Showing 81001 words to 84000 words out of 89788 words

Chapter 28 - ALHUSSAIN Complete Hausa Novel

23 Aug 2025

403

tun wuri yasan irin matakin da zai ɗauka kamin kija mana abin magana". na ɗago na danƙara mata harara kamar idanuwana zasu zazzago nace,"A kaf duniya inda mai yimin mugun baki kece ta farko, Umma ya kamata ki lura ki gane ni ba sa'arki bace, kija girmanki ki kama shi ki riƙe, ni ɗin fa da kike haukar kishinki akaina ba nice kishiyarki ba, amma duk kinbi kin ɗora min karan tsana saboda kawai soyayyar da mahaifina yake min, to hala idan bai so ni ba ke zai so? karki manta kefa matarsa ce da zai iya sauyaki duk sanda yaso, ni kuma ƴarsa ce abadan abadina, so babu yanda kika iya da ganina, da za ki haƙura ma da kin hutawa kanki da cutar hawan jini, idan ba haka ba soon za ki kamu da ciwon zuciya saboda a kullum soyayyata ƙara ninkuwa take a zuciyar Babana, atoh, saboda haka please ki fita a rayuwata. Lalacewa kuma da kike magana ki gani akan Ƴaƴanki, kuma idan Baba ya dawo kika fasa karanta masa komai ke ɗin ba ki amsa sunanki ba". na nufi side ɗinmu zan shige tace,"Sabina" Cak na tsaya na juyo ina kallonta ina kuma jifanta da harara da murguɗa baki. tana nuna kanta take cewa,"Sabina ni kike gayawa waɗannan maganganun saboda ba ki da mutunci ba ki da tarbiyya, ni ɗinfa matar ubanki ce". na taɓe baki nace,"so what, dan kina matar ubana ai ba yana nufin ke ɗin uwata bace, kuma ko mene na gaya miki aike kika jawo tunda ba kya kama girmanki, ke kullum burinki kija tashin hankali acikin gidan nan, to duk wata masifa taki ta ƙare miki ke ɗaya". Yaya Abbane ya iso wurin, ya tambayeni meke faruwa, na zayyane masa komai. ya dubeta cike da jin haushi yace,"wallahi ke dai Umma anyi girman banza, ki zauna ki dinga jan ƴar cikinki da rigima. kuma a haka kike so a dinga yi miki biyayya, to ki fara kama kanki kamin nan aganki da gashin ido, ni dai ina gargaɗinki kar ki ƙara yiwa ƙanwata mugun baki, don gaba abin ba zai mana kyau ba". Umma ta ƙufulu tana huci tace,"to Abba ko dukana zaka yi ne sai nasan da gaske mataki zaka ɗauka". yace,"to wuyar dukan za kiyi ne, ki ƙara taɓa min ƙanwa ki gani".ya faɗi hakan yana cewa da ni,"mu tafi".
[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(28)*
bakin wani tangamemen gate motar tasu ta tsaya ƙirar lexus, kallo ɗaga zaka yiwa gidan kasan ba ƙanan mutane ke rayuwa cikinsa ba, dan tun daga farkon estate ɗin zaka san its not possible ma talaka ya shigo shi, iyakan tsaruwa gidan ya tsaru kamar a ƙasar turai, ƙaryar baki yace zai fasalta haɗuwar ginin, gaba ɗaya wajensa kewaye yake da wasu irin flowers masu ƙawata kyawun wuri. a yayin da mutanen dake cikin motar fuskokinsu ke cike da annashuwa. driver ya danna horn da sauri gate man yazo ya buɗe, suna shiga kai tsaye wajen entrans shiga main part na gidan driver yay parking motan, ƙasan wajen gaba ɗaya shimfiɗe yake da grass carpet sai hasken fitilu multi colour dake haska wurin sai kace hotel, driver ya fito cikin sauri ya buɗe booth ya ɗauko wheel chair, sannan yazo ya buɗe ma Muhsin murfin motar, sai dai bai fito ba yana zaune ya ɗauko waya a aljihunsa yana dialling number. daga cikin kantamemen parlon gidan irin 100 by 100 ɗin nan, parlon ya gaji da haɗuwa kamar ba za'a mutu ba, kewaye yake da wasu