Showing 72001 words to 75000 words out of 89788 words
min na miƙe ina cewa,"kuma ban gode ba". na faɗa ina murguɗa masa baki. kamin na bar wurin ya damƙo hannuna, shima ya miƙe tsaye, dab dani ya tsaya yana cewa,"ina jin haushinki shine za ki ƙara ɓata min rai ko". ashe lallen daya cire min ya kwaso a hannunsa, ban sani ba naji ya mulke min shi a fuska, sannan ya cika ni yay ficewarsa. cike da takaici na ɗauka wayana dake ringing nayi ɗaki, ina tunanin abinda zan masa na huce, haka kawai ni ban san me nayi masa ba yana cewa yana jin haushina, na shiga toilet na wanko fuskana inata jera ƙwafa. ina karkaɗa kai na ɗaga kiran wayar daya kuma shigowa, sallamar muryar dana jine yasa ni rufe ido ina jin faɗuwar gaba, ban san me yasa ba a duk lokacin da naji muryan Proff sai gabana ya faɗi, kuma duk da cewan muryansa iri guda ne dana Yayana amma shi akan Yayana bana jin hakan, sai dai kaina yana ɗaurewa akan wasu al'amuransu. "Beauty nah". ya katse min tunanin dana tafi. "na'am sir". ko taya akai ya gane, sai ji nayi ya jefo min tambayar,"lalala wa ya taɓa min Beauty, wa ya ɓata miki rai umm Beauty nah?". cikin sanyin shagwaɓata nace,"Yaya ne, kuma ba abinda na masa". na faɗi hakan ina turo baki kamar ina gabansa. "Ya Salam shi Yayan da kansa, gaskiya bai kyauta min ba. amma kiyi haƙuri kinji, Yaya ne babu yanda na iya da shi da na ɗau mataki yanzun nan. yanzu kiyi haƙuri kinji, oya yi dariya naji". ya faɗa kamar yana magana da wata ƴar yarinya, ban kuwa san lokacin da dariyar ta subce min ba nace,"ai ka rabu da shi zan rama ne". Yay siririyar dariyar da sai dana furgita da jinta da kuma sautinta, na rantse da Allah irin dariyar Yayana sak, kalle-kalle na farayi a ɗakin naga ko dai shine ya shigo, sai naga babu kowa, na buɗe baki nace, "Proff...". ban ƙarasa ba naji an fizge wayata an jefar a ƙasa, ina ɗaga kai naga Yaya Haidar a kaina. da muryar ɓacin rai yake nuna ni da yatsa yana cewa. "ke ba ki da mutunci ba ki da hankali ba ki da tunani ba kya aiki da iliminki ko. kin maida kanki ballagaza kowane kare ɗora idonsa yake ajikinki, ki kalla a yanda kike fita parlo bayan duk kin san maza ne a wajen, amma saboda shashanci yay miki yawa an gama sangartaki ke ba ki san abinda ya kamata ba. to ki jini da kyau, duk randa kika kuma bari wancan ɗan tsintuwar ya kuma kusanto inda kike ma sai ranki yayi mummunan ɓaci, bare ki bari ya taɓa miki hannu, za ki kalla yanda zan dake". na buɗi baki zanyi magana naga har ya fice ya barni da takaici, ni yau kam gaba ɗaya sun gama ƙona min rai duk su ukun, shi ko meye ruwansa dani oho. Gwaggo kuwa tunda ta isa ɓangaren Umma taga yanayin da take ciki hankalinta ya tashi, ta fashe da kuka tana cewa,"Allah sarki Hajara sannu kinji. Allah ya ba ki lafiya ya yaye miki. wai dama shi ciwon tun yaushe ne?". ta ke tambayar Yaran. Amina tace,"tunfa jiya ne, ɗazu ma Baba ya turo Dr yazo yasa mata drip da allura. harta samu tayi bacci sai yanzu kuma da ta tashi jikin ya kuma dawowa". Gwaggo ta matsi ƙwalla tana ƙoƙarin kamo Umma ta sanyota jikinta tana cewa,"Allah sarki Sannu Hajara insha'Allahu yanzu za ki samu sauƙi, ba wai-wai za kiyi ba adu'a za ki dinga yi". tana gyara yafen mayafinta kuma take cewa,"yanzu ke gaki aba rusheshiya da na miƙar dake zaune ko kya ɗanji daɗi, jiki sai kace buhun masara. ke Amina zo ki taimakan mu ɗagata zaune, wannan kwanciyar ita zata ƙara kashe mata jiki". haka Gwaggo ta zauna a wurin Umma, sai nan da nan take da ita, bata baro wajenta ba sai da ta ga jikinta yayi sauƙi tukunna.
