Showing 51001 words to 54000 words out of 89788 words

Chapter 18 - ALHUSSAIN Complete Hausa Novel

23 Aug 2025

388

ba". na ɗago idona masu ruwan hawaye nace,"au da gaske ne ma na maka satar? To mene na satar maka?". y gyaɗa kansa sau uku kamin nan yace,"ofcourse kin sace min abu mai muhimmanci a tare da ni, amma i promise you i will not tell your Dad for now, but for sure zan faɗawa Momy nah, what ever she decide akai then...". Bai ƙarasa ba ya kanne min ido guda yana cije leɓensa na ƙasa, yana abu kamar Yaya Haidar. Ni kam na shiga uku, wannan rana ta yau bata zo mani a sa'a ba, na kuma fashewa da kuka, naji yana cewa, "shikenan idan kina so na bar maganar to ki bani haƙuri". Ai da sauri na ɗago nace, "kayi haƙuri". "haka ake bada haƙuri?". Na karayar da kai, na kama kunnuwana nayi exactly yanda nake bama Yaya Abba haƙuri idan na masa laifi, "Don girman Allah kayi haƙuri". Hasken flash yasa na ɗago ido ina kallonsa, ƙyasss naji ƙarar ɗaukar hoto, zanyi magana kawai na ƙyaleshi, ba buƙatata kenan ba. "Sabina Auwal right?". Ya jefo min tambaya. na ɗaga masa kaii "ehhh". "nice name Beauty". Na murguɗa masa baki, ya tari numfashina da cewa, "yauwa and i will also tell Baba kina murguɗawa manya baki". Na ɗago zan bashi haƙuri na tuna abinda Gwaggo tace min duk sanda wani yace ina murguɗa masa baki. Na turo bakina gaba nace, "ai dai ko Gwaggo tasan ina yi, kuma ma ai a wurinta na koya. Saboda haka ko an kai ƙarata wurin Baba ba abinda zaice, "Ƙaramar dariya naga yayi, ina marairaice fuska na haɗa hannuna nace, "don Allah kai wane?". a karo na babu adadi ya janyo leɓensa na ƙasa ya cija sannan ya shafo sumar kansa yace, "sunana Muhsin Muhammad Na kowa...". Bai ƙarasa abinda zaice ba na wurga masa tambayan, "a kano kake?". Ya kaɗa min kai, "nop, ni banma taɓa zuwa Kano ba. Mahaifina balaraben sudan ne, also my Mother she's shuwa arab, mu 6 duk an haifemu a misra, wata harƙallar aiki ta kawo Daddy nah nan Abuja, ataƙaice bamu haura 4years ba anan, like you see me ina da asali, kuɗi, gata da duk wani abu na jin daɗin rayuwa, sai dai banda lafiyan ƙafa, as soon kuma zamu koma can ƙasarmu da zaran Daddy ya kammala abinda yake. So kema sai ki shirya becouse we are going along with you, acan ne za ki amsa hukuncin satar da kika mani". Zan buɗi baki nayi magana Malama Muhsina ta shigo. "Brother is time for the meeting". Na kalla ya duba agogonsa yace,"oh shet". Sai kuma ya kalle ni ya kalleta yace, "Sister zo ki tayani lallashin Beauty tun ɗazun ta ke kuka taƙi yin shiru, kuma kin san na tsani kuka bare nata ma da babu daɗin ji kamar kukan shanuwa". Ya faɗi hakan yana wani toshe kunne, Zumbur na miƙe tsaye na ƙwace hannuna daga nasa, don cin mutunci kukana ne mai kama dana cow, ina tura baki na raɓa Malama na ɗauka jakata dake kan kujera nayi ƙofa. Sai dai a rufe take, na juyo na kallesa naga yanda yake dariya ƙasa-ƙasa, na kawar da kaina cike da jin haushinsa. Malama Muhsina ma tayi siririyar dariya ganin yanda na cukule tace, "Soryy Beauty ki rabu da Brother nah, idan kika biye masa zai ta sanyaki kuka ne. Bari nazo na buɗe maki". Ina kallo ta kamashi sosai kana ta ɗora shi kan wheelchair nasa, da alama dai ƙafafunsa basa aiki kwata-kwata, mutum