Showing 42001 words to 45000 words out of 89788 words
masa kar ya kuma zuwar min sashena bane". "to dai ai gashi can yana kallo". Ta juya ta nufa inda yake, tana zuwa ta ƙarasa gaban socket ta kashe tv ɗin da yake kallon news ɗin da bai gajiya, ni nama rasa uwar me yake ji da news ko da yaushe, yana ganinta baice mata komai ba haka itama bata kula shi ba. Sannan ta kirani, ina zuwa tace, "kashe min wannan na'urar sanyin". Na jawo ƙaramin table na ƙara tsayi na kashe. Ita kuma ta ƙarasa taje ta janye table ɗin da ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, ƙafafunsa suka zube a ƙasa, ina kallon yanda ya cika yay fam ƙiris yake jira ya fashe, nasa hannu na toshe dariyar dake ƙoƙarin fitowa, tasa hannu a aljihun gaban rigarsa ta ciro handkerchf nasa sai tashin ƙamshi yake, ta shiga goge table ɗin daya ɗora ƙafafun nasa tana ta magana kamar bada shi take ba. "Haka kawai a dinga shigo maka wuri da sanyin safiya ko tashi baka yi ba ana takura maka. kuma ba taya aikin fari bare na baƙi, sai dai a hakimce a ware maka na'urar sanyi a kunna maka tv ana sauraren yaren da kai ba jinsa kake ba. Kuma Duk abi a zuba maka dattin ƙafa akan glass, ka yiwa mutum magana ya daina zuwar maka wuri amma saboda ba shida zuciya zuwa yaƙi ya daina, dole dai sai an saka magana, to na kashe kayayyakina kar na soma naji an ƙara kunna min kayan kallo". Maganar ta ke kamar bada shi ta ke ba, tana gamawa ta wurga masa hanky nasa. Ina dariya ƙasa-ƙasa naje kusa da shi na ɗauka mayafina da jaka ina cewa. "Gwaggo zan tafi, ai mana adu'a Allah yasa mu shiga a sa'a". "to kin ƙoshi ne? ko za ki sha shayi ga saura naji a cikin butar nan, ƙila wannan yaron ne ya dafa". Na kalla Yaya Haidar naga ya ɗago yay mata wani kallo, ran nan nasa a haɗe, kawai dan na makara ne amma ko dan na ƙara ƙular da shi da sai na sha, na cije Leɓena ina dariya nace. "a'a Gwaggo bana sha, na ƙoshi ai". "to shikenan yana da kyau na tambayeki ne. Saboda ni ba sha zanyi ba ƙarshe zubar da shi zanyi. ban san ma wane shishshigi ne yasa aka zo aka wani yimin girki a kitchen ba tun gari bai washe ba, kamar ka saka mutum, a dai dinga jin tsoron Allah almubazzaranci babu kyau. kuma wani abin dariya da takaicin kai ɗin dai da aka raina duk tsiya wurinka ake zuwa". ni dai kamar kar na tafi haka nake ji, idan kuga yanda Gwaggo ke magana zaku rantse da kanta ita ɗaya takeyi, saboda yanda ta nuna tamkar babu inuwar Yaya Haidar a wurin, shi kam ina da tabbacin a zuciyarsa ji yake inda ace yana da iko baiga me hana shi saka mata hannu ajiki ba. maganarta ta dawo dani daga tunanin sakanni biyun dana lula. "ki shige ki tafi Allah ya bada sa'a". na ansa da,"amin". Zan fita kenan Yaya Abba na shigowa, na gaida shi ya ansa min, ni kuma fice. Part ɗin Baba na wuce, Anty na samu a parlo tana jera masa kayan breakfast, ina zama kan kujera nake gaisheta, amma ƴar matar nan ko iskar da ta kwaso ni bata kalla ba bare nasa ran zata amsa min. nima na bawa banza ajiyarta, sai can dai dana ga zaman ba zai kai min ba