Showing 3001 words to 6000 words out of 89788 words

Chapter 2 - ALHUSSAIN Complete Hausa Novel

23 Aug 2025

377

ta ke, ta kama kaina tayi min adu'a, sannan ina jinta ta miƙe tana surfa zagi da bala'i ga bawan Allah'n dana san bashi da hannu a wannan halin dana shiga. ta dage akan sai ya faɗa ma ta abunda yayi min ko kuma ta kira masa ƴan sanda yanzun nan, shi dai bai saurareta ba dan banji yayi ma ta magana ba...kuma haka ta ƙyale shi ta dawo kaina duk a ruɗe tana ƙara faɗa masa wallahi komai ya sameni sai inda ƙarfin shari'arsu ya ƙare ita da shi, dan ba zata ƙyale shi ba.
da ace tasan irin azabar da nake ji acikin kaina, da kuma hoton dake haskawa cikin duhun idona, da bata tsaya tana wannan jarabar ba, kamani kawai zata yi mu tafi gida a sama min lafiyar ciwon da nake ji. "na banu ni Farhana, ban san me kika shigo yi wajen nan ba, yanzu duba matsalar da kika jawa kanki...yanzu me zan faɗawa Gwaggo". kuka ta ke yi sosai a sa'ilin, kuma har ga Allah maganartata na ƙara ƙarfin iskar guguwar dake wucewa ta kacikin ƙoƙon kaina ne. sai dai cikin lokacin da ba zai haura sakanni takwas ba na manta da halin da nake ciki da duk wani abu da naji yana damuna, hatta hanzarin miƙewar da nayi ban san nayi ba dalilin jin Farhana tana cewa da shi. "ina zaka je? ina zaka tafi? kasan Allah ka ƙara ɗaga ƙafarka daga nan saina yi maka ihu, kazo ka sakar min ƴar'uwa dan nasan koma menene kaine sila". duk da cewar ba sosai nake gani ba, amma a taku biyu na cimma inda yake tsaye, kuma ban manta da wannan kama hannun nasa da nayi ba gudun kar ya tafi ya kai kansa wajen da zaici gaba da cutuwa, hakan zuciyata ke ce min, "barinsa nan wurin zai kai kansa ne inda yafi nan muni". shi yasa komai zai ƙara faruwa dani ba zan sakesa ba, ko da ace zan dawwama anan babu tafiya. amma ga wani maɗaukakin mamakin da al'ajabi, damƙar hannunsa da nai sai kawai naji komai na washewa, ciwon yana tafiya, komai na janyewa, kuma a hankali komai ya tsaya cak, kamin ya tafi gaba ɗaya. sai naji ni nayi sanyi ƙalau, haka kuma wani abu da ban san menene ba na tsargawa a jikina. na buɗe ido ina dubansa, yana nan dai tsaye a wurin, kenan tun a ɗazun bai motsa ba, sai dai wannan karan hannayensa duka biyun na zuɓe ne cikin aljihun wandonsa. sai kawai na ƙara kamo hannun nasa a haka naci gaba da jansa,kuma a yanzu bai min gardama ba, bai yi yunƙurin ƙwacewa ba, kawai bina yake kaman yaron dake bin uwarsa. ni kuwa ƙara saurin tafiyarmu nake dan mu bar cikin bolar da wuri, saboda zuciyata faɗa min kawai ta ke karki tafi ki barshi nan, sai dai komai zai faru ya faru dake. gaba ɗaya na manta ma da wata Farhana sai dana jiyota tana faɗin, "Allah kayi min maganin abunda ke neman yafi ƙarfina...yanzu da kike janshi ina za ki da shi?". ba tare dana tsaya daga tafiyar ba ko kuma na juyo nace da ita. "tare zamu tafi. bana son zamansa anan". "Allah uwar da ta haife shi". sai kuma ta ƙara da cewa,"amma dai kinyi hauka ko Sabina? ba ki san mutum ba, ba ki san shi ɗin ko aljani ne ba, ko kuma macuci