lumtsatstsun cushions na alfarma, a cikin ɗaya daga cikin cushions ɗin mai zaman mutum guda, farar dattijuwar Mata ce kyakykyawa daka ganta kaga shuwa arab, ta dubi agogon gwal ɗin dake hannunta, ta sauke numfashi, damuwa a tattare da ita tace,"Muhsina do you look up the time? your brother is still not yet back, duba ki ga har da additional five minutes on his return time". Muhsina na zaune kan ɗaya daga kujeran dining tana cin fruit tace,"Mom, thats what am thinking, but he might be on his way back ko kuma ya tsaya wurin seminer da Daddy yace zaije". Mom tace,"I don't think so, he could have informed me if that was the case. wayansa ma fa not recherble gaba ɗaya, fatana Allah ubangiji yasa lafiya". she spoke in anxiety way har tana jin ƙirjinta na beating faster. "ni fa am worried da rashin dawowan yaron nan har yanzu, is everything alright? haba he's a determined boy, banda haka me ne zaisa shi fita aiki? ya zauna wuri guda tunda ubansa ya tara dukiyar nan ya ajiye musu. anyway to ya dawo yau ɗin ya sameni". Tsohuwar Matar dake sakkowa daga stairs ke wannan maganar cikin faɗa, sanye take da lapaya orange colour fuskarta kuma ɗauke da glass me yanayin na fashions amma kuma medical ne, kana kallonta kaga mahaifiyar Mom saboda tsananin kamansu, Mom da Muhsina suka maida dubansu gareta. ta kuma cewa,"Fa'iƙa zaman me kike da ba za ki tashi muje dubo shi ba? yaran da ba cikakkiyar lafiya gare shi ba". Mom tace da mahaifiyartata, "Anie we are sitting here driver went to pick him up. ni ba wannan ba ma, not knowing the reason for their returning early shine yafi damuna, since he had never reached such a time. ga wayoyinsa duka basa tafiya". Anie sighed and said,"shi drivern babu waya hannunsa ne da aka gagara tuntuɓarsa aji halin da suke ciki?". dukansu basu kai ga kuma furta ko wacce kalma ba wayar Muhsina ta fara ringing, ta ɗauka da sauri tana cewa,"yauwa Mom gashi ma ya kira". daga ɓangaren Muhsin yace,"Sister am back". yana faɗin hakan ya kashe wayan. dukansu suka sauke ajiyan zuciya, sai yanzu nutsuwa ta samu a garesu hankalinsu ya kwanta, lallai ba ƙaramin ji da shi ake a wannan gida ba, minti biyar kawai ya ƙara akan lokacin dawowansa amma hankalin kowa ya tashi, ana tunanin ko ba lafiya ba, tabbas shi ɗin ɗan gata ne gaba da baya. Anie tace, "lamarin Hassan sai shi, wato har yanzu idan ya dawo dole dai sai Muhsina taje tarbo shi tukunna zai shigo". Mom tace,"ai haƙurinsa ɗaya idan bata nan, amma anan kuma dole ni ce zan fita. yace damuwa yake shiga indai yagansa shi ɗaya yana tafiya a keken nan, kuma baya so yake saka ma'aikata turo shi". Muhsina na isowa entrance ta iske Mami na balbalin masifa, ita dai wannan mata kwai jarababba, ko da yaushe acikin masifa ta ke muddin wani abu zai shiga tsakanin ƴaƴanta dana kishiyarta, Muhsina tayi tsaki taja ta tsaya cike da takaici, ta tsaya ne kawai saboda Mom ta hanasu saurarenta idan tana wannan haushin karen, amma da bata isa ta tsaya kan Brother tana masa wannan hargowan ba. Khaleesat ita dai ƙuri tayi ta rakuɓe daga bayan keken Muhsin, ita kanta yarinyar bata son wannan halin na uwarta, sai noƙewa takeyi gudun karta kawo mata duka, muryarta a hankali tace,"Mami kiyi haƙuri please". aiko kamar ta watsa mata petrol ta damƙo kafaɗarta tana cewa,"kin rufe