Showing 1 words to 3000 words out of 89788 words

Chapter 1 - ALHUSSAIN Complete Hausa Novel

23 Aug 2025

372

*AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

_ina farawa da sunan Allah Mai Rahma Mai Jin Ƙai._

*(1)*
*_ƘADDARA! kalma ce da ta amsa wani suna, wannan sunan mai tarin ma'anoni da yawa...Kowanne bawa na ɗauke da kundin ƙaddararsa, wadda ke ɗaure a wuyansa, kuma kowanne ɗan Adam da yanda salon shafin kundin ƙaddararsa ke buɗewa, inda ta kan buɗe da siffofi guda biyu, ko ta siffantu da alkhairi ko kuma ta siffantu da jarabawa kala daban-daban....ka zalika acikin kowanne duniya kuma kowacce rayuwa, ƙaddara na tafiya ne dai-dai da rayuwa, kuma ta rayu damu cikin farinciki ko akasin hakan, sannan babu wani bawa da yake iya gujewa ƙaddararsa, cikin kowacce rana da kowanne lokaci ƙaddararmu na gudana ne ajikinmu tamkar jini, kuma kamar yanda rayuwarmu ta ke mabanbanciya haka ita kanta ƙaddarar ta ke...yanda kundin ƙaddararsu ya buɗe yasha banban dana saura, kuma tabbas da ace suna da iko, da sun ɗau wannan kundin ƙaddarar sun shafe komai dake cikinsa, tukunna su ƙara tsara shi zuwa wata sabuwar rayuwar da ba zata haɗa hanya da waccen ba...WAYE NI? wannan tambayar me kalmomi biyu da harufa shida ke yawo kullum a cikin kan AL-HUSSAIN, da su yake kwana yake tashi, kuma acikin tsumayin jiran lokacin da ganyensa zai bushe ya faɗo zuwa ƙasa, daga nan shikenan sai ya zama tarihi...sai dai abinda AL-HUSSAIN bai sa ni ba shine; zaren wata ƙaddarar na sauyawa ne a sa'ilin da adu'a kaɗai ke iya sauyata...to amma a ɓangaren SABINA da ta san WACECE ITA fa?, idan har ƙaddara na ɗaure a wuyan kowanne bawa to abun tambayar shine mecece tata ƙaddarar? ya ya ta ke? da yaushe zata fuskanceta? ta wanne irin yanayi zata zo ma ta? mai kyau ce ko kuma mara kyau? zata iya karɓanta ko ba zata iya ba?...wata ƙaddarar kamar zanen dutse ta ke da babu abunda ke iya sauyata!..._*

