Showing 21001 words to 24000 words out of 77635 words

Chapter 8 - WATA UWA

Unknown   

10 Nov 2024

3619

nan ya afka mata"Inda dai jidda ce da ayau yatabbatar ya angonce"yajima yanata juye juye dg bisani har baccin wahala yasacesa.
washe gari tun wajen 5:23 am bilkisu ta farka"time d'in da yah Abdul yashigo d'akin yatasheta sallah yasamu tana raka'atanil fijri"toilet d'in ya wuce yayi alwalah yafito yana fad'in natafi masjeed....bayan ta idar tayi azkhar da karatun alk'ur'ani me girma"ta gyara parlourn"ta kunna tsintsiyar k'amshi"sannan ta gyara bed room d'in ta shiga wanka"alokacin kuma yah Abdul yadawo parlourn"bayan yaje ya gaishe da goggo"koda yashigo bed room d'in bata ciki"motsin ruwa dayaji atoilet yatabbatar masa wanka takeyi"sosai ya yaba da tsabtar bilkisu ko ina k'al yanata k'amshi"parlourn yakoma ya kwanta bbu jumawa bacci yayi awon gaba dashi"ahaka bilkisu ta fito cikin shirinta "sabon lace ne d'inkin riga da siket ajikinta"tayi light make up tanata k'amshi"ta yane kanta da mayafi bak'i"sau d'aya tasaci kallonsa taga baccinsa yakeyi"fitowa tayi dg d'akin tanata jin fad'uwar gaba"kai tsaye parlourn goggo ta nufa Inda taji motsinsu itada meenah"goggo nata mitar meenah ta cika son jiki"ahaka bilkisu tayi sallama sau biyu tana yaye labulen k'ofar tashigo"meenah ta amsa mata tana fad'in masha Allah aranta"har k'asa ta duk'a tana murmushi akunyace ta gaisheda da goggo"ta amsa bbu yabo bbu fallasa"meenah ta gaishe da bilkisu"ita kuma ta maida mata gaisuwar sbd tasan meenah ta girmeta" shiru yabiyo baya"bilkisu ta mik'e tsaye ta musu sallama ta fita"kitchen d'inta ta bud'e ta d'akko gudar tsintsiyar laushinta tafara k'ok'arin share gidan.....tana can k'arshe zata tattara ta kwashe goggo ta fito zata shiga bayi"baki bud'e take kallon bilkisu kafin tace"ikon Allah! ke y'ar nan dg zuwa zaki fara da aiki"so kike asani abakin duniya ace ina wahalar dake?"gaki dai yarinya har yarinya kyakykyawa amma kin kashe rayuwarki kin auri talaka"gsky y'ar uwarki tafiki wayo da ita taguji fatara da talauci ke kika ara kika yafa"indai Abdul ne da gudu kema wata ran zaki gujeshi da k'afafuwan......haba goggo miye amfanin irin wa'annan maganganun fisabilillahi??"cewar meenah data lek'o sbd jin kalaman goggon"yyinda kan bilkisu ya k'ulle"tana tambayar kanta anya wannan tsohuwar itace mahaifiyar mijin nata??"sai kuma ta tuna da kalaman musa na kwanaki"sai kawai tama k'awar da tunanin aranta tacigaba da kwashe sharan da paker"goggo kuwa batace komaiba ta nufi bayi"yah Abdul da surutun goggo yatasheshi yayi tagumi kawai"yana tunanin anya zasuyi zaman jin dad'i awannan gidan?"yanzun dg zuwan bilkisu jiya kawai shine ayau zata fahimci komai na cikin gidan...muryar meenah yaji tana cewa"dan Allah Anty bilkisu dg yau karki koma share gidan nan"nice ke sharewa in bani nan akwai almajiri"kije ki huta dan Allah"sosai yaji dg bilkisun har meenar sun burgesa"yana ahaka bilkisun tashigo cikin parlourn da sallama ahankali"azatonta bacci yakeyi kawai taji ya amsa mata"saurin kallon gefen dayake zaune tayi suka had'a ido"d'age mata gira guda yayi"tayi saurin yin k'asa da kanta ta duk'a tana fad'in ina kwana?"lafiya qlau Mrs