[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN*
_By Oum Ramadhan✍🏼_
*(26)*
shigarmu parlo muka zube kan kujera tare da fashewa da dariya. Gwaggo ce zaune kan carpet tasa Yayana a gaba tana barbaɗa magani a abinci, gefenta kuma wasu ɗaurin magunguna ne na daban suma iri-iri. faɗi take tana cewa,"yanzu kaga idan Allah ya taimaka sai kaga cikin kwanaki kaɗan kayi kuɓulɓul da kai, saboda maganin matar nan akwai kyau sosai, so nake na gama da kai saina koma kan Abba". Yaya Abba yace,"to ni kuma Maganin me za'a samo min?". "shegen cinka da yake damuna shi zan shiga fafutukar neman maganinsa, domin wannan babbar lalura ce kake fama da ita, yawan cinka har tsoro yake bani Abba". ta faɗa tana kuma kunce wani ɗaurin ta ɗibi garin maganin ta barbaɗa acikin abincin. sai da ta gama tas tukunna tasa cokali ta juya, sannan ta tura ma Yaya plate ɗin abincin gabansa tana cewa,"gashi nan maza kaci, kaga sau uku a rana akace, kuma kai da ba ƙaunar abinci kake ba gashi har yamma tayi ko ci ɗaya baka yi ba. gaba ɗaya ni na rasa wanna irin ciki ne da kai wallahi, naso ace ma an haɗa maka da ɗurar ƙwai yanda za ka dinƙa ci babu ƙaƙƙautawa, to matsalar ba bina za ka yi ba Yaya, tunda kai ba sanin ciwon kanka kayi ba". shirun da taji ya mata ne yasa ta tsaya tana masa wani duba tace,"wai ba da mutum nake magana bane?". gaba ɗaya hankalinsa na kan waya, ba wai jinta ne baiyi ba, sarai yana jinta ya shareta, kofi ta raruma ta wurga masa ya sauka a goshinsa, ya ɗago cikin sauri yana sosa wurin yana kallonta. "Gwaggo me nayi miki? da kin fasan goshi fa". harara ta zabga mishi tace,"kai dama baka da mutunci, yanzu duk maganar nan da nake ashe ba saurarena kake ba, ka barni sai zuba nake kamar tsohuwar kanya, su kuma waɗancan mahaukatan suna min dariya. to ni duk wanda yay min dariya kansa ya cuta saboda rage imani ta ke. yanzu da ka ɗago aika fahimci ina magana da kai ko, zaka ɗauka abincin kaci ko ƙaƙa?". yace,"kai Gwaggo, wai fisabilillahi taya za'ayi da girmana na kama cin abinci da wani maganin ƴan yaye, nifa ba yaro bane. gaskiya ni bazan sha wannan magungunan ba da ban san daga ina aka samo su ba". tayi galala tana kallonsa cikin jin haushi tace,"to kana so kace min kasheka zanyi kenan, to ka sani ni ba azzaluma bace, dan ko kishiyoyina ban cutar dasu ba bare kai da kake jikana. kuma dan ubanka Auwalu banda ma ina ƙaunarka kai har kaga na damu da kaci ne, amma saboda baka yo gadon arziƙi irin na Sahibina ba shine kake faɗa min son ranka. kasan irin wahalar da nasha wajen neman gidan mai maganin nan kuwa? da ace kana da imani wallahi sai ka tausaya min, ka duba ƙafafuna tun yammacin jiya da na dawo suke min ciwo har yanzu kuma, amma sam bai dame ni ba saboda nafi so na ganku kullum acikin ƙoshin lafiya". Ya tankwashe ƙafa ya matso kusa da ita, sai daya rungumeta yace,"Hajiya Gwaggo tah ina so ki fahimci su kansu masu maganin hausan nan ba lallai sun san abinda suke badawa ba. da maganin bature ne zan sha, amma wannan da babu Nafdac taya zan aikawa cikina shi, garin neman gira a rasa ido". ta juyo ta kalle ni tace,"ke meye Nauduk ɗin daya faɗa?". irin kallon da take min yasa na gimtse