*Kano, 3:00pm.*
sanye nake da maroon hijab wanda ya ɗauki kyawuna matuƙa, a yayinda Farhana ke yafe da ƙaramin gyalenta wanda itama yay ma ta kyau sosai. Cikin takun natsuwa da hankali muke fitowa daga cikin Sahad Store da ke nan anguwar zoo road. Ledar hannun Farhana kawai zaka kalla ka gane cewa ba ƙaramar siyayya ce muka yi ba. muna tafe muna ƴar magana a cikin nishaɗi, duka fuskokinmu kewaye da glasses, sai dai akwai banbanci a tsakanin glasses ɗina da nata, domin nawa na magani ne wanda ake kira da medical glass, ciwon idon dana gada a wurin Kakata mahaifiyar Abbana, ita kuma Farhana na gayu ne, wanda bata iya rabo da shi a kullu yaumin.
zuwanmu bakin jar motar da ta ke mallakin Farhana ce muka tsaya, sannan Farhana ta buɗe booth ta sanya ledar kayan hannunta, tukunna na buɗe gaban motar na shiga, bayan Farhana ta rufe booth sannan itama ta zagayo ɓangaren mazaunin driver ta shigo ta zauna tana yiwa motar key. "wash Sister wallahi na gaji da yawa yau, kai ni kam sai na kwan biyu ban kuma zuwa wani biki ba". na faɗa a sa'ilin dana ke kunna Ac'n motar. "yanzu ai zamu ƙarasa gida, nima da kika ganni duk a gajiya na ke, buƙatata kawai na jini cikin shower". cewar Farhana tana karya kan motar zuwa kan titin da zamu hau. na ƙara cewa,"ke kin san ma za ki samu ruwa a gida, ni yanzu na koma da wuya idan ba sai na fita neman mai ruwa ba, saboda anguwar mu muna cikin matsalar ruwa...Gwamnati gaba ɗaya bata tausayin rayuwar talaka, ba wuta ba ruwa a inda talaka bawan Allah ke rayuwa, kai Allah kayi mana magani". na numfasa kamin na ƙara cewa,"Allah sarki Gwaggo nah nasan yanzu tana can tana tsumayin dawowa ta, kuma kin san fa sai da ta ce ka da na jima". Farhana ta ce,"kinga ba wannan bama, ni damuwar ma Allah yasa mu tarar da telan nan yana shago, kar musha wuyar banza ga wannan uban go slow ɗin, kalla fa tun ɗazu danja ta ɗaga amma har yanzu motoci sun gagara wucewa". "to amin dai, Allah ya nufemu da ritsa shi a shagon ɓuyarsa". na faɗa ina yatsine fuska alamar gajiya sosai a tare dani. Direct sharaɗa muka wuce shagon da Momin Farhana ta aikemu amso ma ta ɗinki.
Ba ƙaramin takaici muka ƙunsa ba da muka je ba mu sami me ɗinkin ba, tsabar haushi ma ko jiran yaron shagonsa dake mana bayani bamu yi ba muka fice dukanmu rai a ɓace, danni har ji nai kaman na gwaɓe bakin saurayin dana san ƙarya ce kawai yake gilla mana. tun fitowarmu daga shagon nake ta duban jefi-jefin jama'ar da ke layin, kasancewar sa layi ne da bai tara mutane ba, sai ƴan tsirarru haka, unguwa ce bata masu kuɗi ba amma kamar wata babbar estate shiru kake ji. nace da Farhana, "ni kam kiyi sauri mu bar layin nan ina tsoronsa, kin san yanzu kidnappers sun yi yawa a gari, mutane ba tsoron Allah". itama tace,"hmmm sauri ai kece zance kiyi, kina tafiya kamar ba za ki taka ƙasa ba, kee ni ko dai kina da matsalar ƙafa ne?". na harareta sannan nai murmushina mai sanyi ba tare dana ce ma ta komai ba, muka ci gaba da tafiya hannunmu riƙe dana juna kace mu twins ne, sai dai muna gab da ƙarasawa inda mukai parking naji ƙafafuna sun tsaya cak daga tafiyar, yayinda hannuna ya zame daga cikin na Farhana, na bi gefen haguna da kallo kafin naji ƙafafuna na jana suna tafiya da ni zuwa wani wuri, wani wuri da ban san me zai iya faruwa ba idan na riske shi, na bar Farhana naci gaba da tafiya tana ta maganarta ita ɗaya duk tunaninta tare muke. sai da tayi gaba sosai sannan ta fahimci tafiyar tamu ba tare muke ba, ta waigo da kanta sai kawai taga babu ɓurɓushina ma a wajen, kuma a wannan lokacin ɗaga idon da zatai can gefe ta hangeni ina tafiya cikin sauri-sauri har ina harɗewa, saurin da a duniyarta zata rantsewa wani bata taɓa ganin nayi shi ba tun yarintarmu.
tsananin mamaki sai yasa ta riƙe haɓa, cikin zuciyarta na ayyanawa da me zanje yi a cikin bola?.
"Sabina! Sabina!! ke Sabina wai ina ki ke neman zuwa haka? bola fa naga kina neman shiga, wai kin yi hauka ne? Keee!!".
zan iya cewa a sama-sama naji abunda ta ke cewa, dan haka hannu na ɗaga ma ta ta baya kawai ba tare dana yi yunƙurin tsayawa ba, kuma zagin da ta ƙunduma ta wurgo min shi yasa ni ɗaga ƴar muryata ina cewa da ita,"Farhana ba fa bolar zan shiga ba, ki biyo ni ko ki jira ni yanzu zan dawo".
