Showing 69001 words to 72000 words out of 89788 words
yimin gadara da su, duk sanda aka tashi sai azo a kunna min ɗan iskan yaren da ni ba fuskantarsa nake ba". sai kuma ta juya kan Abba da har yanzu yake kan cin abinci, tayi ƙasa da murya tace,"yanzu kai Abba wannan dacewa ne fisabilillahi, abinda kuka yimin kun kyauta kenan?, inata magana kun min shiru kamar da dutse nake magana kun barni sai zuba nake babu mai tarar numfashi na, a haka na raineka? tarbiyar da na baka kenan? idan shi bai san dai-dai ba ai kai ka sani, kuma ni dai ban koya maka rashin kyautawa ba, duk da kaima halinka sai kai amma tunda ka ƙara ɗinkewa da wancan yaron iskancinka ya ƙara hawa sama, shi yasa na ƙagu ya gama abinda ya kawo shi ya koma gidan ubansa, tun kamin ya ruguza min tarbiyar dana shekara 27 ina baka ita". Yaya Abba yace, "amma dai Gwaggo kin san ba kyau ana cin abinci ana magana, kuma ma meye ne kike so muce miki?". tace, "au ku baku da hankalin sanin abinda ya kamata kuce min, idan babu haƙuri ai akwai lallashi. amma babu komai kowa yay na gari kansa, ni dai daga yau na bar ciyar daku. yazo yay min katangar ƙarfe daku, idan ba zai haɗaku da matansa ba to kuma yay muku ɗakin girki idan yaso kuyi ta kwaɓarku kuna ci. amma ni dai na bar girki da gardawa, atou magana ta gaskiya kenan ina dalili, Ƴaƴana basu saka min hawan jini ba Ƴaƴan wasu su saka min".
tana gama faɗin hakan ta shigo ɗakin Sabina. har lokacin bata tashi ba, tana zuwa ta kashe ac, zafin da naji shi ya tashe ni, ina buɗe ido naji tana cewa da Iklima. "ki fito da kayan wankinta gaba ɗaya kamin ta tashi, naji tana batun wankesu kuma ni ba ƙaunar wankin injin nan nake ba sai naga kamar yana yaga kaya, ita kuma ba ganewa take ba saboda ba kuɗinta ne ke ciwo ba wajen saya". na miƙe zaune ina ɓata fuska nace, "Gwaggo ke kika kashe min Ac?". a hasale tace, "ban sa ni ba, mutum sai shegen lalacin banza da wofi, kiyita bacci kamar kasa ko gajiya ba kya yi, to ki tashi haka". "ni fa ban gama baccin ba, kuma ma yaushe ne rabon da nayi bacci irin haka. don Allah Gwaggo ki barni da zaran an koma makaranta fa shikenan". tace, "sai ki koma ai kiyi tayi kar ki tashi har a busa ƙaho, kuma ita dai wannan na'urar sanyi da baki da aiki sai warewa jikinki ita, to billahillazi kibi a hankali don ba gata ne kike wa kanki ba, mijinki za ki cuta, atou gaskiya nake faɗa miki ni babu ruwana". ƙunshe dariyata nayi har sai da ta fita na sa ki, na miƙe naje na kashe AC'n saboda Gwaggo gaskiya take faɗa min, na shiga toilet domin yin wanka. sai dana shirya na fito yin break, Yaya Abba da Yaya Haidar na zaune kan kujera, na gaida su kana na wuce dining, ina zama sai ga Baba ya shigo, gaishe shi muka yi, yake tambayarmu ina Gwaggo bata tashi ba ne?, a tare muka haɗa baki wurin ce masa ta tashi tana ɗaki ne. yana shiga ya tarar tana sallar walha, zama yay ya jira idarwarta, suka gaisa da Baba yace,"Gwaggo tun yanzu kika yi sallar, ai da kin bari sai anjima". tace, "walla kaga Auwalu kwana biyun nan da hadari ke haɗowa sai dai naji kiran azahar kawai, shi yasa nake yinta da wuri na huta". Baba yace, "ina agogon ɗakin ko ya lalace ne?". ya faɗa yana ɗaga kansa ya kalla