Showing 78001 words to 81000 words out of 89788 words

Chapter 27 - ALHUSSAIN Complete Hausa Novel

23 Aug 2025

385

yanda na faɗa miki a baya yanzu ma haka zan maimaita miki, na rantse da Allah bani da niyyar cutar da kowa a rayuwata, bare ku da kuka gama yimin gatan komai. ni kaina da Sabina tai yunƙurin taimakona nayi mamaki saboda babu wanda zai so haɗa alaƙa da mutumin da baya da asali, mutumin da baka san shi ba, ki yafe min Gwaggo, ban cuce ku ba kuma ban yaudareku ba, ina matuƙar godiya da kyautatawar da kuka yi min a rayuwa". ya faɗin hakan yana miƙewa, jikina yay sanyi nai saurin kamo hannunsa na miƙe tsaye, nauyinsa ya kamani sai dai wani gefe na zuciyata na rasa me nake ji, wani abune ya tokare wurin. shi kuma ya ɗauke kai daga kallona yay kauda fuska, yana kuma kiciniyar ƙwace hannunsa dana damƙe, murya a hankali nace,"to amma Yaya idan ba kai bane to shi ɗin daya zo wane?. kayi haƙuri na maka bahaguwar fahimta, Yaya ko kaina ka tsinci kanka a irin yanayin dana tsinci kaina za kayi mamaki." "waike maganar me kike ne?". Gwaggo tace dani, ina riƙe da hannunsa na juyo gareta ina cewa,"na rantse da Allah Gwaggo su biyu ne. surarsu iri guda ce, maganar iri guda ce, yanzu haka dana fita wajensa irin kalar kayan nan dake jikin Yaya shima sune a jikinsa, kuma shima ɗin baƙin glass ya saka saɓanin fari daya saba sanyawa, kamar yanda na dawo na tarar da Yaya zaune shima haka na tarar da shi a mota. Gwaggo dole na tsorata nayi tunanin shi ɗin ba mutum bane". na kama hannunsa ina ja nace," idan baku gasgata ni ba kazo muje na nuna maka shi nasan har yanzu yana nan domin na barshi da abinda ba zai iya tafiya lokaci ɗaya ba". ko da muka je gate babu motarsa bare ƙyallinsa, kaina ya kuma ɗaurewa, abin ya kuma ɗaure min kai da kuma tsoro, anya kuwa?. dariyar Yaya tasa ni juyowa ina dubansa, sosai yake dariya wadda har haƙonsa suka bayyana gaba ɗaya,"yarinya ta gama sa ni a ranta tazo wurin saurayinta tana masa kallon ni ne". shine abinda yake faɗa yana kuma dariya har da tafawa. "Yaya kana ɗaukan maganata wasa ko". naji haushi na bar masa wurin. abinda ya ƙunsa min shi na dawo Gwaggo ma ta kuma ƙunsa min, takaici ya isheni na shige ɗaki. cikin kwana biyu gaba ɗaya sai suka koma cewa wai aljanun kaina ne ke buɗe min ido, haka ina ji ina gani da lafiyata amma kullum a cikin yimin hayaƙi ake. na rasa ta yanda zanyi su gasgata ni amma ni dai yanzu ina da yaƙinin Yaya na da alaƙa mai ƙarfi da Proff idan har da gaske ba mutum ɗaya bane kamar yanda na fi zargi, a yanzu jira kawai nake a koma makaranta kamar yanda Farhana ta bani shawara.
[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(25)*
"oak see u letter". na faɗa cikin wayar dake maƙale a kunnena, kuma daidai lokacin da nayi perking motana a parking lot. Hidaya tace,"yauwa karki manta in zaki shigo ki taho min da Arable crop handout ɗin nan". na amsa mata,"ba zan mata ba insha'Allah, bye". na kashe wayan ina jefawa cikin jaka, yayin da Aisha wacce muka fita tare ta buɗe murfin motar ta fita. tana tsaye daga bakin ƙofar tana cewa,"na tafi zaki shigo da kayan ko na ɗauka?". nace da ita a sanda nake fitowa,"ɗauki ki tafi da su, ba zan shiga part ɗinku ba zanyi karatu ne". "oak". ta faɗa tana buɗe bayan motar ta ɗauki kayan da muka amso a office ɗin Baba.
