Showing 60001 words to 63000 words out of 89788 words

Chapter 21 - ALHUSSAIN Complete Hausa Novel

23 Aug 2025

389

ba".
[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(21)*
Bayan Kwana biyu, Zaune nake kan plastic chair a balcony dake upstairs namu, ina karanta wani haɗaɗɗan novel mai ɗauƙe da wata iriyar soyayya mai burgewa, da kuma sawa kaji kana buƙatar kasancewa da saurayinka a lokacin, banma san sunan littafin ba sai da shafin ya yanke min, da sauri nayi scrolling back na duba sunan novel ɗin. *ƘADDARA TA RIGA FATA* naga an rubuta daga haziƙar marubuciyar nan mai suna Anty Nice, cikin sauri na Kunna da ta na buƙaci da a turo min sauran, babu ɓata lokaci kuwa sai ga Oum Ramadhan ta turo mani, godiya nayi mata sosai sannan na kashe datan naci gaba da karatuna, ban ɗau wani lokaci ba na kammala karanta shi, Soyayyan Hummy da Dr ta ƙayatar da ni, sosai littafin yayi daɗi ya kuma faɗakar, ba ƙaramin jinjinawa marubuciyar nayi ba. Daga nan kuma na ɗora da littafin Al'amari, tunda naci karo da page ɗin da ake zayyano kamannin Hammah Saddam na fara shiga wani yanayi, Gaba ɗaya yanayin kamannisa da ake lissafawa sai yake min kama da Yayana, Banbancin su ɗaya Yayana yafishi haske sosai, wani sanyayyan murmushi na sa ki ina ƙara gyara zaman karatuna, Saurin lumshe ido nayi a lokacin da nayi katari da wurin da Hammah Saddam ke nunawa Tasleem ɗinsa tsantsar so, Na jinginar da kaina bisa kujera ina daɗa lumshe ido ina ƙiyasto ni da Yayana. Ta ke kuma naji ruwan hawaye na cika min ido, kewar Yayana ta dakar min zuciya, ina shirin fashewa da kuka na jiyo ƙarar hayaniya a compound, tashi nayi na leƙa, su Aisha na hanga sun kewaye Inna Karima suna murnar zuwanta, tsallen murna na buga na wurgar da wayata akan gado na fice da gudu ina, "oyoyo Innah". Ina zuwa na ɗafe jikinta. "laaa kunga yarinya zata kada ni". Ta faɗa tana dafe jikin mota, Sakinta nayi ina dariya. Ita kuma ta bini da wani kallo tana taɓe baki, Kamar dai yanda na faɗa muku a baya, Inna Karima macece da Allah ya dasa mata zuciyar kushe, a hakan ma kallon da take mini tana taɓe baki neman makusa take a jikina, kai ni dai na godewa Allah da Gwaggo bata yo halinta ba, na basar kamar ban san tanayi ba, ina ƙara faɗaɗa fara'ar fuskata ina masu sannu da zuwa. Jakar hannunta na amsa, ina kallon Mardiyya a gefe sai wani shashshan ƙamshi ta ke, ko takanta banbi don ba shiri muke ba, na kalla yarinyar da suka zo tare, wanda na fahimci itane ƴar aikin da aka kawo mana, ina mata murmushi nace muje ciki ƴar ƙanwata, ina ta jin daɗi na sami abokiyar hira duk da ni bana zaman kaɗaici tunda ina da Gwaggo. Inna Karima ta yaba gidanmu sosai, ni dai hankalina na kan naji batun kwana nawa zasu yi. Ta kalla Gwaggo tace, "wai Matan gidan basa nan ne?". "suna nan mana". "amma naga babu wadda tazo ta gaida ni". "ni kaina da nake zaune da su ba gaida ni suke ba, gani dai uwar miji, basa ganina da girma wannan tarihin kin sani ba sai na ƙara ba ki ba, don haka kinga ni dai bana son magana don na san halinki, nima adu'a nake musu Allah ya shirya su". Abincin da Inna Karima keci ta tashi akai, ta fita compound tasa aka kira mata su Umma, tayi musu tatas wanda har dukanmu sai da muka ji dama bata