Showing 87001 words to 89788 words out of 89788 words

Chapter 30 - ALHUSSAIN Complete Hausa Novel

23 Aug 2025

401

kinga ke ɗaya Allah ya jarabceni da mahaukacin sonki shikenan sai ki dinga yi min baƙincikin rayuwarki, yanzu idan ba ki sha maganin ba taya za'ai ki samu sauƙi, an san dai sauƙi na wurin ubangiji amma don Allah dan Annabi Sabina ki daure kisha maganin nan ko kema kyaji ƙwarin jikinki, tun safe ake fama dake akan abu guda". na miƙe zaune ina cewa Anty ta bani curstard ɗin na sha, ina kai cokali ɗaya bakina nayo amansa, na fashe da kuka domin nima Allah ɗaya yasan irin wuyar da nake ci. Yaya Haidar ne ya shigo, kowa ya maida hankalinsa ga sallamar da yake. "a'a Haidar an sauka?". da yake yaje ganin gida kusan satinsa uku. "ehh Anty". ya faɗa yana zama a kujerar kusa damu. ya miƙawa su Yaya Abba hannu suka gaisa, kallon ball ɗinsu suke hankali kwance, Yayana da Yaya Abba sai uban musu sukeyi akan ball ɗin. Gwaggo ta miƙe tana masifa taje ta kashe TV ɗin, ta fuskancesu tana cewa,"ku kam dukanku baku da imani, kuna ganin yarinya babu lafiya amma kunzo kun saka ƙwallo a gaba kuna kallo, me makon ku zauna kuyi ma ta adu'ar samun sauƙi". tana rufe baki Yaya Abba ya miƙe ya raɓawa ta gefenta yaje ya sake kunna tv ɗin, bai kai ga ɗago kai ba yaji saukar ranƙwashi zazzafa akansa.
"haba dan Allah Gwaggo, kin san kuwa yanda wasan nan yake da zafi". ya faɗa yana sosa wurin yana kuma ɓata rai. "matsamin". ta faɗa tana bangaje shi a wurin ta kuma kashe tv. "wallahi idan kun kuma ganin kayan kallon nan a kunne to yarinyar nan ce ta samu lafiya. wai ku ina naku ma yake da baku da aiki sai zuwa ku addabi nawa salon ku lalata min, to wallah kar yaron daya kuma kunna min kayan kallo tunda kuma duk ansa muku naku. ni kar a ƙara kunna min ko socket ne tunda jikata babu lafiya, wanda ba zai jura ba sai ya daina shigo min ɓangarena". "mtswww". Yaya Haidar yaja tsaki, ta waigo gare shi tana masa wani duba. "ka dawo zaka fara ɗan iskan halin naka ko Aliyu. ni dai ka kuma yimin tsaki kaje kai da Allah tunda ni ba tsaka bace". ya ɗago ya kalleta ta wurga masa harara. "kai dama sam baka yo gadon arziƙi ba, mutumci sam bai gama ratsa ka ba da alama baka tsotsa ba. banda haka ka shigo ka kallemu da mara lafiya amma ko sannu baka mata ba kasa kai ka wuce, saboda zuciyarka sam babu tausayi bare imani". "to idan na tsaya ni zan bata lafiyar, ke fa Gwaggo akan waccen yarinyar kina da matsala Allah". bata kuma magana ba ta jiyoni ina wayyo Allah nah, ta iyo kaina da sauri tana zabga salati, Amina da Zainab sun riƙeni ina aikin kyala amai kore shar, sai Anty dake zuba min ruwa a fuska. shi kuwa Yayana gaba ɗaya hankalinsa baya jikinsa, tun ɗazu idonsa na kaina ganin idon Anty a wurin ya kasa zuwa inda nake, sai na ɗago ido sai naga yana ta kallona da tausayawa, yanzuma ina maida numfashi muka haɗa ido, ya haɗa hannu yana