min baki ko saina zubar miki da haƙora anan wurin, shashasha wadda bata da kishin uwarta, to dama kin zama ma'akaciyar jinya ne da kika zo kinibibin taimako?, ke ga ƴar neman suna, ko kuma dama ke kike taimaka masa tun asali?. Abid ne ya rasa ƙafa da za ki tashi hankalinki akansa? keken nasa ai da inji yake aiki me ya hana ya kunna ya gurgura da kansa?, a'a ke ga ƴar neman gindi ya zama dole kiyi aikin da babu lada, ni dai wannan ƴa banda a hayyacina na haifeki wallah da zance ba jinina bace ke, tunda na haifeki ba ki taɓa faranta min rai ba kullu yaumin acikin baƙanta min kike, anya Khaleesa kina so ki gama da duniya lafiya kuwa? ni fa uwarki ce wata goma cif haka na ɗau cikinki. na kuma sha baƙar wuya kamin ki fito saboda an riga an min asiri ba'aso na haihu dan baƙin ciki da zalunci, haka aka jefeni da ciwon nono saina waccan shegiyar matar ubanki yasa aka dinga ɗirka miki kina zuƙa, to banda Allah yasa ma na tashi tsaye na nemi maganin tsari a gareki ai wallahi da babu abinda zai hanaki ɗauko baƙin halinta gaba ɗaya tunda kin sha a ruwan nono. banza kawai kin wani taho da rawar jiki kamar ƙanin uwarki ne ba lafiya, ana gudun nakasassu amma ke tusa kanki cikinsu kike saboda hankali bai gama isarki ba, haka kawai ina zaman zamana ki jawo min masifa kema ki shafi ciwon gurgunta a haɗa biyu, dama ana min baƙinciki da ku, yanzu ace akanki tattalin arziƙin ubanki yake ƙarewa, dan shi Ubanki ko duka arziƙinsa zai ƙare wurin ɓarnatarwa wannan gurgun ba zai taɓa gani ba tunda tsatson waccen ne, ta riga ta gama da shi, amma ke kuwa daga ke harni wuya zamu sha". ita dai Khaleesa shiru tayi ta rasa abin cewa, yanzu tana buɗar baki Mami zata aikata abinda tace, ita kuwa bata shirya rasa haƙoranta ba, yanzunma sai dai Allah ya kiyayeta idan sun koma part nasu, dan Mami ba dai mita da jaraba ba. Mami ta maka ma ta wani shegen kallo tare da kamo kunnenta ta murɗe har saida Khaleesa tayi ƙara. "yau ya zama rana na ƙarshe da zan faɗa miki bana so kike kula wannan gadon tsiyar, idan kuma kinƙi ji wallahi saina tsine miki tunda ke kunnen ƙashi gareki, ke ko uwarsu kika gani kika gaisheta ban yafe miki ba, sau nawa zan faɗa miki bana sonsu kamar yanda bana son uwarsu, sam-sam kin gagara gane cewar uwarsu maƙiyita ce saboda ƙwaƙwalwar kifi gareki, to kici gaba da kulasu ki kalla yanda zanyi raga-raga dake a gidan nan, sokuwar banza mara wayo, su ba ki ga duk abinda uwarsu tace ba basa ƙetare shi, amma ke saboda ban isa ba ke maƙiyana su kike so, da ace ke kaɗai Allah ya bani da tuni baƙin cikinki ya kasheni, kina kallo ubanki bai ɗaukeni komai acikin gidan nan ba, sai abinda waccan shegiyar matar tace shi zai hau ya zauna akai, ke wannan bai isheki aya ba ki gane ba'a ƙaunar taki uwar?, Abid kaɗai ke goya min baya kamar shi kaɗai na haifa...to dan uwar ubanki ɓace a wurin nan". ta faɗa tana hankaɗata, sannan ta koma kan su Muhsin tana cewa,"ku kuma daga yau karku ƙara kula Ƴaƴana tunda ba Fa'iƙa ce ta haifa min su ba, idan kuma kunƙi ji da ku da shegiyar uwar taku...". Cikin fushi Muhsin ya katseta da cewa,"saboda muna yi miki shiru hakan baya na nufin muna tsoronki bane, kina cin darajar masu daraja ne, karki ƙara sako mahaifiyata a cikin haukarki, ki tsaya a iya kanmu domin akan mahaifiyata zan mance da darajar