zo ba, saboda yanda tasa Baba a gaba tana masa faɗa tana zaginsa, su kuwa kowacce haƙuri ta shiga bata don suna tsoronta, ita bata wasa kamar Gwaggo da ta ke ƴar barkwanci. Har dare Inna Karima bata bar masifa ba, Gwaggo dai bata ce mata komai ba, don dama idan tana masifa duk bakin Gwaggo mutuwa yake. mai aikinmu Iklima na kusa da ni a zaune, saboda ni bani da ƙyama, tunda suka zo nasa tayi wanka na bata kaya masu kyau ta saka, cikin lokaci kaɗan har mun fara sabawa da ita, yanzu haka ma kallo muke a wayata, Mardiyya na gefenmu tana waya da saurayinta, na bawa Iklima wayar nace taci gaba da kallon kamin na dawo. A parlo na sami Inna Karima tasa Baba gaba sai zazzage shi take akan yaƙi aurar dani, ya barmi sai kumbura nake ina jera kafaɗa da shi da matansa, ba zai aurar da ni ba sai karatun boko ya gama lalata ni tukunna, wannan kayan haushi da yawa yake. Shi dai Baba haƙuri yake bata yana kuma ƙoƙarin ganar da ita, amma kwata-kwata taƙi fahimta, har cewa ta ke da mahaifiyata nan ba zata taɓa zuba ido tana ganina a haka ba ban cika mace ba har yanzu, saboda ita tasan ƙimata kuma tana ƙaunata... "ni kuma da nake riƙonta ai kin san ba ƙaunarta nake ba". Gwaggo ta faɗa a ƙufule. "ni ba haka nake nufi ba Yaya, amma dai zuwa yanzu kam ya kamata ku gane yarinyar ta girma, kuna tare da ita amma kamar ba kwa ganinta". "yo ke da kike ganinta kuma kika gane ta gama haɓɓaka me zai hana ki aurar da ita wai, ni duk kinzo kin isheni da hayagaga baki sai warin goro yake. To ki sami damar yimin shiru tunda bake ce a gaba dani ba, da za ki sa ni a gaba kina min faɗa kamar wata uwata". Ta juya ga Baba tace, "kai Auwalu tashi ka tafi, ɗiyar albarka ce dai ba yanzu zan aurar da ita ba dan haka sai a bini da ido kawai. A jira har sai randa ta kawo min wanda yay male-male a zuciyarta tukunna". Baba ya miƙa ya fita bayan yay masu sai da safe, Gwaggo kuwa taci gaba da sababinta a yayinda Inna Karima taja baki ta tsuke, alamu dai taji haushin maganar da Gwaggo tayi mata. Gwaggo kam bata fasa maganarta ba, sai ta koma ma kamar bada Inna ta ke ba. "shi mutum bashi da shanka bare cinka amma duk yabi ya damu da zamanka a gidan ubanka. To ki faɗi kwanon shinkafarki nawa take ci sai a biyaki tunda kin gaji da ci da ita". "yo na kuma magana kice bakina na warin goro Yaya, gaskiya ce da kai ba'a son ka faɗa. Amma ita ai ba dutse bace da har zuwa yanzu zata ce ba wani abu dake tsikarinta". "yo Allah na tuba shekarun nata nawane gaba ɗaya, sha tara ne fa ta ke yanzu, girman kajin gona tayi shi yasa duk tabi ta tsone miki ido. Ga shi ita ba kazar ba ballantana kice za ki siya ki dafa kiyi mata cin yunwa, wannan luhu-luhun tsokar haka za ki ganta ki mayar da ƙwaɗayayyan yawunki". Dukansu haushin juna suke ji, Sai harar juna suke. Abin nasu yaso bani dariya, Na zauna kan kujera na ɓata fuska ina turo baki daka ganni kaga wadda ke cikin fushi. Inna Karima da baki bai mutuwa ƙara faɗa ta ke, "ji dan Allah yanda nono ya cika ƙirjin yarinya, komai yaji zamzam a halittarta amma an take gaskiya an Kama huɗubar bature. Ga sa'aninki nan a ƙauye duk sunyi aure, harda masu ƴaƴa Kin tsaya nan kina daka ta ubanki". Gwaggo dai ta taɓe baki, ni kuma na ƙara haɗe gira nace, "to