Showing 27001 words to 30000 words out of 89788 words

Chapter 10 - ALHUSSAIN Complete Hausa Novel

23 Aug 2025

396

kuma kallonsa, sannan ta bishi da kallon sama da ƙasa, kamin nan ta ciro Goro a gefen zanenta ta wurga a baki tana faɗin, "to Auwalu nuna min yanda zanyi kaji kai da kasan dai-dai, har ni dana haifeka zaka nunawa kafi ni sanin abinda ya kamata, ahh lallai ne, aikuwa to ka ƙara magana a wurin nan zan tattatara komatsaina na koma ƙauyenmu, tunda na lura kafi ƙaunar ka zauna da Matanka a sabon gida sama da ni da nayi naƙudarka". "ba haka bane, kiyi haƙuri Gwaggo Allah ya huci zuciyarki". "Ameen". Ta faɗa a taƙaice.
sannan ta ƙara cewa, "yauwa ana jina ba. Naji ana cewa babu wata matsala Allah ya bada zaman lafiya, ehh to ameen amma ba anan gizo ke saƙar ba, Ita dai Sabina da bakwa ƙauna ta zame muku ciwon ido domin babu yanda kuka iya da ita, saboda ina tsananin ƙaunarta Mahaifinta kuma na mutuwar sonta, saboda haka muddin ana son zaman lafiya a gidannan dole a ɗauke baƙin ido da mugun baki a kanta, gata nan ita kaɗai mahaifiyarta ta haifa mace, ni kuma na maye gurbin uwarta, A kiyaye ɓacin ranta, domin a duniyar nan idan ana ƙaunar aga ɓacin raina to a taɓa min ita. kun san da wannan amma yana da kyau na maimaita muku don naga baku da hadda. Farincikinta kaɗai nake son gani a gidan nan, kar a kuskura naga saɓanin haka, kallon banza wannan kuka yiwa inuwarta billahillazi ina shaida muku sai kun bar Habuja kun koma gidan iyayenku, musamman ma ke kumbusa (Umma kenan), saboda haka muddin ana son zaman lafiya da kwanciyar hankali ta ɓangarena to kar a taɓan marayun Ƴaƴa, duk da dai shi Abba ba kirki ya cika ba amma a ha nake sonsa, saboda haka a kiyaye, a tou; domin ni nafi ɗan iska iya shege, yanzu sai aga ba dai-dai ba". Sannan ta koma kan ƙannena ta kira sunan su ɗaya bayan ɗaya, "Aisha, Aminatu, Zainab da ke Khadija. Allah ya halicce ku a mutanen kirki amma kun rikiɗe kun koma na tsiya duk kun ɗauko halin uwayenku, to kuma kuji ni da kyau. Sabina dai da kuke gani ba sa'ar ku bace, saboda haka dole ku bata girmanta, ku manta da batun cewa ita zata dinƙa baku kamar yanda kuke so, ita ba waina bace da zaku dinƙa juyata son ranku saboda kunga tana da haƙuri. Ƴan banza masu zubin Ƴaƴan kwaɗi. to dai-dai da rana ɗaya akasin abinda na faɗa ya faru saina kai yarinya ƙauye nayi sadaƙar ta ga tsohon daya kusa shuɗewa, in yaso Yarinya ta zama bazawara da ƙuruciyarta ni babu ruwana". Zainab na turo baki gaba tace, "to ai Gwaggo ba laifinmu bane, mu yanda ake nuna banbanci a tsakaninmu ne bama so, tsakani da Allah muna uba ɗaya amma sai a dinƙa nuna anfi sonta taya za'ai muji daɗi". ta gwame baki tace, "idan so kuke a so ku ai sai ku zama mutanen kirki irinta". ta juwa ga Baba tace, "ni na gama magana. Kaima idan ka gama taka sai kowa ya tashi ya bar min parlo". Baba yace, "ehhh Gwaggo ai tunda kin gama shikenan". tace, "ka dai ƙara dubawa ko kana da ta cewa". "babu Gwaggo". "tom shikenan". Har zata miƙe sai kuma ta koma ta zauna, "au nayi mantuwa, sai batun girki kuma. Bana son wani girkin ƴar aiki a gidan nan, kowacce zagewa zata yi ta dunƙa dafawa marayun Ƴaƴana suna ci suna ƙoshi, tunda