Showing 66001 words to 69000 words out of 89788 words
kike ƙoƙarin aikatawa kuwa?". Ya faɗi hakan ransa a ɓace yana kafe ni da jajayen idanunsa da suka yi jawur. tuni idona ya ciko da ruwan hawaye har yay nasarar gangarowa saman fuskata, na zube gwiwoyina gabansa hawayena na ƙara tsananta gudu. "don Allah Yayana ka bani nasha ko nima na samu sauƙin abinda nake ji a zuciyata. Please ka bani abata nasha damuwata ta yaye, wallahi ina jin zuciyata na min zafi ne". "tashi ki bar ɗakin nan bana son rigima". Ba tare dana miƙe ba nace,"ba zan fita har sai ka bani maganin damuwata nasha, please ka bani a bata, ko kai dana zo na sameka kana sha na hanaka ne? to kuma sai kaine zaka min baƙincikin maganin matsalata".Na faɗi hakan ina ɗaga sanyayyiyar muryata. Shima gwiwoyinsa ya zube a gabana, ya runtse ido yana ajiyar zuciya, sannan ya miƙo min sigarin still idonsa a rufe kansa kuma a ƙasa a sunkuye. nasa hannu na amsa, ina karɓa ne ya buɗe idonsa, ganin da gaske shan zanyi yay saurin miƙo hannu zai kuma ƙwacewa, da sauri na ɓoyeta a bayana ina turo baki gaba.
*Gwarimpa, Abuja.*
ƙarfe tara da rabi na safe, kamar yanda tsarin gidan yake gaba ɗayansu ake haɗuwa a parlo idan za'aci abinci, amma idan Daddy na gari kenan. yanzu ma hakan ta ke, ba ki ɗayansu a dining, Mami da iyalanta, haka ma Mom da nata iyalin sai Anie dake zaune itama, Muhsin ne kawai babu. Daddy yay gyaran murya kamin yace, "lafiya Muhsin bai fito ba har yanzu? ko bai tashi bane?". "ya tashi, na barshi yana wanka ne, ban sa ni ba ko ya fito yanzu". cewar Muhsina. Daddy ya tashi ya wuce zuwa ɗakinsa, yana shiga ya gansa yana kokawan ciro riga a wadrobe, ya ƙarasa da sauri ya riƙe shi dan yana gab da faɗowa daga kekensa, rigar ya ciro masa ya saka masa, yana shafa fuskarsa yace,"me yasa baka kira wani ba?". da damuwa fal tare da shi yace,"Daddy ina so na fara sabarwa kaina da irin wannan ɗawainiyar, Muhsina zata yi aure soon idan Allah ya bata miji...". sai kuma yay shiru bai kuma cewa komai ba. Daddy ya sauke ajiyar zuciya cike da tausayin ɗan nasa, shima bai ce komai ba ya tura shi suka fita a ɗakin. kowa abincinsa yake ci baka jin ƙaran komi saina spoons, ana cikin ci ne Mami taja tsaki ta miƙe ta bar wurin, Abid ya mara ma ta baya, babu wanda yay magana bayan bin bayansu da kallo sai kuma girgirza kai. Khaleesat gaba ɗaya ta fara rikicewa domin wannan tashin da Mami tayi idan har bata bisu ba tasan sauran, ga shi jazaman ta miƙe sai Daddy yay ma ta magana, kuma zaice itama ta fara ɗaukan mugun halinsu ne. abincin ta dakata da ci, sai juya spoon ɗin ta ke, duk abinda ta ke Mom na lura da ita, bayan ta sauke numfashi tace, "Khaleesat". _innalillahi wa'inna ilaihi waji'un._ shine abinda Khaleesat ta ambata a ranta tare da jin faɗuwar gaba. tun ɗazu ta ke adu'ar Allah yasa kar Mom tayi ma ta magana, Mom ta kuma kiran sunanta amma bata amsa ba sai sunkuyar da kanta da tayi, ta rasa wannan wacce iriyar rayuwa ce da mahaifiyarsu ta ɗaukar ma kanta, ita kam wannan dokar da ta kafa ma ta tayi mata tsauri, Mom ta wuce gban komai, saboda macece mai mutunci. doka tsawar Daddy yay dai-dai da kiran sunanta da Mom ta kuma yi a karo na uku. cikin faɗa Daddy ke cewa, "ke dan ubaki ba ki ji Mom ɗinku na maki magana bane kika ma ta banza, ko kema kin fara bin sahun uwar ta ki ne. to ni ba zan ɗauki wannan shirmen