Showing 33001 words to 36000 words out of 89788 words

Chapter 12 - ALHUSSAIN Complete Hausa Novel

23 Aug 2025

382

Tambayan Littafaina kuna da yawa, kuma a haƙiƙanin gaskiya novels ɗina a yanzu idan kuka cire Sirrin Ɓoye da Al'amari Book 1 to banda documents nasu, sai dai kuje wattpad @ Oum_Ramadhan, ko kuma kuje Arewa Books ananne ma zaku sami kowanne book nawa free da paid, shi yafi sauƙi...ina godiya da soyayyarku gareni..._*
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.arewa.arewabooksapp
                 [4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(13)*
Anty ce ta fara shigowa sai Umma da ta biyo bayanta. Suka nemi wuri suka zauna, Umma ta wani karkace sai faman hure-huren hanci ta ke, ta ɗauke kai tana kallon gefe daban kamar bata ga mutane a wurin ba, sai da taji Anty ta miƙa gaisuwa ga Gwaggo kana itama ta juyo tana kumbure-kumbure ta gaidata. "lafiya". ta amsa musu babu yabo babu fallasa. Gwaggo ta miƙe ta gyara ɗaurin zanenta tukunna ta koma ta zauna, kamin ta kalla Umma ta Kalla Anty, sannan ta maida kallonta ga Baba cikin murya mai bada umarni tace. "ka sami damar yi musu bayani, yau ɗin nan nai magana da yawa na gaji". tana gama faɗa ta jefa goronta a baki tana ci. Baba ya zayyane musu kaf abinda Gwaggo tace akan zarginsu da ta ke na ciwona. Yana gama bayani Anty ta rushe da kuka kamar wadda aka yowa aiken mutuwa, faɗi ta ke. "wallahi ina ga kaf duniyar nan bayan iyayen Sabina to duk wani mai sonta ya biyo bayana domin ni zanzo a bayan Gwaggo, amma sam-sam kin gagara fahimtata Gwaggo, gani kike kamar ba ƙaunarta nake ba, kullum cikin haɗa ma ta mugun abu nake, Bayan ba haka bane, Ko abubuwan da suka faru a baya sharrin sheɗan ne, Gwaggo har yanzu kina min mummunar fahimta akan yaran nan. Yanzu fisabilillahi taya za'ai nayiwa ƙaramar yarinya turen aljanu kamar bani da ilimi". Ta ƙarasa maganar tana kuma fashewa da kukan munafurci, Sai kuma taci gaba da cewa. "tunda naga abinda ya sami yarinyar nan hankalina ya kai ƙololuwar tashi, har zuwa yanzu ban samu natsuwa ba saboda damuwar dana shiga, abinci wannan gagarata yayi ina zaune suku-suku saboda hankalina na kan Sabina da kuma hanyar da za'abi ai ma ta maganin wannan lalurar da ta sameta. Amma ƙarshe sai zargi ya shiga tsakani". hmm ni kaina ban san lokacin dana sa ki baki galala ba, lallai Anty ta ƙwarai a iya makirci, tab wannan kafce nata sai ka rantse gaske ne. Umma dake zaune a shirge tace,"to aini gaba ɗaya na rasa abun cewa, yanzu kayi magana ne abun yafi haka tsauri. Sai dai nace Allah ya kyauta ita kuma ya bata lafiya, Allah kuma yayi gaggawar bayyana gaskiya, domin ni gaskiya an shiga da hakkina. Ko wani daban bazan iya cutarwa ta hanyar masa turen aljanu ba bare Sabina da take ƴar mijina, to ni ina nasan ma hanyar wurin bokaye, ai duk rashin son da nake ma ta bana ɗora mata wannan ciwon wahalar ba, amma Allah yana ji yana kuma gani". inaaa ai Gwaggo sai ta saki Baki, hanci da idanu ta zuba musu tana kallon sarautar Allah, duban mamaki takewa Umma, kamin ta dubi Baba tace, "kaga irinta ko, idan na faɗa maka baka yarda, yanzu tunda Allah ya haɗa mu gida ɗaya ka dinga gani ai, ka kalla fa a gabanka nema ta ke tayi min rashin kunya saboda bata ganin girmana, to dama ta ina zata kalle ni da gashi ni ba Asiya(mhaifiyar Umma) ba, amma dai ko ba komai ai ni na haife ka, ta girmamani idan tana neman albarka aure, ta inda nake yabon Halima kenan, Har ta mutu kamar