Showing 39001 words to 42000 words out of 89788 words
na fasawa yarinya baki babu ruwana". yay magana yana kallon Gwaggo kamin ya maida kallonsa kaina yana min kallon za ki sani. "kaga ni kuma sharri ne bana so. Yarinyar na gabana kace ta maka rashin kunya, ta ina to ni ban gani ba. Kai dai ka dinga jin tsoron Allah, Mutuwa ake yi. da ace kana da zuciya ma fa ba zaka dawo part ɗin nan ba". Murmushi kawai yay baice mata komai ba, ta ƙara cewa nayi masa godiya, godiyar da ni ban san akan mene ba, ina ɓata rai nace masa, "na gode". Yay min shiru kamar bada shi nai magana ba, na tashi ina bige-bigen ƙafa zan wuce yasa ƙafarsa ya taɗe ni na faɗa jikinsa, ina faɗowa ya aje wayarsa gefe yasa hannunsa ɗaya ya matsoni jikinsa, ɗayan kuma da mugunta ya matse min baki har na gagara yin ihu, sannan ya kai bakinsa nawa ya kamo leɓena na ƙasa da haƙorinsa ya gartsamin cizo mai shiga jiki. Ganin wannan abu ya sanya Gwaggo tashi da sauri ta iyo kanmu tana tafa hannu tana zabga salati. "ni Hannatu yau naga abinda yafi zare tsayi, ,yo dole yarinya mana tace ka tsotse mata baki, tana faɗa ina basarwa ashe maganar gaskiya ta ke faɗa min, nake cewa tofin magani ne kake mata. ba zaka sakar mata baki ba sai ka cinye mata leɓe". Shi kansa maganar ta Gwaggo ta bashi dariya, ni kuma yana mamakin rashin hankalina da kuma rashin wayona, ashe da nace zan faɗa mata sai dana faɗa. "Allah Haidar ka bari na ƙaraso nan baka rabu da ita ba kai zan shaƙe na yiwa ruƙiya ba ita ba, idan aljanun iskancin ne kaima akanka sai naji, mara ɗa'ar yaro kawai". Dariyarsa ya gimtse yana tankaɗani daga jikinsa na miƙe ina hawaye, Gwaggo na ƙarasowa na faɗa jikinta na fashe da kuka. Ɗagoni tayi tana dubana, ta kalla Yaya Haidar ta zabga masa harara, ta ɓata rai sosai tana ce masa. "nan gidan dai baka ga an rubuta gidan kashe awu daga waje ba, saboda haka ka ajiye barbaɗin iskancin ka acan inda ka baro, tunda nake da Sabina wani ƙaton gardi bai taɓa riƙe mata hannu ba amma kai saboda tantirancinka ya kai intaha a gabana ka ke cafke mata baki saboda rashin kunya irin naka, kaga baki ɗan ƙarami da shi gwanin sha'awa, to billahillazi karka ƙara tunda dai ita ba muharramarka bace. a hakan ma kaje kai da Allah, zunubin daka kwasa ma ya isheka, kuma na dawo kan bakata kar ka sake zuwar min ɓangarena tunda bana ka bane, ruƙiyarka bana so tunda na lura irin ta ƴan iskan Malaman nan ce, Malaman gaibu, to zan nemo sabon Malami da kaina wanda zuciyarsa ta cika fal da tsoron Allah. Yanzu ka tashi ka fice min kamin na sassaɓa maka kamanni dan iya ƙololuwar ɓacin rai ka gama ɓatan rai, Ban san haka halinka yake ba, a gabana ka kama bakin yarinya da tsotso kamar ka biya sadaki, kai ai da sunan ƙanwarka, to da take ƙanwarka ai akwai aure a tsakaninku ko". yace, "idan ni kince na daina iskanci itama sai ki faɗa mata ta daina rashin kunya. Don gaba yarinya ta ƙara murguɗa min baki abinda yafi haka zanyi mata". Dogon tsaki Gwaggo taja, Haidar yana dariya yana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yace, "Easy Hajiya Gwaggo". Wani dogon tsakin ta kuma ja tana zabga mishi harara a karo na ba adadi, cikin faɗa take ce masa, "kai da Easy ɗin na haɗaku na zazzabga muku mari, Wallahi ka fita a idona Haidar, akan Sabina zan saɓa maka yanda baka zato, sarai kasan halina idan raina ya kai ƙololuwar ɓaci, zan ɗauki komai amma bazan ɗau lalacewa ba, don haka kayi gaggawar miƙewa ka bar min parlo, kuma ko sahun inuwarka