Showing 63001 words to 66000 words out of 89788 words

Chapter 22 - ALHUSSAIN Complete Hausa Novel

23 Aug 2025

399

neme ni. ba haka kawai na daina zuwa inda kake ba, mun koma Abuja da zama ne sai yau na sami daman zuwa, kuma na bar niƙab ɗina a can shisa, ita kuma Hajiya bata da shi bare na amsa na saka. Yayana tunda na tafi kowanne rana a cikin tunanin halin da kake nake, haka zalika a cikin kowanne daƙiƙa na bugawan agogo jiran tsammanin kiran wayarka nake amma shiru. Yayana ina ka tafi a wancan lokaci? Me yasa na dawo na sameka a wannan halin?". idonsa na kallon gefe guda yace,"abubuwan da yawa...na farko anyiwa wata yarinya fyaɗe hr ta mutu shine aka ɗora alhakin hakan akaina, na jima kamin gaskiya ta bayyana, ashe Baban Yarinyar yana harkar ƙwayoyi sai suka sami matsala da yaransa shine suka ɗau fansar abunda yay musu akan yarinyar. bayan na fito da ƴan kwanaki aka sace yara anan anguwar, mutane suka ɗora min laifin da banji ba ban gani ba akan cewan ni na sacesu, bisa wannan zargin nasu yasa ƴan sanda suka kamani, nasha wuya sosai a wurinsu har naji inama na mutu na bar wannan rayuwar ƙuncin, a ranar da zamu wuce kotu ranar akaga yaran, sati ɗaya kenan da aka sakeni, na dawo duk inda naje na zauna domin samun mafaka sai an koreni, babu wanda ya tsauyawa halin buƙatar taimakon da nake ciki sai limamin wannan masallacin, shine ya kaini chemist aka bani kulawa". Tunda ya fara maganar nake kuka sosai, har ta kai ga na daina sauraron abinda yake cewa, hannu yasa ya dafa goshina ya ɗago fuskata da tayi shaɓe-shaɓe da ruwan hawaye. Ina kallo ya yagi ƙasan rigarsa yay min tsumman goge hawayena "kina so a kuma kamani ne?". Ya faɗa a yayin da yake gogen gefen idona wanda nake tunanin kwalli ne ya zazzago. Na shiga girgiza masa kai da sauri alamar a'a. "to ki bar kuka, kar mutane su ganki ace nayi miki wani abun, a ƙara kamani ayi min ɗaurin rai da rai". Babu shiri na tsayar da kukana, ina faɗin,"wallahi ba zan taɓa yafewa wanda yay maka wannan sharrin ba, wallahi ba zan taɓa yafewa wanda ya wahalar da kai ba, Allah ya bi maka hakkinka. Me yasa daka dawo baka kirani ba?". "ta ina zan kiraki?". "nafa aje maka letter da zan tafi, na san kuma har zuwa lokacin yana nan tunda babu wanda ke shiga sai kai, kuma nayi yanda ko da iska ba zai iya figansa ba bare ruwa ya lalata shi". Yay wani murmushi mai ciwo, damuwa na daɗa bayyana a tare da shi. "tunda na sanyo ƙafata cikin anguwar nan ake min ruwan duwatsu akan saina koma, da ƙyar wasu bayin Allah suka taimakeni. Ba daban ina da yaƙinin idanuwana zasu ƙara ganinki ba, da ba ki zo kin kuma samuna anan ba". Hannunsa dake cikin nawa ya daɗa matsewa ya damƙe, idanunsa a runtse ya shiga juyi da kansa yana faɗin. "tunda suka kamani, tunda suka sanya ƙafafuna a sasari, tunda suka jefani a ɗakin duhu, a kowanne bugun azabtarwa, a kowanne nau'in horo mai wahala, a duk wani bugu na zuciyata kece a raina, bana jin daɗin duniyar, har saina rufe idona na hasko ki aciki sannan nake samun sassauci. Don Allah kice min kina da alaƙa da ni, ki ce ke ɗin jinina ce, ki ce kin shigo rayuwata ne domin ki share min hawayena". Ya gama faɗin hakan yana mai jinginar da kansa jikin bishiya, ya kuma ƙara damƙe hannuna wanda har sai da jikina ya amsa, yana