Showing 75001 words to 78000 words out of 89788 words
ni na faɗo ƙasa. ya sauko ya wuce toilet ya barni duƙe ina kuka, har ya fito yazo yasa kaya ina nan yanda ya barni ina aikin kuka, dama na tara abuna, gaba ɗaya takaicin abinda ya faru nake, ni dai Allah yayi wadaran halin wannan mutum. tunda ya gama sanya kaya yay tsaye yana mata wani mugun kallo, har cikin ransa yake jin kukan nata, sai da tayi mai isarta tana yin shashsheƙa sannan yazo inda take, ya kamo hannunta ya miƙar da ita tsaye, tare da janyota jikinsa ya rungumeta, yana aikin shafa kanta cikin sigar lallashi. ni dai shimfiɗar da kaina kawai nayi a ƙijinsa ina fizgar numfashi. "ki min shiru". ya faɗa a cikin ɗaurewar murya. ya ɗago kaina yana duban fuskata yace,"ke wai ba'a ce miki ki bar abu ki bari ne". ni dai ban kalle shi ba sai ƙarfi da nasa zan ƙwace daga jikinsa, ya kuma matsoni yana ɗaga min kai yace, "kinji na rantse ba zan sake ki ba har sai kin bar kuka. miye ma akai miki da za ki sa ni gaba kina min ɗan banzan halinki". "ni Yaya Haidar bana son irin wannan abun da kake min, wallahi Allah babu kyau, kaima fa kasan irin haramcin da yake ciki, duk da ni ina ƙanwarka amma ai ba muharramarka bace ni. dan darajan Allah ka daina wallahi bana jin daɗi kuma bana so a rubuta maka laifin zunubi". na faɗa hawaye na gangaro min, shi kuma fuska a tamke yace. "naji, ba zan kuma ba. amma kema k...". sai kuma yayi shiru ya kama hannuna muka fita yana cewa nai masa shiru na goge hawayena. muna shiga parlo Gwaggo ta taso hankalinta a tashe ta shiga tambayata lafiya duba da yanayin da ta ganni, ya saki hannuna yana faɗin. "aljanu ta tayar, ki daina barinta fita da daddare". ya faɗi hakan yana kama hannunta ya damƙa mata magani a kwalba, na kalleshi naga ya haɗe rai kuma yana maganar kamar da gaske, muna haɗa ido na murguɗa masa baki nace,"Allah ya isa". na faɗa a yanda kowa ba zai jini ba sai shi daya ganni. Gwaggo kuwa kuka ta saka sosai, tana faɗawa Uncle lalurar dake damuna, yace insha'Allahu za'ai min maganin da zasu rabu dani. "ita fa ɗaya tilo nake da ita Sulaimanu. baka ga yanda suke takura mata". ta kuma faɗa tana kuka. irin yanda take zuzuta abin kamar kullu yaumin nake tayar da su, ni harta bani haushi ma na miƙe na bar wurin, shi kuwa Uncle cewa yake. "ki bar kuka Mama, adu'a za'ayi Allah ya yaye mata, sai kuma magani da zamu durfafa wajen nemansa". tace,"to Sulaimanu dan Allah kayi taimakon daka za'a dace saboda shi ubanta ba damuwa yay da wannan ciwon nata ba, sam ko a jikinsa, don da na gaya masa ma ko razana bai yi ba. yanzu ka duba banda Aliyu yana gidan nan yanda suka tashi da wannan daren ya zanyi?, ai ni dai wannan yaro babu abinda zance da shi sai dai Allah yayi masa albarka yasa ya gama da duniya lafiya, ya kuma haɗa shi da matar ƙwarai. walla a kaf jikokina babu mai ƙaunata kamar Aliyu". ta ƙarasa maganar tana sa gefen zanenta ta goge hawaye. tace,"Aliyu Haidar". suna gaisawa da Mahaifinsa ya ɗago ya kalleta baiyi magana ba tace,"na gode maka ƙwarai kaji". "ki godewa Allah". ta miƙe zuwa ɗakin Sabina inda ta shiga ta sameta tana aikin kuka. duk yanda tayi dani akan nayi shiru ƙememe naƙi sauraronta, har saida tace zata kira Yaya Haidar yazo ayi min turare ko sune basu tafi. nai saurin cewa da ita,"a'a dan Allah Gwaggo, wallah naji sauƙi". muna haka Yayana ya shigo, kallo ɗaya zaka yiwa fuskarsa ka hangi damuwa acikinta.