dariyata nace,"kai Gwaggo ba Nauduk ba Nafdac, hukuma ce ta tace magunguna da kayan abinci, duk wani magani ko abinci ko nasha idan babu nafdac ajiki ba'a so ayi amfani da shi". "hmm". tace tana taɓe baki, ta ture Yaya daga jikinta, ta yunƙura tana tattara magungunan tana cewa,"naudok mata shegiyo dan uwar ubanta, da ma'aikatar, da masu aikinta da masu bin umarninta na haɗasu na kankantsa musu mari. shegen tsirfar banza da wofi, kai wannan bature anyi ɗan jaraba billahillazi. daga yau ɗin nan indai ni ɗin masoyiyar Sahibina ce, babu ɗan banzan da zan kuma cewa yasha magani acikinku, ku rayu ko karku rayu ba damuwata bace, ana tausaya muku amma ba kwa gani. to ni daga yau babu ruwana na fita a sha'anin kowa. masu shegen ci idan sun mutu ta dalilin haka Allah ya jiƙan rai, suma marasa ci idan ciwon yunwa ya kwantar dasu a asibiti iyakata nabi su da Allah ya kyauta amma babu mai sa ni zaman jinya, nima kunga tattalin arziƙina ya ƙaru, dama wannan ma jiya dubu uku haka nasa na karɓo maganin nan, to ajiye shi zanyi idan Hajara ta haihu na bata in ta tashi yaye, an huta da kuma ɓarnatar da kuɗi". har ta nufa hanyar ɗakinta ta juyo a ƙufule, tana cuna Yaya da baki tace masa,"kai Zagalo daga yau idan kaga dama abincin ma ka daina ci gaba ɗaya, shine zaka burgeni. kuma ka sa ni na bar saka kwano da kai, kaje wurin Hajara ko Zara'u wani ya dinga baka, in kuwa har na kuma ganin ƙafarka tazo karɓar abinci saina bika da muciya". ta kalla Yaya Abba dake dariya tace,"kaje kai da Allah, tunda na faɗa maka bana son dariya, kuma kaima karka kuma zuwar min karɓar kwanon abinci dan ba zaka dinga sa ni almubazzaranci ba, ci sama da sau biyar a rana, ɗan ƙaramin buhun shinkafata ya dinga ƙarewa a kwana uku yo ina dalili haka kawai. amma in kuka daina zuwa nima na huta, kaga ubanka Auwalu sai ya gane ba ni nake cinye masa kayan abinci ba". tayi shigewarta ɗaki ta barmu da dariya, muka haɗa ido da Yayana munawa juna wani irin kallo muna murmushi, yanda kallon ya fara shiga jikina ne yasa nai saurin ɗauke idona. Kaina a ƙasa ina ƴar dariya nace,"ni dai gaskiya ba'a kyautawa Gwaggota, kullum a cikin tattalinmu take amma har ta taƙarƙare taje ta karɓowa mutum maganin ƴan yaye yace bazai sha ba". yace da ni,"to ke me ya hana ki karɓa ki sha?". nace,"aini na tsaya a yanda take so, bana shegen ci kuma bana ƙin ci". Yaya Abba ya haɗe rai yace,"tashi ki bar wurin nan tunda babu sa'anki". na ɓata fuska na tashi na bar wurin, aikinsa kenan idan ana zaune yace na tashi na bar cikin manya. da Magriba Uncle Sulaiman yazo Babansu Yaya Haidar, wanda shine Babba a ƴaƴan Gwaggo sai Baba da yake auta, dama su bakwai ne kuma duk sun rasu sai su biyu yanzu. tunda yazo Gwaggo ke masa faɗa akan rashin sada zumuncinsa, shi kuma yana bata haƙuri. ta dubeni tace,"ke je ki kirawo masa ɗansa yazo, dan nasan dai shi yazo gani ba ni ba". Uncle yace, "Gwaggo wallahi ba haka bane, kin san namu aikin sai a hankali ba ko da yaushe muke samun lokaci ba, amma don Allah kiyi haƙuri zan dinga yakicewa duk weekend na dinga zuwa". tayi dariyar manyace tace,"haba ɗan nan, karka damu wayarma da muke kullum ta isa, ai nasan