ba auroku akayi dan kuci kuyi kashi ba. A tou; nan dai ba tsohon gida bane bare ayi abinda aka ga dama, kar aji laushin katifa da sanyin AC ace za'ake jaɓarewa ana ƙara kumbura". Baba ya dubi Yaya Abba yace, "kai Abba sai ka dinga fita da Sabina kana koya mata mota B4 ending of this month, saboda already na sama mata addmission next month zata fara lectures". "tom Baba, Allah ya kaimu". Baba ya ɗauko wata baƙar leda a wurin, kwalin wayoyi ne a ciki, takan ƙananun ya fara bawa, ya kira Khadija ya bata tata ƙirar Tecno Spark 4, Zainab kuma Infinix S5, Aminatu da Aisha iri ɗaya suma, infinix Zero5 sannan nima ya miƙo min tawa ƙirar iphone 11 yace na bashi waccen daya bamu, kwacce da sim card ɗinta ya bata, kuma take a wurin yay mana recharging ta bank kowaccen su 2k, ni kuma 3k". Dukanmu muna murna muke masa godiya da adu'a. Daga haka kowa ya watse aka tafi kwanciya.


_Na Sadaukar Da Page Ɗin Gareki Siddeeqer Oumar Barde, kiji dadinki kuma ki sani ina yinki over._

*Please Comment, Vote amd Share.**AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(11)*
Shirin sauri nake tayi Yaya Abba na jirana zamu fita koyan mota. Baki ɗaya na hargitso da kayan sawata na rasa wanda zan saka, saboda na riga na saba tun muna tsohon gida bana iya saka kaya idan zan fita sai wanda Gwaggo ta zaɓa mani, gashi ita kuma yau ta shige toilet tayi zamanta kamar ta shiga labour room. Kiran wayar Yaya Abba ne ya shigo a karo na ba adadi, kai na dafe na share ban ɗauka ba, saboda idan na ɗauka fa raina zai iya ɓaci matuƙa, shi mutum ne wanda ya tsani delay a rayuwa, shi yasa ma ba kasafe ya fiya haɗa fita da wani ba. har lokacin da nake tsaye kamar nai kuka banga alaman Gwaggo zata shigo ɗakin ba, kayan na yayiba na fita da su zuwa ɗakinta, a bakin gado na sameta zaune ta riƙe baya tana ta sauke nishi, kayan na zube a gabanta bakina a gaba ina daɗa turɓune fuska. ta ɗago tayi min kallo mai kama da harara sannan tasa ƙafa ta shure kayan. tukunna a ƙufule tace da ni, "ke fa ba ki iya ganin mutum cikin wani hali ki masa sannu ba ko ki tambayi meke damunsa, a'a ke fatanki a biya miki buƙatarki, to sai ki jira sai na gama wartsakewa". "Eyyah Gwaggo tah wallah nai zaton ko kinyi training ne, ban kawo wani abu ke damunki ba". Wani wawan kallo ta wurgo min wanda yasani yin shiru da sauran maganata. "to idan kin aza sai ki sauke ba training nake ba, zawo nake fama da shi, shiga ta banɗaki na huɗu kenan a cikin rabin awa. Ban yarda da abincin jiya da muka ci ba, ina tunanin waɗannan ƴan iskan sun fara mana barbaɗe a abinci". Da sauri na ƙarasa wurinta cike da tausayawa, duba da yanda idonta ya faɗa lokaci ɗaya. "Subhanallahi, Gwaggo Zawo kuma? to taya akayi hakan? me kika ci da za ki kwanta?". ta ƙara kufula tana cewa,"da wanne yare nayi miki maganar da kika kasa fahimta, ko kuma ƙara maimaita miki kike so nayi, ba kiji nace ina zargin masu kama da tantabarun can ba. Mutum na fama da kansa dole sai kinsa yayi magana". taja guntun tsaki, "ke sam ba ki da saurin fahimta, dole idan za'ai miki bayani sai an faɗaɗa shi, kisa aita doguwar magana". nace, "Gwaggo to aini ban zargesu ba ne, tunda abincin nan dai nima na ci shi, wataƙila