uwar dana tsuguna na haifeta haka ta ke girmamani, babu fitsara ko ɗaya a lamarinta, ga ƴaƴanta nan ma sun ɗebo halinta, dama hali ai tushe ne". Umma ta zumɓuri baki ta ɗauke kai, Gwaggo ta dubi Baba tace, "wai baka ji irin maganganun da ta yaɓa min bane, kana jinta fa wai Allah yana ji kuma yana gani, to me ta ke nufi da hakan? Kai kuma kaga solon namiji ba zaka iya tsawatar mata ba". Allah sarki Babana bawan Allah, cikin muryar nan tasa ta rashin son magana yace, "Hajara ki iya bakinki a wurin nan, da mahaifiyata kike magana ya kamata kisan irin furucin da za ki dinga yi". Gwaggo tai siririyar dariya, ta shiga magana ita kaɗai. "hmm wai faɗa yake yi ahaka, yana magana a hankali kamar matsoraci, ta inda nake takaicin haƙurinka kenan, Kai dai anyi dolon namiji, da ace Sulaimanu ne sai ta karɓi hukuncinta wallah". "kiyi haƙuri Gwaggo". Yace da ita, sannan ya juya gun Umma yace, "ki bata haƙuri". Tana faman ɓata rai tace, "To ni me nace, gaskiya ce kawai ba'a son mutum ya faɗa". A tsawace Baba ya katseta, "wai ke me yasa baki da mutunci ne, zaman tare kuka yi da Halima, haka kika ga ita tana yi?". Sai data ga ransa ya ɓaci sannan tace da Gwaggo, "Allah ya ba ki haƙuri". Gwaggo ta jaddada kai kamin tace,"Uhmmm, kowacce sai tayi rashin kyautawa sai su juye abin tausayi idan a gaban mijinku ne, saboda kuna tsoron takardar cika, yo wannan kiran da ace ni kaɗai ce a wurin ai sai iya abinda kuka wanke ni da shi na gani, amma ba komai Allah dai ya bani ikon gano gaskiya. Ku tashi ku tafi makirai". Umma ce ta miƙe ta fita kamar ana hankaɗata, amma Anty har lokacin tana zaune ta kifa kai da gwiwa tana kukan rashin kyautawar da akayi mata. Gwaggo tace da ita,"ke kin dawo nan ɓangaren da zama ne, mu miƙe mu baku wuri ke da mijin naki?". Anty tana goge hawayenta tace,"a'a Gwaggo Allah ya huci zuciyarki". "to kuma zaman mene kike da ba za ki tashi ki tafi ba, ba ki kalla waccen jibgagar mai jiran kaɗan ita har ta kwashi ƙafafuwanta ta tafi ba. ko kuma kina jiran kiji me nake tattaunawa tsakanina da ɗana ne, tsakani da Allah wannan ma ai raini ne". Anty ta nemi rufin asirin Allah tace,"Gwaggo ba haka bane, kawai dai ba zan iya tafiya bane ba tare da zargin da kike akaina ya goge daga zuciyarki ba. Ko dana miƙe ƙafafuna ba zasu iya ɗaukata ba, ko kaɗan bana ƙaunar fushinki". Shi dai Baba yayi shiru kallo kawai yake. Gwaggo ta taɓe baki, ta kau da kai gefe tana cewa da Baba, "kacewa Matarka ta ɓace min anan". "Zahra'u tashi kije". Yace da ita ba tare daya kalleta ba. Kamar munafuka Anty ta miƙe ta fice. tana fita kuma Gwaggo ta ɗauka da cewa,"ko kunnuwa duka jikina bazan taɓa yarda da waɗannan makiran matan naka ba. Sarai nasan wata acikinsu tai wannan aikin, Mugwayen banza insha'Allahu duk wani sharri sai ya koma kansu, ai kaf na gama karantar zuciyoyinsu". Baba ya numfasa yace, "haba Gwaggo ki bar wannan maganar, Zarginsu ne fa kawai kike, kuma zato zunubi ko da ya kasance gaskiya". "to Auwalu tunasar da ni hadisin dana manta, kai gaka mai Mata wato na taɓa Matanka shine zaka ɓata rai. To ni dai wallahi duk wanda ma yay silar cutuwar Jikata bazan yafe masa ba". tasa gefen ɗan kwalinta tana sharar ƙwalla,"Auwalu har mutuwata bana tunanin zan kuma son Matanka, sai dai kayita jin haushina, yanda basu da kyan gani haka zuciyoyinsu basu da kyau, yo akan mene zan so su, ina zaman dole ne da su kawai saboda Allah ya ƙadarta rabo a tsakaninku, amma da kowacce sai ka