yazo ya zauna gefen gado yana min sannu, na tsaya ina kallonsa, kenan shima ya yarda da maganarsu aljanu na tayar, jikinsa na faɗa na kuma sakin kuka ina cewa. "Allah ni Yaya ban tada aljanuna ba, ni bani ma dasu wallahi Sharrin Gwaggo da Yaya Haidar ne kawai". yasa hannu yana shafa gashin kaina, muryansa mai sanyin daɗi yace, "na san Cutie nah bata da wani aljanu, ki rabu dasu kinji. idan ma sune Allah zai rabaki dasu, amma ki share hawayen bana son jin kukanki". ya ɗagoni a jikinsa ya kama haɓata yana goge min hawayena da hanky ɗinsa mai ƙamshin daɗi, ni kuma ina ta sheƙar kukana ina kuma ɓata fuska cike da shagwaɓa. ya haɗe goshina da nasa, ya kashe min ido guda tare da raɗa min wata magana a kunne, muka haɗa ido na ƙyalƙyale da dariya wanda tuni hakan ya wanke ɓacin ran da nake ciki. Gwaggo dake jiƙa magunguna zata bani ta juyo tana kallonmu, tana kallon Yaya da suka yi faɗa tayi ƙwafa tace,"Allah yasa su ƙara tashi suyi maka ɗan banzan dukan da zaka kasa motsawa, tunda ka zama mai ɗaurewa ƙarya gindi, wato rikicin tsufana ne yasa nace tana da aljanu ko?, saboda an faɗa maka bana ƙaunarta, to Allah yasa su bayyana yanzu su gwada maka ko ta hanyar shaƙe maka wuyana sai ka ƙaryatamu da kyau".
[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*
_By Oum Ramadhan✍🏼_
*(27)*
Gaban mirrow nake ina drying gashina, wayana maƙale a kafaɗana muna waya da Farhana, har yau bata bar fushi dani ba akan zuwan da nayi naje na dawo banje gidansu ba, bayan nace mata a gidansu zan sauka. ina dariyar masifar da take aikin yi nake bata haƙuri ina cewa ita dai ta cika mita, nace mata inan zuwa ai, taja tsaki ta kashe wayan. ban kai ga kammalawa ba wayana ya kuma ƙara, na miƙa hannu na ɗauka, sunan Proff na gani a jikin screen na yawo ta hanyar vedio calling, na cuno baki haɗe da yin ƙaramin tsaki na ajiye, na rasa me yasa kwana biyu yake takura min da kira, shima kiran dole sai yace vedio call, idan ban ɗaga ba kuma ya addabeni da message, har saina fusata na ɗaga zan masa tsiwa sai karsashin muryarsa ya hanani aiwatar da komai, ta hakan zargina akan Yayana ya ƙara yawaita, na kuma ɗora ayar tambaya akansa akan abinda zuciyata ke saƙa min a game da shi. inata mita a zuciyata kiran ya kuma shigowa a karo na kusan biyar, dai-dai da lokacin da nake ɗaure jelar gashina, garin kai hannu na katse kiran saina danna answer ba tare dana sa ni ba naci gaba da abinda nake. sai bayan dana kammala na ɗau wayan zan fita kawai naga mutum ya tallabi fuskarsa yana aikin kallona, kallonsa nayi ya sakar min murmushi yana faɗin,"gyaran gashin yayi kyau, sai ya ƙara fito da beauty nah, kin kalla kanki a madubi kuwa ko kuma kin bar min gari na faɗa?". na samu bakin gado na zauna ina zumɓura baki, nayi ƙasa da kaina ina cewa,"to wa yace ka kalle ni?". wani siririn murmushi ya saki yace,"yanzu ni har sai an bani izinin kallon Beauty? kallonki fa shine abincin idanuna". na ɗago ina kallonsa, nayi shiru bance komai ba saboda wata magana da ta haska acikin kaina, wannan furucin nasa yayi salo dana Yayana da ya taɓa cewa Kallon Cutie nah abincin idanuwana. kamar yanda Proff yay ƙuri yana kallona haka nima na ƙura masa ido, don so nake na ga aina yake a zaune, idan har naga wani abu mai kama da gidan nan to tabbas zargin Yaya da nake na shine Proff to ya tabbata, sai dai banga wani alamu na shaidan hakan ba. yace da ni, "Beauty please ki bani aron hankalinki yau muyi magana kinji". "ina jinka". nace ina daɗa haɗe fuska. "ki fito gani a ƙofar gidanku". nai