Abdul! sarkin son aiki ko?"d'an murmushi tayi batayi mgn ba"shi kuma yanata kallonta"ya lura tanada kunya sosai"dama katashi kayi wanka"meyasa tun d'azun ba'a tasheni nayi ba?"naga bacci kakeyi ai"toke meyasa baki kwanta kinyi baccin ba?"ban saba komawa baccin safe ba ai"okay zanyi wankan amma idan yimun za'ayi ba"yafad'a cikin wata iriyar kasalalliyar murya yana tsareta da ido"ita kuma gaba d'aya kunyace ta kamata"tashi ki zauna to"Ahankali ta zauna kan kujera d'in"tana wasa da yatsun hannunta"mik'ewa tsaye yyi ya wuce ciki"troley d'in kayansa yajawo amma yaji sakwaf"alamar bbu komai aciki"mayarwa yayi yabud'e ward rope ta biyun k'arshe"aikuwa yaga kayansa gogaggu duk bilkisu ta jera masa"towel nasa yad'auka yanufi toilet bathroom"yasamu shima ta wanke toilet d'in"tacika masa roba da ruwan wanka"ga sabbin butoci acike acan gefe"sai toot paste da sabon brush dukta ajiye masa.....jidda yaji shaid'an na bujuro masa da tunaninta"hakan yasa yaji b'acin rai"yana wankan yanajan tsaki"bayan yafito yasamu kayansa a gefen bed"riga da wondo na sabuwar shadda sky blue"ga vest fara da boxer ankuma feshesu da turare"kallo d'aya yayiwa kayan yanufi gaban mirror yana tsane ruwan jikinsa"yana tuna inama ya ajiye kayan dayake amfani dasu idan yayi wanka?"tunawa yayi ajiya dayazo ya ajiye kayansa yasasu award rope"aikuwa yana dubawa yagani"anutse yagama shirinsa"yatsaya gaban mirror yana aza hula samqn tattausan suman kansa dataketa shek'i bak'i k'irin da ita"yana k'ara fesa turare wayarsa datake a parlourn yaji ringing nata"da sauri bilkisu ta d'akko wayar tana yin sallama kanta ak'asa tace gashi"gaba d'aya jitayi yacika mata idanuwa bata iya kallon idanuwansa"shi kuwa tab'e baki yayi beyi mgn ba ya amshi wayar"ta juya da sauri ta koma parlourn"kiran ma yakatse"hakan yasa yakoma bin kiran sbd ganin musa ne"dukda ba wani ishashshen credit ne awayar ba"dan 3500 ce kawai tarage masa yanzun aduniya"hidimar biki tacinye komai"amsa sallamar musa yayi Ahankali"musa yace"gani a k'ofar gidan abokina"okay yafad'a yana kashe wayar yasakata gaban aljihu yafito dg cikin d'akin"bilkisu na zaune kan kujera tana waya da umminta"kallo d'aya yamata yad'auke kansa"tabi bayan sa da kallo tana yaba tsarin baiwar halittar da Allah yamasa aranta.....yana fitowa yasami musa tsaye k'ofar gidan yana rik'e da basket madaidaici a hannunsa da warmers aciki harda flast na ruwan zafi"musabuha sukayi saidai musa yafahimci beda walwala"shima fuskarsa bbu walwala yace"Abdul meyasa bakajin shawara?"shin so kakeyi bilkisu ta fahimci wani abu marar dad'i aranka game da ita?"tab'e baki yayi yace"dan Allah mudena zancen"meyasa kakeson dorawa kanka hidima Musa?"hidimarka tawace Abdul"kuma ni sbd bilkisu nayi badan kaiba"yafad'a cikin tsokana yana murmushi yamik'a masa basket d'in yana fad'in ka fara k'yallin anguncci abokina"harara ya Abdul yamaka masa ya amshi basket d'in yana godiya"musa yace"mu had'e shagonku anjiman"okay yafad'a ya nufi cikin gidan"goggo da meenah na zaune acikin baranda kan tabarma"suna break fast"meenah har ta gaji ta rokon goggo alfarmar tabari ahad'a break fast d'in dasu yah Abdul amma ta hana"kai ina zakaje da wannan kayan?"cewar goggo tana tsuke fuska' yah Abdul beyi mgn ba yanadai tsaye"wato rok'o kaje kayi kenan?tunda dama ka rasa yazakayi sbd talauci ai dole kaje kayi rok'o"ai maganin ita bilkisu take kowa? da taji ta gani ta aureka.....✍️

wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
Acc n 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki ta what's app n d'ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika fitarmun Allah ya isa ban yafeba

........ subahanallahi! wace irin mgn ce wannan goggo?"haba dan Allah"yaka mata kibar....zanci ubanki! ban hana idan ina mgn ki samun baki ba?"shiru meenah tayi"yah Abdul zuciyarsa na zafi ya wuce d'akin beyi mgn ba"goggo taci gaba da cewa"yo wai yaushe yazo yashiga bayi har yayi wanka ya shirya ne?"akwaifa toilet ad'akinsu"uban waye yace Ayi bayin ad'aki?"koni mai gidan banida bayi ad'aki saisu?"amma goggo karki manta gidan nan namune nida yah Abdul da yaya kabeer da mukaci gado gun mahaifinmu"kinga kuwa bbu kasonki aciki....dukan data kawowa meenah yasaka ta kauce tanayin shiru"aikuwa ta dinga masifa da zage zage"meenah kamar tayi kuka"gaba d'aya sai taji dama ba'anan yah Abdul yazauna ba"tasan tabbas bilkisu najin komai"tasan kuma saita fassara goggo da abubuwa masu yawa" wani irin tausayinsune taji yaka mata"komai taji yafita aranta ta tashi ta barma goggo wajen ta koma cikin parlour.....
ransa ab'ace yashigo parlourn"ya ajiye basket d'in hannunsa"samqn d'an center table d'in dake a tsakkiyar parlourn, irin colour d'in furnitures d'in bilkisu"zama yayi kan kujera yayi tagumi"idanuwansa sunyi jajir"yana tunanin yaushe damuwarsa zatazo k'arshe??"bilkisu kuwa duk tanajin kalaman goggo"ranta yabata gsky ba mahaifiyar sabace wannan masifaffar tsohuwar"wacce dg safe zuwa yanzun halayenta sukayi mata kamanceceniya da umma magajiya"jin motsinsa a parlourn yasaka ta fito dg cikin d'akin jikinta asanyaye"had'a ido sukayi taga yayi tagumi"agefensa tazo ta zauna"dukda gabanta nata fad'uwa sbd ta lura fuskarsa bbu walwala"cikin sanyin murya tace"yaya Abdulllllll! sosai yaji sunan har cikin kansa"be amsaba saima zuciyarsa yaji ta karye"cikin taushin murya tace"idan ban maka shishshigi ba"kayi hak'uri ka dena tagumi dan Allah" sbd bbu kyau yinsa"komai yayi farko zaiyi k'arshe arayuwa amma banda ikon Allah"tamkar k'aramin yaro haka yafad'o samqn jikinta ya kwanta kan cinyarta yana sabbatu ta hanyar fad'in"menayiwa goggo haka ta tsaneni bilkisu?"ban tab'a ganin Inda mahaifiya ke hantarar d'antaba sai akaina bilkisu"miye zanyi tasoni??"yafad'a yana kama hannayenta dasuka sha jan lalle yasark'e da nashi hannun"wanda hakan gaba d'aya ko wannan su saida yaji canji ajikinsa"dan ita bilkisu jikinta har kirma yakeyi"dataga yah Abdul yayi ale ale samqn cinyarta"ga hannayenta yakama ya rik'e yana murzawa"bata yarda ta kallesaba cikin raunin murya tace"kadena damuwa dan Allah"damuwar beda amfani"addu'a zamuyi in sha Allah wata ran zai zama tarihi"sannan ka dinga k'ok'ari wajen faranta mata"idan kaji damuwar kayita maimaita Innalillahi wa inna ilaihir raju'un"Allah yana tare da masu hak'uri yah Abdul"ajiyar zuciya yasaki yana kallon k'ananun pink lips nata datake motsasu cikin