ko sanda na shiga ma Gwaggo bata san na dawo ba, ɗakina kawai na shiga nai wanka na sanyo english wears na fito, naci alelen da na tabbatar Gwaggo ce tayi shi saboda yanda yay daɗi. ina gamawa kuma na suri maltina a fridge nayo waje.
cikin rumfar bunun dake garden ɗin gidanmu na nufa, na zauna kan deck chair ɗin dake wurin. hannuna riƙe da waya wanda na gaza ɗauke ƙwayar idona akanta tun ɗazu, abar ta batun littafin dana ɗauko zan karanta, dan tuni nayi watsi da shi gefe. kallon screen ɗin wayar nake fuskata sai fitar da yalwataccen murmushi take me cike da annashuwar jin daɗi, hoton Yayana ne na shagala a kallonsa wanda yayi matuƙar kyau, gaskiya shi ɗin kyakykyawa ne, a duk wani kallo biyu da zanma hoton sai na lumshe ido. kuma ban sani ba kawai ta bayana naji an rufe min ido, ban tsorota ba saboda ƙamshin turaren daya daki hancina kaɗai ya riga ya bayyanar min da kowa ne. na ɗora hannuna saman nasa ina ƙoƙarin cirewa, sai ya zuro kansa ta gefen wuyana yana leƙen abinda nake kallo, ina jin hakan nayi saurin kifa fuskar wayan saman cinyata don karya gani. "ni bazan gani ba?". Ya tambayeni cikin zazzaƙar muryarsa me sanyaya ilahirin jiki. ban buɗe baki na ba shi amsa ba, sai ɗaga masa kai da nayi alamar ehh, kuma har zuwa yanzu idona a rufe yake da hannunsa, ni kuwa sai aikin murmushi nake ina jin wani abu me sanyi na tsarga min. "ƙanwar Yaya ki barni na kalla abinda ya ɗauke miki hankali har na jima tsaye anan ba ki san da zuwana ba". gabana ya faɗi, wato ma ya daɗe da zuwa ban sa ni ba. _wayyo Allah yasa bai san abinda nake kallo ba._ na faɗi hakan a zuciyata ina rumtse idona dake cikin hannunsa. ajikina naji ya ƙura min ido yana kallona, duk na jin wani iri a tare dani saboda rigar jikina mara hannu ce, ga saman ƙirjina duk a waje kasancewarsa dukiyar fulanina acike take kuma a sama, abinda ma yasa na fito a haka saboda babu mai zuwa wajen idan ba ni ba, saima Aisha dana gani ranar nan tazo tana karatu zasu fara exams. na yunƙura zan miƙe ya maidani na zauna yana me zagayowa ya zauna kusa dani, yana jana da wasa Alallai saina bashi ya kalla. ina samun damar ƙwace hannuna daga nasa na miƙe da sauri ina ja da baya ina dariyar dake daɗa ƙawata kyawun halittar fuskata, haɓa ya riƙe yana kallona, ni kam sai dariya nake masa. na ɗan tsaya ina cewa,"ka gama ƙiyasce ƙiyascenka amma ni kam bazan baka ka gani ba". nace da shi ina yi masa gwalo. tasowa yay ya biyoni muka fara guje-guje, gaba ɗayanmu ƙyalƙyala dariya muke, banyi aune ba caraf naji ya damƙo hannuna ta baya, muka tsaya muna aikin sauke numfarfashi, ina ƙara ƙanƙame wayata saboda bana so yaga hotonsa da nake kallo. dab dani ya matso kamar zai mannu da jikina, yana zuro kansa ta kafaɗata yace,"wa na kama?". ina maida numfashi na lumshe ido, jikina yay sanyi ina jin wani iri a tare dani saboda yanda tsigar jikina ta tashi sakamakon ɗumin iskar bakinsa dake sauka ajikina adalilin numfashin daya ke saukewa shima. na turo ɗan ƙaramin bakina gaba ina cewa,"to wai miye ruwanka da abinda nake kallo, ni Allah ba zan baka wayana ba". na ƙarasa faɗa cike da shagwaɓata mai narkar da zuciya. juyo dani yay muna facing juna, fuskarsa lulluɓe da murmushi mai kyau, ya kafeni da ido ko ƙiftawa babu, nima hakan take agareni domin tunda na fara kallonsa na