ƙara rumtse idonsa sosai. Nace da shi,"Yayana ba zan iya barinka a wannan halin ba, yau ɗin nazo tafiya da kai ne. Ba zan kuma barinka a cikin ƙangin rayuwa ba...daga yau insha'Allahu ka bar wannan gararin, dan zanyi maka gata a yayin da zan sanyaka cikin ahalina, zan tabbata ƙanwa a gareka a yayin da zaka tabbata Yaya a gareni ka kuma tabbata ɗa a wurin Babana, a inda zaka tabbata jika a wurin Gwaggona. Insha'Allahu lokacin yayewar baƙin cikinka yayi, haka kuma lokacin dawwamarka a farinciki yayi, ba zan kuma bari ka shiga damuwa ba har abada". Sai yanzu ne ya buɗe kyawawan idanunsa ya zuba su a cikin nawa. Ido cikin ido muke kallon juna, har sai da kwarjininsa ya kashe min ido tukunna nayi saurin kawar da idanuwana daga kallonsa. Na miƙe ina jan hannunsa akan ya tashi mu tafi. murya a ƙasan maƙoshi yace,"nan shi yafi dacewa da ni, idan kika tafi da ni ina za ki kaini?". "nan ba shine ya dace da kai ba. Kyakykyawan mazauni shi ya dace da kai, kaifa mutumin kirki ne, don girman Allah Yaya ka tashi mu tafi gidanmu, na rantse maka idan bamu tafi tare ba, ba zan bar cikin layin nan ba zakaji saƙon mutuwata, na tafi inda ba zaka kuma ganina ba sai a aljannah". Zumbur naga ya miƙe, ina riƙe da hannunsa muke tafiya kaman wani yarona, wanda nayi hakanne gudun kar ya tsere min, har sai da muka fito bakin layi na tari me napep kana na sake shi lokacin da muka shiga ciki. Muna tafe ina tunanin yanda zanyi da Yayana, Hajiya ba zata taɓa fuskantar wani zance da zan mata ba, don haka ya zame min dole na koma gida a yau. Na ɗauko waya na kira Baba yana ɗagawa nace,"Baba kana so na?". "Sabina babu sallama babu gaisuwa sai tambayar dake kin san amsarta". Na lumshe ido ina ƙara narke fuska nace,"Baba ni dai ka amsa min". Murmushi mai sauti yayi yace, "ina sonki sosai Sabina, duk cikin ƴaƴana bayan Abba nafi sonki na kuma fi ji dake". Maganan Babana yay min daɗi, na ƙara ce masa,"to Baba indai da gaske kana sona kayi min buking jirgi yanzu, zuwa anjima zan dawo gida". "ki dawo kuma? Wani abu ya faru ne?". Nace da shi,"a'a Baba babu abinda ya faru, kawai zan dawo ne na gaji da zaman". "a'a ban yarda dake ba ki dai faɗa min gaskiya, ko Hajiya tayi miki wani abu ne?". "ko ɗaya Baba, mun gama gaisawa da Hajiya kuma dama ai ita nazo gani, don Allah Baba ni dai a biya min kuɗin jirgi yanzu kujeran mutum biyu, yau nake son dawowa". "tom shikenan, Allah ya dawo min dake lapia". Kai tsaye wani private hospital muka wuce, ƙwararren likita na nema, aka ƙara treating ciwukan Yayana sosai, dan sai da aka sauya masa bandage, aka kuma lodo mana magunguna kamar me, banda allurorin daya sha. Bayan fitowanmu muka nufi resturant, ordering lafiyayyan abinci na sa aka mani wanda nasan Yayana zai san ehh yaci abincin daya amsa sunansa abinci. Gaba ya saka abinci ya kasa ci sai ido daya ƙura min, dana kalla baida niyyan ci na ɗauka spoon na kai bakinsa ina cewa, "oya haaa". Bai buɗe bakin ba sai neman sauke hannuna da yayi. Na ɗan tsuke fuska nace, "Yayana zafa kasha magani naka ne, ko baka so ciwonka ya warke da wuri?, to idan kai baka so ni ina so, plsss kaci abinci idan ba so kake nasa maka kuka ba ka rasa yanda zaka yi da ni, yanzu mutane suzo su tafi da kai a kuma sanyaka a cell". Na faɗi hakan ina