dai ko cikinki ne ya ɓaci kawai". ƴar maganar da nai kuma sai ta jawo masifa da sababi, faɗi ta ke,"auto ni za ki gayawa cikina ya ɓaci dake ban san takan cikin nawa ba. Da can da nake girkina naci lafiya na miƙe lafiya fa, da kika ganni sarai nasan takan lafiyar cikina, wannan girkin dai dole anyi wani barbaɗin a ciki domin nasan halin mugwayen matan Babanki, so suke su ƙarasa ni kuma ba yanzu ba, kema Allah ne ya kiyayeki, saboda haka bazan iya ci gaba da wannan haɗakar girkin namu da su ba, anyi an gama daga jiya, kowacce cikin su tayi nata taci da iyalanta, mu kuma yazo ya samo mana wadda zata dinga yi mana namu, wacce zuciyarta ta cika fal da tsoron Allah". Ni dai ina dafe da bayanta nayi murmushi, saboda ban isa na hanata wannan mitar da masifar ba sai kuma ta samu lafiya, cike da tausaya ma ta nace, "Sannu Gwaggo, bari a kira Baba sai ya turo likita". "ehh kirawo shi ɗin, dan cikina a ɗaure yake ni ɗaya nasan irin azabar da nake ci. Ba don ina gudun haɗa rigima ba ai da saina zayyane masa wannan muguntar da aka haɗa min, amma Allah dai...". sai kuma tayi shiru tare da yin ƙwafa. Cikin faɗa kuma taci gaba, "ni dai kaf cikin Yarana babu mai halin kirki irin Auwalu. haƙuri, mutunci, karamci komai ya haɗa, amma kuma duk cikin Ƴaƴana shi ɗaya ne bai yi sa'ar Mata ba, Mahaifiyarku kaɗaice ta ƙwarai, sauran auran nasa kam sai dai a kira shi da auran ƙaddara, jiya na gama yarda da duk wani mugunta nasu da kuke faɗa nake ƙaryataku, saboda kwana nayi ban runtsa ba ina kokawa da cikina. dama duk wani iya shege da suke ina ɗaga musu ƙafa ne saboda darajar Auwalu da suke ci amma na kusa yiwa tufkar hanci, kaf ɗin su za su gane shayi ruwa ne. Hmmm banda ma dai ina da tausayi ai da sai naja musu Allah ya isa, to idan naja musu binsu zatayi su zo su ƙara lalacewa, ni kuma gyaruwa nake so suyi kar a tafi lahira da tarin zunubai, tunda dai Allah ya ƙaddara auren su da Ɗana". ta juyo ta kalle ni, wadda nayi shiru ina sauraronta, ince tace nace shi yasa ma nayi gumm. tana wurgan harara tace, "kinyi shiru ba ki ce komai ba". nace, "to Gwaggo ni me zance". "ki faɗi abinda yake zuciyarki karta kasheki, saboda ina faɗar gaskiya shine kike jin haushina, to sai dai ko me za kice kice ehe, sirikaina ne amma bana sonsu, saboda mutanan sun cutar min daku, yanda bana manta akhairi haka bana manta sharri. ai tsakanina da su Allah ya...". Sai kuma tai shiru bata ƙarasa ba, ni kuwa dariya ce ta taho min, duk masifar da Gwaggo zata yi akansu da zarar tazo kan Allah ya isa to fa ba zata ƙarasa ba sai tayi shiru. "ki sa ki dariyarki mana ki bar ƙunsheta kina cutar kanki, ina faɗa miki gaskiya tausayinsu nake ji ne saboda bakina kaifi ne da shi kamar wuƙar daba, inaja musu Allah ya isa binsu zatayi kuma tabbata lahu sai sun lalace, ai nayi na gani ne, tunda najawa kishiyata Hussaina har kwanan gobe gata nan halinta bai sauyawa ba, iskancinta sai ƙara gaba-gaba yake taƙi tayi dai-dai". na sauke numfashi ina cewa,"yanzu dai Gwaggo kiyi haƙuri ki rabu da su, kowa yayi na gari kansa, ki barsu da halinsu, kuma insha'Allahu kamin nan kamin anjima za ki sami sauƙi, na kira Baba yace Family doctor zai zo". tace, "ai shikenan nayi