ba isashshen lafiya sai ɗan banzan surutu da neman magana". tana buɗe ƙofa nayi ficewana raina duk a dagule, gefe ɗaya kuma ina saƙa abubuwa da dama a raina ina warwarewa, a wannan lokacin kowaye ya ganni yasan kwai abinda ke ƙasan raina saboda yanda nake zabga ƙwafa. ina kan hanya Yaya Abba ya kirani, na ɗaga wayan nace masa gani nan zuwa, Allah sarki bawan Allah ashe har yanzu yana jirana. Intisar ma ashe tun ɗazun tana waje zaman jirana, tana hangoni ta taso da sauri tana aika min tambayan me ya faru, ni dai shiru na mata ban saurareta ba nayi tafiyata ina sha re hawaye. ina zuwa mota na buɗe na shiga, da shigana na ƙara fashewa da kuka, tambayar duniya Yaya Abba yace me aka mani shima na masa shiru, gaba ɗaya ba komai ke damun zuciyata ba sai kewan Yayana, tausayinsa na kuma ratsa ni, ganin wannan mai kama da shi ya matuƙar ƙara tada min da kewansa, ya zama dole naje naga halin da yake ciki, bazan dawo ba har sai idan da shi ne, Allah yay mana wannan arziƙin da ba zan taɓa barinsa a wahala ba. dan Na gama gane Proff ba Yayana bane shi ya fiya surutun wofi, Yayana kuwa magana ma wahala ta ke masa. a ƙufule Yaya Abba yace, "ke ban san iskancin banza fa. Ina miki magana kin min shiru, exams ɗin ne tayi wahala?". Kai kawai na girgiza masa, sai yaja tsaki ba tare daya ƙara ce min komai ba. ganin yanda ransa ya ɓaci yasa nace,"Yaya Abba dama ana halittar mutane iri guda ko da ba identical twins bane?". Ko kallo na bai ba, sai guntun tsaki daya kuma ja, bai ƙara saurarena ba har muka isko gida. Ina shiga parlo na faɗa jikin Gwaggo dake zaune, ko ta kaina bata bi ba sai taɓe baki da tayi, ganin dai kukan nawa bana ƙarewa bane tace. "ke wai Ubanki Auwalu aka yi miki da za ki zo ki sani a gaba kina faman kuka, bayan kin san ba abinda ke ɗagan hankali a duniyar nan sama da kukanki, za ki faɗan mene ko kuwa?". na mata shiru ina ƙara ƙanƙameta, a gaskiya ina bala'in son ganin Yayana, dan a yanzu jin zuciyata nake na wani matsewa sa zafi. Ta tureni da ƙarfi tana cewa, "je can ki ƙarata da halinki ke ɗaya, idan kika ƙarar da hawayen kya rasa na zuwa ɗakin miji ace ba ki da kunya, ke baza'a taɓa tambayanki mene ke damunki ba ki faɗawa mutane ba a lokacin, sai kin gama iskance-iskancenki tukunna. to Wallah ki ka kuskura kishiya ta gane ma ruwan hawayenki gasa ki zata dinƙa yi". Sai a sannan ne nayi shiru, nace mata, "Gwaggo tunda munyi hutu yau don Allah ina so naje naga Hajiya da Mami da su Uncle Nasir". Ina nufin dangin mahaifiyata. Taja tsaki tace, "amma ke kuwa kina da abin haushi, dama abinda kike wa kukan kenan?". "a'a bashi bane. Wani Malaminmu ne yace na masa sata, har da kirani ofishinsa ya ƙara min wulaƙanci, shine nasa kuka sai yace wai Kukana kamar kukan Shanuwa, ita kuma ɗayar Malamar tamu tace min daƙiƙiya". Gwaggo tai wani zabarin gyara zane tana furzar da goron bakinta tace,"shi Malamin naku? Yace kin masa sata kuma kukanki kamar na shanuwa?". na ɗaga mata kai alamar tabbatarwa. ta jijjiga kai da kyau sannan tace,"To sata ta ƙare a ahalinsu, kuka kuma nasa ne ke kama dana tumaki. Ita kuma Malamar itace babbar daƙiƙiya da ta kasa fahimtarki. Kuma suje da halinsa na rashin kyautawa Allah zai saka miki, yanzu kije ki wanke