kawai dan ɗebarwa kai masifa da nemarwa kai jaraba shine kika wani kama zuwa inda yake harda ƙarfin halin riƙo hannunsa za ki tafi da shi, to ki kai shi gidan uban wa uwar masu son taimako ta duniya...yanzu wannan ɗan wiwin har ina dalilin da za'a taimake shi". "kenan Farhana kawai idan mutum ya tsinci kansa a irin wannan halin sai aƙi danganta hakan da jarabawar rayuwa? saboda hakan kuma sai aƙi taimakon mutum?". na faɗa ina tsareta da ido a sanda na tsaya da tafiyar. "oho ni bance haka ba amma wannan dai ai baiyi kama da wanda za'ace ƙaddara ce tasa shi shiga wannan yanayin ba...dan haka kawai ki sake shi mu tafi, karki so ki tona zuciyata kiga takaicin da ke ciki". "ohhh Farhana ki fahimce ni mana, duk abinda zaka yi kayi shi don Allah kuma zuciya a tsarkake, wataran baka san ta inda za'a taimake ka ba kaima. Nifa kawai na tausaya masa ne, naga kuma bai dace muna ganin halin da yake ciki ba mu tafi mu barshi a haka. Yanzu tafiya zamu yi da shi sai mu sauke shi a gidansu". ta galla min harara tana faɗin,"mtswww ƴan wiwi nawa ki kai arba da su ba ki taɓa yunƙurin taimaka musu ba sai akan wannan mahaukacin". kuma furucinta na ƙarshe ya tsaida ƙafafuna, na rufe ido kaɗan sannan na buɗe, magana nake so na yaɓa ma ta, amma ba zan iya ba, bata cancanci hakan daga gareni ba, kuma hakan ba halina ba ne sam. sai kawai na kaɗa kai da cewar,"su sauran basu yi kama da waɗanda suke biɗar a taimaki rayuwarsu ba ne shiyasa kika kalla banyi hakan ba. shi kuwa sai dai idan idon mara imani ne ya sauka akansa, amma a hoton fuskarsa na farko daka kalla zaka shaida ɗan adam ne da yake cikin wata jarabawar rayuwa, ki kalla ƙwayar idonsa da kyau ki gani, ita kaɗai me shaida miki halin ƙuncin da yake ciki ne, balle shi yanda ba ki ɗaya abunda ke zuciyarsa ya bayyana a saman fuskarsa...Farhana ko kaffara ba zanyi miki ba mutumin nan yana da ciwo a tare da shi, wannan ciwon na damuwa da yake roƙon Allah dare da rana ya magance mishi, kuma wataƙila Allah ya sakoni cikin rayuwarsa dan na zama sila...shi yasa ko dana ganshi naji ba zan iya yin yanda kike so ba...so please lets go, i beg you". ganinta nai kawai ta wuce ta gabanmu bakinta na faɗin,"tabɗijam, ko duniya za'a tasa tafiya da wannan ɗan wiwin ba'a motata ba, don babu abinda zai sanya ni yayibar mahaukaci na kama tafiya da shi, ai yasan da gidan nasu yazo ya zauna anan....mtswww ke da kin kalla ma fa kinga alamun rashin lafiya a tare da shi, saboda haka kinga tafiyata". "kece ki ke masa kallon mara lafiya amma ƙalau ya ke kamar yanda muke". "a'a ba dai kamar ni ba kam, me lafiya dai ba zai zo kusa da bola ya zauna ba har yana shan sigari. Ai da gani kin san waye, cikin biyun dole ɗaya, mahaukaci ko kuma riƙaƙƙen ɗan daba, ki sake kallonsa da nazari tukunna ki dube yanayinsa da idon fahimta". ta ƙarasa faɗa tana nuna shi da baki a yatsine. Kallon Farhana kawai yake yana ganin yanda ta ke banka masa wata uwar harara. na san yaji rashin daɗin abinda tace, amma gani nake kamar nafi shi rashin jin daɗin hakan.