kar na sake gani a ɓangarena, abinci kaje can matan gidan nan su baka idan sunga dama, idan ba su so ba su barka da halin iskancinka ya ƙosar da kai, nk dai har ka bar gidan nan na gama saka kwano da kai". Yaya Abba na dariya ƙasa-ƙasa yace, "idan kuma ya dawo gidan gaba ɗaya fa?". Kansa ta juyo da faɗan da ta ke Yaya Haidar, tasa ƙafa tayi fatali da plate ɗin abincinsa, ta haɗa sunansu dana ubansu gaba ɗaya ta zage, da alama dai ran Gwaggo ya ɓaci matuƙa, dan faɗa takewa Haidar sosai, tana nuna masa kuskuren abinda yayi, wanda shi kansa sai da yayi dana sanin abinda ya aikata. A tsawace cikin ɓacin rai tace da su, "ku tashi ku ɓace min daga gani". za su fita Baba ya shigo, Gwaggo tace,"yauwa ƙwara da Allah ya kawoka, tunda ni basa ganina da gashin ido bare suji maganata, kaja musu kunne kar su ƙara zuwar min ɓargarena tunda babu tsiyar da suke yi min, duk su biyun bana son sake ganinsu anan dai inda nake, suje can su ƙarata da halin su na rashin ƙwarai, dama ance abokin ɓarawo ɓarawo ne to abokin ɗan iska ma ɗan iska ne. Ko kwanon abinci sun daina ɗauka a wurina, idan zaka dinga basu kuɗin saya sai ka basu, idan ma da matanka zaka haɗasu ka haɗasu, kai idan ma aure zaka yi musu ku dai kuka jiyo kai da su, ni ba damuwata bace, babu ruwana, buƙatata dai a daina zuwa inda nake, idan ba haka ba kuma duk abinda nayiwa mutum shi yasa ya da kuɗinsa". Baba ya dube su yay musu kallon tsab, kansu yana ƙasa sun sunkuyar yace da su, "mahaifiyata ce fa, rashin kyautawar mai kuka yi mata?". Da sauri Gwaggo ta ɗaga masa hannu tana cewa, "n ifa bana buƙatar sulhu, su fita kawai kuma ka gaya musu karsu ƙara dawowa". "shikenan kun dai ji abinda tace, ku fara bata haƙuri kamin ku tafi". "Gwaggo kiyi haƙuri".
Suka faɗa tare. tayi musu kallo mai harara, tana nuna Haidar da yatsa tace da Baba, "kai Auwalu wancan yaron idan aikinsa ba mai ƙarewa bane a kusa to ka nema masa wani gidan ya koma can da zama, bana son ganinsa a gidan saboda bashi da mutunci". Ƙaramin tsakin da Yaya Haidar yaja duk sai da muka jiyo, Baba ya juya zai masa magana yaga har ya fice, Gwaggo na jijjiga kai tace, "kagani ko, sam bashi da mutunci. Banda Allah yasa a gabanka ne da zagayowa zaiyi ya bangaje ni tukunna yasa ƙwalelen kansa ya fice. Ɗan banzan yaro mai kama da alkaki sam baiyi halin ƙwarai ba, shi Sulaimanun zai zo ya same ni, naji idan akan hanyar daya ɗora shi kenan". Baba ya nemi wuri ya zauna, nai masa sannu da zuwa, yana kallon yanayina yasan faɗan Gwaggo da su Yaya Abba akaina ne. Gaisheta yayi yay mata sannu da gida, "yauwa". ta ansa mishi. "ya aikin naka?". "Alhmdl". sai naji yana cewa, "Gwaggo tun ɗazu kika ɗaga hankalina, da kika kira kika ce akwai matsala nayi gaggawar tahowa, lafiya dai ko?". "tun a lokacin da na kiraka mai ya hanaka dawowa?". ta faɗa muryarta na nuna ɓacin rai. "kiyi haƙuri ko a lokacin mun riga mun shiga meeting ne, to naso tahowa sai kuma naji kince na kwantar da hankali na amma dai na dawo gida, jin haka nace ba babbar matsala bace har na kammala komai ma". "to dama akan Sabina ne". Na ɗago da sauri ina kallon Gwaggo, gabana na faɗuwa, to ni kuma ƴar gidan Gwaggo na mai nayi. Baba naji yace mata, "me Sabina ɗin tayi?". tace da shi, "kaji na taɓa kawo maka ƙararta ne da zaka tambaye ni me tayi, to ita bata laifi salahar baiwa ce, ka dai ce me ya faru da ita". Baba ya haɗiyi yawu yace, "to mai ya faru da ƴar lelen taki?". "aljanu ne da ita". "aljanu kuma Gwaggo".