roƙona akan na daure naci abinci na sha magani. yanzu kam Allah ya taimaka na shanye curstard ɗin duka sai dai na kasa shan maganin. "Anty kawo maganin". Yaya Haidar yace da ita a lokacin daya iso wurinmu, ta miƙa mishi yace su Zainab su bashi wuri. ya ɗaure fuska tamau yace min buɗe bakin, zanyi gaddama ya ɗaga min hannu yana min wani mugun kallo, ya kalla Gwaggo yaja tsaki kaɗan yace. "don Allah tsohuwa ki mana shiru, duk kin cika mana kunne. kukan naki ne zai sanya ta samu lafiya". aikuwa cikin masifa tace masa,"ba zanyi ba, ba zanyi ba, nace bazanyi ba ɗin idan ka isa kuma ka hanani. mara mutunci kawai". ta kuma rungumeni tana ci gaba da kukanta. a hankali yace,"dama ta mutu kowa ma ya huta". "ɗan banza mai mugun jafa'i kaga mutuwa akanka. dalla Malami ka tashi anan wurin uban wa ma ya kawoka". bai kulata ba ya kama bakina ya matse ya zuba min maganin, tukunna ya zuba ruwa ya matsen hanci yace idan na dawo da shi sai raina ya ɓaci, haka babu yanda na iya dole na shanye inata kakarin amai. "ina da ina ke miki ciwo dama?". ko kallonsa banyi ba na nuna masa kaina kawai, ya kama kan yay min adu'a tukunna ya tashi ya fita. ba jimawa kuwa bacci ya ɗaukeni dan naji daɗi sosai dama ciwon kan ne ya addabeni. washegari da safe ina zaune ni ɗaya a parlo na ɗan ji daɗin jikina, Yaya Haidar ne ya shigo, nai saurin miƙewa zan wuce ɗaki saboda irin rigar dake jikina, ya kalleni ya taɓe baki, na harare shi ta ƙasan ido nima na murguɗa masa baki na wuce ɗaki. a dining na dawo na sa me shi yana zuba tea a cup, na wuce na kwanta kan kujera ina ci gaba da kallon cartoon ɗina, ya dawo ya zauna a kujeran dake facing ɗina. ya ɗau remote ya sauya channel yana kurɓan ruwan tea, ina marairaicewa nace,"Yaya Haidar dan Allah ka mayar min". ta gefen ido yay min kallo ɗaya, kamar ba zai mayar ba sai kuma ya maida ya aje remote ɗin, ya ɗora kafa ɗaya kan ɗaya yana cigaba da kurɓan tea ɗinsa. "tashi zaune". nayi kamar ban jisa ba, sai daya kuma ɗaga murya yace,"ba za ki tashi zaune ba. ke ko gajiya ba kya yi da kwanciya, a haka za ki ji ƙwarin jikinkin naki". nan ma shiru na masa sai murguɗa baki da nayi ta gefe. "idan ba ki miƙe zaune ba babu abinda zai hanani juye miki ruwan tea ɗin nan idan na iso nan wurin". ya faɗi hakan yana ƙoƙarin miƙewa, aiko nai saurin tashi zaune ina aikin zumɓura baki, dan nasan kaɗan daga cikin aikinsa. Gwaggo ta fito tana cewa,"kai dai wannan yaro anyi mugun mutum. to ni dai karka ƙara ɗaga ma ta murya bata da lafiya. ka barta taji da jikinta". "ina kwana Gwaggo". yace da ita. "lafiya". ta amsa masa a daƙila kafin ta kuma cewa,"na ganka da sassafe haka". ya ɗaure fuska dan yasan yanzu zata yi halin nata, yace, "breakfast nazo yi". "to baka da labari na daina ciyar da ƙatti ne, to gaskiya anjima karka dawo saboda ni yanzu bana girki da ku. Zara'u ce ta ke dafa muku saboda Allah ya shiryeta, yanzu