Daddy da kike ci naci muntuncinki iya gwargwadon ikona, dan haka ki kula ki kuma kiyaye". yana faɗa ya kunna kekensa ya bar wurin. Muhsina tayi wani murmushi tana nunata da hannu sama da ƙasa tace,"ki ji, ki kuma kiyaye, domin idan kika gama hassala Brother nah da wannan haukar naki da baida ranar ƙarewa, abin ba zai miki kyau ba. dama darajar Daddy da Mom yasa muke ɗaga miki ƙafa, su kuma ƴaƴanki da kike magana akai sai ki jira wanda ya isa damu yazo ya bamu wannan umarnin tukunna, dama Khaleesat ce kaɗai tamu ba wannan ɗan daban yaron ba". tana faɗa taja tsaki ta bangajeta ta wuce. tunda ya shigo Mom ta kalla yanayinsa tasan anyi ta faru, kasancewarsa mutum mara fushi, da wuya kaga ransa ya ɓaci, ya kanyi duk yanda zaiyi wajen ɓoye ɓacin ransa. cikin hanzari ta bar abinda takeyi ta ƙaraso inda yake, tayi swith ɗin machin nasa off ta ƙarasa tura shi, ta kamashi ta zaunar da shi kan kujera, da duka tafukan hannunta ta tallabi fuskarsa tana cewa,"whats happened to my one and only son? what made him sad? after knowing Ɗana baya fushi me yasa zanga hakan yau?". Muhsina dake shigowa tace,"wace banda waccan akuyar matar, don Allah Mom allow us to teach her lesson since she will never be smart. kawai sai ta dinga haukarta tana sakoki ciki tana zaginki, we know your worth, please Mom ki bamu go ahead ɗin gyara ma ta zama". Mom tai ma ta wani kallo tace,"idan baku gyara ma ta zama ba kwa kashe mahaifinku ai, you know him very well he does'nt like any commotions, yanzun nan sai jininsa ya hau. him self knows muna haƙuri ne da ita that is why he use to praises us. so ni ban baku goyan bayan biye mata ba, duk abinda zata yi muku kuyi banza da ita, babu ruwanki da shiga sha'anin haukarta, idan kuma kun shirya rasa mahaifinku to ni ban shirya rasa mijina ba. duk wanda ya kuma saurarenta cikinku i will be angry with him". Muhsina ta zauna tana fushi bayan ta kauda keken Muhsin zuwa ma'ajinsa. Anie tazo ta rungume Muhsin tana masa welcome, dake wannan itace al'adarsu. tana cewa da Mom,"wai Fa'iƙa har yanzu Na'ima bata sauya zane ba dama?". da yake 2days kenan da zuwanta daga Mali. Mom tayi murmushin takaici tace,"tana nan a yanda kika santa, sai abunda ma yake ƙaruwa. ba dan ma Daddynsu tsayayyen namiji bane ai saita fi haka". "To Allah ya shiryeta ya ganar da ita. ke kuma Muhsina Allah ya fiddo miki mijin aure ki tafi naki gidan kema ki huta da takaicin matar uba". "tab ai Anie ai hankalina ba zai kwanta ba, saboda Mom sanyi-sanyi zata dinƙa ma ta, ƙwamma na zauna kusa da Mom yanda duk randa na kasa haɗiye fushina zan kwarfe ƴar banza ta zube a ƙasa". Mom ta dawo ɗauke da tray na abinci tana cewa,"a wani hadisi manzon Allah S.A.W yana cewa ba mai ƙarfi ne yake buga mutane da ƙasa ba, mai ƙarfi shine yake mallakar zuciyarsa yayin fushi. ni ba komai yasa nake daɗa tausar zuciyoyinku ba sai dan tunawa da wannan hadisi da nake saboda hadisi ne da yake nuni da muhimmancin haƙuri. so kiyi ma ta abinda yafi kwarfewa ma in kin tashi, ni dai duk wanda ya kashe min miji ba yarda zanyi ba, dan mijina zaman lafiya yake so...kuma akan mijina zan iya kai ƙarar mutum kotu". Muhsina tayi ƴar dariya tace,"Mom nima fa ina son Daddy, inaga ma na fiki sonsa". Mom tace,"banga alama ba kam". ta zauna tana feeding Muhsin kamar