Baba ya faɗa yana zare ido, don maganar sosai ta dake shi. "ƙwarai kuwa, amma basu yi nasarar shigarta ba, sun dai shafeta ne, wancan fitsararran baƙon yaron shi yay mata ruƙiyya kasan Malami ne, ƙwaƙwalwarsa taf da haddar qur'ani amma babu tsoron Allah a zuciyarsa, amma haka dai na haɗashi da ita yay mata karatu da adu'oi, sannan ya fita cikin gaggawa yaje islamic chemist ya haɗo magunguna da turare aka haɗa mata, nan da nan cikin ikon Allah komai ya lafa. amma farko fellawa tayi da gudu, da ace babu mai gadi ma ba'asan inda zata nausa ba, nan ta faɗi tana aikin shure-shure da buge-buge da ife-ife. Ashe ajiye shirgegiyar mace ma acikin gida yana da amfani, don wannan ƙatuwar matar taka ita ta ɗaukota duk uban nauyin da suka sa Sabina tayi, don ni dana ɗaga hannunta ma banyi zaton hannun mutum na ɗaga ba...yau ai Ƙatuwar can tayi min rana". jin abunda ta ke cewa yasa na fashe da Kuka, gaba ɗayan su hankalinsu ya tattaro ya dawo gare ni, musamman ita da ta ke bada bayani. "me kuma aka yi miki?". ta jefo min tambaya. ina shashsheƙar kuka nace, "Gwaggo aljanu fa kike cewa ina da su, kinsan kuwa mene aljanu, na rantse ni lafiyata ƙalau". Wata harara ta jefa min kamin tace, "nufinki ƙatuwar mace da ni zan zauna ina gillawa ubanki ƙarya ne, to ribar mai zan samu idan nayi miki fatan wannan lalurar da ba'a so, mtswww shi yasa ɗazu nake gaya miki da ku masu aljanu da mahaukata ɗaya kuke, tunda duk bakwa sanin abinda kuka aikata a lokacin da kuke kan ciwo. To a faɗuwar da kika yi ɗazu sune suka zo, Allah shaidata, Haidar Shaidata, Matan gidan nan shaidata, a tou balle ace nayi ƙarya, ƙwamma na sanar miki gaskiyar komai kamin ki ƙullaceni a zuciya". Shiru nayi ina ci gaba da kukana, ƙasan zuciyata kuma ina tantamar anya Gwaggo bata fara daina ƙaunata ba. "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Shine abunda Baba ke nanatawa cike da al'ajabi da kuma tsoro. "Sabina garin ya haka ta faru, me yasa kikayi sakaki da azkar?". "Allah ni Baba bana da wata iska, kawai dai faɗar gwaggo ce kuma ka kira shi Yaya Haidar ɗin ka tambaye shi, anyi haka ko ba'ayi ba, tare ma mukaje koyon mota, kuma har yanzu ma muna zaune da su shida Yaya Abba babu abinda ya sameni. Ina jin dai ko Gwaggo ta fara rikicin tsufa ne, shine ta fara rikicewa ta kaina". Ta kalleni ta jijjiga kai, "to ai kaji, itama ta hau sahun waɗancan fitsararrun yaran, amma ba laifinta bane ita zan mata uzuri, tunda yanzu ta zama ba ita ɗaya ba, adu'a kawai zan bita da ita, idan na fahimci kuma sune sai na hauta da duka". Ta kalle ni tace, "ki sami damar yimin shiru, Allah yasa a gaban ubanki ne bare kija ace zane miki jiki nayi, kin ɓare baki kina kuka mara daɗin saurare, Kefa dama haka halinki yake wani zubin, sam-sam ba ki da daɗin sha'ani". na kuma fashewa da sabon kuka na miƙe zan bar wajen. "dawo". Tace da ni. Na koma na zauna ina jin kamar nayi me saboda baƙin ciki. "to yanzu Gwaggo mene abunyi?". Baba ya tambayeta. tace, "abunyi shine ka tattaro min kawunan