Showing 6001 words to 9000 words out of 89788 words

Chapter 3 - ALHUSSAIN Complete Hausa Novel

23 Aug 2025

376

gefe guda ina jiran abinda zai fito daga bakin Gwaggo, abunda naji tana faɗi ne yasa na ɗaga ido ina dubanta. “wanne Mahaukaci ne wannnan har da zai ɗaga maki hankali haka?, Sabina kin san halina fa sarai, ina da sauƙin kai amma bana son shashanci, waye shi?”. sai naji zuciyata tayi min nauyi saboda kalmar mahaukaci da Gwaggo tayi amfani da ita wurin kiran Yaya da shi, na turo baki gaba ina daɗa dubanta ta cikin glasses nawa nace. “don Allah ku daina kiran shi da mahaukaci, baku san yadda zuciyata ta ke duka ba, kalmar mahaukaci ai bata danganci mutum musulmi ba, mahaukaci ai sai dabba, shi kuma mutum ne mai kamala, don a maganar shi bata yi min kama da mai taɓin hankali ba, kawai halin rayuwa ne ya mayar da shi haka”. Zuru Gwaggo tayi tana dubana, maganganuna sun bata mamaki matuƙa gaya, cikin faɗa-faɗa ta kama cewa, “yo wai ke shin kin yi hauka ne, a ina ma kika gan shi ne tukun har kike faɗin haka, kin san dai Farhana ba zata maki ƙarya ba ko?”. “Gwaggo Allah ba mahaukaci bane, kawai dan ta gan shi a cikin kango kan bola shikenan sai ta kira shi da mahaukaci, idan ita aka faɗawa ɗan uwanta haka ai ba zata ji daɗi ba, ni idan bata yi wasa ba ma sai na daina kulata akansa wallah”. Gwaggo ta wurgo min daƙuwa tana faɗin,"ungo wannan, nace ungo, yau naji Mace, ke anya ma kuwa da kike je wurin shi bai shafa maki haukan ba, wannan wace irin macece ke, wai ke baki san duniya ta lalace haka ba, waye ke yadda da irin su musamman ma masu zama cikin kango, wannan waya san adadin yaran daya lalata daya fake a cikin nan, kar na sa ke jin wannan maganar a bakinki, kar in kuma jin kin amabace shi da sunan Yaya’n ki balle damuwa akansa...ince ko kin jini da kunnen fahimta?”. na muskuta gefe guda, ji nake kamar nayi kuka da kalaman Gwaggo, ƙasan zuciyata tuni yayi baƙi tana bugawa da sauri da sauri kamar zata fito waje. Bance da Gwaggo komai ba na Miƙe haɗe da buga ƙafa a ƙasa na bar wurin, ta biyo ni da faɗin, “ai ba ki buga ƙafar da kyau ba, da kinyi yanda zan shaida kin zama mara kunya, sai na san ta inda zan karɓeta". da faɗin hakan ta miƙe ta nufi inda wutar gawayi take ta zuba kuɓewar, kana ta shiga toilet dake tsakar gidan don ɗora alwalar magriba. ni kam shigewa ɗaki nayi na faɗa kan gado ina kukan irin cin zarafin da Gwaggo tayiwa Yaya, yau da ace ba Gwaggo bace ta faɗa haka da ko waye mun rabu da shi kenan.
