Showing 45001 words to 48000 words out of 89788 words

Chapter 16 - ALHUSSAIN Complete Hausa Novel

23 Aug 2025

392

ta hau mota. a dawowarsa, mazauninsa inda yake rayuwa, wata sabuwar ƙaddarar da zai iya kiranta da mafi muni ta kama ƙafarsa, kuma bata sake shi ba har sai data kawo shi nan, cikin wannan cell ɗin da kwanaki ashirin da biyar kenan yana cikinsa, ba zaman daɗi ba, zama na wahala da uƙuba, zaman da a kullum yake cewa inama mutuwa tazo ta ɗauke shi. sai dai a kullum abu guda zuciyarsa ke faɗa masa, ba zaka mutu yanzu ba, ba zaka mutu ba Alhussain har sai gaskiya tayi halinta, ba zaka mutu ba har sai ka fita daga wannan zargin. lokaci ɗaya yaji wani abu da bai san menene shi ba ya wuce ta maƙogoronsa, yayinda Sabina ta tsaya masa a ƙirji ta tokare wucewar komai ta wurin. ya sani! ya san cewar zuciyarta me kyau ce tun kamin ya kai ga kallon kyawun surar dake saman fuskarta...wataƙila ta sake komawa wurinsa tunda bata jin magana, duk da jikinsa na bashi cewar ta koma ɗin fiye da yanda yake lissafawa...tunda yazo nan hankalinsa da tunaninsa suna kanta, suna kan zuwanta wurin zamansa daya zame masa baƙar ƙaddara, yana tsoro, a tsorace yake sosai, shi yasa tunanin halin da take ciki ya kasa barin ruhinsa da gangar jikinsa gaba ɗaya.
ya sake kulle idonsa gam sannan yaja wata doguwar ajiyar zuciya ya sauke, cikin ransa yana adu'ar. _"Ya Allah ka kula da ita, ka tsareta daga dukkan wani abun cutarwa"._
kuma buɗe ƙofar cell ɗin daya ji anayi yasa komai dake cikin kansa ya tsaya cak, illa bugun zuciyarsa daya ƙaru sosai. har yanzu ya kasa sabawa da wannan horon da akeyi masa, bai kuma san ranar da zai saba da shi ba. abu guda ɗaya ne kawai yake anan, a duk sanda yake ansar wani tsatstsauran hukunci, ya kanji yana samun sauƙin abun idan yana ambatar sunan Allah, kuma ya kanji kamar zafin komai na yayewa ne ya zama kamar babu idan ya tunata, jikinsa yana bashi cewar zata zo ta goge komai, zata zo ta ɗauke shi, zata zo ta fitar da shi, wataƙila nan kusa ko da jimawa...amma da jimawar shi yake lissafawa kuma yake hangowa.
maganar Captain da suke shigowa ciki tare da Sajent ta ratsa cikin kunnensa. "Yallaɓai duk wani bincike da ya kamata muyi munyi shi. kuma har yanzu abu guda muke samu, irin bayanin da yake fita daga bakinsa...ƙwarai ba shi da alaƙa da kano, haka kuma mun kasa gano daga wacce ƙasa ko kuma garin daya fito har ya shigo nan. abunda yafi ɗaure kai shine rashin sanin sunansa kaman yanda shi kansa yake faɗa". Sajent jin bayanan Captain yake har sanda ya sami kujera ya zauna, kujerar dake fuskantar Alhussain.