"haba don Allah Farhana, ya za ki dinga aibata ɗan'uwanki musulmi da irin waɗannan kalmomi marasa daɗi, bayan ba ki da masaniyar komai a kansa. Ki tuna fa addininmu ya yi hani da tozarta musulmi". "hmmm! lallai har yanzu ba ki da wayo Sabina, kuma indai za ki ci gaba da biyewa wannan zuciyar taki zata kaiki ta baroki akan saurin taimako da kuma tausayi. kuma ina mai gaya miki tun wuri ki bar wannan ɗan shaye-shayen kizo mu tafi, don wallahi irinsu ne tantiran ƴan iskan nan masu lalata ƴaƴan mutane, waɗanda bakin uwa ya gama binsu". maganarta ta ƙarshe tai wani dukan ganga a zuciyar Alhussain, dan haka yay saurin rumtse ido da gaggawa ko ya sami sassaucin raɗadin da maganarta ta haifar masa. yau rana ɗaya kuma rana ta farko da aka taɓa faɗa masa kalma mafi muni da ɗaci a rayuwarsa. lalata! bakin uwa!, to shi da bai taɓa ma yin gaba da gaba da wata ƴa mace ba ta ina zai lalatata? wama ke raɓarsa daga maza har Mata? Babu! Shi ɗaya ne a rayuwarsa, kuma bashi da iyaye balle yace yana da uwar da bakinta yabi shi...amma sai gashi yau har ana kiransa da ɗan daba, zai iya rantsewa a iya tsayin rayuwarsa baya tunanin ya taɓa riƙe wuƙa ko makami, yaji yana shan wiwi amma baya taɓa ɗarawa daga kanta, itan ma dan ya kanji sauƙi ne idan yasha...sai gashi yau ƙanƙanuwar yarinya na gaya masa son ranta ba tare da ta san shi ɗin waye ba kamar yanda shima bai san kowaye ba. ƙwayar idonsa tai masa nauyi kamar an baɗa masa ƙasa a ciki, buɗe su yayi da matsananciyar damuwa gami da ɓacin rai, bai da ikon yi ma ta komai saboda ya cancanci a faɗa masa dukkan wasu kalmomi masu muni. idonsa yana bin Farhana da kallo da saƙa wasu abubuwa cikin ransa, yana jin tsakin da ta ke taja acikin kansa.
sai ya cire hannunsa daga nawa, na dube shi da rashin jin daɗin abinda Farhana tai, tausayinsa naji ya daɗa kamani, ko da wannan ɗaga ƙafar kaɗai da yayi mata zan iya shaida na rantse yana cikin wannan halinne kawai dan bashi da yanda iya, amma ba da son ransa ba. Muryarta a sanyaye nace da shi, "don Allah Yaya kayi haƙuri da abinda ƙawata tayi maka, rashin fahimta ne ya janyo hakan, amma a madadinta ina mai baka haƙuri, na san kowane aka yi masa ba zai ji daɗi ba, karda ka sanya ɓacin ran hakan a ranka ya kuma haddasa maka damuwa". sai kawai naji ya buɗi baki yana cewa, "kema kar da ki damu, dama na shirya fuskantar wannan ƙalubalen, irin wannan kalaman ba zasu dameni ba, ko da finsu ne ma ba zanji ciwo ba...da sannu kema za ki faɗa min su ne, wataƙila yanzu, wataƙila zuwa wani lokaci". "Allah ya kiyaye bana fatan hakan ko da ba akanka ba". sautin muryarsa ya washe da ce min, "ke kam wai ba kya da tsoro ne?". Ya faɗa murya da ɗan ƙarfi. sai nace, "Allah shine abin tsoro ai, kuma kai ɗin ai ba kayi kama da mugu ba da har zan tsorata da kai. Yanzu dai kazo mu tafi kaga magriba na gabatowa kuma Gwaggo nah zata mani faɗan ban dawo da wuri ba". "baki sanni ba, baki san wane ni ba amma kina nema na raɓe ki, nace miki bani da gida, anan wurin nake rayuwa ta. Shin wai baki gudun na cutar dake ne ke kam?". na marairaice idanuwa ina dubansa da rashin jin daɗi nace, "Annabi S.W.A yace *KAMATUDINI TUDAN* (duk abunda kayi sai anyi maka). kai ɗin kana da Mama, kana da Ƙanwa, ƙilan ma kana da Yaya mace, nan gaba zaka auri mace, kuma ta iya yiwuwa ka haifi ƴa mace. Kaga kuwa nayi amanna da cewar