kuma kai abincin bakinsa, ya dafa hannuna yana tayani kai cokalin bakinsa, haka naita bashi abincin har sai dana tabbata ya ƙoshi kana na ƙyale shi, na sauke kaina ƙasa ina ɓallo magani cike da jin nauyin kallon da yake min, na bashi magungunan duk daya dace yasha yanzu, sannan muka bar wurin muka wuce wani boutique na kayan maza. Kayan maza nake ta ɗauka sama da kala nawa, duka ƴan kanti ne kowanne haɗe da takalminsa, duk wanda na ɗauka saina kara ajikinsa don tabbatar da cewan zai masa, kuma duk wanda zan gwada mashi sai ya dace da shi, hakan yasa na ƙara jin ƙananan kaya sun kuma shiga raina, domin ni ina son naga namiji nasa ƙanan kaya amma na mutumci. Shi dai bina da ido kawai yake har na kammala na kuma riƙo hannunsa muka fito, kansa na kalla wanda gashinsa ke buƙatar aski, amma saboda ciwon dake goshinsa babu damar yi. Ina kallon Hajiya nata kirana naƙi ɗagawa, na kuma taran mota muka wuce kasuwan kwari, nan ma manyan shaddojiji na saya, yadi da boyel da huluna. Muna fitowa daga kasuwan naga kiran Baba, ina ɗagawa yace da ni yasa abokinsa ya kammala komai, bakwai na dare jirgi zai tashi, ina murna nayi masa godiya, dama cikin tunanin inda zamu wuce yanzu nake. Ko rabin awa bamu yi ba a airpot jirginmu ya tashi, cikin ƙanƙanen lokaci sai gamu mun sauka a abuja, minti biyu da isowanmu Yaya Abba yazo ɗaukana. Sai yanzu ƙirjina ya hau bugu, to waima mene zance idan na kai masu shi? ta ina zan fara bayani? lallai fa nayi wawta da yawa, ko Gwaggo da nake sa ran zata fahimce ni to zan sha gwagwarmaya kamin ta aminta da buƙatar da zani da ita. Tsaye nayi na kasa ƙarasawa gaban motar, na ɗago na kalla Yayana, hannunsa da nake riƙe da shi na saki, maganganun bakina na neman rasasu nake. "Karfa naja maki matsala a gida". Nace, "babu wani matsala ka jirani anan bari na dawo". ko dana isa wurin Yaya Abba da ƙyar nasha kansa ya fahimceni, shima don yana da tausayi ne kuma mutum ne mai son yin taimako, ba komai na faɗa masa ba, hasalima ce masa nayi a yaune na fara ganinsa. Baya Yayana ya shiga ni kuma na shiga gaba, su kaima juna musabaha, naji daɗin hakan, muna shiga gida muka tarar da Yaya Haidar shima ya dawo, kallo kawai ya bimu da shi ya amsa key ɗin part nasu wurin Yaya Abba ya wuce. Na kalla Yaya Abba nace masa, "ga wannan kayan na saya masa, ka ajiye a wurinka kamin Allah yasa muji amincewan su Baba". Ya amsa ya wuce ciki bayan yacewa Yayana yaji tsoron Allah ya faɗi asalin tarihin rayuwarsa karya ɓoye komai. A parlo nayi masa masauki, na wuce ɗakin Gwaggo domin kiranta, sai na tarar bata nan, na fito zan duba kitchen saina kalleta tsaye tayi turus tana kallon Yayana dake zaune kan kujera kansa na ƙasa baima san da zuwan nata ba. Zuwa nayi na rungumeta tare da fashewa da kuka, nan ta ke hankalinta ya tashi maganar dake bakinta ta mutu. A ruɗe ta hau tambayana mene ya faru, ni dai shiru na mata ina ci gaba da kukana, sai da ta tsawatar min kana na ɗago ina kama hannayenta na shiga roƙonta. "Gwaggo nah kene kika ce min duk wanda ya taimaki wani shima Allah zai taimake shi, kika ce mana mu taimakin mutumin da yake cikin tsaka mai wuya domin Allah yana son masu taimako...". "ke ni naji duk, ban son kuma wani bayanin, idan har ba za ki mani shiru da wannan kukan naki