"me yasa ba zaka yarda ka ansa wannan laifin ba?". Sajent ya jefa tambayar ga Alhussain wanda kansa ke ƙasa. "saboda bani na aikata ba". ya bashi amsar kai tsaye, kuma ba tare daya jira ƙara cewar Sajent ɗin ba yace. "inaji zan iya ansar wani laifin da ƙaddara zata ɗora min shi, amma banda laifin aikata fyaɗe. bani nayi ba, dan haka babu dalilin da zaisa na amsa cewar ni na aikata. dan haka zaifi muku kyau ku kashe ni ko kuma ku bar wahalar da kanku akan tambayata kuyi abunda ya dace". shirunsa ya haɗe da dukan da Captain ya bashi a gadon baya da gwiwar ƙafarsa, hakan yasa shi saƙin wata azababbiyar ƙara tare da ambaton sunan Allah. "ka yarda kai kayiwa Yarinyar nan fyaɗe, ka yarda kai kayi mata fyaɗe kuma baka ƙyaleta ba har saida ta mutu". "ba zan yarda ba tunda bani nayi ba". "idan ba kai kayi ba to waye yi?". "nima ban sani ba, Allah shine masani". "amma me yasa aka sami gawarta acikin kangon da kake zama? bayan jama'a sun bada shaidar kai kaɗai ne kake rayuwa acikin wannan kangon". "wataƙila Ubangiji ya jarabceni ne da wannan jarabawar saboda ta kawo sauyin wannan ƙaddarar dake ɗaure da rayuwata...jikina na bani cewar rayuwata zata sauya silar wannan jarabawar". Sajent yay wni murmushi yace, "ba fa zamu taɓa yarda da kai ba...duk da cewar likitoci sun bamu tabbacin babu semen ɗinka ajikin yarinyar amma hakan bashi zai wanke ka daga wannan laifin na fyaɗe ba". Alhussain ya rufe ido hoton abunda ya faru a wancan lokacin na haskawa a duhun idonsa. bayan ya raka Sabina ya wuce masallaci, bai dawo ba sai gefin magriba, kuma yana zuwa kai tsaye ya shige cikin kangon don ya samu ya kwanta kasancewar kansa da yaji yana masa ciwo sosai. ya tuɓe rigarsa ya saƙaleta a jikin garun wajen kawai sai yaji jiniyar motar ƴan sanda, bai kawo komai a ransa ba ya wuce ya shiga zuwa ɗaya ɓangaren dake cikin kangon, inda yana shiga yay tozali da budurwar yarinya kwance shememe acikin jini, tsoro da firgici suka sa shi ya razana yaja da baya yana zazzare ido. bai taɓa gani ba, a baki kawai ya san kalmar ta Fyaɗe!. sanda yay yunƙurin saurin fitowa lokacin ƴan sanda suka faɗo ciki, aikuwa nan da nan suka saita shi da bindiga suna faɗin hannu sama, ta ke anan yaji duniyar na juyawa da shi sannan ta tsayar da komai nasa ya tsaya cak, haka ƙwayar idonsa ta komai kan yarinyar. wani ɗan sanda yazo ya wuce ta gabansa ya durƙusa ya ɗauki wayar yarinyar dake yashe a gun, wadda ta bin lokacation ɗin wayar ne ya kawosu gurin. kuma duba da yanayinsa wanda yake daga shi sai gajeren wando yasa ƴan sanda taso shi ƙeyarsa aka sa shi a mota aka taho da shi nan. "kanata wahalar da hukuma. ka faɗa mana gaskiya ka hutawa kanka haka muma ka sawwaƙa mana". Maganar Sajent da dukan day kawo masa na kulki suka baro shi daga duniyar tunanin daya tafi. "har yanzu amar guda ɗaya ce a wurina shine bani na nai fyaɗen ba, haka ban san ya akayi komai ya kasance ba". kuma buɗar bakin Sajent zaiyi managana wani ɗan sanda ya faɗo cikin cell ɗin yana faɗin, "Ranka ya daɗe ɗaya daga cikin waɗanda suka aikata laifin Fyaɗen nan ya kawo kansa...yace shi yaron Alhaji Musbahu Wasai ne". jin hakan yasa Sajent saurin miƙewa suka fita daga cikin cell ɗin cikin hanzari. yayinda Alhussain yabi bayansu da kallo, zuciyarsa na wucewa da wani abu mai kama da sanyi.

