Showing 30001 words to 33000 words out of 89788 words
murna sosai, na tambayeta yaushe zata zo suga gidanmu tace sai anyi hutun islamiya, nace ma ta Allah ya kaimu, har na bata labarin nima an samo min addimission, tai min congratulations tare da bada shawarwari saboda karatun Uni ba ɗaya yake dana Secondry ba. tun fara wayarmu so nake na tambayeta Yayana amma gudun kar ran junanmu ya ɓaci na haƙura, mu kai sallama na kashe wayar raina ba daɗi. ina ƙarasawo parking lot gabana naji ya faɗi, ƴaƴan cikina naji sun kaɗa har jakar hannuna ta kusa faɗuwa ƙasa, na kuma yin ƙasa da kaina ina takawa kamar bana son tafiyar, don ina ƙwaƙwƙwarar tafiya zan kifa ƙasa, gaba ɗaya a tsorace nake da Yaya Haidar wanda tunda na taho idonsa ke kaina, fuskar nan tasa a haɗe kamar hadarin gabas ya taso, sai wurgan wani mugun kallo yake. Ni dai har na iso inda yake tsaye jingine a jikin mota ƙirjina bai bar duka ba, tsorona da fargabana kar dai ace da shi zamu fita yau. sam shi mutum ne mara daɗin sha'ani, miskilanci da masifa su kaɗai yasa a gaba, kuma tunda yazo gidan ya hanamu sakewa, Amina ce ma take iyawa da shi saboda mara kunya ce ta ƙarshen gaske. ni kam da magana ma bata isheni ba, sai dai yay min son ransa, shi yasa duk na ƙagu ya koma gidansu. kuma tsawar daya doka min ita tai sanadiyar gurɗewar ƙafata. "kin bar mutane tsaye kamar aikinki suke kina biyansu, za ki ɗago ƙafa ko kuwa nima sai nayi tafiyata". A ruɗe nace, "Yaya Haidar to ina Yaya Abban?". bai bani amsa ba ya wurgan harara ya zaga ya buɗe gaban mota ya shige, dana tashi nima na buɗe baya na shiga. ta cikin madubi ya jefo min harara yace, "who is your driver?". Na haɗe fuska ina shirin fashewa da kuka, muryata a sanyaye nace, "Ohh Yaya Haidar then where should i stay? ". "dilla Malama fito ki dawo gaba, sai anyi magana ki nemi ki ɓarewa mutane baki, ki jawa mutane masifa a wurin waccan tsohuwar da bakinta bai gajiya da magana. a'a ke gaki ƴar gwal ba'a isa an taɓa ki ba. Kamar akan ki ne aka fara yin mutuwar uwa". matsalar ɗaya ni ban iya rashin kunya ba, furucinsa na ƙarshe shi yay sanadin taruwar ruwa a idona, na fito na dawo gaba na zauna, ko ƙarasa rufe kofan banyi ba ya figi motar kamar wanda zai tashi sama. kuma tsoratar da nayi ya haɗe da sakkowar hawayena, shi ko a jikinsa ma dan ba lallai ne ma idan ace na faɗa waje ya lura ba. har muka hau titi ban bar kuka ba don sosai maganarsa ta bani haushi, idan shi bai damu da tashi mutuwar uwar ba aini na damu da tawa, sam Yaya Haidar baiyi halin Uncle Sulaiman ba don ba haka Babansa yake ba. Shi ko tausayi ban bashi ba, saima tsaki daya dinƙa ja yana shafo sumar kai har muka isa wurin koyan motar, hakan ya ƙara bani haushi, saboda ni fa ina takaicin naga ina kuka aƙi lallashina, nafi so ko ya na fashe to a karkato da hankali kaina, ta irin haka ne ma muke faɗa da Gwaggo wataran, idan na bata haushi sai tayi biris da ni. Ni dai yau nayi dana sanin fitowa koyar motar nan, gaba ɗaya ma naji koyon ya fice min a rai, kullum da murna nake fitowa nake komawa indai da Yaya Abba ne, kuma muna wasa da dariya yake koya min, amma yau tsabar tsoron Yaya Haidar