Farhana ta sauke numfashi tana zubawa sarautar Allah ido, tabbas banda tasan wace ƙawarta lallai zata iya cewa aljanu ne da ita ko kuma tana da ciwon hauka ne, amma a yanzun ma ba zata ƙi cewa Sabina ta sami matsala ba. Gani tai sam ba zata iya barinta ita ɗaya ta shiga cikin wannan bolar da shigarta babu abinda mutum zai kwasowa kansa fa ce musiba, hakan yasa ta bi bayanta itama cikin sauri, abunda ya ƙara bata mamaki kuma hangenta da tai ta tsaya gaban wani mutumi da ke zaune saman bulon wani kango a jikin bolar. Farhana tai turus ta tsaya domin ita kuwa al'amarin ya fara bata tsoro, gwara ta tsaya daga nan ɗin idan taga abin bana tsayuwa bane saita arta ana kare, domin ta fara tantama da lafiyar ƙwaƙwalwar Sabina.
Saurayi ne kyakykyawa na ajin ƙarshe zaune saman bulo a bakin wani kango, shekarunsa zasu kai 27-28, shi ba fari ba kuma shi ba baƙi ba, hasken sa dai-dai misali, jikinsa sanye da yadi me arha ruwan madara wanda ya amshi jikinsa, a kallo ɗaya zaka yiwa kayan jikinsa ko da ace daga nesa ne ka gane cewar yadin a koɗe yake, irin koɗewa da jemewar da suka gaji da duniya, Farin silifas ne wanda ya ɗanji jiki sanye a doguwar ƙafarsa me ɗauke da zara-zaran yatsu, Kansa a ƙasa yake hannunsa riƙe da taba sigari, cikin ƙwarancewa yake zuƙa yana fesar da hayaƙin ta gefensa. zai kuma zuƙa kenan yaji an ƙarɓe ta daga hannunsa, ya ɗago jajayen idanunsa domin ganin mahaluƙin dake da ikon karɓe masa abokiyar rayuwarsa.
Idonsa ne yay tozali da ƴar kyakykyawar budurwa tsugune gabansa, tana sauke masa kyakykyawan murmushi, da wannan idanun nata masu zurfi, kallo ɗaya yay ma ta yay saurin ɗauke idonsa saboda faɗuwar gaban daya tsinci kansa a ciki, ba tare da sanin dalilin hakan ba, kuma haka kawai sai yaji ƙirjinsa na bugawa da sauri da sauri abinda bai taɓa riska ba tsawon shekarun rayuwarsa. ina lure da shi da yanda yake bina da kallo ta ƙasan ido, wucewar sakan ɗaya, biyu, uku, ya ɗago da kansa gaba ɗaya yana sauke kallonsa gaba ɗaya akaina, har yanzu ban bar yi masa murmushi ba, hakana ban ɗauke idona daga ƙwayar idonsa ba dake haskawa da ƙyallin mamakina ba, kuma zan iya rantsewa a wannan lokacin abinda yake rayawa acikin ransa shine _ko dai ni mahaukaciya ce?._
na gyara zaman glass ɗina sannan nace da shi, "Hy Mr Man". na faɗa ina ɗaga masa gira sama, sai dai shi idonsa na kan tabar dake hannuna da ban yar da ita ba, sai na kalli tabar tukunna na maida kallona kansa kamin na shiga ce masa. "wannan tana cutarwa, ba ta amfanar da mai shanta, Almubazzaranci ce, tana cutar da na kusa da kai. a bisa haka Malamai suka ce tunda duk abinda ta ke haddasawa haramun ne to itama ta zama haramun".
ina gama faɗa na jefar da sigarin a ƙasa, na ta ke da takalmina, sannan na maida glass ɗina dana cire nai cleaning ɗinsa. yaji sanda iska ta ɗebo abunda tace ta shigar cikin kunnensa, kuma yaji yanda kalaman nata suka sami zama acikin kansa, ya tantance maganartata cikin kowanne futar harafi, sai dai ya kasa tantance zaƙin sautin daya fita acikin amon muryartata. ni kuwa ƙura masa ido sosai nai ko tsoronsa ma banji, kuma shi ma sosai yake kallon ƙwayar idona, sai dai Allah masanin gaibu, dan ban san me zuciyarsa ke karanta masa ba.
sai kawai na ƙara murmusa kuncina a karo na babu adadi, tare da harɗe hannayena a ƙirji ina faɗa masa abunda bai tambayeni ba, haka kuma babu nuni na yana baƙatar sanin hakan. "Sunana Sabina Auwal, anan garin kano nake. And you?". a wannan lokacin abinda Sabina bata sa ni ba shine, zuciyarsa na gaya masa cewar_anya ita mutum ce kuwa._
bai bani amsa ba, babu kuma yunƙurin hakan a tare da shi, abu ɗaya ne kawai ke ɗawainiya dani, aiwatar da wasu abubuwa da bana sanin lokacin da nake yinsu ba...matsowa kusa da fuskarsa nai, na ɗaga masa kai alamar ina jiran cewarsa akan tambayar sunansa da nai. sai naji shi da saɓanin abunda na tambaye shi ɗin. "me yasa ki ka faɗan sunanki bayan ban tambaye ki ba?". "ka fara bani amsar tambayata tunda ni na fara". na faɗa ina ɗan karayar da kai gefe.