gaza ɗauke idona ko da na second. sautin murmushinsa ya fito har haƙoransa farare na bayyana, ya ɗan zoro min ido kaɗan yana ɗaga gira duka biyun. da sauri na sauke idona ƙasa cike da wata muguwar kunya, na fizge hannuna zan gudu ya kuma kamoni yana faɗin,"zo nan sai kin faɗa min mene kike yi da hotona?". gabana ya faɗi na ɗago na kallesa, ya sake ɗaga min gira yana cewa,"uhmm tell me, ai ina ganinki tun ɗazu, me yasa kike kalle min hotona? idan ba haka ba yanzu na shigar da ƙararki kotun Gwaggo". na hankaɗo baki gaba ina ɗan tirtirjewa nace,"wane yace maka hotonka nake kalla, to ni mene zanyi da hotonka da zan zauna ina aikin kallonsa bayan gaka a gida. na ma gane wayo ne kake son yi mani kuma naƙi wayon bazan dai nuna maka abinda nake kallo ba". na ƙarasa faɗa ina siririyar dariya me bayyanar da haƙora. shima dariyar waskewar da nake neman yi yayi, ban aune ba kawai naji ya fizgi wayar hannu, nan da nan kuwa na hau dukan ƙafafu kamar zanyi kuka ina cewa ya bani wayata kar ya buɗe min. na murguda baki ina cewa,"to ai dai ma baka san password ɗin ba, ni ka bani kayata bincike babu kyau". na faɗi hakan ina miƙa hannu zan amshe shi kuma yana kaucewa. kallona yay kawai yayi dariya kaɗan kana yace,"ki ƙaddara ban san password ɗin ba, amma idan na buɗe kyautar me za ki bani?". na ɗaga kaina sama ina nazari, tsawon daƙiƙa ɗaya nace,"shikenan naji in har ka buɗe ni kuma duk abinda kake so ka faɗa zan baka ko menene shi". na faɗi hakan saboda ina da tabbacin ba zai iya buɗewa ba, kusa da shi na tsaya ina kallon yanda zai buɗe ina masa dariya ƙasa-ƙasa. gani nayi yana rubuta Yayana, abinda ya matuƙar bani mamaki, taya akayi yasan password ɗina? bayan wayata bata taɓa zuwa hannunsa ba, kuma ban taɓa buɗewa agabansa ba tunda fingerprint nake amfani. muka haɗa ido ina masa kallo mai alamar tambaya da kuma tuhuma. na tsuke fuska na kama ƙugu ina cewa,"taya akayi kasan passowrd ena? wato ka jima kana ɗaukar mani phone kayi min bincike ban sa ni ba ko?". yanayin irin yanda yara ke rantsuwa yayi yace,"ni wallahi Allah ban taɓa ɗaukar maki waya na buɗe ba, kawai fa nayi guessing ne....to ni dai bama wannan ba tunda na buɗe saiki ba ni kyautar da kika ɗau alƙawari". ya faɗa yana sarƙe hannayensa ta baya. zanyi magana ya tari numfashina da cewa,"tsaya tsaya! tukunna ma kika ce mene za kiyi da hotona?, to yanzu mene wannan, gashi nan a wallpeper kuma gashi a screensaver. shikenan ma gano ki yarinya, wato kina kallona kowanne lokaci don ki cinye min kyawuna ya dawo kanki, saboda na fiki kyau, shine ma idan mun fita kike jin haushi idan ƴan mata na bina, to kuwa wannan kyan ƙwalelenki, ba za ki taɓa ƙwace min shi ba ki kashe min kasuwa". na kalleshi ina hararansa, na ɓata fuska na juyar da kai gefe ina cewa,"su ƴan matansu sune basu san kyau ba da har suke maka kallon me kyau, ni kam dana ke wise ai ban taɓa ganin kyan ba bare har ya burgeni...yanzuma Malaminmu ne yace mu zana mutumin da yafi kowa muni a duniya za'a buga shi a kafa hoton a gidan zoo, ni kuma ina shawara da zuciyata tace nayi drowing ɗinka, kaga ma na taimaka maka tunda kana jin daɗi ƴan mata na kallonka, kaga idan ka fita yanzu sai ake biyan naira biyar naira goma ƴan wahala suyita zuwa can suna ganinka". dariyar da ya bushe da itane yasa na juyo