bata jan kati. Har yanzu bana manta baƙin sharrin da kowacce tayiwa marayun ƴaƴan nan, waccan shirgegiyar mara kyan fasali tace Sabina tayi mata sata, ita kuma Ƴar-wadar can tace Abba ya shigar mata ɗaki, ko me zaiyi da waɗannan zubabbun nonuwan nata oho, kai kuma ka hau ka zauna akan maganarsu saboda kana tsoronsu, kaci zarafin Yaranan, to ta ina kuwa kaima zan daina jin haushinka, da wani ƙaton kanka tun na haihuwa". Baba ya ɗago yana duban mahaifiyar tasa da ta ke ta matsar ƙwalla, yana mai takaicin abinda ya aikata mana a baya yace, "kiyi Haƙuri Gwaggo, ni kaina nasan nayi kuskure amma na tuba". ta galla masa harara tace, "ka riƙe haƙurinka kai zai yiwa amfani. Na gama maganar da zanyi da kai, sai ka tashi ka tafi kaje can ka ƙarata kaima". Ganin Baba yaƙi tafiya ita ta tashi tana cewa da ni, "ke tashi mu wuce". Ta juya ta kalla Baba tace, "idan ka ƙaraci zaman naka sai ka kashe min tv da fitilu, kuma ka rufe min ƙofa". Ni dai yanda naga jikin Baba yay sanyi sai na kasa tashi, jira nake Gwaggo ta wuce na samu zantawa da shi, har tayi gaba sai ta juyo tana dubana tace, "aufa na taɓa ubanki shine za ki nuna min matsayina ko, ina magana kinyi banza dani ga susu na magana, yo acikin abinda na faɗa ƙarya nayi masa ne, ba watsi yayi da ku ba akan matansa, kamar marasa gata haka ya watso ku waje, shine yanzu dan nayi magana za ki ɗaura gaba da ni". ina kallon gefenta nace, "ni fa ba wani abin kika ji nace ba Gwaggo. to ma dai ina ce mun yafe masa abinda yay mana, ba sai ki bar tuna bayan ba, tunda ba shi da laifi amma da an fara zance sai kice yay kaza-kaza, tsakani da Allah bama jin daɗi ki daina". tsawatar min Baba yayi, hakan yasa nayi shiru ina goge hawayena. ita kuma ta ɗora faɗanta, "da ka barta taci gaba ai, itama aljanun nema suke su koya mata fitsara, bakaga tana yi kamar zata watsa ni gefe ba, kuma fa wannan ba halinta ba ne, amma yanzu tana neman koyar mummunar ɗabi'a irin ta Abba, ni tsoro na ma kar naje cikin dare su tashi su rufe ni da duka, gashi mu biyu ne kawai ban san ya zanyi ba, ita Allah ya jarabce ni da sonta ba iya barinta ita zanyi ta kwana ita ɗaya ba a cikin wannan halin ba, yanzu dole dai a san abin yi". Ni kam fashewa nayi da kuka, na kifa kai da gwiwa, har ga Allah bana so naji tana ambatar min aljanu, yanzu nai magana ta kuma cewa nayi mata rashin kunya shi kuma Baba ya rufe ni da faɗa. Baba yace, "to Gwaggo ko yaran zan tado daga ɓangaren su, sai suzo nan su tayaku kwana". da saurin baki tace da shi,"su wa ka ke nufi kenan?". "su Aisha". Yace da ita. Da sauri Gwaggo tace, "a'a rufa min asiri, waɗannan ai da gayya zasu tashi su illata ni, kai baka san yanda suke jin haushi na ba musamman ma Aisha, dan kawai ina fifita Sabina akan su, to su akan mene zan so su bayan basu ɗauko halin ƙwarai ba. kaga in baka labari, Ɗazu fa yarinyar nan Amina kaɗan ya rage ta rufe ni da duka, saboda ta kawo abinci nace ta mayar da shi ba zamu ci ba, kuma fa ba walaƙanci ne yasa nace ta mayar ba, abincin nan nasu barbaɗe suke masa yana sani cikin wani hali, baka ji yanda suka tugunzuma masa yaji ba kuma sarai sun san bana so, abinci ya koma kamar na mayu, jiya kwana nayi ban runtsa ba ina fama da ciwon ciki, faɗa maka ne kawai ban ba gudun kar ranka ya ɓaci, amma har yanzu gani nan ban wartsake ba. Shi yasa ma nace zan faɗa maka wannan haɗakar girgin namu kawai a barshi bazan iya ba, haka kawai ina zaman-zama na lafiya lau a dinga ɗora min