koyan kwanar da na kasa yi sama da sati biyu sai gashi cikin rabin awa na iya, mu kanyi awa biyu zuwa uku idan muka zo amma yau ko ɗaya bamu cika ba naji yace tafiya zamuyi shi ya gaji. muna ɗaukan hanya na ɗago na dube shi, murya a ɗarɗace nace, "Yaya Haidar ai bada wuri fa muke komawa ba, Baba yace Yaya Abba yake tsawa ya tabbatar da na iya sosai kamin mu koma". Farko banza yayi min, sai can naga yayi wani miskilin murmushi yayi revers, a bakin filin wurin yay parking, kansa na gaba kamar bada ni yake ba yace, "buɗe ki fita". nai sororo ina kallonsa. ya ƙara ɗaga murya wanda na tabbata har na waje sunji. "nace ki buɗe ki fita. in yaso ki sami wani ya koya miki sai ki biya shi, ko kuma ki kira shi Abba'n ya koya miki shi daya ga zai iya aikin wahala amma ni ba kalata bace sanya daƙiƙiya a gaba ina koya mata abu tana kasawa". "Amma tsakani da Allah Yaya Hydar ai kasan koyon driving ɗin nan da wahala, kuma ma yau ai nayi ƙoƙari dai, gashi kai baka encouraging ɗin mutum, sai dai kai ta faɗa. kuma fa ni ba daƙiƙiya bace Allah, saboda ina da ƙoƙari akan komai, kaje makarantarmu ma ka tambaya, har na gama first class nake ɗauka". Na faɗi hakan ina turo baki gaba, na san wannan ƴar maganar da nayi ba zai barni ba, ile kuwa ina rufe baki ya ɗalle min laɓɓana da yatsansa wanda sai daya sani yin ƙara ina sosa wurin. "karki yi min rashin kunya saboda ni ba Abba bane, tun kamin a haifeki nazo duniya, sai da nayi shekara ɗaya-ɗaya har 13 kana aka haifeki a tsumma, kashinki da tunbuɗinki babu kalar ƙazantar da ban gani ba, saboda haka ki iya bakinki wajen yimin magana, ni ba sa'anki bane". Haushi ya tuƙeni hakan yasa na shiga ƙunƙuni. ina jinsa yana faɗin, "banda kinci darajan Baba daya ce na kawoki, kuma motar ba ta gidan mu bace, ai da sai kin fita in yaso ki daɓa a ƙafa ki koma gida...mara kunya fitsararriya ana magana kina tura baki gaba kamar shantu, ke ai gaki goyon Kaka goyon gata, to ba gata wannan tsohuwar ke nuna miki ba, dan a nan gaba wuya za ki sha da wannan halin naki". Ni dai bance masa komai ba har muka iso gida, bare ya kuma gaya min no sugar, na cika nayi fam saboda haushi, Allah ko da kuɗi, kai ko shi ɗaya ne mai koyar da mota a duniya ba zan ƙara binsa mu fita ba sai dai har na mutu kuwa ban iya motar ba. Yana yin parking na buɗe na fice, Ina ji yana min magana nayi masa banza kome ma yake cewa oho, ɗakina na wuce kai tsaye na kifa kan gado ina kuka, to fa dama da biyu kukan nan nawa, tun jiya kewan Yayana ya isheni, ga shi yau kuma wannan matsolon raken ya ɓatan rai. Ina kwance ina faman shashsheƙar kuka Gwaggo tayo sallama, ina jinta ta buɗe wadrobe ta zuba kaya ta mayar ta rufe, kana ta karkato kaina tana faɗin. "ke kuma yaushe kika dawo? Me akayi miki kike kuka? Me Abban yayi miki? Ko kuma shigowarki wata a cikin gidan nan tai miki hali na rashin kyautawa?". Duk a jere ta jefa min tambayoyin, na miƙe zaune ina goge hawayena ban dai ce ma ta komai ba, ƙaramar wayata dake gefena kawai nake kallo naga ko kira mai sabuwar numba zai shigo, don a kullum bana yanke tsammani da kiran Yayana. ta kama ƙugu tana faɗin,"yau naga sarautar Allah". "keee