nace da ita,"Anty ina Baba?". tace, "ba dai kinzo ɗakinsa ba, sai ki jira ki gani idan zai fito ko ba zai fito ba. Ni bana son kinibibi". ta faɗa tana wucewa ɗaki ta barni zaune anan, nafi minti goma zaune banga alaman Baba zai fito ba, hakan ya tabbatar min bata sanar masa da zuwana ba. Raina duk yay ba daɗi, na ɗauka wayana na kira Baba, ringing biyu kam ya ɗaga, yanayin da yaji muryana ya shiga tambayana ko lafiya. na kauda ɗacin dake ƙasan maƙoshina nace,"lafiya lau Baba, nazo wurinka ne kuma ban sameka a parlo ba". sai muryarsa ta far fita da sautin faɗa-faɗa. "a'a to wannan wane irin shirme ne, ba sai ki hauro saman ba. Tun yaushe kike nan a zaune?". Dan dai ban iya haɗa rigima ba da nace masa Anty tasan da zuwana, to amma saboda bana son ɓacin ran Baba kuma ni bana so naga ana fitina acikin gidan sai kawai nace masa,"tun ɗazu ne, kuma zan tafi school ne gashi harma na makara". "sorry my daughter gani nan bara na sakko". Ko minti biyu ba'a ƙara ba sai gashi ya sakko, ya zauna kan kujeran da nake, kaina na ƙasa yasa hannu ya ɗago da fuskana, ganin idona ya ciko ya ɗaga hankalinsa. "whats wrong?". Ya tambaye ni. na girgiza masa kai alaman ba komai. "no no ba kya min ƙarya fa". Ina goge guntun hawayen daya sakko min nace, "ban ganka bane". nai mas aƙaryar hakan, wanda a haƙiƙanin gaskiya a lokacin ina kewar mahaifiyata ne, sai Yay murmushin manyance yace, "rainon Gwaggo sarkin shagwaɓa, to yanzu gani me kike so?". Dai-dai lokacin da Anty ta ƙaraso da tea flask hannunta, ta aje kan dining sannan tazo ta zauna itama, tana murmushi ta ke ce min. "Ƴar gidan Babanta har an fito, yau za'a fara shiga makaranta ko, to Allah ya taimaka a maida hankali sosai kinji, banda wasa don Allah, abinda aka je yi shi kawai za'ayi". Tsabar mamaki kasa ce ma ta komai nayi, nai kamar ban jita ba don kar ma Baba yace wani abun. Nace da Baba, "dama zan wuce makaranta ne nace bari nazo na gaisheka". "oh yaune fa za ku fara taking lectures ko, eyyah sorry dear na ɓata maki lokaci". Ya zaro 2k a aljihu ya bani, na amsa ina sambaɗa masa adu'a da kuma godiya. Nace masa ko zaisa Yaya Abba ya kaini, idan naje yau naga yanda yanayin school ɗin namu sai na fara zuwa da nawa motan. Ya kira Yaya Abba a waya yace masa ai yanzu ya tashi ko wanka bai ba. "ina Haidar fa?". Ban san me Yaya Abba yace masa ba naji yace, "to kace masa ya fito ya kai Sabina makaranta, yay sauri tayi late". Mu kai Sallama da Baba na tashi zan tafi, Anty tace, "Sabina tsaya kisha tea mana nasan ba lallai kinyi break ba". "na ƙoshi". nace da ita ataƙaice. cike da ƙwaracewa na kissa tace, "a'a ni dai nasan ba ki ƙoshi ba, saboda ba ki ci komai ba tunda ban kai muku ba, ki daure kizo ki zauna ga plantain nan kici ko kaɗan ne, ba kya tafi makaranta a haka ba". Shi dai Baba wayarsa yake dannawa, ni kuwa mamakin kisisinarta nake. ta kuma cewa, "to ko na zuba miki a flask ne sai ki wuce da shi?". Ƙaramin tsoki naja, na ɗaga kai na jefa mata harara nai tafiyata. sai ga su Aisha sun shigo, suma jikinsu