ma idan kaje ƴan'uwanka suna can suna kwasa, da mai cin da mara cin duk acan suke yanzu. jiya ma naji batun katan ɗin taliyarta ya ƙare, nace ai sai dai haƙuri kuma". yace,"to ni gaskiya anan nake son cin abincina kuma anan zan dinga ci". "tabɗi aikuwa dai baka isa ba, wannan na baka trki hanyar neman zaman lafiya ba. sam ba zan iya ci gaba da ciyar da ƙaton gardi kamar ka ba, kalla fa yanzu daga dawowarka ka yashe min rabin madara, dama kai anan kafi kauri. ni fa na gaya maka zancen gaskiya ma banji daɗin dawowar nan taka nai ba...irin kune abun gudu, lokacin da muna tsohon gidanmu ai baka zuwa, amma da ike mun dawo gidan aljannar duniya shine ka gagara zama a naku gidan". shi dai bai sake ce mata komai ba, ita kuma ta kwashe kayan tea ta wuce da su kitchen tana mitar yashe mata madara da yayi. na gyara zan kuma kwanciya saboda ganin idon Gwaggo ya kuma doka min tsawa, babu shiri na saita hankalina, kamar an jefo Gwaggo sai gata ta fito tana cewa. "kaga Aliyu ni dai idan ba zaka iya zama haka kawai ba dan girman Allah ka bar min ɗaki, ba fa ni na gayyatoka ba, haka kawai ba zaka zo ka dinga firgita min Ƴa ba na rasa yanda zanyi da daddare, dama ya aka cika da wannan zafin zazzaɓin nata, ni kaina idan ka ɗaga murya furgita nake yi da wannan ƙatuwar muryar taka". ya ɗaure fuska yace,"dama meye ne yake damunta?". sai kuma tayi ƙasa da murya tana cewa,"wallah tun tafiyarka take fama da zazzaɓi mai zafi, gaba ɗaga fa sai yaune ta samu kanta". "kunje asibiti?".
"ehh to likita dai yazo har nan ya dubata. ni kuma kasan ba son takura ma ta nake ba tunda naga bata son asibitin nace a ƙyaleta". "saboda anga Baba baya nan ko, da yanan ai ko gwal ce ita sai taje asibiti". ya dubeni yace,"tashi kije ki shirya muje ai miki test". nai saurin ɗagowa ina dubansa, ya haɗe rai yana min wani wawan kallo, na shagwaɓe fuska na kalla Gwaggo ina shirin fashewa da kuka. "Gwaggo ni fa naji sauƙi". nace da ita ina karayar da kai. tace da Yaya Haidar, "shi abunda ka faɗa idan anyi ma ta zata samu sauƙi ne?". "me zai hana, ai kawai ki rufe ido ki barni da ita. haka za'a zuba ma ta ido ciwo na cinta. idan kuma kinƙi sai na ƙyaleta zazzaɓin yanzu ne kashe mutane yake". babu shiri ta juyo tana ce min. "kinga miƙe dan Allah bana son tashin hankali". na miƙe ina dukan ƙafa nayi ɗaki, ba dan naso ba shirya na fito, na samu Yayana ya shigo ma Gwaggo sallaman zai tafi makaranta, na taho tagal tagal kamar zan faɗi, ya riƙoni zuwa jikinsa yana tambayana sauƙin jikin. "da sauƙi". nace da shi ina kuma kwacewa a jikinsa. "me zan taho miki da shi idan zan dawo?". yace dani yana sunkuyo da fuskarsa saitin tawa. "pure bliss wafer". nace ina ɗago ido na kalle shi. murmushi yayi ya ɗan ja hancina yace,"Cutie nah wai sai yaushe za ki girma ne? pure bliss pure bliss dai". na karyar da wuya bance koma ba, ya kama hannuna ya zagaya dani na zauna a