fuskarki kizo kici abinci, na san babu abinda kika ci ki ka fice karatun da ba lada ba zunubi". na goge hawayena ina tambayanta cewa,"to Gwaggo zanje ɗin?". "za kije mana, ba kunyi hutu ba?". "ehh munyi har na wata guda ma". "to kinga kuwa kina da lokacinma da za ki je ki zazzaga musu. Ki bari idan Karima tazo sai ku wuce tare idan zata koma". Na miƙe ina cije leɓe nai ɗakina, gado na faɗa ina jin farinciki da nishaɗi, zanje naga Yayana, kuma mu taho tare da shi don bazan kuma barinsa acan ba, dole ne ma ya biyoni. Na rugume pillow inata murmushi ni ɗaya, dana rufe idona babu hoton dake haska min sai nasa, zumuɗi duk ya hanani sukuni, na ɗauka waya na kira Inna Karima na tambayeta yaushe zasu tace sai nan da sati biyu, ina jin haka ban san lokacin dana gilla mata ƙaryar ai Gwaggo bata da lafiya ba, aiko hankalinta a tashe tace min suna kan hanyar zuwa gobe ko jibi. Na kashe wayar ina dariya sai kuma na fara Allah na tuba Allah ka ƙarawa Gwaggo tah lafiya, ina haka ta shigo, hannunta ɗauke da kwanon abinci, yanayin da ta riske ni yasa tace, "ke lafiya?". "lafiya lau Gwaggo". Ta dire min abincin saman table tana faɗin, "da dai sauƙi kam, Allah ya bada lafiya inda rabon samunta". Ta juya za ta fice na dakatar da ita da tambayata. "Gwaggo kin taɓa ganin Halitta ɗaya a mutum biyu?". ta wani juyo a sukwane tana ambaton sunana, jin na amsa yasa ta cewa,"ohh ke ɗince dai". sai na ɓata fuska na turo baki gaba nace,"wai Gwaggo ba zaki bar ce min mai aljanu ba". tana gyara ɗaurin zanen da a ko yaushe nake takaicinsa tace,"to ai tambayar taki ce Sabina ta a bincika ce". "to ni dai ki bani ansata". "ansar me zan baki Sabinan Gwaggo?". na ƙara jefa mata tambayar, a wannan karon daya kasance tana fuskantata ne sai kawai ta bini da ido tana kallona da kyau cike da nazari, sai kuma tasa kai tayi hanyar fita tana faɗin,"to Allah yasa ba gamo kika yi ba...ni dai Rakiya Allah kayi min maganin abubuwan da suke neman fin ƙarfina".


*Please Vote, Comment and Share.*[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(18)*
bayan fitar Gwaggo kuwa raina fes nake jin shi, murmushi kuwa idan ka kalla fuskana kai kace gonar auduga ce saboda yadda haƙorana suka gagara rufewa. Har sai da Gwaggo ta dawo ɗakin ta iske ni kwance kan gado still dai murmushin nake, ina kuma ta faman juyi akan gado, sai da ta ƙare min kallon tsaf kafin ta samu gefen gadon ta zauna kana tace. “Allah mai girma da ɗaukaka, yau naga Mace. Anya Sabina lafiyarki kuwa, na fita kina dariya haka zalika na shigo kina dariya, to ki daiyi a hankali don wallah dariya illah ce, kuma kin san bana son dariya”. matsowa nayi kusa da ita, na kuma sakin murmushi. Sai naga ta miƙe tsaye zata nufi hanyar fita nayi caraf na riƙe hannunta, ina ƙunshe dariyar da ta ciyo ni, don nasan sarai abinda ke ranta nace,“wai Gwaggo me kika gani, ina zaki je dana ga kin miƙe?”