ba zaka cutar dani ba saboda ba zaka so wani ya cutar da naka ba". sai yaja dogon numfashi ya sauke sannan yace min, "ki dinga kiyayewa. Yanzu kibi bayanta ku tafi gida, kar Gwaggo'n ki tayi miki faɗa". maganarsa ta haddasa jikina yin sanyi, naji raina fayau, nai ƙasa da idona ina kallon yatsun ƙafata nace,"to idan na tafi kai fa?". "so nake ki yarda dani, bana magana balle har ta kai ga nayi ƙarya. inda kika ganni anan nake rayuwata tsayin shekarun dana faɗa miki, idan har nabi ki bani da wani gida da zan nuna miki nace ina da alaƙa da shi. don haka ki tafi kawai ki ƙyaleni". "to amma kayi alƙawari idan na tafi na barka ba zaka kuma shan wannan abar me cutarwa ba?". sai ya rufe ido ya ɗan kauda kai gefe, ba zata taɓa fahimtarsa ba, ba zata taɓa ganewa ba. "akan mene zan ɗauki alƙawarin da bazan iya cika shi ba? Kawai ni dai ki tafi kuma karki kuma dawowa inda nake". "kana nufin ba zaka iya daina shanta ba kenan? Na faɗa maka fa shanta haramune, ko ka fi so ka aikata abunda Allah ya haramta?". idonsa a kulle ya shiga girgiza min kansa alaman A'a. "to in dai haka ne, don Allah kar ka kuma shanta daga yanzun nan. Kaga shi yasa ma mutane ke maka kallon ɗan iska, kuma alhalin kai ɗin ba shi bane. Wannan ba zata yi maka maganin damuwa ba sai dai ta cutar da kai, ka miƙa lamuranka ga ubangiji sai kaga ya yaye maka damuwar dake tare da kai. Ƙilan mu kuma haɗuwa ƙilan ba zamu kuma haɗuwa ba, amma ina roƙonka da Allah karka kuma shan taba, ka nisance ta nisa na har abada kaji Yaya". kawai sai na kalla ya runtse ido yana jijjiga min kansa alaman yaji kuma zaiyi yanda nace. har cikin raina sai naji daɗi, na saki Murmushi kana nace masa, "na gode Yaya nah. Kuma ka sani idan ni bana ganinka Allah yana kallonka, dan haka ka riƙe alƙawarin daka ɗauka...alƙawari yana da girma, kayana ne karka manta da wannan". na juya cikin rashin kuzarin jiki na barshi a tsaye, yayin da nake jin kallonsa da yake bina da shi ajikina, kuma har sanda na shiga mota na zauna idonsa na kaina, zuwa lokacin da Farhana ta yiwa motar key sannan naga ya juya ya koma inda muka fito.
kuma tun bayan zaman Alhussain da kuma bayan tafiyar Sabina, tunaninsa guda ɗaya ne yake yi, _dama akwai ranar da zata zo wani ya kusance shi da nuna kulawa gami da tausayawa irin haka? Dama a cikin Mata akwai masu uzuri da kirki irin haka?_
tambayoyin da yay ma kansa kenan, a yayin da hoton Sabina ke haska mishi a ido da amsar tambayar tasa. ta kasance a tare da shi alhalin bata san shi ba, bata san waye shi ba, ba zagi, babu ƙyama, babu walaƙanci, babu tozarci, sai ƙoƙarin janyo shi a jikinta domin ta nuna masa illar halin daya jefa kansa ciki, halin daya na zaune acikinsa ne ta dole bisa ƙaddara. ayau kuma sanadinta yaji yana bala'in son kasancewa da ahalinsa, ya gansu ko da ace ba zasu kalle shi ba, ko da ba zasu karɓe shi ba, ko da zasu wulaƙanta shi. Wani abu mai zafin gaske yaji ya taɓa zuciyarsa, *SHIN WANENE SHI?*, *SU WAYE IYAYESA?*, *MENE SILAR KASANCEWARSA A WANNAN HALIN*, *YAUSHE ZAI FITA DAGA WANNAN ƘANGIN RAYUWAR?*, *HAR TSAWON WANNE LOKACI ZA'A ƊAUKA KAMIN ƘADDARARSA TA SAUYA FUSKA?