kujera, yace "Gwaggo zan tafi". "to ɗan albarka a dawo lafiya Allah ya bada sa'a. duk cikin jikokina kai ɗaya ne mai tausayi, cikin Abba da Haidar babu mai yiwa yarinyar nan magana a hankali sai kai". Ya murmusa kawai, sannan yay hanyar fita ina cewa,"Yaya a dawo lafiya". sai daya kalleni ya sakar min wani ƙayataccen murmushi tukunna ya fita. shi kuwa Yaya Haidar tunda na fito ko kallona bai kuma yi ba, har Yaya ya fice, sai daya gama jan ajinsa da miskilancinsa tukunna ya miƙe yace na biyo shi. muna isa hospital ɗin ya samu wani likita abokinsa, yay min tambayoyin abunda yake damuna, duk na faɗa masa, yace ba kya iya cin abinci ko? na gyaɗa masa kai alaman ehh, yay rubuce rubuvensa ya dubi Yaya Haidar yace ga wannan, ni dai tunda naji batun test hankalina ya tashi, dan naƙi jinin allura, tuni na fara kuka a hankali, na ruƙo hannunsa na damƙe ina roƙonsa, yay banza da ni kamar bada shi nake ba. test har uku haka likitan ya rubuta, ya miƙo masa takardar ya amsa, ya kalle ni fuska a haɗe kamar hadari yace,"tashi muje". na miƙe har lokacin ina riƙe da hannunsa har muka isa lab ɗin, suka masa bayanin wurin biyan kuɗin, yace dani na zauna anan na jira shi, bai jima ba ya dawo da reciept hannunsa, ya miƙawa mutumin, nan yace na taso dan ma a hakan ya roƙi alfarma ne amma da mutane da yawa kan layin. muryana a dashe nace,"dan Allah Yaya Haidar kar a min allura wallahi bana so, ka tambayi Gwaggo kaji ba'a min allura magani nake sha". yay min wani kallo yace,"to ni Gwaggo ne, dilla Malama tsaya kiyi abinda aka ce miki". na runtse ido kawai nayi surrender, Nurse ɗin yace dani na ɗaga hannun rigata, ina jinsa nai masa banza dan har shi nake jin haushi, Yaya Haidar yaja tsaki ya kama hannuna ya yaye hannun rigar tawa, sai dai lokaci ɗaya yaji tausayinta ya kama shi yanda yaji jikinta yayi zafi rau. yay ƙasa da Murya ya kira sunana, na amsa da umm, yace,"kiyi haƙuri ki daure ba za'a miki da zafi ba". ina sheƙar kuka nace ni fa ko da zafi ko babu bana so a ɓula min jikina. shiru yay ya jawo kujerar da yake zaune kusa da ni, ya kwantar da kaina saman cikinsa, a hankali yaji zafin jikinta yana ratsa kayansa ya shiga jikinsa, ya rumtse ido ya furta"Ya Salam, dama haka jikinki yay wannan zafin shine za kice wani ba za'a maki allura ba". ina jinsa ni dai bance masa komai ba, Mutumin ya kama hannuna ya tsira min allurar da har ta sa ni zillo ina sakin ihu. "dalla can tsaya".yace dani murya a ɗage. na maida kaina jikinsa ina sheƙar kuka. _wannan zafin jikin is worst, to me ya sameta haka?_ ya yiwa kansa tambayar da bashi da mai bashi amsa sai likita. haka aka kuma yin sauran test aka gama duk ban motsa ba, sai bayan da aka gama yaga ashe ma nayi bacci, kamar ya zareni daga jikinsa sai ya yatsinci kansa da kasa aikata hakan, dan haka da sanyin jiki ya gyara mata kwanciyar kanta, ya zauna jiran amsar result ɗin test ɗin.