. tace, “yo Sabina na sani ko aljanun ki ne suka dawo, wannan dariyar haka sai kace an maki bushara da shiga aljannah”. “yo Gwaggo kika sani ko busharar aka min, kinga ai sai mu tafi tare”. sai kuma na kwaɓe fuska nace,“amma fa gaskiya Gwaggo kibar cewa ina da aljanu, waye ke son su, amma ke duk magana ɗaya sai kice aljanu, mutum ba zaiyi dariya ba sai ya zama jinnu”. na faɗa ina yin ƙasa da kaina tamkar zanyi kuka. Ganin haka yasa Gwaggo kamo hannuna tace, “haba ƴar lalen Gwaggo, kinga kece naga sai murmushi kike ke ɗaya kuma kin san Allah da yayi ni ina da tsarguwa shisa kika ga nace haka, ko kuwa akan maganar ɗazu shi ne duk kike faman wannan murmushin, ko dai a makaranta kin samu ɗan..”. bata ƙarasa maganar ba muka haɗa iɗo, sarai na gane inda ta nufa sai na waske nace. “Gwaggota kenan mai abin mamaki, ki bama mutum daɗi ki bashi haushi, nasan fa abinda kike nufi, to ni bashi yake sakani nishaɗi ba, kawai dai ina son zuwa Kano saboda naga Farhana, kuma naga dangin Mama shi ke sani nishaɗi wallah. Kuma duk lokacin dana tuna yadda Kike tattalina kamar ƙwai sai hakan ya kuma tsundumani cikin nishaɗi da jin daɗi, ke dai Gwaggo Allah kaɗai zai biyaki ya kuma ƙara maki nisan kwana mai amfani ya ɗora ki kan maƙiyanki. Ina son ki Gwaggota”. na ƙarasa faɗa ina bata sumba a goshi. Gwaggo ita ma ta shafa bayana tana saka min albarka tana faɗin, “ai kema kin san indai akan kine sai inda ƙarfina ya ƙare, Allah dai ya haɗaki da miji nagari. Oh Allah ka nuna min wannan rana, gaskiya ranar akwai shagali, ke ranar sai na kwaso shoki, don ma wai babu Sahibina a kusa da nake faɗi maki abin sai yafi armashi”. Dariya nayi na janyo kwanon abincin da ta kawo min ɗazun na fara ci kafin nace, “ɗakko wata hirar don yanzu idan kika fara labarin Sahibin kin nan sai mu kwana mu yini baki gama ba, sai kace Sahibin kin nan yafi kowa”. ta ɗan dungure min kai, “munasira!, yo har kya faɗi min wani zancen Sahibina, baki ji akace kowa da bazarsa yake taka rawa, to ni tawa rawar da ta Sahibina ce, yo Allah na tuba ke har kya yimin zancen zan ɗakko maganar Sahibi, kema fa idan kika samu wuri tsaf nasan sai kin zarce ni, yarinya baki san loɓe ba(love)”. wata dariya ce ta suɓuce min wadda yayi sanadiyar zubar da abincin da nake ci waje, Gwaggo tamin duban sheƙeƙe kafin tace,“kinga ba nayi magana kice ke baki san zance ba, yo meye abin dariya anan?”. ta tambaya babu wasa a fuskar ta, da alamu ta ƙulu, don haka nayi gaggawar tsayar da dariyar da nake yi kafin nace,“yo Gwaggo kece da fama, sai kice sai kinyi turanci kuma baki iya ba, ai sai ki haƙura haka, idan kuma ba haka nace maki zan fara koya maki haruffan hausa shima kinƙi da duk kin san yadda ake faɗan words a hankali”. “ke kika san wani was(words), hakan ma tunda zan faɗa a gane ai shikenan tunda ba wurin wani naje na faɗa ba, bare naji kunya ato”. “yo ai kuwa wataran zaki faɗa a wurin wani wallah idan baki daina ba”. Gwaggo tace, “yau naga iya shege, ke Sabina fice min da gani”. Daga haka na miƙe ina dariya har na fice a ɗakin, dama yau na gama shiri na ba zan kwana wuri guda da Gwaggo ba duk tabi ta dameni da hayaƙi. Kai na tsaye nake tafiya dariya nacin cikina, har na isa corner da zata sadaka da kitchen kaina a ƙasa naji nayi tuntuɓe da abu da sauri na ɗago kaina ina duban meye ne, karaf muka haɗa ido da Yaya Haidar, da sauri na zaro ido shima ni yake kallo da irin kallon wanne abu zan maki na huce. ni kam ganin kallon da yake watso min tuni na sauya hanya, nayi gefe da niyyar wucewa yace,“dutsen da kika taka hala bai ji maki ciwo ba?”