a hankali naji muryarsa na fita, kuma a lokacin so nake na toshe hancina saboda warin sigarin dake fita a bakinsa, amma na kasa saboda bana so na nuna masa walaƙanci. "duk da bana jin yaren da kika yi min tambayar, amma zai iya yiwuwa na fahimta. indai yanda na fahimci tambayar taki ne to ni ba ni da suna, kuma bani da sunan Baba, ban san kuma garin da na ke ba". sai kawai na saki baki galala ina ƙare masa kallo da maɗaukakin mamaki, kuma ƙwayar idona na haska masa da cewar ban yarda da abunda ya faɗa ba.
"tun ina ƙarama kamin Mama nah ta rasu, ina tunawa kamin ta rasu ta gaya mun babu kyau ƙarya, don haka kar na yi kuma kar na koyi yinta, kuma kar nayi tarayya da me yinta. Sannan da na girma, Gwaggo nah wata rana ta yiwa Yaya nah faɗa cewar Babba baya ƙarya. So dan haka kaima karka yi ƙarya kaga babba ne kai, kuma ni yarinya ce, idan kayi zan koya a wurinka, kuma nasan ai ba zaka so hakan ba ko Yaya?". ina masa maganar ne da yanayi irin na yara. "me ya kawo ki nan wurin?". Ya tambayeni yana mai tsareni da ido da alamu na tuhuma.
na tsarota sosai, kuma tsoron bai sa ni yi masa ƙarya ba, na faɗa masa ainihin abunda ya kawo ni. "na zo ne domin na hanaka shan sigarin da ta ke haramtacciya".
"to ki tashi ki tafi, ni ɗin bana son kowa a kusa da ni, ki tafi kar naji miki rauni".
yanayin da yay maganar kuma ya ke dubana ba ƙaramin kaɗa ƴaƴan cikina yay ba, ina kallo ya zura hannu a aljihu ya ɗauko kwalin sigari ya buɗe ya ɗauki ɗaya, sannan ya ƙyasta lighter ya kunna, zai kai baki kenan na miƙe da zafin nama na ƙwace ina yin jifa da ita. kamar zan fashe da kuka nace, "don Allah kar kasha, ba zan iya ganinka kana shan abunda zai cutar da kai ba. Kazo mu bar nan wurin don Allah". na faɗa ina kamo hannunsa don mu tafi. a tsawace yace da ni,"kar ki ƙara cemin Yaya, ni ba Yayanki ba ne".
"shikenan ba zan kuma ba. Amma sai ka faɗa min sunanka idan ba haka ba ni kuma bazan daina ce maka Yaya ba, tunda kai ɗin ka girme ni ka yi sa'a da Yaya Abba, tarbiyar gidanmu bata koyar damu faɗan sunan na gaba damu ba gatsal". Ƙwace hannunsa yay anawa yana doka min tsawar da tasa naja baya babu shiri, yana faɗin, "ki tafi ki barni ko. Nace miki bana da suna bana kuma da sunan Baba, banda kowa, na tsinci kaina ina rayuwa ne ni ɗaya kawai...dan haka bana son kuma jin maganarki anan wurin ki wuce ki bar nan". na kawar da tsoronsa ina kuma kamo hannunsa, roƙonsa nake kamar tsohuwar mayya ina cewa, "Yaya kar kayi fushi ka duke ni, na maka alƙawarin ba zan kuma tambayan sunanka ba tunda baka so. Amma yanzu ka zo mu tafi gida, zamanka anan zai cutar da kai, ga warin bola ga sigarin da kake sha, abun yayi yawa". cikin wata razananniyar muryar ya ƙara ce min. "shekaruna goma sha tawas ina rayuwa anan Wurin, anan nake yini nake kwana, sigari itace abincina kuma itace abokiyar rayuwata, Allah shi ke tallafe da rayuwata, maƙociyata da nake jin daɗin mu'amala da ita wannan bolar, warinta shi nake shaƙa naji daɗi. Duk tsawon wannan shekarun ban cutu ba sai a yau da kika zo?, to wace ke? me kika isa ki sauya a rayuwar da Allah ya tsarata a haka tuntuni?...kinga ki shige ki tafi ki bani wuri tun ban maki rauni ba".
Tsantsar tausayinsa naji ya kamani, da wani firgici da kalamansa suka haifar min, saboda ganin yanda damuwa ta kuma bijirowa a saman fuskarsa, har yana maganar tana rawa kamar zai fashe da kuka saboda ɗacin rai. saina sauke kaina ƙasa ina goge ƙwallar da ta tarar min, wucewar sakanni uku na ƙara kamo hannunsa naja shi da ƙarfin da Ƙafafunsa basu iya yin gardama ba. yayinda a lokaci ɗaya naji ihun kukan jariri na ƙwala ƙara acikin kunnena, ƙarar kukan da yasani saurin gimtse ido, tare da damƙe hannunsa da ƙarfi babu shiri, inda hasken hoton wani jariri ke giftawa acikin duhun idona, sai naji kaina na wani mugun sarawa da wannan tsala kukan da jaririn yakeyi...wani abu da ban fahimta ba a lokacin shine, wataƙila anyi amfani da gatari ne wajen sara shi a tsakiyar kaina ya rabe gida biyu, ta yanda yin gaba da komawa baya zasu gagara a tare da ni.