bango. tace, "a'a yanayi, ai ɗan albarkar yaron nan Haidar shi ya koya min ma yanda ake gane lokacin, ranar yini mukai muna abu guda har sai dana iya. to kuma yanzu kasan idon sai a hankali ni ba kallon komai nake daga nesa ba, ita kuma waccen ƴar bata tashi sai azahar". Baba ya saita mata alerm ɗin landline ɗinta, yace duk sanda taji ya buga to lokaci ne yayi. idan kuma da daddare ne ya buga asuba ce tayi. sallama yay mata akan zai fita aiki, ya ɗauko kuɗi ya bata, ta amsa tana tasa masa albarka tana masa adu'a. ta fito masa rakiya ta kalla Yayana daya shigo babu jimawa, ta dakatar da Baba da cewan. "yauwa Auwalu ni namanta inata so na maka magana. kaga dai magana ta gaskiya bana jin daɗin abinda wannan yaron yake min, wai ba zai tashi cin abincin safe ba sai rana ta take zaka gansa ya shigo zagalo-zagalo ya wuce kitchen, kuma idan ya tashi du-du ɗan abinda zaici bai wuce cokali biyar ba zai ambatar min baƙar kalmar da bana so a gare shi yace wai ya ƙoshi, kuma daga wannan ƙoshin in Allah ya yarda ba zai kuma cin komi ba sai dare. to dan Allah irin haka ba sai yaja min zagi da tsinuwa ba ace bana bashi abinci, ina zaluntar maraya bayan ba halina bane. idan ciwon yunwa ya kama shi fa tsakani da Allah, idan shi baya son lafiyarsa aini ina so, haka kawai yaja min tashin hankali ya hanani natsuwa, na koma zaman jinya. to gaskiya kayi masa magana tun kamin ya kassara kansa". Baba yace,"wa kike magana akai ne?". tana cuna Yaya da baki tace,"gashi nan wannan yaron da Sabina ta kawo. ni fa ka ganni duka su ukun ba jin daɗin zama nake yi dasu ba, ina haƙuri ne kawai da halin kowa acikinsu. kuma duk maraicinsu nake tausayawa, bare shi wannan zagalon da babu uwa babu uba, duk cikinsu yafi ɗagan hankali, amma shi baya tausayin kansa, ni kuma abin yana ci min tuwo a ƙwarya. to gaskiya idan ba zaka yi musu faɗa su sauya hali ba ni zan cewa tsohon bazawarina ya fito muyi aure kawai na huta, banda Sahibina ma ya rasu ai da basu ganni a gabansu in tattalinsu haka ba, har suji daɗin min iya shege. dan haka ni dai don Allah kaja masa kunne ya bar zama da yunwa kar yaja min tashin hankali, na kasa tsaye na kasa zaune na ƙare a zaryar neman magani". Baba yay ƴar ƙaramar dariyar rikicin Gwaggo, yana duban Yayana yace,"to kai Yaya me yasa baka son cin abinci? ya kamata ka dinga ci kaji ko, kaga ulcer dai yanzu ta zama ciwon zamani Allah ya rabamu da ita. a dinga yin abinda Gwaggo take so kunji ni gaba ɗayanku, idan ba haka ba mu daina shiri da mutum". gaba ɗayansu suka ce "to". kamin nan Yayana yace, "Baba nifa ina son cin abinci, itace sai tace dole da safe shayi ne za'a sha, ni kuma ba sha nake ba. shi yasa nake haƙura sai da rana". caraf Gwaggo tace, "to nufinka zama zan dinga yi ina dafa maka abinda kake so, to wannan sai ka bari sai kayi aure shine kake da iko akan matarka". tace da Baba, "kaga Auwalu tafiyarka Allah ya bada sa'a. ni zanma tufkar hanci". Baba na murmushi ya fita, yana fita tace da Yayana,"to yanzu daka zo min wuri ƙarfe tara mene ya kawoka?". bai bata amsa ba saboda idonsa na kaina yana kallona, haushi ya isheta ta daki cinya tace. "kanka ka walaƙanta ba ni ba". ta faɗa tana wucewarta ɗaki.