saurin ɗagowa ina dubansa da mamaki,"gidanmu kuma?". yace,"kar ki ɗauka wasa, am serious". ina daɗa dubansa nace,"taya akai ka san gidanmu, ni fa ban yarda da kai ba". Yay murmushi mai sauti kamin yace,"Beauty me nayi kuma na rashin yarda, kin kalla nan". ya faɗa yana nuna min wata ƙatuwar waya dake ɗaya hannunsa. map naga yana aiki, lallaima mutumin nan wato wayo yay min kenan ya kirani ya biyo sahun kiran, kamar ya san tunanin da nake yace,"nayi miki wayo ko. kiyi haƙuri nazo ba tare da izininki ba, yanzu dai ki fito waje muyi maganan da ya kamata". nace,"ai bani nace kazo ba, don haka sai ka koma". "aikuwa to yanzu zan shigo da kaina, dama yau weekend nasan Baba na gida kinga saina sanar masa da abinda ke tafe dani". nayi zumbur na miƙe ina faɗin, "ni ban saka ba, gani nan". ƙaramin gyalena na ɗauka na yafa na fita, na ce da Gwaggo nayi baƙo ina zuwa, ta bina da kallo baki a sake wato abin ya bata mamaki, ina buɗe ƙofan parlo naji tana cewa,"wayyo ni Hannatu daɗi barni da raina, yau Sabina taga zaɓin ranta, yau zanyi kwanan farinciki, dama zuwan wannan rana nake ta jira, Allah yasa dai ku daidaita, fargabata Allah yasa kar jami'an tsaron kanki su sauya miki ra'ayi, domin nima a yanzu banda burin da ya wuce naga na kaiki gida mafi girma da daraja a wurin ƴa mace". tana ta murna take faɗin haka don harda ƴar rawarta, ni dai ban kulata ba nayi ficewata. gaban gate ɗin gidanmu kaɗan yay parking motan nasa, na ƙarasa wurin da sallama, da jikin motar na jingina sai haɗe rai nake, ni har ga Allah banso wannan zuwan nasa ba, wayana yay ringing, ina kallo naga sunansa ne, na ɗaga ina cewa,"to mene kuma na kirana bayan gani nazo, ai nasan ka ganni ka fito mana". na faɗa cike da tsiwa a lokacin dana ɗaga, da murya mai ban tausayi yace,"Beauty da ace ina da ƙafafun da zan taka, da kamin fitowanki zan iso tarbanki, ki tayani da adu'a na samu lafiya naci gaba da takawa kamar yanda nake lokacin da ina ɗan shekara uku, na rantse miki Beauty daga wannan lokacin za ki zama sarauniya ta gaske, domin ni zan zame miki bafadanki a duk wani taku na tafiya naki". gaba ɗaya sai naji wani nauyi ya kamani tare da yin da nasanin furucina, dan sosai ya bani tausayi har naji dama ban faɗa masa hakan ba, driver ne ya zagayo ya buɗe min murfin motar, na leƙa kaina ciki nace da shi, "ba zan iya shigowa ba saboda Gwaggo ta hanani shiga motan kowa, ka faɗi ko mine daga nan ina jinka". yace da driver ya fito masa da wheel chair nasa, jin hakan nace. "a'a barshi kawai, bari na shigo ɗin amma sai dai ka hanzarta". kuma nima dama na faɗa masa ne don na gwada shi, saboda in har ya damu da maganar da ta kawo shi to zai fito da ƙafafunsa, ashe dai da gaske bayada ƙafan ba wasan kwaikwayo ne yake ba, tabbas shi ɗin ba Yayana bane. bayan na zauna na ɗan dube shi kaɗan naga mood na fuskansa ya sauya, raina naji babu dadi domin nasan magana ne silar hakan, nayi ƙasa da kaina ina wasa da yatsuna nace," kayi haƙuri don Allah, nasan baka ji daɗin furucina ba". kwantar da kansa yayi a jikin kujera, hakama idonsa a lumshe suke, da raunin murya ya fara magana yana cewa. "wannan shine rashin yarda da kika yi da ni? Beauty miye ribana idan na ɗorawa kaina cutar ƙarya, don kawai na samu shiga a wurin mutane? to me na rasa? ban rasa komai ba na jin daɗin rayuwar ba, ki yarda dani Beauty wallahi babu yaudara a tare dani, dukkan abinda kike gani tare dani gaskiya ne, wannan ƙafafun da ki ke gani shekaru 27 kenan rabon da su taka, anyi maganin amma shiru, kullu