to ko kin gamu da ciwon baki ne da kika gagara bani amsa? Ina daɗa tambayarki me Abba yayi miki? Za ki bani amsa ko sai na ƙwala miki wannan murfin tasar". Sanin zata aikata yasa da sauri na buɗe baki nace, "ba Yaya Abba bane, Yaya Haidar ne". "Haidar dai! shi Haidar ɗin da yake baƙo ya ɓata miki rai? To me ya haɗa ku? Ki faɗan gaskiya ke dai ban sanki da rashin kunya ba". ina goge ƙwalla nace, "ni fa ba abinda nayi masa, tunda na fita yake tayi min masifa har muka je muka dawo, har cemin yake wai kinyi min goyon lalacewa, banda taɓara babu abinda na iya, da anyi min abu dana fashe da kuka sai kace a kaina aka fara mutuwar uwa". sai ta shaki ƙugu ta kama haɓa. "shi Haidar ɗin ne ya faɗa miki haka?". na ɗaga kaina, "ehh mana. Ni dai daga yau bazan ƙara binsa ba in dai shine zai koya min mota, acan ma harda ce min daƙiƙiya, ya bige min baki saboda na faɗa mishi gaskiya ni ba daƙiƙiya bace, Gwaggo har muka je muka dawo fa ba abinda na iya wai shi ai ba bawa bane, hakan ma daya fito dani darajar Baba naci". ta shiga tafa hannaye tana faɗin,"iko sai lillahi, duk shi Haidar ɗin yayi miki wannan rashin kyautawar yaci zarafinki da yawa haka?". "Allah Gwaggo ba zan ƙara binsa ba, ki faɗawa Baba indai Yaya Abba bayanan na haƙura". ta dire farantin dake hannunta, tana gyara ɗaurin zane tace, "yo dama ai ba za'a kuma na biyu ba, anyi na farko anyi na ƙarshe. yo ni kuwa ina dole irin wannan cin mutunci har haka, idan kuka ci gaba da fita tare waya san irin cin kashin da zai yi miki agaba, daga ke sai shi sai Allah'n daya ke kallonku. gashi ke ba ki iya halin rashin kirki ba bare ki rama. Saboda haka kwantar da hankalinki, ki sha re hawayenki haka kar ya rainaki, ni nasan yanda zanyi da shi, kuma idan shi gyatumin naki ya dawo ki sa me shi ki faɗa masa...ina dalili wannan ɗibar albarka har ina". Na kuma turɓune fuska ina fizgar numfashi, ta matso kusa ta cire ɗan kwanlinta ta gogen hawaye tana lallashina. "ki kwanta ki rama baccin safiyar da Abba ya azalzale ki, kamin anjima muje wurin bayerabiyar nan ta wanke miki kai, domin ba zan iya da wannan ƙazantar gashin naki ba, haka kawai muna zaune ƙalau ki jajuɓo mana abinda yafi ƙarfinmu, kwarkwarta ta shafeki. na rasa inda zan saka kaina, nan dai ba tsohon gida bane bare nasa miki omo, yafi nai ta kaiki inji suna dirje shi yanda ya kamata, tunda ba ƙaunar kitso kike ba". ni dai duk ba wannan zancen nake son ji ba, so nake ta fusata ta tafi wurin Yaya Haidar kai tsaye, ita da shi hali ɗaya ne, ya kaishi bango ya fusata ya kwashi kayansa ya tafi shine kawai abinda nake so. sai na shiga rera kuka a hankali, hakan kuma yasa ta hauni da banbami tana faɗin tunda dai na faɗa ma ta ba shikenan ba, na zuba ido kawai naga abunda zata yi, ai nasan bata barin ta kwana akaina.