Washe gari da Safe kuwa ina gama ayyukan gida nace da Gwaggo zanje gidan su Farhana, bata yi yunƙurin hanani ba, sai ma ɗumamen tuwo data zuba a plask tace na kaiwa Hajiyar Farhana saboda ta san tana son ɗumamen tuwo. fitowana na tari mai napep, tunda na hau ko passenger bai ɗauka ba har muka isa ƙofar gidansu Farhana, na fito na ba shi kuɗin shi na shiga gidan. A parlon gidan na iske su duk, suna ta hira gwanin burgewa, gaishe da su nayi har yayunta Maza suka amsa suna min tsiya. na miƙa plask ɗin hannuna gaban Mamansu ina cewa,“Hajiya gashi inji Gwaggo tace na kawo maki”. Hajiya ta amsa tana murmushi ta buɗe, ƙamshin ɗumamen ya daki hancin Hajiya har da lumshe ido tana faɗin, “kaii Masha Allah, kuma kamar kin san yanzu nake cema Farhana ta kiraki ko Gwaggo tuwo tayi yau ashe kuwa shi ɗinne, kaii madalla nagode ƙwarai Allah yayi albarka”. na amsa da Amin sannan muka haura sama nida Farhana inda ɗakinta yake. kamar bani nai fushi da ita ba jiya, itanma kaman ba itane ta shareni ba, tunda muka zauna hira kawai muke zubawa ba ƙaƙƙautawa, sai ma can da ta lura ne kaman hankalina ya rabu gida biyu ta ke faɗin, "wai wani abunne kuma?”. na girgiza mata kai, ta ƙara cewa,"to sai ki bani complete attention ɗinki dan ban iya ta magana alhalin ba sanin me nake cewa kike ba". sai na ɗan yamutsa fuska nace,"ke ni yanzu ma zan wuce, amma tukunnama me kuka dafa yanzu?”. tana hararata tace,"ban sa ni ba. wannan wanne irin kuturun wulaƙanci ne, muna hirarmu me daɗi kawai kice za ki tafi. hala fushin da kike da ni ne har yanzu bai baki daina ba?". "dilla ni ba haka bane, kawai dai ina so zan tafi ne. idan ban bar fushi dake ba ai ba za ki kalla ma nazo ba". "to amma daga zuwa sai tafiya abinda ba ki taɓa ba, to ina ma zaki je wai wanda ban sani ba?, dan dai ba za ki zo ki wuce gida da wuri haka sanin cewar za kisha tambaya gun Gwaggo". naja tsaki cikin ƙosawa nace,"ke dilla Malama ni ina tambayanki me kuka dafa kina wani tsareni da tambayoyinki kamar kin kama me laifi, na faɗa maki bana son irin haka, idan kuma abincinne ba za ki banba ki faɗa min na sa ni, daɗin abun gidanmu ma akwai". duba da yanda raina ya ɓaci kuma nake magana a hasale yasa tace,"ahh ba rami me ya kawo zancen rami?, kinga ni ba baƙuwar zafi bace Allah ba ki haƙuri. indai abinci ne irish potato ne da ƙwai, kawo maki zanyi ko da kanki zaki zubo tunda Allah yasa kin san inda yake?". na kuma jifanta da harara, ban saki fuskata ba sai ƙara ɗaureta da nai, na miƙe ina cewa,"muje kitchen ɗin". itama kuma sai ta ɓata tata fuskar, tai kicin-kicin da ita har muka sauko muka shiga kitchen, kuma da yake zuciyar kowa a wuya take ko Hajiya dake mana magana ma bamu saurara ba muka shige Kitchen, na ƙarasa drowern dana hangi ƙaton cooler ɗinsu da anan ake zuba abinci, ita kuma ta tsaya gefe tana kallona, ƙaramin plask na ɗakko na zuba dankalin da ƙwan a ciki, na samu wani plask na tea ƙarami bayan na haɗa tea ɗin na zuba a ciki sannan na dubi Farhana nace,"muje ki raka ni". tana dubana da mamaki tace,"gida ko ina? ban fahimce ki ba, cin abincin ne ba zakiyi anan ba ko me?”. na ƙara jan ɗogon tsaki saboda tana neman ta ɓata min lokaci da wannan shegiyar tambayar tata. "kinga Gwaggo Farhana, wannan abincin ban zuba dan cikina yaci ba...so rakiya zaki yi min, idan baza ki raka ni ba sai na tafi ni ɗaya ba komai bane ai tunda ni ba makauniya bace balle tafiyata ta zama dole saida ɗan jagora". na faɗa ina bin gefenta zan fice, sai tayi saurin kamo hannuna tana faɗin,"daɗina da ke kenan, babu baya ni sai saurin fushi. kin shigo da damuwa tare dake, ke biki yi min bayani ba sai neman sauke fushinki kike akaina...ina zamuje dama?”. "anguwa”. na bata amsa a taƙaice.
