba, ko dan mutunci da karamci irin na mahaifinki babu abinda zaki nema ki rasa daga gareni. dan haka kuje Allah yay muku albarka, gidan ku ai kaman gidansu ne itama...kya gaida Abban naki don na kwan biyu bamu haɗu ba". godiya muka yi masa sannan muka miƙe muna nufar hanyar fita. “au ko sallama don iya shege ba zaku min ba, shi ne kuka miƙa kai kamar ƴaƴan zabi”.dariya sosai Baba yayi, ita kuwa Gwaggo ko dariya bata yi ba, Farhana tace, “wallah Gwaggo kin iya yanka, salon muce wani abin kice mun ce”. “yo ai gaskiya na faɗa, ina kallo fa ko kaya bata ɗauka ba. Ko haka zata tafi babu kaya? ko da yake zumuɗi na gaba da suturta jiki ai”. na manta da Baba yana wajen nace da ita,"Allah Gwaggo kin fiya sa ido, haka zanje ɗin ni don Allah ki ƙyale ni...Baba mun tafi”. ina faɗa naja hannun Farhana zamu fita. Gwaggo ta kuma cewa, “yo ai sai kiyi kuma, da wuyanki kamar mariƙar lema, na san dai kayan Farhana ba zai maki ba ko ɗaya, dan haka ki dawo ki ɗauki dai-dai ke”. duk wannan maganar da take saboda dai a fasa tafiyar ne, dan haka ban tsaya tanka mata ba balle ta sami abinda take so, naja Farhana muka fice, muna jinta tana faɗin,"Allah dai na kallonku, ni bance sai kunji tsorona ba amma kuji tsoron Allah". A mota kuwa muna tafiya Farhana sai dariyar kalaman Gwaggo takeyi, yayin da ni ko kaɗan dariya bata zo min ba, tunanina kaf bai wuce neman mafita ba. idan muka bar garin nan sai yaushe zamu ƙara dawowa?, idan na tafi ba tare da nayi sallama da Yaya ba shin idan na dawo zan sake ganinsa?, ban ɗau tsawon lokaci tare da shi ba, amma ya fara sakewa na san da wannan, ba kullum nake kasancewa da shi ba, amma a jikina nake jin rayuwarsa ta fara sauyawa, haka zalika ajikina nake jin sauyin rayuwarsa na gab da zuwa, gab, kusa-kusa, kusan da bata da wuya wurin Allah, sai da a wurinmu ƴan adam...to amma abunda na kasa ganewa shine, tun a ranar farko zuciyata ke faɗa min kece wannan ƙaddarar, kece ƙaddarar da zaki sauya rayuwarsa, silarki komai nasa zai warware, wataƙila yanzu wataƙila sai an ɗau tsayin lokaci. kuma ayau da wannan abin farin cikin ya samemu, tun bayan dana gama murnata, haka zuciyar tawa ke faɗa min, ki tafi da shi, karki barshi anan, acan inda zaki je, acan inda zaki je zaren wata ƙaddarar zai warware, zuwa Abuja alkhairi ne...abinda zuciya faɗa tana ƙara faɗa kenan tun a ɗazu. kuma maganar Farhana data kutso cikin shirun da nai yasa ni rufe ido ina sauke numfashi, tukunna furucin nata daya fito ya tsaya a iska ya sami damar shiga kunnena.

   

_Masu Karatu what do you think will happen on this trip?_

_ta yaya zamu fassara kalaman zuciyar Sabina?_

_kuna ganin akwai yiwuwar ƙara haɗuwarsu da Al-hussain kamin tafiyarta?_

 
       
#Vote.
#Comment.
#Share.
#Mikiyawriters*AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(9)*
"Sabina tun a washegarin ranar da idanuwanki suka sauka akan ɗsn wiwin kan bola na kalli wani abu acikin ƙwayar idonki akansa, sai gashi ayau abunda na gani a saman fuskanki ya ƙara tabbatar min da shi...Sabina a haƙiƙanin gaskiya ba tausayinsa kike yi ba, sonsa kike, irin son da kika kasa ganewa balle har ki gasgata shi". Nai mata wani kallo na rashin fahimtar maganar

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login