acikin gidana ba kinjini ko. idan kina so mu shirya kiyi abunda nake so idan kuma ba haka ba babu ruwana dake". muryarta a sarƙe tace, "kayi haƙuri Daddy". shine abinda tace da shi hawaye na sakko ma ta. "ba ni za ki bawa haƙuri ba". jin abinda yace sai ta juya saitin Mom sai dai ta kasa yi ma ta magana haka kuma ta kasa kallonta sai hawaye da take saukarwa. hakan yasa Mom ta fara fahimtar wani abu, dan haka ta dafata tana faɗin, "Maminki ta hanaki yimin magana ko?". ta ƙara yin ƙasa da kanta, duk tabi ta dabarbarce ta rasa abin cewa. "kar ki damu Khaleesat kinji, ki taiwa mahaifiyarki adu'a domin abunda ta ke buƙata kenan". kai kawai ta iya jijjigawa ba tare da tace komai ba. Anie na gefe tace, "Allah dai ya kyauta halin wannan Mata, ni na rasa randa zata yi hankali wallahi". ran Daddy a ɓace ya miƙe ya bar wurin yana cewa Khaleesat ta biyo shi. Khaleesat na gaba yana biye da ita a bayansa, tana kuwa yin sallama parlo Mami ta damƙo wuyanta ta fara sauke ma ta ruwan bala'i. "saketa". Daddy daya shigo ya ce da ita a tsawace. sakinta tayi ta kama ƙugu tana faman cika tana batsewa sai hure huren hanci ta ke. shi kuma yaci gaba da magana a zafafe,"wai ke Na'ima me yasa a rayuwarki sam ba ki son zaman lafiya ne. yanzu abu da kika aikata a tunaninki dacewa ne?...". ai bat bari ya ƙarasa ba cikin hargowa yace,"to me nayi kuma ni ƴar gidan laifi, ni da aka tsana ake ɗora min laifi ko da yaushe". yay ƙaramin tsaki yace, "kinji matsalar taki ai, babu wanda ya tsaneki a gidan nan sai dai kowa ya tsani halinki, wannan ban zan halin naki shine ba'a so...yanzu kawai ki kama sakin tsaki a gaban babbar mace, fisabillahi wannan ɗabi'a ce mai kyau?". ta taɓe baki ta juya masa baya tana harare harare. "to ita ɗin uwa tace da ba zanyi tsaki a gabanta ba. kaga ni fa Alhaji na gaji da wannan takurawarka akan waccan baƙar matar taka, akan abinda bai kai ya kawo ba bini-bini sai kazo ka kama sauke min buhun masifa, to ni na gaji, na gaji gaskiya". ido kawai ya bita da shi yana kallonta kamin yace, "to ita kuma Khaleesat da kika hanata kula Mom ɗin nasu mene dalili?". "saboda ba ita ta haifeta ba, ba kuma ta tayani naƙudarta ba". "amma aini ubanta ne ko, kuma na isa da ƴata ko". ya kalla Khaleesat yace, "ke kije ki tattaro duk kayanki ki koma wurin Fa'iƙa da zama har sai randa na ba ki umarnin barin wajenta kinji ko". Ta ke kuwa Mami ta lailayo wata ashar ta yarfa sannan tace, "wallahi ba zai yiwu ba. ba'a isa an maida ni ɓora ba acikin wannan gida. a rasa inda za'a kai min ƴa sai wurin kishiya saboda ba'a sona ba'a ƙaunata. tun wuri Alhaji ka sauya shawara ko kuma wallahi na ɗaga hankalin kowa a cikin gidan nan". yay guntun murmushi da takaici sannan yace,"kije gidanku sai ki ɗaga hankalin kowa acan...ai tunda har yanzu kika gagara hankali to tabbas baki da ranar da hankali, kin girma amma sam baki san abunda ya dace ba. to ki bar min gida na ba ki hutu". "mtswww". taja tsaki da ƙarfin daya doki kunnuwansu. "to sai me da hutunka dama. ko baka faɗa ba dama zan tafi, abunda kawai nake so ka sa ni shine baka isa ka kaimin ƴata wurin kishiya ba, ehh wallahi kayi kaɗan". Daddy yay mata wani kallon banza kamin yace,"ba ina nufin na ba ki hutu bane. kije na sake ki saki guda". ya kalla Khaleesat yace, "wuce muje". ya bar Mami anan da ife-ife tana zage-zage kamar mahaukaciya sabuwar kamu.