lalura". ran Baba a ɓace yace, "wace tayi abincin?". "wannan bunkusar matar taka mana, itama ɗayar shekaranjiya da ta kawo nata maggi bai ji ba. Abba kansa kasa ci yayi sai wani ya dafa, ni dama ba kaina nake ji ba, marayun Ƴaƴan nan da basu da uwa nake tausayawa, su na lura basa tsoron shiga hakkin maraya, to ita dai mutuwar nan na kan kowa. Wallahi raina yana ɓaci matuƙa idan naga irin walaƙancin da sukewa ƴaƴan nan, kai kuma baka ɗaukan mataki, yanzu idan na mutu ya zasu yi, shi yasa nake roƙon Allah ya kawowa Sabina mijin ƙwarai kamin wucewa ta". Ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka sosai, kukan da duk sai daya taɓa zuciyoyinmu. Tausayinta ya kamamu duka, lallashinta muka shiga yi har tayi shiru. sannan tace da Baba ya tashi ya tafi dare yayi, Baba ya miƙe yay mana sai da safe sannan ya fita. Ranar dai ban kwana a ɗakina ba, saboda Gwaggo cewa tayi bata yarda ba, bata san me zai iya faruwa ba cikin dare, haka dole na bita ɗakinta, har kuka sai dana yi dalilin hayaƙin da ta saka min, ita wai so ta ke su barni tun abun bai yi tsamari sosai ba, ganin zan cutu na miƙe zan bar ɗakin da gudu, ta damƙo ni dalilin harɗewar da nayi. Hawaye na sakko min nace, "Gwaggo don girman Allah ki ƙyale ni, wannan hayaƙin fa yana cutarwa". "ke dallacan rufen baki, ɗazu da baki hayyacinki da Haidar ya banka miki ai ba ki ce komai ba". "to amma yanzu ai lafiyata ƙalau. Allah likitoci na bayani sosai aka shaƙar hayaƙi". ta taɓe baki, Bata tankani ba ta lakuto wani mai a cikin kwalba ta shiga mulka min, gaba ɗaya warinsa babu daɗi, hannunta nake turewa tasa hannu ta make ni taci gaba da aikinta. Bata ƙyaleni ba sai dana sha maganin islamic kusan nawa, sannan ta barni. sai bayan da muka kwanta kuma ta ke min maganar cewar. "ni Hannatu yanzu nazo na kori Haidar da shigowa ɓangarena, idan aka sami matsala ko me zanyi dan ya kawo agaji ba zuwa zaiyi ba saboda akwaishi da ƴar banzar zuciya, lamarinsa yafi kama dana mahaukata, ba zai gane a ɓacin raine yasa nayi masa haka ba don ya kiyaye gaba ya gyara, to Allah dai ya rufa asiri". Ni dai ina jinta bance mata komai ba, har bacci ya fara ɗaukata naji tana tambayana. "yauwa ke ɗazu ice ko a iya tsotse miki baki Haidar ya tsaya?". Nayi kamar ba zan ansa mata ba, sai ta miƙe zaune tace, "idonki fa biyu kuma nasan kinji me nace". Ina turɓune fuska kamar tana gani na nace, "ehhh, bayan shi bai yi min komai ba". "to gwara da Allah ya tsayar a haka. Kuma dai kina jina da faɗan dana saba yi miki kullum, ki kiyayi ɗa namiji a duk inda yake, Shi iskancinsa ado ne, kina gani dai ɗazu a gabana saboda bashi da mutunci bashi da kunya ya nemi ya kuma maimaita miki, to babu ruwanki da shi tunda mummunan halinsa ya fito fili, kinga ke dai ba halinki bane rashin kunya, karki ce za ki soma, Duk abinda yayi miki ki kawo min ƙararsa ni zanji da shi, kina dai jin me yace idan kika kuma masa rashin kunya abinda yafi haka zaiyi miki, to yana nufin ciki zai ɗirka miki don haka ki kiyaye wallahi, kuma ni fita zanyi a sha'aninki nama bar muku gidan, atoh ni gaskiya nake faɗa miki, ɗan uwanki ne ban isa na raba zumuncinku ba amma dai ki san irin mu'amalar da za ki dinga yi da shi". Na rungumeta ta baya ina kuka nace mata, "ai makamancin hakan ma ba zai kuma faruwa ba, tunda na lura rashin kunya ce baya so ba ruwana da shi, ina tare dake har abada Gwaggo ba za ki taɓa tafiya ki barni ba". Na ƙara ƙanƙameta tsam a haka har muka yi bacci.