*Bayan Wata Biyu.*
To alhamdulillahi karatunmu na ta tafiya yanda ya kamata, kuma na raba ƙawance da Asma'u saboda ita shirme ne ta sanya a gaba, na samu sabuwar ƙawa mai hazaƙa da ƙwazo kamar ni muka ɗinke da ita, sosai nake jin daɗin harka da Intisar, saboda yarinyar akwai hankali da natsuwa, ita ɗin ce dai-dai da ra'ayina. sosai na maida hankali a karatuna babu wasa, Yaya Abba da Yaya Haidar ƙwarai matuƙa suke taimaka min akan abinda ban gane ba, dama ga shi ni tun a secondry school sarkin read ahead ce, yanzun ma haka ta ke, ko ajikina dan Malami ya shigo yace zaiyi unexpected test saboda bani da shakku akan abinda zan rubuta, karatu ne nake wanda babu dare babu rana shi yasa komai ke zuwar min cikin sauƙi. Gwaggo tayi ta bambami tana takaici, "karatun da bana Allah da Annabi ba a dinga bauta masa, yo ina kuwa jiki zai yi kyan gani, gaki nan duk kin bi kin ƙare kamar ragowar yaƙi". Ni dai bana ce ma ta komai sai dai nayi murmushi, mafi akasari ma Yaya Abba ke bata amsa idan yana kusa, yay dariya yace, "to ai Gwaggo karatun ita zaima amfani ke kuma kiji daɗinsa". sai tayi masa kallo mai harara, idan taso ta bashi amsa idan bata ba so ba tayi masa banza. Yauma kamar kullum nasa littafi a gaba ina karatu, kawai naga an ɗauke shi daga gabana, ina ɗagowa na kalla Gwaggo tsaye ta ɓata rai, tana min faɗa tace, "tashi kije ki kwanta ki matse idonki, kar ki soma farkawa sai na zo na tasheki, wallahi idan ba haka ba sai na ɓata miki rai". Zanyi gaddama naga babu fuskar hakan, na miƙe na wuce ina faman buga ƙafafu a ƙasa, ina ji tana ta faɗin,"ƙarshen buga ƙafa ki fasa tiles ɗin ki faɗa ciki, haba Mutum idan ba so yake ya haukace ba wannan karatun ai yayi yawa, tun takwas kike anan a zaune ga ƙarfe ɗaya na neman kawo kai, duk kinbi kin wani sukurkurce kamar ba ke ba, ƙashi kamar kayi magana su amsa maka, ɗan kumatun nan naki babu shi, su kansu dukiyar fulanin naki sun rame, yo to ni ai ba mahaukaciya bace da zan barki kina lalacewa ba, nifa idan ma babu dole wannan karatu sai ki barshi, tun farko da nasan haka yake ba za ki soma ba, iya wanda kika samu a baya Allah ya amfana". taja tsaki ta ƙarasa wurin Yaya Abba, tana zama kusa da shi tace, "kai kira min Babanku, kace masa idan zai taho ya taho min da tsire irin wanda yaji ƙuli a jiki sosai, Ita kuma Sabina ya sayo mata kaza mai nagartaccen haɗi da kuma youghrt shima mai kyau, ya haɗo da kayan marmari ma namu ya ƙare". Ya ɗago ya ƙura mata ido yana kallonta, jin yayi shiru ta waigo daga kallon tv ta kalleshi, "to abinda na faɗa ne ba dai-dai ba dana zama abar kallo, ko kuma ƙa ƙa?". yace,"a'a Gwaggo, ke da kuɗin ɗanki, duk wani faɗi tashi fa kece kika yi a kansa har ya samu ya kai wannan matsayi, don haka ko garin Abuja kike son ci gaba ɗaya ai dole ya saya maki". Ta masa kallo mai kama da harara ta ɗauke kai, "to aini ba Gara bace da zan kama cin gine-gine, idan zaka kira min shi ka kirawo shi, idan kuma baka iyawa na tashi naje na sami Haidar ya kira min shi, tunda shi yanzu sai dai na taka ƙafata naje inda yake, ban kai matsayin da