yana zaman jira sai ga wani abokinsa ya kawo matarsa shima, sun jima basu haɗu ba nan suka shiga musabaha, matarsa ma ta gaida Haidar kafin ta nemi wuri ta zauna itama. "a'a kace kaima Madam ka kawo". cewar Mustapha dake kallon Haidar. Yay masa wani kallo yace,"who told you she is my beb, rigimammiyar ƙanwata ce na kawo babu lafiya. kasan ranon Kaka sai a hankali". "ehh gaskiya kam, rainon Kaka ai akwai rigima". suna hira nurse ya kawowa Haidar result ɗin, ya shiga tashinta a hankali har ta buɗe idon, ni kaina nai mamaki dan ba ƙaramin bacci nayi ba, yana riƙe da hannuna muka koma office ɗin wancan likitan, ya amsa result ɗin yay masa bayanin typhoid da maleria suka haɗar min, nan ya rubuta mana magunguna muka fito muka wuce pharmacy, ni dai duk na gaji da tafiyar hakan yasa naja na tsaya ina hutawa, sai da yayi gaba ya juyo ya ganni na jingina da bango. "mene kuma?". "Allah Yaya Haidar na gaji da tafiyan, kamar zan faɗi nake ji". tsaki yaja ya harare ni kamin ya dawo ya kama hannuna ya kaini mota yace na jira dawowansa. ya jima kamin ya dawo, a hanya ya tambayeni ko da abinda nake son ci, ina kallonsa nace,"Pure bliss wafer da choculate". sai kawai yay min kallo mai kama da harara ya ɗauke tare da cewar,"ba zan saya ba". har muka iso gida kuma bai kuma ce min komai ba, yau dai ƴan mutunci yake ji dasu dan sai nan da nan yake dani, yanzu ma daya ga zan faɗi kamani yay ya jingina ni da jikinsa. muna shiga parlo yace na nemi wuri na zauna, zan kwanta yace,"karki sake ki kwanta". na langaɓar da kai ina yamutsa fuska yace,"ke abu kaɗan kuka ko gajiyaba kya yi, mtsww". yaja tsaki ya wuce friedge, roban faro ya ɗauko ya buɗe ya haɗa min ɗaya daga cikin maganin da akace da mun dawo na sha. ya haɗa ya miƙo min yace nasha, ban samu fuskar gaddama ba na amsa na sha, Iklima tazo tana min sannu. nace ma ta ina Gwaggo tace taje wajen Anty. na tashi zan tafi wajenta naji muryarsa yana dawo ki zauna, na koma na zauna ina kumbura fuska. "kalla yanda kika bi kika wani rame". yana maganar yana hararata, ni dai na tashi na bar masa wurin nai wucewata ɗaki dan ban shiryawa bala'insa ba. ban fito ba sai dana jiyo muryan Gwaggo, na sameta ta riƙe ledar magungunan da ya bata tana ta masa godiya tana faɗi,"ai kaf cikin jikokina babu mai halin kirki irinka Haidar, shi yasa kake burgeni a ko da yaushe, yanzu ka duba waɗancan yaran, daga zagalon har lagwanin duk cikin kwanakin nan babu wanda yay tunanin kaita asibiti, kai dai Allah yayi maka albarka yasa ka gama da duniya lafiya". "ameen". yace da ita. Yaya Abba kuwa yace,"daga baya kenan". ta harare shi bata ce masa komai ba. Haidar yace ma ta,"idan da gaske kina son ta samu sauƙi da wuri saiki sa ta dinƙa shan magani, idan kuma kin biye ma ta sai kiyi ta zaman jinya". "insha'Allahu Haidar". ni ko alluran da aka mani har naji daɗin jikina sosai, har na ɗau wayana na kunna data muka hau hira da ƴan school namu ina tambayansu game da lectures. har yamma Yaya bai dawo ba, na ɗau waya na kira shi ina tambayansa Pure bliss dan Gwaggo ta hana a siyo min wai na fiya cin zaƙi. ina jinsa ya sa ki murmushi yace,"go slow ne yay tsaida ni amma saura ƙiris na ƙaraso, ki haƙuri Cutien Yaya". kamar ina gabansa nayi knooding kaina nace,"Allah ya dawo da kai lafiya". yace, "amin Cutie nah".

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login