tai ɗan jim tana min kallon tsanaki, sai da ta gama nazartata tsaf tukunna tace,"wurin mahaukacin jiya zamu koma?". tayi tambayar da rainin hankali. a ƙufule kuwa nace da ita,"kin faɗa sau biyu kenan, karki gigin ƙara jingina shi da wannan mummunar kalmar a karo na uku, ina faɗa miki ne dan kinji da kyau. Farhana mamaita kalmar can daidai ta ke da yankewar alaƙar dake tsakaninmu, i dont fucking care dan mun rabu". ina faman huci nasa kai zan fita taƙi matsawa,"ki ban hanya zan wuce. ina ce kince ba ki rakani ko. kinga ki daina ganin kamar idan babu ke ba zan iya tafiyar nan ba, nasan hanya sarai, so da ace jagora za ki min sai na tsaya ki gama faɗa min baƙaƙen maganganunki...kinga tafiyana". ina kaiwa nan na tureta na fita, ta ƙofar baya nabi yadda Hajiyarsu ba zata ganni ba.
nayi sa'a yanda nake saurin nan ina fita na sami napep, Allah ya taimaka bai tsawwala min kuɗi ba, dama ba isashshen kuɗi ke garen ba, shi yasa ma nace Farhana tazo muje tunda ita a motarta ne. ina sauka daga napep ɗin na nufi cikin bolar, kai tsaye kuma cikin kangon na faɗa, a tunanina zan ganshi amma sai ban ganshi ba, na fito ina ƙara dudduba bakin bolar da gefe da duk inda dai idona idan ya wurga zaiga mutum, amma sam babu shi, sai naji wani abu mara daɗi na bin jikina, na koma cikin kangon na aje basket ɗin abincin na fito ina ƙara dube-dube. ta hannun haguna na gange shi can ƙarshen bolar kwance shame-shame, da sauri na nufi wajen, ina zuwa ban kula da komai ba na durƙushe a wurin na rarumo shi jikina ina faɗin, "subhanallah! Yaya meye sa kazo nan ka kwanta, baka da lafiya?". na tambaya duk a ruɗe ina taɓa kansa, amma babu zafi. "Yaya tashi mu bar nan dan Allah". Kallona kawai yake yi, yayinda ko leɓan shi bai samu damar furta kalma ɗaya ba, yayi min nauyi amma a hakan nake ƙoƙarin ganin na janyo shi da iya ƙarfina, sai dai sam na kasa, kuma ganin hakanne yasa shi miƙewa zaune kafin ya dubeni da kyau yace,"tashi”. muryarsa na fitowa da kaifi kamar na reza. na miƙe lokacin da idona ya cika tapp da ruwan hawaye, sannan shima ya miƙe, nai saurin kama shi ganin kamar zai faɗi, kayan jikinsa duk wari suke amma wannan sam bai dameni ba, haka nake kamashi ajikina bana ko lura da ɓacin da kayana zasu yi da najasar wurin. ya ƙwace a jikina yana cewa,"bar nan wurin". ƙwayar idonsa ce ta shaida min baya so ya ƙara maimaita min, hakan yasa naja da baya har na sauka daga saman bolar, tukunna naga ya fara takowa a hankali har ya sauko daga kan bolar shima, bai ko kalleni ba ya wuce ya shige cikin kangon, ganin haka yasa nima nabi shi na shiga ciki. A ƙasa na same shi zaune, nima na samu wuri na zauna ina duban shi kafin na furta, “Yaya baka da lafiya?...au ina kwana". bai amsa ba, sai ido daya kafe ni da shi yana nazarin rashin hankali irin nawa, tsawon wasu daƙiƙu kaina yana ƙasa na jiyo muryar shi na fita da faɗin, “Sabina ko?”. nai saurin ɗago kaina, “eh” .na bashi amsa. sai kuma muryarsa tayi ƙasa, "me yasa kika dawo inda nake?, wai meye sa baki da tsoro ne?, ke bari kiji na faɗa maki, nifa ɗan iska ne, ɗan yan kan kai ne, ina yanke kan mutane na kai ayi tsafi dasu, ki daina zuwa wuri na idan ba ki son na yanke kanki, ko nayi maki fyaɗe, dan duk na saba yinsu”. abunda zance a wannan lokacin maganarsa ta bani nishaɗi, furuci ne da ko kusa baiyi kama da shi ba, ya faɗa ne kawai dan ya tsoratani, dan da ƙyar ma ya dinga haɗo kalmomin. na saki ƴar ƙaramar dariya ina