_😅Masu cewa maganar Gwaggo yayi yawa hakana zakuyi haƙuri, dan Kakata nake tunawa in akazo babin Gwaggo, mu ma tamu Kakar idan ta fara sababi sai mun matseta Babban Yaya ya juye mata coflin a maƙoshi tukunna muke samun salama😅, so ku barni nake tunawa da Marigayiyata._
[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*
_By Oum Ramadhan✍🏼_
*(23)*
cikin ɗagin murya yace da ni. "ba za ki bani ba?". nima na cukule ina kauda fuska nace, "ehh ai kaima ga taka can kaje ka ɗauka ka ƙarasa sha, idan kuma ka ƙoshi da itane sai ka ɗauka wani sabo a kwali ai akwai da yawa". Na faɗi hakan ina fito da ita zan kuma kaiwa bakina, cikin amon muryarsa nan mai dadi ya dakatar dani. "don girman Allah karda kiyi gangancin sha, wallahi Allah bata dace dake ba, babu abinda takeyi fa ce ƙara damuwa amma bata maganin komai...". na saki wani yalwataccen murmushi da sautinsa ya amsa acikin ɗakin. sai ya ɗago yana kallona da kallo irin na mamaki. na ɗaga masa gira nace,"Yayana wai ni zaka ma wayo ko, saboda karna sha zaka ce min haka, to naƙi wayon sai nasha nima naji irin daɗin da kake ji acikinta har yasa kake min rowa". Kasaƙe yay yana dubana yayinda yake jin wani abu ga me dani na ƙara ɗarsuwa a zuciyarsa. sai ya kulle idonsa ya wani fizgi numfashi. "na rantse ba wayo ne nake miki ba. Da gaske nake miki bata maganin komai kuma wallahi bata dace...". Bai ƙarasa ba nayi saurin sanya yatsana a leɓensa alaman yay shiru. "Yayana". Na kira sunansa kiran daya ji har ƙwaƙwalwarsa, ya zuba min ido kamar yanda na zuba masa idanuna da suka taru da ruwa. "Yayana idan har wannan abar bata dace da ni ba to na rantse da Allah kaima bata dace da kai ba, saboda mutumin kirki baya shanta, mutumin da yake jin tsoron Allah baya shanta. idan har kana son lafiyarka ba zaka shata ba, idan har kana so damuwarka ta yaye ba zaka sha ba sai dai ka ɗauka maganin damuwa kankat Al-qur'ani me girma ka karanta, wannan shine hanyar da ma'aiki ya koyar damu, ba wai mu ɗauka abinda mun san zai cutar damu ba don magance damuwarmu, ita ɗin fa haramun ce na faɗa maka haramunce mene yasa ba zaka haƙura da ita ba?". Bayan na numfasa naci gaba da cewa,"haƙiƙa ba zan hanaka damuwa ba amma ba zan bar damuwa ta dameka ba Yayana, amma ina so ka fahimci cewar ƙaddararka ce a haka domin tuni Allah ya rubuta hakan zai faru da kai, dole ne kayi imani da ƙaddararka muddin kana son cika mumini na ƙwarai. A baya na faɗa maka bayan imani da ƙaddara akwai haƙuri, Yayana kayi haƙuri da yanda ka sami rayuwa, Allah da kansa yake cewa ana cikawa masu haƙuri ladansu ba tare da ƙididdiga ba. Yayana shaye-shaye babban zunubi ne mai girma ya kamata ka nisance shi, musamman abinda zai kawar da hankali ko kuma yasa maye, Allah ya mana umarnin mu guji kayan maye zamu rabauta, da kansa acikin littafinsa mai girma ya ambaci kayan maye da aikin shaiɗan. Ka sani lallai fa aikata saɓo yana hana arziƙi ya kuma gusar da ni'ima da albarkar dukiya. Don girman Allah Yayana kayi haƙuri da ƙaddarar da ta sameka, ka bar shan abinda yake haramun". Na faɗa hawaye na sakko min. Ganin yanda nake hawaye gaba ɗaya sai yaji ya ƙara shiga damuwa, ya rumtse