yaumin a zaune suke basa iya sarrafa kansu sai da taimakon wani". yay shiru tare sauke wani nauyayyan numfashi, na goge ƙwallar dake neman sauko min nace,"Allah ya baka lafiya". har lokacin idonsa a rufe ya amsa min da amin kamin ya ɗora da cewa,"tun da nake a rayuwata ban taɓa jin wata mace ta shiga raina ba sai dana fara ganinki Beauty, duk da nasan ke ɗin kinfi ƙarfina amma ina da yaƙinin za ki iya kasancewa tare dani a cikin kowanne irin hali, domin ke din kina da zuciya mai kyau, halinki mai kyau, ko mai naki me kyau... ko da nace miki kin min sata ba satar komai nake nufi ba fa ce zuciyata da kika sace, Beauty na rantse miki labarinki yasa mahaifiyata acikin farinciki, yasa ƴan'uwana a farinciki, Daddyna kaɗai ya rage ya sanki kuma shima ina jiran dawowansa ne, Beauty shin za ki iya yimin alfarma? ki aminta dani ki zama matar aurena?". na wani ɗago a zabure ina kallonsa, da gaske ne dama sona yake? me yasa na bashi fuskar da har ya iya furtamin wannan maganar? cikin tsiwata nace,"dama wannan maganar ce ta kawo ka wurina?, dana san ita ce da ban fito na ɓata lokacina ba anan, idan kai kana sona to ni bana sonka domin ina da mijin aure". mtswwww naja tsaki na fito daga motan na wuce gida raina a ɓace, ba tare dana tsaya sauraron me yake cewa ba. abinda na gani a parlo ne ya razani, har ban san lokacin dana jefar da wayana a ƙasa ba na ruƙunƙume Gwaggo, sosai ganin Yaya ya furgita ni, idan nace muku shine Proff karku musa min, abinda ya bani mamaki taya akai ya rigani shigowa cikin gidan nan? na rumtse ido sosai jikina ya hau mazari, idan Yayana ba aljani bane to shi wane? adu'oi na shiga karantowa cikin raina ina ƙara damƙe hannun Gwaggo wadda ta zubawa sarautar Allah ido, har ina neman tasar hankalinta. gaba ɗaya su ma kuma saina basu tsoro saboda yanda nake yi, ina buɗe idona naga yana kusanto inda nake wanda shima ya cika da mamaki gami da tsoron abinda ya sameni, na shiga nuna shi da hannu ina karkaɗawa nake cewa,"karka zo inda nake, karka kusanto ni tunda kai ɗin mayaudari ne". yanda nake kamar wata wadda ta tada iska, ni kuwa tsabar baƙin cikin yaudararmu da yay shi ya tsayan a rai, lallai yayi wasa da hankalina, naji Gwaggo ta doka wani uban tsaki ta yarfar da hannuna. domin itama ta fahimci abinda ke tsakanina da Yaya, sai dai tunda ta gane soyayya muke ta nuna min bata so domin ba abune da zai ɗore ba. ta wuce tana faɗin,"aikin wofi, to da yake sonki sai akace miki da ke kaɗai zai zauna? to ko ni da kike ganina duk wannan uban kyan nawa Sahibina bai zauna dani ɗaya ba, haka ya ringizani da ɗai ɗai har ɓiyu, atoh tun wuri ma ki bar damun kanki akan ɗa namiji". wani takaicinta ya kamani, ni ga abinda ke damuna ita kuma tana wani zance na daban. Yayana yana zuwa ya damƙi kafaɗuna yana girgiza ni da tambayar mene, nayi watsi da hannayensa, kallonsa nake da takaici ina zubda hawaye, sam bama zan iya kwatanta haushinsa da nake ji ba a raina. cikin muryar da ta jiƙu da ɓacin rai nace. "a tunaninka mu kayiwa,? to ka yi babban kuskuren tunani domin kuwa kanka ka cuta, Allah ma ba zai barka ba domin kaci amanarmu, musamman ma ni kaci amanata kuma bazan yafe maka ba, mayaudari munafuki kawai". ai ban kai ga rufe baki ba tass naji an ɗauke ni da mari, ina kallonsa yake nuna kansa yana cewa,"me nayi miki da har za ki dinga dangantani da waɗanan maganganun?". cikin ƙunar rai nake kallonsa, cikin baƙin ciki da takaici na ɗaga hannu nima na yarfa masa maruka har guda biyu, domin nima a hasale nake kamar yanda yake.