faɗin. “Yaya ai babu mai yiwa bawa wani abu fa ce abinda Allah ya rubuta zai sa me shi, kuma idan kai ɗan yankan kai ne, ai da baka zauna a haka ba, da baka zauna anan ba, da tuni kana da dukiya mai yawa kamar yadda masu yi suke da ita, ni bana jin tsoronka, hasali ma sai ƙaunarka da nake yi. tun jiya dana ganka zuciyata ke faɗa min ko me zaka yi min kar na rabu da kai, tana faɗa min akwai wani abu da zai kasance a tsakaninmu, tana faɗa min kai mutumin kirki ne, tana faɗa min an halicceni ne domin na tambayeka...so ka bar tsorata ni, ni bana tsoron kowa da komai saboda ina tare da Allah. yanzu dai ga abinci nan kaci mu tafi gida”. Kanshi ya kai duba ga plask ɗin da nake turawa gabansa. “Bana ci, ki ɗauka ki tafi, idan baki so nayi maki fyaɗe”. "banda lokacin ɓatawa". abunda nace da shi kenan ina buɗe jaka na ɗakko pure water, na miƙe na isa har gaban shi tukunna na kama hannunshi na wanke mishi, shi ko sai bina yake da ido yana ganin ikon Allah, sai dana wanke masa duka biyun sannan na buɗe plask ɗin na saka mishi a gabansa, na ɗakko kofi na zuba tea shima ta ajiye a gabansa ina faɗin, “Oya Yaya kaci mu tafi gida”. shi dai yayi shiru na zame masa abar kallo, zuciyarsa na cika da al'ajabina. ni kuwa ganin baida niyyan ci yasa na ɗauki tea cup ɗin na nufi bakinsa ina faɗin,"haaa". sai kawai ya koma kamar ɗa me biyayya ga uwarsa, babu musu ya buɗe baki ba tare da yasan ya buɗe ba, na saka mashi dankali da ƙwan ya taune ya haɗiye sannan na bashi tea ya kora. haka na dinƙa feeding nasa yana ci, ci sosai, kuma duk wannan bashi ɗin da nake ina jin yanda idonsa yake akaina, ni kam cin abincin da yake sai naji kamar ina tare da wata matsala me a rayuwata amma ta akan hakan ta yaye. har saida ya cinye irish ɗin nan tass baima sa ni ba, sai ji yay ina goge masa baki ina faɗin,"yauwa Yaya Nah ko kaifa...yanzun idan ka huta sai mu tafi gida ko?”. Tsaye ya miƙe da yanayi na fusata yace,"ba zan iya zama da mutum mara yadda ba, Sabina fice anan, ki fice anan wurin kamin nayi miki abinda har ki mutu ba zaki bar kuka ba. Kuma daga yau kar na ƙara ganinki anan na faɗa miki wannan". Ya faɗa a tsawace yana nuna min hanyar fita. Kallonsa na tsaya yi a lokacin da idanuna suka kawo ruwa, sannan na duƙa ƙasa na kwashi kwanukan abincin, zuciyata sam-sam ba daɗi, na fita na bar kangon ina mai waigen shi, maganganunsa na min yawo acikin kaina. Sai bayan fitowana tukunna ruwan hawayen da suka gama cika idona suka sami damar zuba, na sanya gefen hijabina na goge, sannan na saita kaina naci gaba da tafiya.
shi kuwa tana fita ya sauke dogon numfashi, idonsa a rufe ya nemi wuri ya zauna yana mai jin ransa da zuciyarsa duk babu daɗi. to amma ya zaiyi, ita macece, yanzu idan tana zuwa wurinsa sai ta ɓaci a idon mutane, a dinƙa yi mata irin wannan kallon da akeyi masa, kuma ya tabbata iyayenta suka san da hakan zasu iya saɓa mata, kuma kamar yanda ta faɗa ne, shi ba macuci bane dan haka ba zai taɓa iya cutar da ita ba. hasalima abu guda ɗaya ne yake nan, Allah ya sani, yana so ya dinƙa kasancewa da yarinyar ko da ba koda yaushe ba ne...bai yi tunanin zata kuma dawowa wajensa ba, amma ya tashi da tunaninta a yau. sai ya rumtse ido ya shafo sumar kansa yana fesar da iskar baki, wanda hakan ke ɗabi'arsa ce, kamin nan ya nemi waje ya zauna yana bin wurin da ta zauna da kallo, inda hoton zamanta a wurin ke haska masa cikin ido, maganganunta masu taushi kuma na yawo cikin kansa.