ina kallonsa cike da jin wani abu a raina da na kasa tantance menene, ya dage sai sheƙa dariyar yake babu ƙaƙƙautawa harda su tafa hannu yana kifawa, sai ya ɗago ya nuna ni da yatsa ya kuma kifawa ya tuntsire da wata dariyar. kamar na fashe da kuka don haushi, na juya zan tafiyata ya biyoni yana dakatar dani da cewar,"Malama dakata mana. kin manta da kyautata fa. ki tsaya ki bani sai kiyi tafiyar kije kici gaba da aikin zane na tunda na zama celebriry". "sai ka faɗi abinda kake so ai". ina faɗa ina murguda masa baki don duk haushinsa nake ji, na rufe ido ina ƙara tamke fuska ina hura hanci, kawai kuma sai kuka ya taho min lokaci ɗaya hawaye ya shiga sauko min. jinsa nayi ya kama haɓata yana ja yana haɗa ƴar waƙarsa wai nayi shiru sai kace yaga wata ƙaramar yarinya. "ki taimake ni ki bar kukan nan, ki rufan asiri a wurin Gwaggo kar na shigesu yau a wurinta". na bige hannunsa ina cewa,"ai duk saina faɗa mata ka sa ni kuka, dama tace zata rama min kwaɓe min lallan da kayi. ni ka faɗi abinda zan baka nayi tafiyata, kuma daga yau na bar kulaka". hannuna ya kamo ya jawoni kusa da shi sosai, wanda tazaran dake tsakaninmu ko 1inch bai kai ba. tukunna ya juyar dani ya ɗora haɓarsa bisa kafaɗa yana kewaye cikina da duka hannayensa, ban nuna masa haramcin hakan ba saboda ni kallon matsayi guda da Yaya Abba nake masa, ga kuma wani yanayi da na shiga wanda nasan dole ba zan iya hana shi ba. "Cutie". a hankali ya faɗi sunan daya ke kirana da shi yanzu, yana kuma manne gefen fuskarsa da tawa. na daɗa lumshe ido ina haɗiyar wani yawu kamin na amsa. "ummm". a kasalance sakamakon iskar numfashinsa dake sauka cikin ƙirjina. hannunsa ya ɗago ya nuna ƙirjina saitin ɓangaren zuciyata da manuniyar yatsansa, da wata iriyar murya ya furta, "Cutie nah, Cutien Yayanta, abinda ke cikin nan, abunda ke cikin nan nake so, shi nake so ki mani kyautarsa...kinji dan Allah". da rashin fahimtar abinda yake nufi nace,"ban gane ba. miye ne dama acikin nan ɗin banda ƙashi, indai ba kaina zan baka gaba ɗaya ba ka kaiwa Gwaggo ta dafa maka ka cinye". yay wani murmushi, yana kuma yin ƙasa da murya yake cewa. "nima nafi so ki mallaka min kan naki gaba ɗaya amma bazan cinyeki ba saboda ina buƙatarki". yana juyo dani na fuskance shi yake ƙarasa cewa,"sai dai na tsaga ƙirjina na adanaki a ciki ta yanda babu wanda zai ke kalle min wannan cute face ɗin sai idan ni naso". yana faɗin hakan yana shafa kumatuna da babban yatsansa. tsintar kaina nayi sakin murmushi, iskar bakinsa daya hura min a ido ita ta dawo dani daga duniyar tunanin dana tafi cikin ƙanƙanen lokaci, nai saurin sanya tafukan hannuna ina rufe fuskata. hannunsa yasa ya ɗauke hannun nawa, shima murmushin yake amma mai ɗauke da wata ma'ana, tun daga tsintsiyar hannuna ya kama har zuwa yatsuna yana mai tsugunawa agabana ya dire gwiwansa ɗaya a ƙasa, ya kamo yatsana na kusa dana tsakiya yana cewa dani,"please close your eyes". na rufe idona, zuwa wani lokaci naji ya saki hannuna yana cewa na buɗe idona, ina buɗewa na gansa ya miƙe tsaye, ya kalleni ya lumshe ido, sannan yay min nuni dana kalla yatsuna. ina duba hannuna na furta,"wow". da ƙarfi tare da yin tsalle, ina matuƙar nuna jin daɗina. kallon zoben nake ina jin wani farinciki a raina don ba ƙaramin kyau yayi ba, tsanin jin daɗi