ba, kukan zan saurara ko kuma bayanin". Nai shiru ina goge fuskana. Tace, "to mene dama?". Na kama hannunta zuwa kujera ta zauna ni kuma na durƙusa a gabanta nace. "Gwaggo baya da gatan kowa sai na Allah, ko iyayensa bai taɓa sa ni ba, shine wanda na ba ki labari kika ce na fita sha'aninsa ko ki saɓa min, wallahi wallahi Gwaggo ki yarda dani shi ɗin mutumin kirki ne, jarrabar rayuwa ce ta jefa shi cikin wannan mummunar rayuwar ta shaye-shaye, Sai dai nasan ba za ki taɓa yarda dani ba sai idan kinji daga bakinsa, don Allah Gwaggo kiji tausayinsa ki taimaka masa kamar yanda muma Allah ya taimakemu ya daɗa rufa mana asiri, ina so naga ya fita daga wannan halin kuma kema nasan za ki so hakan". ta sauke ajiyar zuciya, ta kalle shi wanda tuni ya sauko daga kan kujera ya durƙusa a ƙasa. "tashi ka koma ka zauna". tace da shi tana dubansa da tausayawa, don jikinta yay sanyi da kallon yanayinsa da tayi. ta kalle ni tace, "Sabina ba wai ina ƙin ta taki bane, a'a ina tsoron yanda halin wannan rayuwar ta koma. za ki kalla mutum abin tausayi har kiyi masa kuka ki taimaka masa amma ƙarshe yazo ya cuceka, yaci amanarka, kuma kinga ke macece ina tsoron abinda zaije ya biyo baya, ba kowa ne kake yarda da shi ba yanzu. Kar muzo mu taimake shi yaci amanarmu daga baya". Sannan ta kalle shi tace, "bawan Allah tsakanin ka da Allah har zuciyarka baka da wata mummunar manufa, baka da wani ƙuduri na cutar da wannan yarinya dake tausayinka?". "Gwaggo zuciyata tsarkakkiya ce, bani da fatan cutar da wani a rayuwata". "to shikenan Allah yasa da gaske kake, ina son dukkan abinda Sabina ke so, dan haka zamu taimaka maka da iya abinda ta buƙata, sai dai bazan fasa ce maka kaji tsoron Allah ba. Bari mahaifinta yazo". "na gode Gwaggo Allah ya saka da alkhairi". Wayyo Allah nah wani sanyin daɗi naji ya baibaye ni. tace da ni, "kinje kin gudo ko. Bamu jima da gama waya da Hajiya ba tace za ki sani karki kuma zuwar mata gida. Kuma kayanki bayar da su zata yi, karta soma ganin koɗaɗɗiyar ƙafarki da sunan ɗaukan kaya". Dariya kawai nayi bance komai ba, tace naje na zubowa Yayana abinci, na miƙe naje na kawo masa abin sanyawa a baki, ina duƙawa zan aje masa yace,"na gode amma ki koma da shi, a ƙoshe nake da wanda kika ciyar dani ɗazu". Zuwan Baba Gwaggo ta zayyane masa komai. Baba ya numfasa yace da shi, "bawan Allah ka duba girman Allah ka faɗa mana wane kai". Ina kallon Yayana yay saurin rufe ido, kuma da alama tambayar ta Baba ta jefasa a wani yanayi na baƙinciki, ya buɗi baki muryar na fita da ainihin damuwar dake ransa yace,"wanene ni? Da ace nasan wanene ni da ban kasance a cikin wannan rayuwar ba, wallahi Baba ban san asalina ba. Abinda kawai na sa ni shine na taso a hannun wasu bayin Allah har na tsawon shekara biyu, suma kuma sun tsince ni ne a bola lokacin ba zan wuce shekaru huɗu ba a duniya a cewarsu. Amma mene asalina? daga ina nake? wanne gari? mene asalin sunana dana iyayena? ina zan bi in neme su? ina zan dosa? duk ban sa ni ba. Wallah summa tallahi bani da masaniyar komai a ga me da tarihin rayuwata". Ya faɗi hakan yana kuka. Baba Yace, "to su ina waɗanda suka tsinceka ɗin?". "sun gaji da riƙona shi yasa suka koreni daga garesu saboda mutane na zargin cewar ƴarsu ce tayi cikin shege. tun ban