yanayin aikin naku shi yasa ma nake maka uzuri nake kuma tausaya maka. ni dai fatana yace ko baka karɓar cin hanci? dan ƴan sanda halinku ɗaya ne". Uncle ya murmusa yace,"a'a Mama, ai a kullum ina tunawa da nasiharki da kuma faɗanki. kuma na tabbata hakan shi yasa nake samun ci gaba". taji daɗi ta kuma ƙara yi masa adu'a. ta kuma ɗora masa compalin da cewar,"ka ɗau matakin hana Junaidu zuwa gidan nan, sam bashi da kirki baiyi halin ƙwarai ba, yaran nan daga nayi masa tsiyar idan zai zo gaisheni bai iya kawo abin arziƙi ba kamar Haidar, sai dai yazo ya sa ni gaba da surutun banza, shine shekaranjiya daya tashi zuwa ya ɗuro ruwa da gishiri a kwalbar lemu ya kawo min. wallahi Sulaimanu na zaci lemun gaske ne nayita masa godiya nace yasa min a freezer sai ansha ruwa, ana shan ruwa na hau kwankwaɗa harshena ya ɗaure, ai ɗan nan ya shiga da hakkina. ni dai inaga a duniya ni kaɗai ce banyi sa'ar jikoki na arziƙi ba, Sabina ce kaɗai ƴar albarka, dama-dama ma Aliya da Husnah sai Muklas, duk da shima bai cika halin ƙwarai ba wataran, amma dai yafi su Abba a haka, dama su Aisha ba'a magana. saboda haka ni dai ka hana Junaid zuwa dan gaba zai iya jiƙa min barkono ya karni. kaga yanzu shi Haidar yau kwata-kwata ma ban sa shi a idona ba, ko gaisuwar safe wannan babu, dama sa'anni yake ganina da shi, to ban damu ba tunda gaisuwarsa ba zata ƙare ni da komai ba haka kuma ba zata rageni da komai. ni dama gaba ɗayansu maraicinsu nake tausayawa to amma sun maidani abar banza. ina faɗa maka fa Haidar har gaba ya ɗora dani a gidan nan, daga nacewa Auwalu yana shigowa da sassafe yay min sata a kitchen, shikenan ya daina zuwa inda nake sai dai yaje waje ya siyo abinci yaci". sai kuma ta fara matsar ƙwalla tana cewa,"hakan da yayi ya kyauta min kenan Sulaimanu, idan na tuna basu da uwa hankalina tashi yake, wallahi duk sanda ban saka yaran nan uku a raina ba bana samun kwanciyar hankali. to shi gaba ɗaya ya ɗauke ƙafa da shigo min, Abba da Yaya ne kawai masu zuwa na gansu naji daɗi, shi kuwa sai dai ya barni da tunanin halin da yake ci, tsakani da Allah idan na kamu da ciwon zuciya fa". Uncle ransa ya ɓaci, ya hau bata haƙuri ni kuma yace, "Sabina je ki kirawo min Haidar". ko da naje na ɗau 2minutes ina buga ƙofan ɗakinsa amma shiru, ina murɗa handle ya buɗe, nayi tsakin ɓata lokacin da nayi ina aikin bugu, ina shiga na ganshi kwance kan gado yana kallon sama, ko vest babu jikinsa sai towel dake ɗaure a ƙugunsa, na ɗauke kai da sauri ina kallon gefe. nace,"Yaya Haidar Uncle yazo yana kiranka, ya kira wayanka duk baka ɗauka ba, kuma Gwaggo ma tun safe take nemanka". nayi magana a ƙalla ta kai huɗu bai amsa min, ganin yaƙi motsawa kuma bai amsa min ba yasa na matso ina cewa,"Yaya Haidar Uncle yana kiranka". na faɗa ina ɗan taɓashi dan a tunani na ko bacci yake. nan ma bai motsa ba, ina leƙa fuskarsa nake ƙara ɗan bugun hannunsa ina ƙara kiran sunansa, abinda ya bani mamaki ya kuma bani haushi idonsa biyu kawai ganin damar amsawa ne bai yi ba. naja tsaki a ƙasan maƙoshina nace,"Yaya Haidar magana fa nake maka, ai dai nasan ka jini ma, idan kaga dama karka zo". na faɗa cikin jin haushi, na juya zanyi