wai Inna da kika damu da nawa ita Mardiyya da take jikarki mene yasa ita ba za ki sa mata ido ba". "au saboda ba ki da kunya ni kike faɗawa wannan maganar, yo ba ƙwamma ita bazawara ce ba, ke kuwa fa. Shekaru 19 kina ƙoƙarin dosar ashirin amma ba ki taɓa leƙan gidan miji ba. Ba tun yanzu ne nake tambayar yaushe ne za kiyi aure ba? Ganin sa'anninki duk sunyi aure, Amma ganin laifina ake ba'asan mutunci nake nema miki ba". abun yay min ciwo, ban san lokacin dana fara ce ma ta, "Addah Jummai, Inna Talatu, Gwaggo Ladi, Hajiyan Jos. Inna Sa'anninki da yawa duk sun jima a ƙabarburansu, mene yake faruwa dake ne? Ya akai ke shiru haka? Ya naki labarin tafiyar? Yaushe ne za ki mutu? me yasa aka zuba maki ido har yanzu ba ki mutu ba?". Ina dubanta naga tayi shiru, nace, "Inna tambayarki nake ki bani amsa". Nan ma shiru tayi min, na sake cewa, "To Innah Yanda mutuwa bata da lokaci haka ma aure, yanda mutuwa ba gasa bace hakama lokacin aure, yanda burin kowa Aljannah haka burin duk wani marar aure abokin rayuwa nagari. Yanda ba'a rubuta ma kowa lokacin mutuwarshi a goshin shi ba, hakama wasu ba'a rubuta musu rabon aure a rayuwarsu ba, kuma ba'a rubuta musu lokacin auransu ba a goshi. Ni kuma bana rasa mijin aure bane, ban shirya yi yanzu ba, ki bar ganin banda mashinshina. Don Allah Innah ki sakar min mara kiji da Mardiyya ita da zaman ɗaka kawai ta ke babu arabi babu boko". Ina kallon Gwaggo na dariya ƙasa-ƙasa, ni kuwa na miƙe nai wucewa ta ɗaki, ina jinta tana faɗin, "to aini da na shigo wannan daular niyyata na jima ina shan jar miya mai naman ɗawisu acikinta, ashe tafiyata dole ta kama gobe goben nan". Gwaggo tace da ita, "kofa mene ke kika ja ta gaya miki haka, akan me kuma za ki ji haushinta". Kwanan Innah biyu muka wuce kano, naji daɗi da bamu taho da Yaya Abba ba, a gidan Hajiya na sauka wadda ta haifi Mamana, tayi farincikin ganina sosai. Abinci kawai naci na miƙe na shiga wanka, ban ɓata lokaci ba a shirin da nake yi, nayi kwalliya mai kyau, hijab ɗina sai tashin ƙamshi yake na fito, Hajiya dake kishingiɗe a parlo ta dube ni tace,"ke kumburin burodi ina zuwa kuma daga saukarki? Ko abincin da kika ci fa bai gama tsarga miki ba". Ni kam bana son wannan sunan da Hajiya ke kiran da shi, da yake itama ƴar ayi ce irin Gwaggo, na ɓata rai ina cewa, "Hajiya na fa yi girman da ya kamata ki daina ce min kumburin burodi". "to Mama'nki ma har ta mutu ban daina ce mata kumburin burodi ba, kinga kema kuwa banga ranar daina faɗa miki ba tunda kinyo gado". Na turo baki gaba ina yin kamar zanyi kuka, ta kamo hannuna ta zaunar dani Saman cinyarta, ko nauyina ba ta ji. "haba jikar Hajiya da Gwaggo sarkin shagwaɓa, ƴar lelen Babanta, maida bakin naki kar ya tsaya a haka samari suce basa so, kinga yayi dogo da yawa sai kace payis". Ta faɗi hakan tana ɗan yimin cakulkuli, na ƙyalƙyale da dariya kamin na kuma cewa,"amma dai kin daina cemin Kumburin burodin ko?". Tace, "kema kin san ba zan iya ba, saboda duk sanda na tsokane ki da haka kina tuna min da marigayiya ne, komai naki sak na mahaifiyarki har wannan shagwaɓar. Itama idan nace kumburin burodi haka zatai ta aikin buga ƙafa tana cewa bata so, Babanta kuwa hake yake ce mata kazar gona, shi kam daya