sanye da uniform, Zainab da Khadija ne kawai suka gaida ni, amma Aisha da Amina da suke ganinmu kai ɗaya kallo ɗaya suka mani suka ɗauke kai suka wuce inda Baba ke zaune. Kuɗin makaranta ya basu, ina ji kuma yana musu faɗan latti da suke kullum. Suka bashi haƙurin kan zasu daina. Aisha tace, "Baba yau Umma bata da lafiya tace ba zata iya kaimu ba, sai dai ko Anty ta taimaka mata ko kuma kasa Yaya Abba". Anty tayi karaf tace, "a'a ga Haidar nan zai kai Yayarku, sai ku tafi tare ya saukeku". Baba yace, "ehh hakan ma yayi, kuje Allah ya bada sa'a". A bakin mota muka tsaya muna jiran fitowarsa, ni dai kamar na haƙura da binsa na hau motana kawai na wuce, tun fa ɗazu Baba ya kirashi ko shirin me yakeyi ai yaci ace mun fito mun same shi ma yana jiranmu, kuma duk dan ni zai kai ne shi yasa yake wannan delay ɗin. "Yaya anya kuwa Yaya Haidar yana nan. Kalla fa morethan 5minutes muna tsaye nan muna jiransa bai zo ba. Ni kam yanzu ma nasan an rufe gate". Khadija ta faɗa kamar zata yi kuka, da yake itane autarmu. Har na taka ƙafana zan bar wurin sai gashi ya fito yana gyara zaman hularsa, fuskar nan a ɗaure babu alaman kawo wargi, sai wani takun ƙasaita yake kamar jinin sarauta, na taɓe baki na harari inda yake, ya ƙaraso ya buɗe motan, na buɗe da sauri na shiga. Ya duba su Aisha dake ƙoƙarin shiga yace, "ku kuma fa?". "Baba yace ka aje mu a hanya".
Amina ta bashi amsa, ya wurga musu harara ya shigo cikin fushi ya figi motar, Allah yasa na rufe ƙofar da ba abinda zai hanani faɗawa waje. su muka fara saukewa tukunna muka wuce tamu makarantar, sai daya raba tafiyar biyu naga yaja yay parking, ya kashe motar yana danna wayarsa, naga bashi da alamar ci gaba da tafiyar na kalle shi nace, "Yaya Haidar ya dai, ko wata matsalar ce ta sami motar?". Shiru yay min kamar bada shi nake ba, sai dana ƙara magana a karo na uku tukunna ya juyo a fusace yace, "Get out". Na tsaya ina kallonsa, zan kuma magana ya doka min tsawa, "ba za ki fita ba". Na buɗe motar na fice, dama jira yake ina fita ya figi motarsa ya buɗe ni da ƙura. Na samu na tari mai napep ya ƙarasa da ni. Yau na kuma yarda da cewan karatun university bana wasan yara bane, sai na tuna Farhana tah da idan ta dawo tana min complain nayita ce mata raguwa, ita dai bata son karatun ne kawai. Ashe abin ba haka yake ba, lectures uku muka yi ayau kuma duk masu zafi, Har sai dana ji dama ba Accounting na zaɓa ba. Ƙawar da nayi Asma'u tai dariya tana cemin, "to ce miki akayi sauran courses ɗin sauƙi gare su, kowanne da irin nasa wahalar, ke dai Allah ya bamu sa'a kawai". "kuma fa haka ne". Na faɗa ina zura sauran littafaina a jaka. Nace ma ta, "muje ko". Har titi muka zo ni da Asma'u, Anan ne muka rabu, ta hau mota ta wuce ni kuma na tsaya jiran wani, saboda hanyanmu ba ɗaya ba. Sai dana jima tsaye rana duk ta gama zane ni sannan na sami taxi na hau. A matuƙar gajiye na dawo gida, ina shiga parlo nai wurgi da jakata na haye kan kujera dan ko ɗaki bazan iya ƙarasawa ba, takalman ƙafata ma ban cire ba. "Lazy lazy".