na goge hawaye na Kwanta, Gwaggo ta gyara min abinda zata gyaran a ɗakin...har ta gama idona na kanta, godiya nake ga Allah daya bani Kaka kamar Gwaggo tunda ta fita nai luff jikin pillow na tafi duniyar tunanin Yayana da nake matuƙar kewarsa. Gwaggo na fitowa ta sami Haidar zaune kan kujera a parlo, ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya akan centre table, hannunsa riƙe da cup yana kurɓan lemu yana kallon tv yana ssuraron labarai. bata ko bi ta kansa ba saboda tana jin haushinsa ta wuce ɗakinta. ta ɗau tsawon mintuna a ɗakinta yana nan, kuma har ta shiga kitchen ta gama abinda zata yi ta fito still yana nan zaune, amma yanzu waya yake latsawa saboda an gama news ɗin. tsayawa tayi tana tunanin abinda zata yi masa ta huce takaicinta, Amina ta shigo parlon ɗauke da sallama bakinta, hannunta kuma riƙe da basket na kayan abinci. Gwaggo ta ansa gaisuwartata a ciki, ta nufi Dining zata aje abincin Gwaggo tace, "ke tsaya, mene wannan?". "Gwaggo abincinku ne". "to koma da shi, jiya kwana nayi ban runtsa ba har safiyar yau lafiya bata ishi cikina ba, kuma duk sanadiyar abincinku da naci ne. don haka tsautsayi ba zai kuma sawa naci ba, dan ban san me zai kuma faruwa ba, ki koma da shi kice Allah ya amfana, kuma daga yau kar a kuma kawo min". A ciki Amina ta saki dariya, burin Ummanta ya cika, dama girkin jiya da gayya ta rambaɗa masa attaruhu yanda zai kasa ciyuwa ko kuma ya ɓata ciki, ta yanda Gwaggo zata ce a raba girki. Haka Amina ta juya da abincin tana mai jin haushin Gwaggo, tana kuma dariyar mugunta, kuma da alaman yanda ta fita sai ta ƙara akan abinda Gwaggo tace ma ta. Kujerar da Haidar ke zaune ta nufa, kansa ta tsaya ta ƙare masa kallo tukunna tace da shi. "Mulkakke, hamshaƙi, ɗan masu isa da taƙama. ka wani hakimce min a kan kujera kamar ɗakin uwarka, sarai dai kasan wannan jibgegiyar ƙafar taka mai kama da doya tafi ƙarfin wannan teburin nawa, amma saboda mugun hali kazo ka ɗora min akai. don haka ka sami damar ɗauketa kamin ka fasa min glass, tunda babu sisin Sulaimanu a siyota". Yaja guntun tsaki a ciki, da yayi niyyar ɗaukewa amma tunda ta haɗa da sunan ubansa ba abinda zai sa shi ɗaukewa. cikin hasala tace, "ɗaukewar ce aiki ko kuma ɗaukewar ne ba zaka yi ba Aliyu?". Nan ma shiru yayi ma ta, hakan yasa ta duƙa ta ɗauke ƙafafun nasa ta watsar a ƙasa. ta hau sababin cewa,"ni dai duk a cikin jikokina ku biyu ne banyi sa'ar samu na kirki ba kai da Junaid, to gwara Junaidu ma sdaya zo ya tafi naga ya ɗanyi sanyi, inaga rayuwa ce ta fara gara shi. kai kuwa rashin mutuncinka ƙara hauhawa yake. To baka isa ba kayi kaɗan tunda dai ni na haifi ubanka ba kai ka haife ni ba, kuma ka ajiye min kofi, lemun dana aje ai ba kai na ajewa ba amma saboda hannun ɓera gareka shine kazo ka ɗaukar min ba tare da neman izininina ba. to ko Abba baya yi min haka shi da ubansa ma ya siya kenan, saboda haka kake fara neman izini kamin ka taɓa min abuna". Cup ɗin ya aje ya ɗauke kansa gefe yaci gaba da kallon tv. "to waima da ka shigo min wuri kayi sallama ne saboda ina ɗaka banji sallamarka ba?". can ƙasan maƙoshi yace, "amsata ne yake wajibi ba yinta ba". "yo to kai Aliyu dama ai ba mutunci ka cika ba, dan na faɗa ka faɗa wannan ba komai bane a wurinka, kuma dai kasan nafi ƙarfin kayi min rashin kunya tunda dai ni na tsuguna na haifi ubanka. ni ban taɓa gasgata rashin kirkinka ya kai intaha har haka ba sai yau, tsakani da Allah ka kama marainiyar Allah ka duketa ka sata kuka, haka ake rayuwa