nutsuwa"bilkisu banaso mutuncin mahaifiyata ya zube a idonki"dan Allah ki girmamata"sannan komai tamun karkiji zafinta"kamar yadda kika mun nasiha akan komai zai wuce"to nasan zai wuce Inda rai wata rana...in sha Allah karka damu mahaifiyarka nima tawace"kuma sirrinka nawane"addu'a shine namu"katashi kayi break ko?"tafad'a tana k'ok'arin zame hannayenta daya rik'e"dan hannayenta har kirma sukeyi"kina dai son guduwa dg guna ko bilkisu ?"shiyasa zaki fake dana tashi nayi break fast"ni banma tab'a ganin matsoraciyar amarya kamarkiba"d'an murmushi tayi batace komai ba"shi kuma yak'i sakin hannuwan nata"tana k'ok'arin ta koma masa magiya yacika hannun kawai sukaga anyaye labulen k'ofar.....goggo tasaki salati tana kallonsu"tana dg tsaye daga bakin k'ofar tayi d'aurin k'irji"yah Abdul yayi saurin janye kansa dg samqn cinyarta"yyinda kan bilkisu ak'asa"innalillahi wa inna ilaihir raju'un! kai yanzun bakaji kunyaba?"k'ato dakai kamata ale ale a samqn cinya sai kace wani k'aramin yaro?"goggo dan Allah kiyi hak'uri kije gani nan zuwa"ah ah yi zamanka mai mata"kazo kashige d'aki kayi bulum"dama kayan wanki nane zaka zo kamun wanki"bazan koma bada wanki ba"kaine zaka cigaba damun"tunda ba afanuwata dakomai kakeyi ba"shikenan kije zqn fito idan munyi kari"karma ka fito d'in"ta fad'a tana tab'e baki ta fita"matsowa gefen bilkisu yake k'ok'arin yi tayi saurin tashi"yyi murmushi bece komaiba"ita kuma ta fita dg cikin parlourn"cups da spoon ta d'akko a kitchen" taje ta d'aurayesu awajen maguji"goggo tayi saurin fitowa tana fad'in ke! karki koma yimun amfani da ruwa tunda ba Abdul bane yasiyamun"wanine mai zuciyar nema yasiyamun" to akan me ke dashi zaku mora?? kan bilkisu ak'asa tace"dan Allah kiyi hak'uri zan kiyaye in sha Allah.....goggo na k'ok'arin mgn kabeer yashigo tsakar gidan bbu ko sallama" sigari a hannunsa yana zuk'a"tunda yashigo yatsare bilkisu da ido yana kallo"d'an albarka kaine haka tafe?"cewar goggo tana washe baki"Eh nine mom muje mu gaisa Abuja zan wuce"bilkisu kallo d'aya ta masa taji be kwanta mata raia ba"kanta ak'asa tace"ina kwana?"lafiya qlau"goggo ta tab'e baki tana fad'in"matar Abdul ce ai"ka ganta kyakykyawa da ita"amma taji ta gani da aurensa....kabeer bece komai ba idanuwanta k'yam akan bilkisu"bilkisu kuwa na lura da kallon dayake mata tayi saurin nufar d'aki"tana k'ok'arin shigowa yah Abdul shi kuma zai fito sbd yanajin abinda ke faruwa....cikin rashin sa'a bilkisu ta fad'o jikinsa"yayi saurin rik'eta"ta rintse idanuwanta sbd jin kansa agefen wuyanta"dama kece zanje na kira sai gashi kin shigo ko matsoraciya"nifa Allah banida wani tsoro"tafad'a cikin narke murya tanason ta janye jikinta dg nasa" dan har cups d'in hannunta sun fad'i k'asa"matseta yayi yace"to yanzun in baga tsoroba ina kikeso kije zaki k'wace"kaifa zan had'ama tea ka barni nayi aikina"shima wannan ai aikine ko?"kumafa harda lada zaki samu"yafad'a cikin rad'a agefen kunnanta"wanda har sajen fuskarsa na shafo baby face nata"ta lumshe idanuwanta"yah Abdul kuwa k'amshin jikinta ne yaketa shak'a"yazagaye k'ugunta da hannayensa"wani irin yanayi na buk'atuwa yakejinsa aciki"dan iya saninsa da girmansa bilkisu ce kawai macen daya