. Na ɗan ɓata fuska nace, “eh bai jimin ba”. ina faɗar haka na kuma niyyar wucewa. aiko a zafafe ya damƙo hannuna, tuni ido na ya raina fata, duk lokacin da muka haɗu sai naga kamar zai kuma tsotsen baki ne, fuskata ta cika da tsoro, baki na fal in-ina nace, "ka..kaj..kaji tsoron Allah kaga dai ba abinda nayi maka karka tsotson baki don Allah”. ina gama faɗar haka hawayen da suka cika ido na suka samu nasarar sauka kan ƙafar Yaya Haidar ya kuma ƙulawa fuskarsa tamkar ta bijimin sa yace,“an faɗa maki kowa ɗan iska ne kamar ke, da za’ayi tayin abu guda, ko an faɗi maki kowa maye ne kamar ke sha uku kawai, goge min ƙafa na ko na zane maki ƙaramin mazaunanki nan”. takaici ne ya ishen, a zuciyana nace, _wallah kamar na zabga maka mari nake ji._ zaro idon da Yaya Haidar yayi yasa ni tsorata ba ƙarama ba, don wata iriyar damƙa ya kuma yima hannuna ya matsa min ya kuma galla min mintsini, take na buga tsalle idona ya cigaba da zubar da hawaye da ƙarfi ya buga min tsawa yace,“ni sa’an kine, Sabina ina wasa da ke ne, ni zaki kalli tsabar idona kice za ki mara?”. ya ƙarasa maganar yana nuna kansa. “wallah zancen zuci ne ya fito fili ban san na faɗa ba, don Allah kayi haƙuri please Yaya Haidar Allah ban san ya fito ba”. ɗan cif-cif gemunsa ya kama yaja kana ya kawar da kanshi gefe guda, ban ankara ba yaja hannuna fuuuuu sai ɓangaren shi. ina ta bashi haƙuri amma sam bai kulani ba, saboda maganar tayi mashi ciwo, yana shiga yasa key a ƙofar ya saki hannuna, nan na shiga bashi haƙuri akan ya barni na tafi kar ya kuma tsotson baki, sai kawai na tsinkayo muryar shi yana faɗin,“abinda yau yafi tsotsar maki baki shi zan maki, za ki gane shayi ruwa ne zalla, za ki san kince ni za ki mara marar kunya kawai”. Nan ta ke ya shiga cire rigar shi ya zama daga shi sai gajeran wando, na saka hannuwa na rufe idona, gabana sai dukan dubu-dubu yake yadda kasan ana surfe akan ƙirjina, zuciyata kamar zata faɗo ƙasa tayi dancing haka nake jin yanayin yadda ta ke duka. Ta cikin hannuna nake ganin shi yana takowa, sai daya iso har inda nake naji ya cafki hannuna, sai ji na kawai nayi ya wulla ni kan gado, yana ƙoƙarin hawa gadon nace,“na rantse da Allah idan ka hawo gadon nan kamar a bakin Baba, tunda na kalla sam baka tsoron Gwaggo ka mayar da ita sakarya Kuma wallah Allah indai...”. Ban kai aya ba na jiyo muryar Gwaggo tana ƙwalo min kira. Da sauri ya mayar da rigar shi da wandon shi ya samu wuri ya zauna ni kuma yace min, “tashi ki shiga toilet ki tabbatar kin wanke fuskarki ta wanku, zance ma Gwaggo kina wanke min toilet kuma wallah idan naji kin faɗa mata magana ɗaya akan abinda na maki”. ya nuna ni da yatsa alamun kin san sauran. Cikin hanzari kuwa na diro daga gadon na faɗa toilet ina shiga Gwaggo ta turo ƙofar ɗakin ta shigo tana faɗin, “a’a Zainab tace min Sabina’n tana nan, ko kuwa tayi wani ɓangaren?”. “Eh tana nan, tana wanke min toilet ne”. ya bata amsa ataƙaice, kansa na ƙasa kamar me yankan farce. “Tolet kuma?, yau kuma ƴar wankin tolet ka mayar da ita bayan wulaƙancin duk da kake mata a baya bai ishe ka sai ka haɗa da folishwan?”. ina toilet amma yadda ta faɗi kalmar Punishment ba ƙaramin dariya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login