gama wayo ba nake yawo kwararo², idan na samu abinci naci idan ban samu ba hakan zan kwana da yunwa, banda matsuguni da makwanci sai kanguna, sai dai ina zuwa makarantar almajirai a duk garin dana tsinci kaina a haka har nayi sauka, sai dai duk inda na shiga jama'a ƙyamata suke suna hantarata. sigari na fara shanta ne saboda samun sauƙin abunda ke damuna, amma ni ɗin ba mutumin banza ba ne". Yanzu na ƙara jin tausayinsa ya kamani, su Gwaggo ma hakan take a gare su, Baba yace,"haƙiƙa duk wanda yaji labarinka dole ya taimaka maka in har yana da damar hakan. To ka kwantar da hankalinka, munyi maka alƙawarin zamu taimake ka mu share maka hawaye ka fita daga rayuwar ƙuncin da kake ciki, zan kuma maidaka tamkar ɗan dana haifa da cikina. Ina fatan ba zaka taɓa cin amanarmu ba". Furucin Baba ya sa ni shauƙi a ruhina ba kaɗan ba, ta yanda fuskata ta gaza ɓoye farincikin da nake ciki. "Allah yay miki albarka Sabina, lallai ke ɗin kina zuciya mai kyau tunda har kika yi tunanin taimako irin haka, tabbas nayi dacen ƴa ta gari. Kina da halin kirki da mutunci kamar mahaifiyarki". nayi ƙasa da kaina ina wasa da yatsun ƙafata ina jin daɗin adu'ar Baba da kuma yabona. Yayana na zubar hawaye yake yiwa Baba godiya, nima kuma yake ƙara gode min. Da wannan ya samu kyakykyawan matsuguni a cikin gidanmu, kamar yanda aka bawa Yaya Abba part nasa haka shima aka mallaka masa nasa part ɗin wanda dama shi ɗaya ne ya rage a gidan, da har su Umma na zargin Baba da munafurtarsu yake aure ne zai ƙara, to yanzu da aka bashi sai hankalinsu ya kwanta. Kowa na gidanmu Yaya yake ce masa har Baba da Gwaggo, kuma naci sa'ar ƙannena akansa. Sun zama kamar tagwaye shi da Yaya Abba, kuma duk sanda Baba zai fita office da shi yake fita, haka duk saturday and sunday yana zuwa makaranta mai suna Comprehensive collage, har mota Baba ya bashi, haka ma duk dare su kanyi zaman karatu shi da Yaya Abba don babu girman kai a tare da shi. Bayan kwana biyu na fito ɗauke da flask ɗin abinci zan kaima Yayana ɗakinsa, Ina shiga parlonsa na lumshe idanuwana ina shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren dake tashi aciki, na lura Yayana dai ma'abocin son ƙamshi ne. Kamin na kai ga gama shaƙar ƙamshin tuni wani mugun warin taba ya dakar min hanci, nayi saurin buɗe idona nasa hannu ina toshe hancina dan ƙiris na kwara amai. Raina a ɓace na wuce cikin ɗakinsa, zaune na hangeshi daga can ƙuryan gado yana zuƙar abarsa hankali kwance. idan da abinda ke sa zuciyata ɗaci na tsince shi a irin wannan yanayi, nafi minti biyu tsaye ina masa wani duba, baima san da zuwan nawa ba, zuciyata naji tayi zafi. plastic chair na ɗauka naje gabansa na ajiye, sannan na ɗauko kwalin sigarin daya ajiye saman table na ɗauka guda biyu, tukunna na dawo kan kujeran na zauna, ƙafa na ɗora ɗaya kan ɗaya ina girgizawa, ashana na kunnawa sigarin, duk wannan abin da nake ina kallonsa ta gefen ido yana kallona, irin kallon kissima abubuwa da dama a rai. Zuciyata na lugude na rufe idona na kai sigarin bakina ina ƙoƙarin zuƙa, da mugun hanzari ya miƙe daga zaunen da yake ya warceta a hannuna. tsawa ya doka min wadda tasa ni firgita, yana huci yake cewa, "ke ba ki da hankali ne, kinsan me

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login