Matanka suzo nan. Don ina tantama da wannan Al'amarin, ni dai ba aljanu ba, kai ba su ba, uwarta har ta mutu babu wata alama data nuna tana ɗauke da aljanu, kai kafatanin dangina ban samu labarin wanda ke ɗauke da su ba, kaga kuwa bana gado bane. Bugu da ƙari shekarar mu nawa a wancan gida kamin mu dawo nan, babu wata alama da taɓa nunawa tana da mutanen ɓoye sai da muka zo nan. To da sake a wannan lamarin, su zo idan acikinsu akwai mai su sai ka kwashe su daga gidan nan, kuje can kai musu magani idan sun warke sa dawo. Idan kuma ma wani mugun ƙullin aka ɗaura to azo a warware shi anan, don wallahi aka kuskura na gano ture ne akayiwa Jikata ba za'aji da daɗi ba". Baba yace, "To amma Gwaggo ai a cikinsu kaf babu mai aljanu". a harzuƙe tace, "shine ai nace maka ka kirasu suzo koma wace acikinsu, to ta kunce baƙin ƙullin da tayi tun wuri, dan billahillazi bani da kyau, ni gaskiya ce nake faɗa babu ruwana. Kar na ɗau mataki kai tsaye ace nayi rashin kyautawa...dan kai kanka ba zaka ji da daɗi ba".
*Please Vote, Comment, and Share.*
[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*
_By Oum Ramadhan✍🏼_
*(14)*
*Monday Morning.*
kasancewar yau monday tushen aiki, kuma yau ɗin da izinin Allah zan fara ɗaukan lectures, dan haka tunda na kammala azkhar ɗina ban koma bacci ba shiri kawai na fara yi, kwalliya nayi sosai wanda ta ƙarɓe ni matuƙa musamman dana ɗora da medical glass ɗina, dama gani ƴar son kwalliya da ado, tabbas duk wanda ya kalle ni dole ya so kuma gani na. Tunda na fito parlo na kalla yanayinsa nasan Gwaggo bata tashi ba, saboda indai ta farka ta fito zata sa karatun ƙur'ani ta kuma saki turare. jakata da mayafina na aje kan kujera na wuce kitchen don samarwa kaina abinda zanci, dai-dai da zan shiga nayi karo da Yaya Haidar zai fito, da sauri naja baya nayi gefe a tsorace, Allah ya taimake ni ban tankwaɓar masa da tea cup ɗin dake hannunsa ba. Na murguɗa baki gefe don banda niyyar gaida shi, sai naji kamar na koma idan ya fita sai na dawo, sai wata zuciyar tace min kawai na tsaya na ƙara bashi hanyar wucewa, ina kallonsa ya wani haɗe rai yana jifana da harara, bai yi niyyar saurarena ba amma saboda neman magana yaja tsaki yana kallon kayan jikinsa kamar nayi masa ɓari a jiki. Ya ɗago ya kalle ni yana kuma hararata, ya ƙara jan tsaki yace, "ba kya gani ne da ba za ki iya lura da tahowar mutane ba". Na kalle shi kaɗan nace, "ai ban san da tahowan naka bane, kuma ina sauri ne". Tsaye yayi yana kallona ta ƙasan ido, "stupid girl". Ya faɗa yana ƙare min kallo ta ƙasan ido, ni dai zumɓuro baki nake ina alla-alla ya wuce, wayarsa ce tayi ƙara, ya ɗauka yana waya, sai daya gama wayar kana ya bar wajen, nabi bayansa da murguɗa baki. Ni dana shiga kitchen ɗin ma rasa me zan dafa nayi, na duba agogon dake saƙale a wurin, lokaci ƙara tafiya yake kuma yau tara ne zamu shiga lectures, ga time har takwas tayi, na doki ƙafa a ƙasa, ko me fa zan dafa sai yaja min lokaci tunda ni bacin Indomie nake ba, ko da tea