ƙaramin yaro, shi kam cike da jin daɗi yake amsar abincin yana kallonta, sai hira ta ke masa duk don ta kawar masa da ɓacin ran da abokiyar zamanta ta haifar masa. ta duba Muhsina dake aikin ɓata rai tace,"am sorry daughter". tayi knooding kanta kawai bata ce komai ba. bayan Mom ta gama bashi abinci ta ɗauko magani ta shafa masa a ƙafafunsa tana massaging a hankali. tace da shi,"when will your Daddy going to return?". yace,"tomorrow by now insha'Allahu". "Allah ya dawo mana da shi lafiya". tace tana ɗaga ƙafafunsa ta ɗora kan tumtum. Anie tace,"to ke dama ba ki san lokacin dawowan mijin naki ba sai kin tambayi nawa mijin". Tana murmushi tace,"Anie ai ya fini kusanci da shi ta wannan ɓangaren, da lokacin tafiyansa dana dawowansa duk a wurinsa nake ji. ina so ya dawo ne mu koma wurin mai maganin nan tunda yana jin daɗinsa, yanzu fa har motsa ƙafan nasa ya kanyi kuma ba ta cika yi masa ciwo ba". Anie tace,"to ai dama kune da kuka liƙewa na asibiti, tunda naga irin kuɗaɗen da ake kashewa daga wannan ƙasa zuwa wannan ƙasa an gagara gane taƙamemen me yake damun ƙafar jikina ya fara tsinkewa da lamarin ciwonsa, tun a baya na faɗa miki a haɗa da wurin Malam ƙwarai a nemi ayoyin waraka za'a dace tunda lamarin yafi kama dana jinnu". Mom tace,"Anie it's not my fault. Daddy ne ba zai yarda ba sai yace dole sai asibiti. yanzu kinga shi wannan Malamin garin habba yace a kwaɓa da man zaitun Allah idan na shafa mishi ba ki ga daɗin da yake ji ba. amma asibiti sai muje a haɗo mu da maganin sama da 50k in za'ayi kwana nawa ana amfani da shi ba wani sauƙi da za ki gani". "to Allah ya bashi lafiya. itama kuma Muhsina ya kamata a nemar ma ta magani gaskiya. dan na fara tsorata da al'amarinta. ace shekara 30 mace taƙi auruwa duk wanda yazo sai an gama magana al'amari ya lalace. dole itama akwai ayar tambaya akanta, idan zaku koma ɗin har ita za'a tafi". Mom ta kalla Mushina taga yanda ta shiga damuwa, sai tayi saurin kawar da zancen da suke da Anie, don bata son ganin yarinyar a damuwa. a ɓangaren Mami kuwa rufe Khaleesat tayi da duka, sai da ta tabbatar jikinta ya gaya ma ta sannan tace ma ta,"kuma kinji na rantse miki ko, kallon arziƙi wannan kika kuma yiwa Uwar nakasashshen yaron can sai kinci uwar ubanki, bare ta kai ga har kin buɗi baki kin mata magana. matsawar ba zaginta za kiyi ba to wallahi ban yarda da kiyi ma ta magana ba ko da kuwa a gaban ubanki ne". Khaleesat na kuka sosai tace, "Amma Mami...". cikin tsawa ta dakatar da ita da faɗin,"idan kika min magana sai na miki abinda yafi haka, ke kinga irin cin zarafin da wannan figaggiyar kazar tayi min yanzu kuwa?(Muhsina), amma ke shegiya sam ba ki lura da irin walaƙanta ni da ubanki ke yi akan uwarsu sai kike liƙe ma ta kamar itace tayi naƙudarki". "to Mami ai shi Daddy ba sonki ne ba yayi ba halinki ne baya so". a fusace Mami ta gwabje ma ta baki,"ni kike gayawa haka saboda ba ki da mutunci, uwarki ce fa ni, Khaleesat anya ban taɓa yi miki baki ba kuwa saboda na fara tsorata da lamuranki". kuka sosai Khaleesat ke yi, suna haka sai ga ƴar aikinsu ta shigo, ta duƙa ta gaida Mami amma ko amsa ma ta bata yi ba, sanin hali yasa ba ta damu ba, ta miƙawa Khaleesat baƙar leda tana cewa,"Anty gashi mai gadi ne ya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login