idonsa ya buɗe sau uku a lokaci guda. "don Allah ki bar kuka bana son zubar hawayenki". Muryana na rawa nace,"wallahi Yayana wannan hawayen ba zasu taɓa daina zuba ba har sai randa ka rabu da wannan haramtacciyar abar. Na rantse maka idan har zaka dinga shanta to ko da yaushe hawayena zai dinƙa zuba a ƙasa ne. ka faɗa min a yanzu mene ka nema ka rasa da har ba zaka iya rabuwa da ita ba? Ka faɗa min ko mene shi na maka alƙawarin samar maka shi ko don ka bar cutar da kanka in har baifi ƙarfina ba. ko kuma Baba ya gaza yi maka ne?, Adu'a fa itace maganin damuwarka ba wannan muguwar abar ba". na numfasa na goge hawayena sannan nace," *ALLAHUMMA INNI ABDUKA, IBN ABDUKA, WABNI AMATIKA, NASIYATI BIYADIKA, MADIN FIHA HUKMUKA, ADLUN FIHA ƘADA'UK. AS'ALUKA BI KULLI MIN HUWA LAKA, SAMMAITA BIHI NAFSAK, AU ALLAMTAHU AHDAN MIN KAL'IK, AU ANZALTAHU FI KITABIK, AU ISTA'ASARTA BIHI FIL ILMI GAIBI INDAK, AN TAJA'ALIL QUR'ANA AZIMA RABI'A ƘULUBINA, WA NURA SUDURINA, WAJALA'A AHZANINA, WA ZAHABA HUMIMINA WARMUMINA*, wannan adu'ar itace Annabi ya koyar damu, kuma yace in har ka karanta Allah zai tafiyar maka da damuwarka ya kuma musanya maka da farinciki a maimakon damuwar. Don Allah Yayana kafi ƙarfin zuciyarka ta hanyar hanata abinda take so in har na saɓon Allah ne". abunda nake gani a ƙwayar idonsa dabanne, wani abu dake haskawa yana motsawa tare da zuciyata. motsin yatsunsa kawai nake iya gani a wannan lokacin, kuma kamin ƙifatawar idanuwana sai ganinsa nai ajikina, ya rungumeta tsam, kuma duk jarumtar namiji, duk yanda yaso ya hana wannan ruwan hawayen zuba ya kasa, sai kawai ya fashe da kuka yana daɗa matseni a sanda yake cewa. "haƙiƙa ke ɗin kina da baiwar da ba ki san kina da ita ba, iliminki da kyawun halinki sun dace dake, ki godema Allah da wannan baiwar da yayi miki. na rantse miki daga yau na barta, na rantse ba zan kuma sha ba tunda ba kya so. na barta har abada. Nima ban san lokacin da nake sha ba, baƙincikin ta yanda aka sa me ni shi yake jefani cikin wannan hali, iyayena basu kyauta min ba, Amma wallahi nayi miki alƙawarin daga yau ba za ki kuma ganina da ita ba har mutuwa, kin riga kin gama yi min gatan da duk abinda kika ce a gareni zanbi umarninsa". Jikina na rawa na raba shi da jikina. "Yayana ba don ni nake so ka daina ba, nafi so ka daina don Allah". Murmushin daya ƙawata fuskarsa ya sa ki yace, "zan daina don Allah kuma zan daina don ke". Ya faɗi hakan yana bani hanky na goge hawayena. Ina kallo ya tattara sigarin ya zuba a baƙar leda, yana cewa da ni,"kin gani ma na kwashe su duka, Yanzu zanje na zubar a shara". Ni dai tsaye na miƙe ina kallonsa, yellow t-shirt da black jeans ɗin daya sa sun masa matuƙar kyau, ya juyowa muka haɗa ido nayi saurin rufe idona. Dab dani naji ya tsaya, yasa hannu yana shafa kumatuna yace, "ƙanwar Yayanta bayan wannan akwai wani abun da kike so na daina?". Na buɗe lumsassun idanuna ina kallonsa, ya ɗaga gira yana waro min ido yace, "ehen yi magana mana". ina murmushi na buɗe masa tafin hannuna, ya kalla ya kalleni, na ɗaga masa gira kaɗan ina cewa, "duk dana yarda da kai amma ina so ka mani alƙawari, saboda idan harna