****
_Hey Guyz how are you doing, hope you are all doing fine. how was the first charpter? loving the story already bah? encourage me by comments and voting, thats the only way i will know my effort is beaing appreciated...it's not a new story buh an old story am updating, i just changed the story name, kuma no disappointment insha'Allahu☺....ina fatan zan sami haɗin kanku daga farko har zuwa ƙarshe. Allah ya bani ikon gamawa lafiya, amin Ya Rahman...mai karantawa kuma Allah ya cire shi daga sahun mugwayen da zasu karanta littafi suƙi appreciating, dan mugunta ne da munafurci ai karatu aƙi appreciating, mutum sai ya nuna kaman bai karanta littafin, honestly speaking babu daɗi irin hakan...promise you ba zanyi delaying maku posting ba, so you people ma karku ji ƙyashin yin vote da comment.👏👏_


#love you my readers😘
#mikiyawriter's
#2022.
#Share.*AL-HUSSAIN*

_By Oum Ramadhan✍🏼_

*(2)*
kusan daƙiƙa huɗu kaina na juyawa kafin na iya sakin hannunsa na ɗan matsa gefe da shi na dafa jikin gini. sama-sama nake jiyo muryan Furhana na faɗin,"wai Sabina kin san shi ne?". ta faɗa tana ƙarasowa inda nake. na buɗe idona da ƙyar na dubeta ina cewa,"a'a ban san shi ba, ban ma san waye ba". cikin ƙarfin hali nai magana ina dafe da kaina, ta matso kusa gareni da tashin hankali tana dafa kan nawa da shiga jera min tambayoyin,"lafiya?". a wannan lokacin babu abinda nake so irin a cire min kaina a dire shi a gefe, in yaso a barni naci gaba da rayuwa a haka idan da yiwuwa kenan, idan kuma har cire kan zai zama silar rasa raina to tabbas zaifi min sauƙi a cire shi dan na rabu da wannan tsananin sarawar da yake min, da kuma amsa kuwar kukan jaririn da har yanzu ban bar jinsa ba. "na shiga uku menene naga kina dafe kai? innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...kinga abinda kike neman jawa kanki ko Sabina, ni uban me ma kika gani da kika yo cikin bola sai kace mahaukaciya". muryar Farhana na fita ne cikin faɗa sosai da kuma tsananin nuna kulawa gami da matuƙar nuna damuwa. magana nake so nayi amma na kasa, sai laɓɓana dake aukin yin rawa, ko idona dake buɗe kaɗan dishi-dishi nake gani da su, jiri ya ɗebeni na nemi na zube a wajen tai saurin riƙeni ta zaunar akan bulo ɗin da Yaya ya tashi. hawayen azaba ya shiga min sintiri a saman fuskata, Farhana ma ko da bana kallonta amma a yanda muryarta ke fita da rawa nasan kuka

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login