faɗa zata fashe da kuka sai ansha da ƙyar zata yi shiru, Sabina wallahi komai naki babu maraba da Halima". "Allah sarki Mamana Allah ya jiƙanta. Hajiya naso ace naga Mama ko da sau ɗaya ne, amma ko da yaushe sai dai na kalleta a hoto ina jin kamar na fito da ita tayi min magana". Ta goge min hawayen daya sakko tana cewa, "karki kuka mana kuma ki ɓata kwalliyar taki, ba gashi Allah ya bar miki mu ba. Ina za ki ne haka kamar wadda ta shirya gasar kyau?". "da gaske Hajiya nayi kyau?". "wallahi sosai ma kinyi kyau, tsab za kisa ɗa namiji tuntuɓe a hanya. amma ni kin san bana son fice-fice ina zuwa haka?". Ina roƙonta nace, "don Allah Hajiya yanzu zanje na dawo, gidansu Farhana zanje". Da ike itama tasan Farhana tace to saina dawo amma kar na jima. ina tsokanarta nace, "to Hajiya idan kinji shiru sai ki bini Abuja". Dariya kawai tayi ni kuma na fice, sai dana bari nayi nesa da gida kana na tari mai napep saboda kar Uncle Musbahu ya ganni, don naji yana shago yana ɗinki. Sharaɗa nace masa ya kaini, har inda Yayana yake zama ya sauke ni, na fito ina kallon wajen har ya fara sauyawa saboda yanda aka yiyyi gine-gine, shi kansa kangon da Yayana ke zama ciki har an fara sa masa dakin, waje ma anyi masa fulasta. Ƙafata tayi sanyi, ƙirjina na bugawa na ƙarasa ƙofar kangon, gaba ɗaya na dudduba banga alamar ƙyallin ko inuwar mutum ba. Tuni naji komai na duniya ya daina min daɗi, na shiga tsananin damuwa, ina taka ƙafa da ƙyar na ƙarasa wurin wani mai shago, sallama na masa ya amsa min, na tambayeshi don Allah ko yasan wani bawan Allah dake zama a kangon nan na kusa da shi. "wani ɗan shaye-shaye ko?". Ya tambaye ni. banji daɗin tambayar da yay min ba, domin da a hayyacina nake zan gaya masa babu daɗi, na ɗaga masa kai kawai. Yace, "Ayyah ai wannan ƴan sanda sun jima da yi mana maganinsa...". Bai ƙarasa ba na katse shi, "ban gane me kake nufi ba?". "ina nufin yana gidan maza, kusan wata shida da kamashi kenan". Nai ƙoƙarin tare kukan dake neman fito min nace, "a bisa wanne laifi aka kama shi?". Yana ƙulla madara a leda yace, "yo Hajiya irin waɗannan ai annoba ne a unguwa, hukuma tayi ram da su shine dai-dai". Ban iya cewa da shi komai ba na juya na fita da ƙafafuna da suka min nauyi, idanuwana na tsananta zubar hawaye, zafin da nake ji a zuciyata ba zai iya misaltuwa ba, ni ɗaya nasan tashin hankalin da nake ciki, saura kaɗan wani mai mashin ya bigeni naji an jawo ni, mutumin ya hauni da masifa ina tafiya ina tunanin banza zan haɗa accident. Sam ban san halin nake ciki ba sai a yanzu da yay maganar, na kalla inda nake tafiyar na kalleni tsakiyar hanya da ababen hawa ke wucewa. "kayi haƙuri don Allah". Ina faɗa ina ƙoƙarin barin wajen. "idan ba damuwa ki tsaya zanyi magana dake. Zan shiga wancan shagon naga kin fito kina kuka, na tambayi mai wurin yake gaya min wanda kike nema". Ni dai bance masa koma ba, sai dafe kaina da nayi wanda naji juwa na neman ɗibata ta zubar a ƙasa. Maganar da yay ne ta dawo dani hayyacina nayi saurin ɗagowa ina dubansa. "ya ce mashayin bakin bola kike nema?. Duk abinda ya faɗa miki gaskiya ne amma bai san da cewar an fito da shi ba. Sai dai ya bar wurin da yake zama, idan kika zaga bayan masallacin nan daga wajen wata