*... sai yaji zuciyarsa ta matse sosai, ta yi rauni, ya dafe goshinsa ya kuma runtse idonsa da ƙarfin gaske, ya cije leɓensa na ƙasa hawaye masu zafin gaske suka shiga malala a fuskarsa, sai kuma ya fashe da kuka mai ƙarfi tare da kifa kansa a saman cinyarsa yana riƙe da kansa dake mugun sara mishi tamkar zai bar jikinsa. wannan yanayin, wani yanayi ne da yake tsintar kansa a duk sanda ya rasa amsar waɗan can tambayoyin, ya ɗau tsawon lokaci a haka cikin rera wannan kukan mai ƙaramin sauti tamkar ba matashin saurayi ba, tukunna ya miƙe ya tafi masallaci dalilin kiran sallar daya ji ana yi, bai baro cikin masallaci ba har sai da akayi sallar isha'i kana, nan ma sai da za'a rufe masallacin sannan ya fito. A dawowarsa ya tsaya a dai-dai inda motar su Sabina tayi parking ɗazu, kallon wajen yake da haskawar hoton abunda ya faru a ɗazu, bai san dalili ba, amma haka kawai yaji yana so yarinyar ta ƙara kasancewa da shi. sai yasa hannu ya matse idanunsa dake rufe, ƙasan zuciyarsa na raya masa da cewar _ko zata sake dawowa?._


*Please don't forget to comment, vote and share.*
*AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(3)*
da wannan tunanin ya samu wuri ya zauna, zuciyarsa tana cigaba da tunani iri-iri, tunanin duniya, tunanin rayuwarsa da tunanin yarinyar da ta fara raɓarsa tun bayan sanin kansa da yay. motar Farhana na tsayawa ban ce komai ba na buɗe murfin motar na fita cikin fushi ba tare da ko na dubi inda Farhana ta ke ba, can ƙasan murya na furta,"nagode ki gaida su  Hajiya". tace da ni,"zasu ji insha'Allah, amma ba ki ɗauka kayan da muka saya ba”. wani irin kallo na bita da shi ta ƙasan ido, ban ko yunƙurin amsa ma ta ba, dan abunda tayiwa wancan bawan Allah'n ji nake tamkar Yaya Abba da muke ciki guda ta yiwa, shi yasa tun tahowarmu nake fushi da ita, kuma ina ganin kaman ba zamu shirya ba har sai mun koma wajensa ta bashi haƙuri yace ya haƙura tukunna.
ban rufe ma ta ƙofa ba sai dana ja tsaki tukunna na fara tafiya na ɗauka hanyar gida, ganin hakan yasa Farhana fitowa daga motar ta buɗe boot ta ɗauko kayan da muka saya ta biyo bayana da shi. A ɗan ƙaramin tsakar gidanmu wanda yasha shara baka ganin ko da ɗigon datti, na tarar da Gwaggo tana goga kuɓewa, sallama kawai nayi na shige ciki, ban ma san ta amsa ba ko bata amsa ba, kuma ajikina nake jin yanda Gwaggo ke bin bayana da kallo, kuma shirunta ya bani tabbacin tana tunanin yanayin da ta ganni aciki ne. Farhana ta shigo, Gwaggo ko amsa sallamarta ba tai ba tace mata,“yauwa yanzu kuwa zance to ya akayi baki shigo ba, ashe kina bayanta, meye sa me ta ne? naga daga sallama ta shige ciki, Allah yasa lafiya ne". Farhana tace, “lafiyarta lau, ai kin san halinta da ɗan banzan saka damuwa a rai, wai fa wani mahaukaci ta gani a hanyarmu ta dawowa gida shi ne ta ɗaga hankalinta haka". ta duƙa a gaban Gwaggo ta aje ledar hannunta da cewa,"ni dai zan wuce Gwaggo sai wani lokacin, ga shi wannan nata ne”. Gwaggo ta maida hankalinta kan kuɓewar da ta ke gogawa tace, “to madalla, kyace ina gaida Hajiyarku”. Daga haka Farhana ta gyara zaman glass nata ta fice. Maganar Farhana ta tsayawa Gwaggo a rai, don kuwa sarai ta san halin Sabina, zata iya yin komi akan wannan mahaukaci kamar yadda Farhana ta faɗa mata, to amma meye nata na damuwa haka, koma meye dai zata ji. ina kishingiɗe jikin pillow naji Gwaggo na Ƙwala min kira, kaman ba zan amsa ba sai kuma na buɗe ba ki nace da ita ina zuwa, na miƙe jiki babu ƙwari kamar mara lafiya na fito. na rakuɓe

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login