*5hours letter.*
da Yayana da Yaya Haidar na zaune kan kujera kowa da abinda yakeyi, Yaya Abba ma ya shigo daga baya, gaba ɗaya basa iya zama a ɓangarensu. ni ina zaune an saka min lallai duk na gaji da shi, gashi ko 1hr ma bai yi ba, na kishingiɗe a wurin ina bacci, muryan Gwaggo ce ta farkar da ni. "har yanzu wannan lallan bai yi bane?". tace dani tana zama a kujera. "umm baiyi ba, kuma ni walla duk na gaji". tace, "ke daɗina dake kenan kin cika raki, to kuwa karki cire shi har sai naje na dawo, dan ba za ki sani asarar kuɗi ba. ina kuɗin dana ba ki ki ajiye min ɗazu?"."yana ɗakinki cikin ƙaramar drower". "nawa ne dama da kika ƙirga?". nace, "sha biyar ne". tace,"kai Allah dai ya yiwa Auwalu albarka ya ƙara masa arziƙi...ke Iklima". ta ƙwala mata kira, tazo cikin gaggawa ta durƙusa tana cewa gata,"kije inda nace ki ɗaukon goro ranan, za ki ga kuɗi ki ɗauko min". ta tashi ta tafi ta kawo mata, ta karɓa tana dubansu, sabbin ƴan dubu-dubu ne wanda aka cira a rapa. Yaya Abba na gani ya taso ya dawo kusa da ita yana yin ƴar murya akan ta bashi nasa kason. kamar ba zata bashi ba sai kuma ta cira dubu biyu ta bashi, ta bawa Yaya Haidar ma biyu, sannan tace da Yayana kai Zagalo kaima ga naka, ya taso ya amsa yana cewa,"na gode Matar". "uhmm kaji da shi dai, ai ka kusa bani takarda ta matsawar ba zaka sauya halin cin abinci ba. haka kawai ciwon yunwa ya kamaka ka mutu ka barni da zawarci ina budurwata ɗanya shagab". ta faɗa tana miƙewa, kamin kuma tace da shi yazo ya kaita unguwa zata dubo mijin ƙawarta babu lafiya, tunda yazo dama ta daina yarda Yaya Abba ko Yaya Haidar wani ya kaita anguwa, acewarta su tuƙin sai da rai sukeyi, ita kam bata shirya tafiya yanzu bata kaini ɗaki ba. na shagwaɓe fuska nace,"to Gwaggo nifa ba ki bani nawa kuɗin ba". ta waigo daga tafiyar da take tana cewa,"ayyah ke fa muna tare, waɗan nan da kika gani asu zan cira na saya kayan dubiya, sauran kuma nemawa Yayanki maganin cin abinci zanyi, akwai wata Mata ƙawata Hajiya Me Riga zata min kwatace, ko yaye yaro za'ayi can ake kaishi a bashi maganin cin abinci. ki bari idan aka kuma bani wasu gaba ɗaya ma naki ne, aike ƴar lele ce". nayi murmushi ina jin daɗi, nayi mata adu'ar a dawo lafiya, tana amsawa da amin, tana kuma cewa su Yaya Abba duk wanda ya kuma taɓani bata yafe ba, tunda ita sai bata nan su dinƙa sani aiki kamar jaka, to yau ko banzan kallo akayi min ta bar mutum da Allah, gani nan amana ce, wanda yaci amana kuma ya san sauran a lahira. Yayana yazo ya wuce ta kusa da ƙafata har yana tankwaɓe min lalle, wanda nasan kuma yana sane, ni ban san me nayi masa ba yake jin haushina kwana biyu, ko magana nayi masa sai yaga damar amsa min.[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*
_By Oum Ramadhan✍🏼_
*(24)*
nabi bayansa da kallo ina hararsa kamar zanyi kuka, banda ina tausayinsa da saina faɗawa Gwaggo yanzun nan ta rama min.