shiru tunda kinsa baki, amma batun haɗakar girki kam ya ƙare, ni lokacin hutuna ne yazo tunda Allah ya kawo mu cikin wannan ni'imar, kema kuma bana so ki wahala, wannan aikin gajiyar kin gama shi tun a tsohon gida sai kuma bautar gidan mijinki. Saboda haka zan kira Karima idan zata zo ta samo min ƴar budurwar yarinya mai hankali da tsoron Allah". Kamin na buɗi baki nayi magana Zainab ta shigo ɗakin ɗauke da sallama bakinta, Ta tsuguna har ƙasa ta gaida Gwaggo. "lafiya". Gwaggo ta amsa mata fuska a haɗe, murya a can ƙasa. Nima tace min, "Yaya ina kwana". "lafiya lau Zainab". Na amsa mata fuskata ɗauke da fara'a. Yaran dukansu sun hankalta tun jan kunnen da Gwaggo tayi musu, don sun san sarai zata iya aikata komai, ba kasafai ta ke faɗa bata aikata ba, abu ne mai sauƙi a wurinta tai musu auren ƙauye. "kin shigo min ɗaki kin wani tsareni da idanu lafiya aka mutu kai na motsi, ko wani kinibibin ne?, ko kuma an aiko ki gulma ne?. To idan ma itace aka aikoki sai a sami damar juyawa don babu abinda za ki ɗauka". baki Zainab ta turo gaba, bata tanka ma ta ba tace min, "Yaya". nace, "na'am". "Yaya Abba says if you did'nt come out he will leave, becouse you are westing his time". na dafe goshi nace, "Ya rab, tell him yayi haƙuri dan Allah, am comming out now". kuma bata kai ga fita ba Gwaggo ta Gwame baki tana cewa. "idan ka haɗu da abinda ya isheka sai ka zubawa sarautar Allah ido. wannan barbaɗin rashin mutunci har ina?, a shigo min har cikin ɗaki a dinga sauya harshe a gabana, to duk wanda ya zageni kansa ya zaga tunda dai ba iyawa nayi ba bare na rama, ni dama tunda na ganki a ɗakin nan nasan ba alkhairi ne ya kawoki ba...ke kuma da ba ki da wayo kiyita biye musu suna ɗoraki a hanyar lalacewa, kaf gidan nan dai kin san babu mai ƙaunarki sama dani, amma tunda ubanki yay arziƙi kike neman juyawa min baya, to indai waɗannan makiranne gaki gasu nan". Zainab tace,"kai Gwaggo bafa zagi ne akai ba". sai ta kauda kai tace,"sarai ai na sani, Abba ne yayo aike yana jiran ta fito, banji yaran ba amma na fahimci me akace tunda naji an faɗi sunansa...to hakan da kika ga nayi gargaɗi ne nayi saboda kar a ƙara kwatanta hakan wataran, dan baza'a ji daɗin martanin da zan mayar ba...bana son sauya yare a gabana wannan halin munafukai ne". Zainab dai tai murmushi ta juya ta fice. "to ni kam Gwaggo tunda kinji sauƙi zaɓar min kayan na fita, kin san halinsa yanzu zai ƙara yo aike ko kuma yay tafiyarsa". "wa yace miki sauƙi naji, ƙarfin hali ne fa kawai nake...ni matso da kayan na gani". na tura mata kayan gabanta, ta ɗaga wata red ɗin riga tawa ta aje a gefenta tana faɗin,"wannan kamar sawarki uku ko. bari na bawa ƴar aikin gidan can da aka aikota t gaishe dani". tukunna ta zaɓar min wata doguwar riga ta shadda wadda taji aikin stones a jiki, ɗinkin yay kyau sosai. na ɗauka na saka na zaɓi gyale na yafa, na duƙawa nayi zan kwashi kayan tace, "ki barsu idan na miƙe zan gyara miki na kai miki, ko ba ki kalla duk karin guguwar ya hargitse bane, kuma kika tsaya cewar sai kin kai ɗaki wancan ɗan masu kwazazzafan sabon aike zai kuma danno miki, ma za jeki sai kun dawo Allah ya kiyaye". nai mata wani hug irin wanda ta gani a