Yaya Abba yace da ni cikin sigar tsokana. "Yaya Abba wallah ba wani zancen Lazyness, kaga wuyan da muka sha kuwa, Allah ya haɗamu da wani lecturer mara mutunci mugu harda mana test". "to yace ko kinyi abin arziƙi?". "ahh na rubuta masa abinda na iya, na bar masa wanda ban iya ba. Allah tun ƙwaƙwalwata na ɗaukar komai har nazo na daina kwashewa". "dagewa za kiyi yarinya. Karatun bana yara masu lalaci bane". Nai murmushi kawai na juya na gyara kwanciyata, kamar an tsikare ni na zabura na miƙe, na duba Yaya Haidar wanda ke kwance shima kan kujera, na sauko na buɗe jakata na ɗauko littafina na nufi wurinsa. "Yauwa Yaya Haidar kaine kayi Statistic, Please help me to solve this". Kamar bada shi nai maganar ba, "Yaya Haidar please mana". Ya kuma share ni. Na miƙe da sagaggiyar gwiwana zan tafi sai kuma yace, "lem me see". na dawo da ƴar murnata na miƙa masa yace, "i dey hear you; readout". ya faɗa ba tare daya dubi ko inda littafin yake ba balle ni. ina waro ido waje nace, "tabɗi ai bazan iya karantowa ba, wasu numbers ne fa a watsaltsale". sai ya saki wani Silent smiling, ya miƙe zauna ya amsa littafin yana dubawa. tamkar wanda na matsewa baki na masa dole haka yake magana, to ni me ma nake ji, shi ɗaya yake maganarsa a cikinsa, kuma nan wai bayani yake min yana aikin buga calculator, na kallesa na zabga masa harara kamar yana ganina, na haɗe girar sama da ƙasa na warce littafina na tashi na bar wurin nayi ɗakina, Gwaggo dake fitowa daga kitchen ta bini da kallon yanda nake ɓata rai ina jiran fashewa da kuka. Ta juya ta kalla Yaya Haidar daya koma yay kwanciyarsa, sannan ta kalla Yaya Abba wanda ke ɓaɓɓaka dariya ko akan mene oho, shi dai da wayarsa ne, tayi ƙwafa ta koma kitchen da plate ɗin abincinsu da zata kawo musu. Ta hau sababin. "yanzu fisabilillahi yarinyar daga dawowarta makaranta dan zalunci aka ɓata ma ta rai, ko hutawa fa ba'a barta tayi ba ta numfasa, kawai saboda ana Ma ta baƙin ciki, to mutum yaje shi da Allah dan ni dai ba yarda zanyi ba, kuma abincina ne ba zan bayar ba, aje wani wurin aci". Ta sawa kitchen ɗin ƙaton padlock ɗin da tace Baba ya sayo mata ɗazu, saboda Yaya Haidar daya ke zuwa yay mata ɓarna a ciki. Yaya Abba daya jita tana wannan sababi ya taso yana bata haƙuri, saboda shi baya wasa da cikinsa, akan abinci zai maka ladab iya ladab, Gwaggo ta masa wani kallo ta ɗauke kai. "kauce ni zan wuce".
"haba Gwaggo, bafa a wasa da yunwa, kina kallo har ƙarfe biyar bamu ci abincin rana ba, ni dai don Allah kiyi haƙuri ki bamu abincin nan. Waccan yarinyar babu abinda aka mata halinta ne kawai". "mtswww babu abinda aka mata zata zo ta wuce ni haka fuuu kamar tashin iska babu magana, ko fa sannu da gida bata yi min ba. Kuma sarai nasan kune kuka ɓata mata rai, dan wannan ba halinta bane na rashin kyautawa, saboda haka idan kana so na baku abinci kaje ka taso wancan mara kunyar yaron kuje ku sameta ku bata haƙuri, idan ta haƙura shikenan idan bata haƙura ba kuje wani wurin kuci". "please mana Gwaggo". Ya faɗa yana haɗa hannayensa. "please ɗin gidanku, dilla ni gafara min ina da abinyi, ai ni Abba kana bani mamaki, irin girmamawa da biyayyar da yarinyar nan ke maka wallahi sam bata cancanci wani abu ɓacin rai daga wurinka ba, a rayuwa bata da wani zance sai Yaya Abba, wanne kalar bauta ne bata maka ba, bini-bini tana cikin maka wanki da guga, har gajeran wandonka wankewa take, amma ka rasa da me zaka dinƙa saka mata sai dai ka taƙarƙare ka ɓata mata rai, babu batun sanyata farinciki. To kaje kowa dai yay na gari kansa". Ta ture shi ta wuce, taje ta ɗauke mayafina da jakata ta barsu anan da yunwarsu dan ta rantse ba zasu ci abincin ba.