***Ƙwiiiiii kake ji a sanda Alhussain yay wani mugun take burkin motar, Allah ya rufa asiri baibi ta kan matar da ta ɗauke yaronta ba daya fito daga cikin shop, Alhussain ya kifa kansa akan sitiyarin motar idanuwansa a rumtse. a wannan lokacin da wasu hawayen da bai san sanda suke saukowa ba, a wannan lokacin Gwaggo dake gaban motar ta sauke wata nauyayyiyar ajiyar zuciyar data amsa gaba ɗaya acikin motar. ta buɗe baki tana ta fitar da numfashi, gefe ɗaya ƙirjinta sai lugude yake kamar allon ƙirjinta zai faso waje. a yanda take ji inda za'ace zuciyarta ce ta fito tayoyin motar tasu tabi ta kan zuciyar ta mitstsike ba zata musa ba, tsawon wucewar wasu daƙiƙu kamin ta dawo hayyacinta, sannan ta dubi gefenta inda Alhussain yake wanda har sannan goshinsa ke akan sitiyarin. sautin muryarta ya fito da wannan fargabar da bata gama barinta ba. "Yaya kasheni zaka yi?, saura kaɗan fa kabi ta kan ɗan mutane ina hankalinka ya tafi?". magana take tayi amma sam bai ɗago ba kuma babu alamar zai ɗago ɗin. hakanne ya ɗarsa tsoro a ranta ta miƙa hannu ta ɗago shi, sai ta ganshi ruwan hawaye duk ya wanke masa fuska, yayinda da idonsa dake buɗe ke kallon waje, inda wannan matar da ɗanta ke tsaye tana rungume da shi tsam ajikinta. "kai lafiya? menene? kai ka juyo ka faɗamin halin da ake ciki, kukan namiji ko tashin hankali". yasa hannu ya goge hawayensa, sannan muryarsa ta fito cikin wani irin rauni me tsinka zuciya yace,"Gwaggo wasu iyayen Mata suna tsananin son ƴaƴansu, irin soyayyar da zasu iya jefa kansu a kowanne irin hatsari". sai yay shiru wani hawayen na ƙara sauko masa, kuma har wannan lokacin ƙwayar idonsa bata ɗauke daga kan wannan matar ba da yake jin wani abu akanta na tsarga masa ba. Gwaggo da tai kasaƙe tana dubansa tace,"hakane. amma maganar daga ina haka?". a wannan lokacin da ya shiga magana muryarsa na fita ne da karyewar kowanne harafi, kuma a yanzu kuka yake sosai. "Gwaggo me yasa tawa mahaifiyar bata kasance irin sauran ba? me yasa tata zuciyar babu wannan ƙaunar dake tsakanin ɗa da uwa?...Gwaggo ni ba ƙaramin yaro bane, na girma, na zama cikakken namiji, amma me yasa kullum nake jin ina buƙatar mahaifiyata a kusa da ni? ina tsananin buƙatar na jita a kusa dani...in da tasan ba zata so ni ba me yasa ta zaɓi ta samar dani ta hanyar da bata dace ba?, ta samar dani ta gurɓatacciyar hanya, dalilin da yasa ta jefar dani kenan a bola...ina sonta, duk da haka ina sonta Gwaggo, kuma na yafe mata ba, kuma zanso tazo gareni ko da na second ɗaya ne, nima na samu naji wannan ɗumin jikin na uwa da kowanne ɗan sunnah yake samu, wallahi ina sonta Gwaggo, ko kaɗan bana fushi da ita". ya ƙarasa furucin da wani irin murmushi me ciwo dake fita a saman fuskarsa, yana mai saka hannu ya goge hawayen fuskarsa sannan yaywa motar key suci gaba da tafi. "ka tuna me likita yace maka?". Gwaggo ke cewa da shi, kuma ba tare da ta jira cewarsa taci gaba da faɗin,"yace damuwar dake danƙare a zuciyarsa zata iya haifar maka da matsala nan da lokaci kaɗan...ka daina damuwar haka, ajikina ina jin akwai wani ɓoyayyan lamari tare da kai". tai shiru tana saka yatsa ta dungure masa kai. "kaje dan kanka tunda ni baka ƙaunar kasancewa tare da ni". sai kawai fuskarsa ta washe da wani murmushi, yasa hannu a kafaɗar Gwaggo, haka yaci gaba da driving ɗin har ya kaita inda take son zuwa.