fisabilillah, kawai saboda kaga tana da haƙuri bata raina na gaba da ita shi yasa ka zageta son ranka, da ka san ba zaka koya mata ba ai saika faɗawa shi Auwalun daya saka, bawai ka juye haushinka a kanta ba, to ka kiyaye ni Haidar, ka kiyayi ramata, ka kiyayi abunda zan aikata. kuma Allah ya saka mata". Ya waigo gareta yace, "ita maƙaryaciyar haka tace miki na daketa ko na zageta?". tace, "ai ba ƙaryata tayi ba, cikin abunda ka lissafa wanne ne baka yi mata ba?, to kaga ni ba zuwa nayi nai doguwar magana da kai ba, Zuwa nayi na faɗa maka muddin kana so zamanka ya ɗore a cikin gidan nan to ka kiyayi ɓacin ran Sabina, idan kuwa ba haka ba sai ka tattara komatsanka kaje can ka kama wani gidan ka zauna zuwa randa zaka gama shi aikin naka ka koma. Haka kawai kazo kana cin arziƙin uban yarinya kuma sai ka nemi ka takurawa rayuwarta, yo ina dole anan sai ka bar gidan Wallahi, ni ba zan ɗauki ɓacin rai ba". Kan Haidar a kan wayarsa har ta kammala baice ci kanki ba, hakan kuma ya ƙara bata haushi. "ina maka magana baka ce komai ba, wato gani banza a wofi ko, ina ihun kare. kai baka iya bada haƙuri akan laifin da kayi ba, ta inda Junaid ya fika kenan, yasan na gaba da shi amma kai dai banda Ubanka Sulaimanu babu wanda kake gani da gashin ido". "to me kike so nace miki Gwaggo, salon nayi magana kice kema na zageki. Ita dai da kike ɗaurewar ƙugu takewa mutane sharri ba rayuwa ce mai kyau kika ɗorata akai ba, randa babu ke wuya zata sha Wallahi". "ɗan baƙin ciki, kamin ta rasa ni insha'Allahu na damƙata a hannun na gari mai gaskiya da amana". ta kama gefen zane tana gyara ɗauri. "Kaga ni tashi tsaye ma, kaji wani laushin kujera kana neman kassara min ita saboda ba'a saba ganinta a gida ba, zaka tashi ko kuwa? Haidar in maka magana kana gyara zama". "wai idan na tashi me zanyi miki? kina fa da takura Gwaggo. Naga dai nima gidan nan na ubana ne, kuma ɗakin nan mallakin kine kuma ke ɗin Kakata ce". "Laaa kaji min mutum; ta ina gidan nan ya zama na ubanka?, wannan gida dai na uban Sabina ne bana ubanka ba, bana son kalen jaraba". sai kuma ta fara faɗa sosai, faɗa na gaske bana wasa ba. "ka miƙe na nuna maka hanyar fita, idan ka fice kuma bana so ka ƙara dawo min sashena har ka bar gidan nan, tunda ba naka bane, mara mutunci kawai, wanda bai tausayin maraya...na rantse Aliyu idan ka ƙara taɓa min Sabina ba zamu kwashe ta daɗi da kai ba, banza wanda bai girmama kansa. shashasha kawai dogon wofi". Haidar Yaja ƙaramin tsaki ya miƙe yana zura wayoyinsa a aljihu ya raɓa ta gefenta ya fice fuuuu kamar mai shirin tashi sama. Gwaggo ta daki cinya tace, "oho dai tafi nono fari, Idan kayi zuciya har ka bar gidan nan karka ƙara shigo min sashe ko da kuwa gaisuwa ne, ni idan mutum naso muyi shiri to ya kiyaye ɓacin ran marainiyata". Yazo fita ni kuma na fito, bamu lura da juna ba muka bugi goshi, na saki ƙara da ihu ina dafe wurin, shima dafe goshinsa yayi da alama yaji zafi, ina niyyar bashi haƙuri naji ya doka wani uban tsakin daya daki dodon kunnena, ya sanya kai ya fice bayan ya jefan mugun kallo. a wannan lokacin banda a ƙule yake da ba abinda zai hana shi kawo min hannu.
*_Masu