yasa na faɗa jikinsa tare na rungume shi. "thanku so Much Yayana, gaskiya naji daɗin ring ɗin nan ya mani kyau kamar ni. na gode, na gode Allah ya ƙara maka kuɗi da yawa". na sake shi ina cewa, "Yayana taya kasan ina son zobe matuƙa". kallona kawai yake da numsassun idanunsa ba tare daya furta komai ba, ina kallonsa na ɗaga masa kai alaman mene, duba da yanda mood nasa ya sauya zuwa damuwa saɓanin ɗazu da yake cikin nishaɗi. kai ya girgiza min alaman babu komai, na zunɓuro baki ina cewa,"to kai kurma ne, kayi magana mana". ya rumfe ido ya buɗe, har yanzu kuma bai ce min komai ba, ina wasa da zoben daya samin nayi ƙasa da kaina ina cewa,"Yayana to ka faɗa min kyautan dana maka alƙawari, ɗazun ban gane me kake cewa ba". murmushi naga yayi, ya lakuce min hanci yana cewa,"zama ki gane ne yarinya mai wayo". yana faɗin hakan ya kamo fuskata yay min kiss a goshi, tukunna ya zuba hannayensa a aljihu ya juya ya tafi, ya barni tsaye ina aikin juya zoben dake hannuna wanda har yanzu jin daɗi ya hanani rufe bakina.
dukkan abinda ke faruwa tsakanin Sabina da Alhussain akan idon Haidar dake window a tsaye, be saki labule ba sai daya ga barin Alhussain a wurin, samun zuciyarsa yayi da babu daɗi, ya jingina kansa da bango tare da rumtse idanuwansa. lokaci ɗaya kansa ya hau ciwo, ya dafe ɓari ɗaya daya fi masa azaba, idanuwansa suka fara tara zafin baƙin ciki, zuciyarsa kuwa ta canza takun bugunta, gaba ɗaya duk wasu sassa da gaɓoɓin dake jikinsa sun fara shiga wani yanayi na azaba. jiri ne ke ɗibarsa sosai dan haka ya faɗa kan gado yana fuskantar sama, yana sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya. idonsa na rufe yake hasko abubuwan da suka wakana tsakaninsu, mai kama da zallar soyayya, abunda yafi tsaya masa arai yanda Alhussain yasa hannunsa acikinta da kuma haɗa fuskarsu, gashi har yana da damar yi mata kiss kuma yasa mata zobe, Wata bahaguwar ajiyar zuciya ya ƙara yi, hannunsa dafe da saitin zuciarsa. tunda yake bai taɓa shiga tashin hankali irin haka ba, sai yanzu ne Yake mamaki ƙwarai matuƙa da yanda yake jin Sabina a ransa, me yasa tun farko ya kasa ɗaukan hakan a matsayin *SO* ?, mai yasa ya kasa barin yarinyar ta saba da shi ko da ace bada sanin yana sonta bane, shi kansa ya san babu kowa a zuciyar Sabina amma yanzu gashi farat ɗaya wani daban yazo ya shige zuciyarta, wani irin ƙullutun baƙin ciki ne ya tsaya masa a maƙogaro. da ƙarfi yasa hannu ya daki goshinsa, jin zuciyarsa yake na neman fitowa, ƙululun abinda daya tokare masa zuciya SO ne ko kuma KISHI? idan duka biyun suka haɗe suka tabbata ya zaiyi? dan ba zai taɓa iya furtawa yarinyar cewar yana sonta ba, kuma gashi ba zai iya jurar ganinta da wani ba.
zuwana compound nayi kiciɓis da Umma, na rissina ina cewa,"Umma ina yini, ya sauƙin jiki? Allah ya ƙara lafiya". na haɗe maganta duka don na san ba lallai ta amsa min ba. ina kallo ta taɓe baki bayan ta kalleni, na duƙa ƙasa zan cire abu a takalmina naji tana cewa. "ahaka dai za'a lalace, anƙi ai aure sai aikin jera kafaɗu da manya saboda babu kunya, anje an ɗauko mutum da niyyar taimakonsa an ɓige da iskancin banza a bayan idon mutane, to bari Baban naki ya dawo zan zayyane masa komai saboda baza aci amanata da shi ba,

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login