ɗin zan dafa it will take time too, tunawa nayi da Yaya Haidar zai fita da tea Kettle a hannunsa, da sauri na suri cup da spoon, na zuba madara da bounvita da nescape na fita, ina zuwa kuwa na sa me shi kan kujera yana kurɓan shayinsa, naje gabansa na tsaya ina sosa gefen kunnena. Ya saci kallona ya ɗauke kai kamar bai ganni ba, na turo baki gaba na duƙa gaban table zan zuba tea a tsawace yace da ni,"kee". Na ɗago ina marairaice fuska nace, "Please Yaya Haidar, Makaranta zan tafi and idan nace i will wait to cook something i will be late. tea ɗin da yawa, barinsa ma za'ayi tunda Gwaggo is not drinking". Na faɗa ina ɗaga kettle ɗin na jijjiga naji yawansa. "wallah idan ba ki aje min kayana ba sai na zabge ki da mari, ke kika dafa min da za ki zo kice na ba ki, mara kunya kawai ana magana kina turowa mutane baki, me zai hana ki jira Kakar taki tazo ta dafa miki, ko kuma ni sa'an kine da zan dafa abu kici". ya faɗa yana ƙara tamke fuska. Na aje ina ƙunƙuni ina cewa, "to amma ai dai a kitchen ɗin Gwaggo tah aka dafa". Ashe ya jiyo ni, hakan yasa yace, "an dafa a kitchen ɗin nata kuma baza'a bayar ba, bar min nan wuri ko kuma nayi ball da ke". Na miƙe na bar masa wurin, cikin raina ina faɗin mutum ba abinda ya iya sai shegen ci, tunda yazo gidan nan kamin kowa ya tashi zaka kalla ya tashi ya dafa abincinsa, kuma aikinsa kenan shan tea ko da rana ko da dare, sai kace wani balarabe. Kitchen na wuce na ɗora ruwan zafi, yana tafasa na sauke na dama curstad, na fito na wuce dining nayi zamana ina shan kayana, Gwaggo ta fito ta sameni, tana kallona ta fahimci akwai abunda akai min. dan haka ta dakata daga gyaran ɗaurin zane tace min, "ke kuma me aka maki kike faman ɓata rai da sanyin safiyar nan? duk daƙe dama uwar miskilanci ce, ko ba'a taɓa ki ba iskokanki zuwa ɗaukar fansa suke". Na aje cup ɗin na ture shi daga gabana, daga tashinta zata hauni da faɗan da baya ma ta wahala. Taja ƙaramin tsaki tai juyawarta zata bar wurin tana cewa, "ke dai kika sa ni da halin nurƙufancinki da baida kyau, tashi na kenan ban bawa cikina ba, ba za ki sa ni magana ba". Na fara shashsheƙar kukan ƙarya nace, "to ba Yaya Haidar ba ne". Cak ta tsaya ta juyo tana kallona, "aina kuka haɗu da Haidar ɗin har kika masa rashin kunya, ban hana ki shiga sabgarsa ba, ina ce na miki faɗan babu ruwanki da shi ko". "ni fa ba sabgarsa na shiga ba, shine don nace ya sammani tea yaƙi, kuma nace masa na makara a school amma duk da haka ya hanani yace zai zabga min mari, yace naje na taso Kakartawa tazo ta dafa min". a wani sukwane ta dawo da dubanta kaina gaba ɗaya. "to shi aina ya sami tea ɗin bayan su ba kitchen garesu ba, kuma dai matan gidan nan basu isa tashi ba bare ace sun dafa sun bashi". "anan fa yazo ya dafa, na fito zan wuce na gansa ya fito daga kitchen". ta jijjiga kai kamin tace,"shi Haidar ɗin wai? Kai wannan yaro akwai baƙin hali, ruwan shayin da zai sammaki ba wata tsiya ba, ɗan ƙwal uba ina ce ma arziƙin ubanki yazo yake ci. tukunna ma ban ce