#Vote.
#Comment.
#Mikiyawriters.*AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(4)*
hidimar aikace-aikace nake tayi tun wayewar gari, yau babu inda ban gyara ba acikin gidan nan lungu da saƙo, hakan yasa ɗan ƙaramin gidan namu ya sake yin fayau da shi yay ƙal-ƙal, haka nake sam bani da ƙiwar aiki, Gwaggo na yawan faɗa min Mamana na gada, amma duk wata bauta da nake yi a gidan nan Yaya Abba baya ganinta dai-dai da misƙala zarratan. wuyarta nayi wuyarta ya ɓata kuma ya kushe, wani binma idan ya ɓata yay ficewarsa nai zuciya nace ba zan gyara ba, to bala'i ko sai dai idan bai dawo gidan ba, amma sai ya sauke min shi, ya dinga cewa Gwaggo wai tana sangartani, zan lalace na zama ƙazama. Gwaggo tace masa to ubanwa ke faɗawa idan na gyara, ta hakanne kawai nake samun salama, amma ni kaina na san banda ciki guda muka fito da shi la shakka ba zan ke raga masa ba, ina da haƙuri dai-dai gwargwado amma ba kanwar lasa bace.
kiran sallar azahar ɗin dana jiyo yasa na shiga sauri-sauri na kammala aikin kamin lokacin tafiya islamiya yayi, dan lokaci babu wuya yanzu agogo ya buga ƙarfe uku, dama da safe naji Gwaggo na cewa da Yaya Abba ya saka mata sabon batiri a agogonta, agogon me shegiyar ƙara da zarar cikar daidai yayi zai kama kiɗinsa me hawar min kai. Gwaggo ta fito zata shiga banɗaki tace da ni, "Sabina sannu da aiki".
na amsa, "yauwa Gwaggo, kin fito alwalar ne, bari na zuba miki ruwan". Ɗaya daga cikin botikan dake nan tsakar gida na buɗe na zuba ruwa cikin buta kana na bawa Gwaggo. Alwala Gwaggo tayi ta koma ɗaki domin ta gabatar da sallar azahar. Idarwarta kenan sai ga sallaman Baba, ɗakin ya shigo inda ya zauna nan bisa kujera yana gaida ita. na shigo a lokacin na durƙusa na gaida shi tare da ajiye masa ruwa da abincin dana kawo mishi. bayan ya amasa min yace,"Yau ba makaranta ne?". nace, "a'a da akwai, ai da sauran lokaci. Amma yanzu ma zan shirya da mun gama cin abinci". "to madallah. Ana dai dagewa ko?". "ehhh Baba muna yi sosai". Fuskar Baban ta washe da fara'a yace, "Allah ya bada nasara, ya kuma yi muku albarka...ai ba'a bina kuɗin makaranta ko?". Ya faɗa a yayinda yake zuba ruwa a cup zai sha. "amin amin Baba na gode. ehh ba'a binka". na miƙe naje na ɗauko namu abincin ni da Gwaggo, ina cin abincin ina satar kallon mahaifina da nake jinsa mafi soyuwa a gareni. kusan tare muka cinye abincin da shi, saboda muna ci ana hira, nan da nan muka tashi kan shinkafa da waken daya ji haɗin kayan lambu. na tashi na haɗa kan kwanukan da muka ɓata na kai kitchen, na dawo na gyara wurin duk da ba wani ɓata shi muka yi ba, sannan na wuce zuwa ɗakinmu da muke kwana ni da Gwaggo.
nai wanka na shirya cikin uniform ɗina na islamiya milk colour, kayan sun mun kyau sosai, jakar littafaina na ɗauka na rataya kana na fito nace da Gwaggo da Baba zan tafi. a gaban Baba na duƙa ina cewa da shi, "Baba kayi

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login