*Please Vote, Comment and Share.*
[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*
_By Oum Ramadhan✍🏼_
*(15)*
*Kano, Bompai Police Station.*
*9:00pm, Officer Office.*
"wallahi ba zan yarda ba, kuma ba zan yafe ba, dan haka Officer kayi moving case ɗin nan zuwa court a gobe". Dattijon dake zaune kan kujerar dake fuskantar Officer Yahya Murtala ya faɗa, cikin hargowa yake maganar, yayinda fuskarsa ke ɗauke da tsananin ɓacin rai da kuma tashin hankali. wannan tashin hankalin daya sameshi tun a ranar da aka sami gawar ƴarsa da aka yiwa fyaɗe. Officer ya sauke numfashi sannan ya koma baya ya jingina daga jikin kujerarsa dake juyawa da shi gefe zuwa gefe. biron dake riƙe a hannunsa a saman leɓensa yay shiru yana nazari, tsawon wucewar daƙiƙa uku tukunna ya sake sauke numfashi ya fuskanci Alhaji Musbahu Wasai yace da shi,"Alhaji karfa ka manta har yanzu bamu da wata ƙwaƙwƙwarar hujjar da zamu tura wannan yaron kotu, zarginsa kawai muke, har yanzu bamu tabbatar ba". Alhaji Musbahu Wasai ya taso masa sama acikin muryar faɗa yana cewa,"Officer babu wani batun zargi anan. akwai wata hujja da za'a samu ne bayan wacce muka da ita?...sai dai kuma idan wanda yay wannan aika-aikar ne ya biya...". bai kai ga ƙarasa maganar ba Officer ya ɗaga masa hannu. "Alhaji ba'a ɗakin matarka kake ba, saboda haka ka iya bakinka anan wurin". sai kuma shiru ya sake ratsa ofishin gaba ɗaya na wucewar wasu sakanni. kamin daga bisani Officer ya ɗaga waya ya kira, cikin daƙiƙar da ba zata haura ɗaya ba Corporal Murshid ya shigo, tsaye daga gefen table ɗin Officer ya sara masa, sannan muryar Officer ta fito cikin bada umarni. "Corporal". "yes Sir". "kaje ka faɗawa Sergeant a ƙara komawa kan yaron nan. ayi duk yanda za'ai musami abunda muke so ayau ɗin nan". Corporal ya ƙara sarawa yana cewa,"Oak Sir". daga hakan ya juya ya buɗe ƙofa ya fita. Officer ya kalli Alhaji Musbahu yace,"kai kuma kaje zamu nemeka...sai dai abunda nake so kayi keeping a mind ɗinka shine, hukuma bata gudar da aikinta ta irin tsarinka...mun san abunda muke, mun kuma san abunda ya dace...i hope you get me". Alhaji Musbahu bai ce komai ba ya miƙe tsaye yana bin Officer da wani irin kallo sannan ya taka ya wuce zai fita, sai daya je bakin ƙofa maganar Officer ta dakatar da shi. "ina fatan kasan inda ka kawo case ɗinka, Bompai!". Alhaji Musbahu ya jijjiga kansa kawai sannan ya buɗe ƙofar ya fice.
*9:30pm, cikin Cell.*
kansa duƙe yake a ƙasa, yayinda hannayensa ke riƙe da kumburarriyar ƙafarsa, ciwon dake saman goshinsa na zubar da jini kaɗan-kaɗan. yaja dogon numfashi ya sauke tare da rumtse idonsa sakamakon zafin ciwukan dake ratsa ilahirin jikinsa. _"Ya Rahman ka kawo min agaji, ka kawo min ɗauki, ubangiji ka wanke ni daga wannan laifin da ake zargina da shi. Allah ka bani ikon cinye wannan jarabawar"._ zafin ciwon dake kafaɗarsa yasa shi ƙara rumtse ido sosai, wanda ya tabbata idan ba karaya bace to ya sami targaɗan ƙashi. _"Ya hayyu ya qayyum"_ itace kalmar da yake ta nanatawa a fili har zuwa lokacin daya fara samun sassaucin zafin ciwon. sannan ya ɗago da kansa ya jinginar jikin bango yana sauke numfashi a hankali a hankali.
kuma lokaci ɗaya hoton Sabina ya shiga haska masa acikin ƙwayar idonsa, maganganunta kuma na waccen ranar suma suka haska a kansa, ranar data zama ta ƙarshe daya gargaɗeta akan karta ƙara zuwa inda yake, har yay mata rakiya zuwa titi