na ɗaga muryar da ta karaɗe duka parlon nace,"an gaya maka ɗin, idan da kalaman da suka fi wannan you deserve them, me kake nema a rayuwarmu da ka biyo mana ta wannan siga? who are you?". wani irin kallo yake min na rashin fahimtar inda maganarki ta dosa, na cakumi kwalar rigarsa ina daɗa ɗaga siririyan muryana nake cewa,"Ka faɗa min waye kai? kuma mene dalilinka na shigowa rayuwata?". yay watsi da hannayena, shima ransa a ɓace kuma murya a ɗage yace,"na shigo rayuwarki ko kuma kika shigo da ni rayuwarki? idan ke zan miki ƙarya tunaninki zan zauna nayiwa manyan mutane ƙarya ne, wallahi inda na san nufinki wulaƙantani ne da cin zarafi ne da ban jinginu dake ba...me tasa za ki saka min da hakan a lokacin da na riga na gama sakankanewa?". na juya na kalla Gwaggo nace,"Gwaggo shi ɗin azzalumi ne kuma mayaudari, kice ya faɗa miki gaskiyar shi wane, ni ban yarda da shi ba, wallahi idan ba mugun mutum bane to aljani ne, ki tambaye shi Gwaggo kiji". kamar bada ita nayi magana ba tayi min shiru, Ya juya zai fice ransa a dagule. nac,"idan kana da gaskiya ka tsaya mana". tsayawa yay ba tare daya juyo ba, naje gaban Gwaggo ina daɗa ce mata,"Gwaggo ki tambayeshi shi ɗin wane? waya aiko shi? kuma me yazo yi mana?". tana sauya channel tace,"yo dama ki tsinci mutum a bola kiyi tunanin bil'adama ne, a wannan yafi kama da aljan". na turo baki ina mata wani duba saboda gaba ɗaya ita ɗaukan abin wasa take, na kuma ce mata,"Gwaggo ki bar batun wasa Alah shi ɗin dama na jima ina zarginsa, yau kuma na ƙara tabbatar da zargina akansa, yaudararmu kawai yake da sunan shi ɗin ba kowa bane, yana wasa da hankalinmu, Gwaggo ki kore shi kice ya bar mana gida kar ya cutar min daku". sai yanzu dai taga da gaske ne nake maganar, babu batun wasa, ta dube shi dake tsaye hannayensa zube cikin wandon aljihu kamar yanda ya saba, sai idonsa dake rumtse gam. a hankali yake magana. "Dama bada niyyar taimakona kika shigo rayuwata ba?, me kike zargi akaina da har kike min kallon macuci?". "na shiga uku". na faɗa ina ɗora hannu akaina. "Gwaggo ke faɗin ni dai daka zo gidan nan tsakani da Allah na ɗauke ka, ina jinka kuma tamkar jikina, bana taɓa banbantaka dasu Abba ba, shin Yaya maganganun da take gaskiya ne?". gabanta yazo ya durƙushe ƙafafunsa. "Gwaggo kamar