bishiya za ki gansa zaune a wurin, yanzu muka fito daga masallaci tare da shi". Ban jira sauran maganarsa ba, haka Ko godiya ban tsaya yi masa ba, tuni na juya ina tafiya cikin sauri har na isa inda yay min kwatancen. Ina zuwa kuwa na hangi mutum zaune akan dutse ya juya baya, ban san lokacin da murmushin jin daɗi ya subce min ba, na ƙarasa wurinsa ƙafafuna na rawa, na tsaya a bayansa ina jin kamar na rungume shi saboda yanda nake jin wani farincikin a raina. "Yayana". Na kira sunansa ina mai jan harufan ta wani irin siga ba tare da nasan nayi hakan ba. shi da yake zaune yaji muryar da har mutuwarsa ba zai taɓa mantawa da ita ba, yay shiru yana jiran ƙara sauraron zaƙin muryar, ganin bai juyo ba hakan yasa na zaga gabansa cike da zumuɗin son ganin fuskarsa. Annashuwar farinciki na ƙara bayyana a saman fuskata na zube a gabansa, haƙorana duk a waje saboda na kasa ɓoye jin daɗina, sai dai yanayin da idona ya hau kansa komai nawa ya tsaya cak, hankalina yay ƙololuwar tashi, a jere na jefa masa tambayoyi baki na karkarwa a yayinda da ruwan hawaye ya cika min ido suna zuba. "Yayana mene haka nake gani a jikinka? Wannan bandage ɗin na mene? Aina ka sami ciwuka masu yawa haka? garin ya ya hakan ya faru da kai? wane yay maka hakan?". Nayi maganar gefen zuciyata na harbawa da tsananin zafi, a yayinda tsananin tausayinsa ya kanainaye ilahirin jinin jikina, na miƙa hannuna dake rawa zan kamo fuskarsa ya janye kansa. a hankali laɓensa na sama dana ƙasa suka tale suka buɗe wajen faɗin. "ina kika tafi watanni da yawa? me yasa kika daina zuwa inda nake? me yasa na daina ganinki? a haka kika fito da fuskarki waje jama'ar duniya suna kallonki? Ina niƙab ɗinki? Me yasa ba ki saka ba?". A wani irin yanayi tambayoyin nasa suka jefani, yanayin dana kasa gane mishi, na kasa jurewa kallon da yake min na sadda kaina ƙasa, nafi buƙatar daya amsa min nawa, ina ɗagowa naga ya kauda fuskarsa gefe, idonsa a lumshe, yana ƙoƙarin tashi ya bar wurin nayi saurin kamo hannunsa na maido shi ya zauna.
[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(22)*
harufan bakina na fita a kakkarye nace da shi,"Don Allah Yayana". kalaman bakin suka fito acikin siga ta roƙo ina mai ƙare damƙe hannunsa. Cak ya tsaya ya dawo ya zauna, yana ta so ya ƙwace hannunsa daga riƙon dana masa amma na hana, kansa na kallon ƙasa yay shiru bai magana ba, damuwa na ƙara bijiro min na datsi shirun da cewan,"Yaya zuciyata matsewa takeyi, dan Allah ka faɗa min wannan ciwon fa?". ya ɗago ya sareni da ido, sannan ya buɗi baki yace,"ni me yasa ba za ki amsa min nawa ba?". "to aini na fara tambayanka". Yace, "idan har aka ɗora duka tambayoyin a bisa mizanin ma'auni, nawa ita tafi muhimmanci da cancantar amsawa sama da taki, duk da cewan tambayanki yafi yawa amma girman tawa zata rinjayeta. Na rantse miki idan har ba ki bani amsar dalilin da yasa kika fito babu niƙab ba, zan tashi na tafi, tafiyar da har abada ba za ki kuma ganina ba". Ban san lokacin dana haɗa yatsuna da nashi wuri ɗaya ba ina wasa da su, na fara magana ina cewa,"kamin mu bar gari nazo har sau huɗu bana samunka, har a ƙarshe na bar maka saƙo wanda idan ka gani zaka

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login