tv sanda muna kallo, yanda Patriva ta rungume kakarsu shine tace to nima nake yi ma ta hakan tana so dan Allah. nace,"Gwaggona na gode, Allah ya bar min ke ya ƙara maki lafiya da nisan kwana". Na faɗa fuskana ɗauke da murmushin jin daɗi tare da bata sumba a kumatu. Sauri-sauri na isa dressing mirrow na ɗauka faran powder na shafa, na ɗora da man leɓe sannan na zira takalmina. Duk abinda nake idon Gwaggo akaina, ina ƙoƙarin fita tace. "ke wai dan manzon Allah wacce kalar macece, kina nufin a haka za ki fita da wannan buyagin gashin naki da ba kya so a taɓa shi, ke kin ganki kuwa kamar sabuwar kamu". na yatsine fuska nace, "Gwaggo wancan satin fa aka taje shi, kuma naga baiyi komai ba ne, kuma fa na sanya hula babu mai ganewa sai ɗan sa ido". tace, "ni Hannatu yau naga abinda yafi zare tsayi. to Sabina da aka taje shi wancan satin ma ai tsami yake, Ina taje shi fa ina tara yawu a bakina, kuma yanzu har kina faɗin kin saka hula, ke dai kin shiga uku da ƙazantar kai wallahi, samu ki kai ma shi yasa. to kizo ki wuce ki ɗauko wannan abar mai kama da indararo kizo ki busar da shi ki taje don bazan gayara miki ba, kuma baki isa kin fita a haka ba bare kija min zagi ace Gwaggo bata gyara ki". kamar zanyi kuka na maƙale jikin ƙofa ina roƙonta akan ta ƙyaleni, don ni wallahi idan da abinda na tsana taɓa kaina, da ace Gwaggo ta bani dama tuni na jima da aske shi, to sai tace wallah bazan aske ba haka kawai na rasa mijin aure, tunda ta lura mazan yanzu idan ba gashi ba ƙirji sai su raina mace. "wai kuwa ba za ki zo kiyi abinda ya kamata ba ki wuce kije ku tafi sai kunyi yamma. Kin wani tsaya kina turon baki gaba kamar wadda za'a bawa nono, to bari na kira Abban nace masa gaki anan ba uwar da kike kawai dai ba za ki fito bane". nai saurin cewa, "don Allah Gwaggo ki bari sai na dawo, ko a yanzu zafi yake min, kuma kin san ko ya na taɓa sai ciwon kai". "ai kuwa dai kika je gidan miji da wannan ƙazantar baƙar wuya za ki sha, a tou ni dai gaskiya nake faɗa miki. dan ba zai juri ganinki tsab-tsab ba yana jiyo tashin ƙamshi ta ko'ina a jikinki sai ya doshi kai yaji hammm, yasin sai to miki hanyar gidanku zai yi, idan za ki gyara tun wuri gwara ki gyara". na ƙara cewa, "to Gwaggo nace ki barni na aske ba shikenan sai na huta ba kema ki huta da mita". "yo dama aini ban isa na faɗa maki gaskiya ba, shikenan sai ki ce na cika mita. to kije Allah ya kiyaye, ina kuma faɗa miki karki yarda da tuƙin ganganci irin na Abba, da kinga yana neman wuce gona da iri ki sauka ki nemi mota ki dawo gida, ranki ɗaya ne ba biyu ba...sai kun dawo". Fita nayi ina jinta kuma tana ci gaba da faɗa akan rashin gyaran gashin, idan na dawo ya zama dole ta kaini wajen bayerabiyar nan ta gyara min kai, ba zan kasheta da tsamin kai ba lokacinta bai ba, kuma wallah kaina ba wani wari da yake sharri ne irin nata kawai. ni na lura sababin Gwaggo ma ƙaruwa yayi tunda muka dawo gidan nan. Ina isa ƙofan parlo kiran wayar Farhana ya shigo, ina murna na ɗaga domin mun kwan biyu ba muyi waya ba, hiran yaushe gamo muka hau har tana bani labarin exams ɗinsu ta fito ta sami second class, na tayata

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login