kuma ka maka kana shan sigari wallahi nima sai na sha". Ya ɗora nasa tafin hannun kan nawa yana cewa, "na maki alƙawari". Na sauke numfashi nace,"to ka bari ka fara cin abinci tukunna kamin ka fita yarda wancan abun. abincin yana parlo na ajiye maka, Gwaggo tace idan ka gama tana nemanka". Fita nayi na barsa yana zuba abinci, zan shiga side ɗinmu Yaya Haidar ya kirani. Na ƙarasa wurinsa nace gani, fuskarsa a murtuke yace,"me ya kai ki side ɗin wancan ɗan tsintuwar?". Na ɗago da nuna rashin fahimtar maganar tasa. Cikin ɗagin murya ya kuma ce min, "ba ina miki magana bane". Ya miƙo hannu zai buge min baki yana cewa, "za ki maida bakin ko saina fasa shi". "to aini ban gane wa kake nufi ba". "ni za ki rainawa wayo. Ba ki san wanda nake nufi bane, tunda yazo gidan nan na fahimci kanki na rawa, kina wani shishshige masa. Shi sarki ne da ba zai iya zuwa ya ɗauka abincin da kansa ba kamar yanda mukeyi? sai kin wani ɗibi jiki kin kai masa". Na ɓata rai nace, "to ai naga shima Yayana ne tunda ya zama ɗan gidan nan". Bai kuma cewa da ni komai ba naji yaja dogon tsaki ya bar wurin a fusace, nabi bayansa da harara.
***
Gwaggo ce ta fito daga ɗakinta, wanda sai yanzunne ta fito tun tashinta, ganin Haidar da Abba akan dining yasa taja ta tsaya daga shiga kitchen. ƙugu ta kama ta riƙe tana ƙare musu kallo, wannan abu nasu na bata takaici. Iklima dake aikin goge-goge ta durƙusa ta gaisheta. "lafiya lau Iklima, sannu da aiki kinji". "yauwa Gwaggo, ga abincin naki can bari na kai miki ɗaki". tace da ita, "a'a barshi tukunna ba yanzu ba. tun yaushe waɗancan Ƴaƴan suka shigo nan?". tace, "ehh sun ɗan jima". tsaki Gwaggo taja ta hau sababi,"wannan ai shine nayi banyi ba rufe ƙofa da ɓarayi, sam na rasa irin wannan abu, sai a kama zuwar maka wuri tun sassafe ko tashi baka yi ba, a shigar maka kitchen babu izininka, banda uban ci babu abinda aka saka a gaba, sai shegen kashi kamar ɓerayen daji, ina jin Auwalu rannan yana maganar sokawai ɗin gidan nan na neman cika, na rufa muku asiri nace matansa ne. to tsakani da Allah haka akeyi, gaskiya ku rage ci, ni ba zai yiwu ayita zuwar min waje ana aikin turawa ciki ba kuma babu taimakon da za'ai min, ko shara wannan ba'a iya min ba sai dai a ɓatan wuri a zunguri ƙatunan kai kamar randa a ƙara gaba. to gaskiya ni nama gaji da dafawa ƙarti abinci, Auwalu yazo ya shiga tsakanina daku, duba fa don Allah inata magana amma kun min shiru kun cika min kunne da ƙaran cokali kamar ba daku nake magana ba, saboda ni bakwa ganin girmana...to daɗin abin dai ni na haifi iyayenku, idan ku ba ku yimin biyayya ba su sa yi min ai". duk cikinsu babu wanda ya saurareta, sai abincinsu da suka ci gaba da ci, Abba yana kai cokali bakinsa ya ɗago ido ya kalleta, kamar jira take ta zabga mishi harara. Haidar na gamawa ya tashi daga dining ɗin, ta gabanta yazo ya wuce yana rataya earpiece a kunne yaje ya kunna tv, da ido ta bishi, sai daya koma kan kujera ya zauna tukunna tace da Iklima. "ke kashe min kayan kallona kinji, idan kin kammala aikinki na kunna idan zan kalla tunda kayan nawa ne ba na wani ba, kuma Auwalu ya saya min ba uban wani ba da za'a dinga