basu dawo ba sai bayan la'asar, tana shigowa ko zama batayi ba Zainab tazo tace mata Umma babu lafiya, ta zabari ƙafa ta fice a kiɗime sai salati ta ke zabgawa kamar ance mata ta mutu ne. yanzu ma da Yayana zai wuce da gayya ya kuma sa ƙafa ya shafe min tafin ƙafata, ya kuma yi wucewarsa kamar bai san abinda ya aikata ba, baƙinciki ya isheni kawai na fashe da kuka, Yaya Abba dake bacci ya farka ya doka min tsawa akan nai musu shiru, ni dai ban kula shi ba naci gaba da kukana ina kiran Gwaggo. "wai ke me yasa kuka baya miki wahala?". Yayana dake durƙusawa kusa dani ya faɗa. na ɗago na kalle shi na ɗauke kaina, na maida kaina ƙasa naci gaba da kukana. ina kallonsa ta gefen ido yana murmusa fuska saboda walaƙanci, na ɗago ina miƙa masa hannuna nace,"ni dai kunce min na cire shi haka nan kamin ka ƙarasa dagule minshi ya koma dungulmi". na faɗi hakan bana kallonsa saboda ina jin haushinsa. murmushin mungunta yayi, yay ƙwafa kaɗan kamin yasa hannunsa ya kuma dame min na hannun gaba ɗaya, ai ban san lokacin da na kuma fashewa da kuka ba ina dire diren ƙafa, cikin tsawa Yaya Haidar yace. "dilla Malama wannan wane irin rashin hankali ne?". ina sheƙar kuka nace, "don Allah Yaya Haidar kazo ka kunce min na hannu ɗaya na cire sauran, duk an dagule min shi karya zama na tsofaffi". harara ya zabga min yace,"uban wani ya sa ki yin ƙunshin? idan ba ki shiga hankalinki kin cire shi kin tashi kin wuce ciki ba sai na tashi na ɓarar dake anan wurin. kuma karki rufe mana baki ki kalla yanda zanyi dake". ina kallon yanda ya kafeni da ido yana min wani mugun kallo. ni kam ina zumɓura baki nace,"to ni ya kake so nayi, ba zan iya cirewa da kaina ba, kuma Iklima ta tafi islamiya. kawai dan anga Gwaggo bata nan sai a dinga cin zalina, da ace ma ina da Yaya mace babu me min irin hakan". can shima Yaya Abba ya hauni da masifa,"na rantse da Allah kika katse min bacci gaba ɗaya saina taso nazo nan na faffale ki da mari, shashasha kawai, har yanzu ke ba za ki girma da kuka ba". ba shiri naja bakina na gimtse, saboda ko kowa ba zai iya aikata abinda yace ba shi zai iya, dan ya tashi yasa waya ya tafasan jiki ba komai bane a wurinsa, ganina yake kamar ƴar shekara biyar. ni ban san me nayi musu ba suka tsaneni haka, babu mai tattalina acikinsu matsayina na ƙanwarsu, abu kaɗan zanyi su hayayyaƙo min, dama ga abinda ke ƙara basu haushi shagwaɓa ni da Gwaggo ke yi, ina sheƙar kuka naketa ƙunƙuni, Yaya Haidar ya taso a harzuƙe zai bige ni. Yayana ya riga shi isowa, ya tankwashe ƙafarsa tare da kamo hannuna yana kunce min lallan. "Malami kai kuma miye hakan?". Yaya Haidar ya faɗa yana mai jifansa da harara cike da jin haushinsa. Yayana yayi masa shiru, yana sa cokali ya kankare min lallen, dama tunda yazo sam basa shiri da juna, ko magana basa yi, idan kuwa ta kama dole to a rigima za'ayita. sai can ne kuma yay maganar a fizge yace,"kai yanzu idan aka barka sai ka daketa?, Haidar kana abu kamar ba wayayye ba". Yaya Haidar ya mayar masa da cewar,"to kai abinda kayi a wurinka wayewa ne? ka kama hannun yarinyar da ba muharramarka ba da sunan kai mai ilimi". na kalla Yayana naga yana murmushi, a tunanina hannu ɗaya zai cire min sai naga ya kamo ɗayan ma ya shiga cire min, yana gamawa da hannaye ya shiga cire min na ƙafata ma. Haka Yaya Haidar ya gama kwasar haushinsa anan tsaye ya fice ya bar parlon a fusace. ni kuwa yana gama cire