*** Ɓangaren Alhaji Auwal kam tunda ya koma yakewa Munubiya faɗan yajin da ta saka a abinci, ya kuma ce kar a ƙara girki da yaji, kowa ya haƙura da cin yajin, ai sun san mahaifiyarsa bata so saboda rashin adalci suka tashi suka saka. aikuwa maganar tasa ta tada balli, nan da nan ta kawo wuya ta miƙe ta kama masifa. "haba Baban Alhaji, kowa fa acikin gidan nan da nasa ra'ayin. Ita da bata ci ta dafa nata mana, ko kuma ta saka wannan yarinyar ta dafa mata tunda ita girkin ne ta ke jin ƙyashin yi, kowa ba ɓangarensa daban ba, to da wama yake dafa musu, ni wallahi ba za'a takurani ba, abinda nake so shi zanyi, dan haka banga dalilin da zaisa ace dan wata bata son yaji ba nima ba zanci abinci da yaji ba". shima cikin hargowa yace da ita, "to shikenan kiyi son ran naki, ni kuma kiga yanda zanyi dake, kuma dole a duk sanda aka yi girki a kaiwa mahaifiyata...kuma in har kina ƙaunar Allah karki fasa girka mata abinci da yaji kiga yanda zamu kwashe dake acikin gidan nan". Ko haƙuri bata bashi ba, yana gama faɗan ta tashi ta bar masa wajen yaci kansa, itama ba cin yajin ta ke ba saboda Gwaggon ne dama ta saka, to kuwa duk bala'in da za'ai indai girki da ita ne ba zata fasa sanyawa ba.


*Please Vote and Comment and Share.*
[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(12)*
Buguwar da nayi da goshin Yaya Haidar ashe ba ƙarama bace, dama ga kansa kaftarere, sosai kaina ya shiga juyawa nai sauri na dafe bango ina ganin wasu abubuwa na wucewa a duhun idona, na ɗaga ƙafana zan ɗora saman steps sai idona ya rufe gaba ɗaya, nayi baya zan faɗi sai gani na faɗo a hannun Yaya Haidar, caraf ya cafeni kamar wata ƴar Baby, to ni kam tunda na buɗe ido na kalle shi dishi-dishi na mayar da murfin idona ban kuma sanin inda kaina yake ba, sai dai kamar na jiyo salatin Gwaggo. Shuɗewar wasu awanni na farka, na ganni shimfiɗe a ƙirjinsa Ya kewaye ni da hannayensa, kuma a cikin ɗakinsa, na rufe idona yafi sau ƙirgen hannu ina kuma buɗewa don tabbatar da abinda nake gani, ni ce dai a tsakankanin cinyarsa kuma kwance bisa ƙirjinsa, bacci yake ko mene oho, idonsa dai a rufe yake, da sauri kuwa na miƙe daga jikin nasa a zabure na dira ƙasa daga kan gadonsa, domin zuwa wannan lokacin dukkan wani tashin hankali ya gama bayyana a zuciyata da gangar jikina. Duk tsoro ya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login