zai zo wurina ba, sam yaron nan baya girmamani". Abba ya fashe da dariya, bayan itace ta kora Haidar da muciya tace idan ya kuma zuwa inda take saita mummuƙa masa muciya aka, ta gaji da zuwan da yake yana mata dafe-dafe a kitchen, kuma tunda ta kore shi ɗin ya daina zuwa, tana cewa ta sami lafiya amma kullum zancenta ina Haidar, har zuwa ɗakinsu ta ke ta gani ko yana lafiya, shi kuwa yay biris da ita ko a compound suka haɗu ɗauke kai yake. Abba ya zura hannu a aljihu ya ɗauko wayarsa, sai bayan daya kira Baba yake roƙon Gwaggo akan don Allah ta barni nake karatun nan, hutun yana gaba yayin dana gama exams, yanzu jarabawa ce zamu fara dole take ganina ko da yaushe akan littafi, kuma hakan shine dai-dai, dole sai na dage zan cimma nasara. "sai na barta jikinta ya lalace saboda ba kai zaka aureta ba ko, mtswww ni karka ɓata min rai Abba. Akan wannan karatu yarinyar nan ko lokacina bata da shi, to yanzu dai na ware masa lokacinsa, ba zan ɗauka ba, kuma fa karatun nata lissafi ne naji Zahra'u na faɗa, tace har hauka yana sanya mutum, ta kwatanta min da ƙanenta tace idan na ganshi ai zan lura bai cika hankali ba, to itama haka kake so ta zama? ko da yake kai dama ba ƙaunarta kake ba, aikinka shine kasata gaba kana faman tayata dukan wannan abar ta lissafi sai kace za ku ƙirge kuɗin duniya". Baice mata komai ba sai dariya da yake ƙasa-ƙasa, sababin Gwaggo na saka shi nishaɗi, idan ta fara magana baka ce zata yi shiru ba, taita jera zance kenan. a ƙufule tace da shi, "nifa kasan Allah na tsani ina magana naga ana min dariya kamar anga sha uku-sha uku, abin yana ƙonan zuciya, wannan yana ɗaya daga cikin abinda ya taɓa haɗani da wani saurayina nace na fasa aurensa, Sahibina shima wataran haka ya taɓa min, na kuwa doka yaji na wuce gidan Kakanni na, sai daya sha fama kamin na dawo". Yanzuma dariyar yay ba tare daya bari ta lura ba, ya miƙe ƙafa ya kwantar da kansa saman cinyarta, tana shafa sumar kansa take faɗin, "Abba ya kamata ka aske wannan sumar taka haka kaji ko, haba tayi yawa ai, gashi sai kace bana ɗan musulmi ba". "tom Hajiya Gwaggo". Yace da ita. saiga hawaye ya shiga sauka saman kuncinsa, hankalinta ya ɗaga ta shiga tambayarsa ko lafiya, yay shiru baice mata komai ba, itama saita fashe da kukan, ganin haka yace, "Gwaggo ina kewan mahaifiyata ne fa". Ya faɗa yana sa hannu ya goge mata hawaye. Ta mayar da shi saman cinyar tata, tana shafa kansa,
"kayi haƙuri Abba, Allah ya jiƙanta da rahma kai kuma ya haɗaka da abokiyar zama ta gari wadda zata dinga ɗebe maka kewa". Ta kuma fashewa da sabon kuka, "yanzu haka dole nima wataran zan tafi na barku, mutuwa rigar kowa ce. Allah ya bamu cikawa da imani ya kuma nufe ni da ganin aurenku, ina son Allah ya ara min rai da lafiya naga hannun waɗanda zan damƙa ku". Ya miƙe zaune ya riƙe hannunta, "insha'Allahu Gwaggo za kiga aurenmu har da ƴaƴanmu, duk da mutuwa bata barin wani don wani yaji daɗi amma ai ta bar mana ke tunda ta ɗauke mana Mama, so ki bar kuka don Allah kar Sabina ta jiyoki". Hakan daya ce tai saurin sa hannu tana sha re hawayenta.