tafiyata sai kuma naji tsoro ya kamani, dan idonsa ne kawai a buɗe amma baya motsi, anya lafiya kuwa? duk walaƙancinsa da mikilancinsa dai ba zanyi wannan maganar ba ya shareni ba. tsoro ya kuma kamani sosai na dawo hankalina a tashe, ina ɗan bugun hannunsa nake kiran sunansa. naji shiru babu alaman ma yana numfashi, ina kallon fuskarsa idona ya ciko da ruwa, saboda yanayinsa zam na matattu, idonsa a buɗe yake ya juye sama. tuni na fara hawaye na kama hannunsa ina cewa, "don Allah Yaya Haidar ka tashi". sai kuma na fara ƙwala kira, "Gwaggo, Yaya Abba, Baba". ina jijjiga shi. zubar hawayenta a ƙirjinsa yasa shi fizgota ta faɗo jikinsa. a tsaroace na shiga kallonsa, shi kuma ya tsareni da kallo da numsassun idanunsa waɗanda suka tara ruwa, gashi sun sauya kala zuwa ja kuma shimfiɗe da damuwa a cikinsu, sai zallar ɓacin rai da yake kwance a saman fuskarsa. yanayin Sabina matuƙa yana burge shi, dukkan abunda yake buƙata a wajen ƴa mace ta tara, kama daga ilimi har zuwa kyawun halittar jikinta, ga irin shagwaɓar da yake biɗa a wurin ƴa mace, haka kuma yana son mace mai saurin kuka yanda zai dinga saurin sakata kuka, ba shi da wani buri da wuce na ya mallaketa, to amma kuma baya so yarinyar ta raina shi, zai ƙwammaci sonta ya zama ajalinsa akan dai ya bayyanar mata da abinda ke ransa, a ganinsa ma ya aureta to ajinsa ya matuƙar faɗuwa. shi yanzu ma bai san dalilin da yasa abun ɗazu ya dame shi ba, so yake ya yakice soyayyarta ya watsar a gefe bare har kishinta ya dame shi amma ya gagara. kamo tafin hannuna yay ya haɗa da nasa ya damƙe kamar zai ɓallani, na sa ki ƴar ƙara ina ƙoƙarin sauka ajikinsa,"Yaya Haidar Leave me". nayi maganar cikin rawar murya. bai kulani ba sai rufe ido da yayi ya buɗe, wannan karon kallon da yake min saina tsorata da shi, anya kuwa lafiyar mutumin nan ɗaya, ya gaza controlling abinda yake ji, hakan yasa ya shiga zura hannusa a rigarta yana yawo da shi a bayanta, na haɗiyi wani yawu mai wuya na ture hannunsa, murya a ɗage nace. "Yaya Haidar wai mene hakan, babu fa kyau ni ka sake...". ban ƙarasa ba naji bakinsa a nawa, duk ƙoƙarin da nayi wajen ganin na ƙwaci kaina abin ya faskara, ya kama leɓena na ƙasa sai tsotsa yake kamar mai shan alawa, yana kuma ta yawo da hannunsa a bayana zuwa cikina, tuni jikina ya fara amsawa, idanuna suka rage girma ina kallansa cikin wani yanayi. nan da nan hawaye ya shiga reto a fuskata, ganin hakan ya sakar min baki yana goge min hawaye, jikina banda kyarma babu abinda yake, na buɗe baki zanyi magana ya ƙara sa bakinshi cikin nawa, yanzu kam harshena ya kamo, ido na lumshe sai samun kaina nayi da maida masa da martani, sumbatar juna muke sosai acikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa. jin ina aikin kuka yasa ya rabu dani, a hankali ya ɗago fuskata yana kallona da idanunsa da sukai jaaa, na ƙara rumtse ido ina ci gaba da kukana, a hankali cikin magana mai kamar ta raɗa muryarsa a ɗan disashe kuma cike da ɓacin rai yake ce min. "me yasa ke ba ki san abinda ya dace ba, mene yasa....?". Yay maganar raunin zuciyarsa na neman rinjayar furucinsa. bai ƙarasa tambayar ba ya ture ni daga jikinsa ya hankaɗa