*****
Yaune zamu zana last papper, kwana nayi ban runtsa ba ina karatu da nafila, amma fa a hakan sai da muka yiwa Gwaggo dabara tukunna, saboda tuni ta hanani karatun cikin dare, Yaya Abba ne ya sayo maganin bacci muka sa mata a lemu ta kwankwaɗe gashi har gari ya waye sai sharar baccinta ta ke. Allah sarki Yaya Abbana abin ƙaunata, kamar yanda naga rana naga dare haka shima ya gani, da daddare da Gwaggo zata kulle ƙofa ya ɓuya ga bayan labule, bayan ta wuce ɗaki ya fito, nima ko da na wuce kwanciya sai dana tabbatar tayi bacci kana na fito parlo muka hau karatu ni da shi, kamar shima exams ɗin zaiyi. Shap-shap nayi wanka na fito, ko mai ban tsaya shafawa saboda bani da lokacin wannan, mayafinma a bai-bai na yafa, sai dana fito Yaya Abba ya gyara min, shi yace zai taimaka yau ya kaini, da zamu fita muna jiyo ƙira'ar Yaya Haidar na tashi a masallacin cikin gida, na kirashi a waya nace idan ya idar ya sani a adu'a, yace "toh, Allah ya bada sa'a". Ƙarfe takwas dai-dai muka shiga ɗakin jarabawa, ba ƙaramin tsaro aka sa mana, duk an tarwatsa mu, wannan course ko bala'i, Allah dai ya bamu ikon hayewa, tun ba'a fara ba sai haɗa zufa muke, kwanciyata nayi kamin a raba peppers, har bacci ya fara ɗaukata, ganin Malamarmu ta taho da sauri Intisar ta dokoni, dama tazarmu da ita 1seat ne. Na farka a gigice na miƙe zaune, "masha'Allahu". wannan kalmar ko da yaushe ita nake furtawa a duk sanda nai tozali da Malama Muhsinah, ta ko'ina bata da makusa matar nan sai dai ban sa ni ba ko a halinta, amma iyakar kyawun halitta Allah ya bata, farinta tamkar wani madara-madara haka yake, amma a duk sanda nake zuzuta kyawunta sai Instisar tace wallahi na fita kyau, ko da yake dama ance wai mutum bai ganin kyawunsa, nayi dariya kawai idan naga tana ɓata rai ita alalle ba zance banda kyau ba. Inda nake Malama Muhisina ta ƙaraso, "get up". Shine abinda tace min, na miƙe, tace, "follow me". Na kwashi kayan rubutuna nabi bayanta, seat ta sauya mini ta maidani front seat, har wani lokaci ba'azo an raba mana script ba, nasa biro a bakina ina kallon wani bawan Allah dake zaune kan wheelchair a saman stage, ya juya baya baka ganin fuskarsa, Allah sarki ya bani tausayi sosai, shi kuma tasa jarabawar kenan, _Allah ka barmu da lafiyarmu, Alhamdulillah._ na faɗa a cikin zuciyata. Script aka fara raba mana, gabana ya faɗi, na runtse ido ina karanto wasu ayoyi da Baba ya bani, har aka gama raba mana questions pepper, kun san dai yanda ake tsintar kai a lokacin da aka shiga ɗakin jarabawa idan aka miƙo takardar tambaya musamman ma ace na course mai wuya ne, wani murmushin jin daɗi na saki da naga tambayoyin duk na sansu, aiko inata faman murmushi na duƙa kai na fara amsawa, cikin awa guda da farawarmu wasu suka fara submitting, kuma ni ce ta kusan 6 a gamawa. Ina sakkowa daga steps naji a jikina ana kallona, don koya aka ƙura min ido bada sanina ba sai naji a jikina, na ɗan dakata da saukar ina yatsine fuska, Supervisor namu naji ya doka min tsawa, "hey my friend what are you still waiting there?". Na tura baki gaba naci gaba da sauka ina murguɗa baki, na san dai koma wane mai kallona ya gani, ni ban son saka ido, dan bana buƙatar sanin koma wane dana ɗago na banka harara. Na ƙarasa na miƙawa Malama Muhsina script ɗin, har nai gaba naji ta kirani, na dawo tsna cewa da ni, "are you stupid?". na ɗago ina kallonta, tana nuna min script ɗin ta ke cewa, "what about your name and regestration number?".


*Please Comment, Vote and Share.*[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(16)*
ban ko bi ta kan Malama Muhsina dake bina da banzan kallo ba, abunda ya dameni shi ya damen, dan haka a wannan lokacin dafe goshi nayi cikin fargabar abunda ka iya faruwa da ace basu lura da rashin rubuta sunana ba. wallah shaf ni na manta da batun suna saboda zumuɗin fara ansering, daɗin question ɗin ya mantar da ni. na bawa Malama Muhsina haƙuri na amshi script ɗin na duƙa ina rubutawa, haka kawai sai na tsinci gabana da faɗuwa a lokacin, ga kallon da ake min ya tsananta yawa, naja tsaki ni ɗaya, sannan na ɗaga kaina sama nai harare-harare da murguɗe-murguɗe, yanzu kam dai koma wane nasan ya gani ya kuma san da shi nake, sannan na ɗago na miƙa mata. "your ID card". Ta ƙara cewa da ni, na miƙa mata

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login