tab'a runguma"gashi yajawowa kansa.....be gama wannan tunanin ba yaji tana masa chakulkuli"yacikata da sauri suna dariya atare"ta duk'a ta d'auki cups d'in"mayafin samqn kanta yazame"duk'awa yayi yad'akko yazo gefenta kan carpet ya zauna yana kallon bak'in gashin kanta data d'aure da bant"akunyace ta had'a masa tea"dan madaran ta gwangwanice pick"da milo na sachet guda 4"ta zuba masa biyu"sannan zuba masa chips a plate ta tura agabansa"tana d'an shek'a tea d'in"yadubeta yana cewa ke ina naki?"lipton kawai zansha"nima shi zansha"to Ayi yaya da wannan?"tafad'a tana satar kallon sa"caraf suka had'a ido"saurin k'asa da kanta tayi sbd wani irin kallo dayake binta dashi"cikin cool voice yace"mrs Abdul! ki kalleni nabaki amsar tambayar ki mana"batace komaiba kuma bata kallesaba saima ajiye masa cup d'in tayi"idan baki had'a kamar wannan ba nima bazan shaba"dama bakyason cin abinci ko?"bafa haka bane"tafad'a tana k'ok'arin had'a wani tea d'in"shi kuma yanata kallonta"bbu laifi mai kaurine amma be kai yawan nashiba"be tursasata ba sbd yasan harda bak'unta yanzun ke damunta da rashin sabo....atare sukayi break fast d'in"yana d'an janta da fira sbd tasake"bbu laifi kuma tasake aranta tana masa kallon mai sauk'in kai"bayan sun gama yakalleta yace"kinga rana tayi har 9:5am"bana so na wuce 10 ban fitaba"bara naje nayiwa goggo wankin ko?"bilkisu da kanta ke ak'asa tana k'ok'arin mgn sukaji muryar goggo tana fad'in wai Abdul hakeem bazaka fito kamun wankin nan ba??"kazo ka shige d'aka ko?"da sauri yatashi yana kallon bilkisu yakama hannun ta suka mike tsaye"d'akin labalen goggo tayi"muje saina tayaka ko?"ah ah bilkisu kije ki kwanta ki huta yanzun zan gama"ke kinyi aiki kingani"nidai inaso dan Allah.... tafad'a cikin muryar shagwab'a"shi kuma yanata kallonta.....wannan wace irin jarabace ni y'asu??ga marar aikinyi kabari a tsakar gida tana mgn kai kazo ka kama mata ka rik'e ko?"bece komaiba yacika hannun bilkisu yafita"goggo na mita ta bashi kayan" girgiza kanta bilkisu tayi sbd tsananin tausayin yah Abdul dataji"komai ta kwashe tasameshi tsakar gidan yana duk'e yafara wanke kayan bama wasu masu yawa bane"kitchen taje takai kayan hannunta ta fito da roba mai fad'i ta wanke wanke"ta koma d'akin ta shiga toilet"ruwa ta zubo aciki ta fito tsakar gidan"agefensa ta tsugunna ta d'auki soap d'in da nufin tafara yin sab'i na biyu" bilkisu ki barshi nace kinjiko?"batace komaiba amma fuskarta na nuna bbu dad'i"cikin k'asa da murya yana kallon ta yace"miye abun fushi kuma?"to bakai bane kace bazan tayaka ba" murmushi ya sub'uce masa sbd tabashi dariya takuma burgesa"dan yadda tayi maganar kamar wata k'aramar yarinya"to shikenan kitayani *billy nah* dama ina tsoron kar goggo tasamemu ne tayi fad'a"insha Allah bazata zoba"tafad'a tana k'ok'arin fara sab'in"meenah dake mopping zuciyarta acunshe tana tir da halin mahaifiyar tasu aranta"sai kallonsu takeyi cike da burgewa"ranta na bata tabbas yayanta yayi dace" in sha Allah bilkisu zata bashi farin cikin daya tasa awajen UWAH"harta gama mopping nata bilkisu da yah Abdul na wankin"wannan idan yayi sab'i na farko wannan yayi na biyu"suna kuma d'an fira jefi jefi"bayan su gama yazuba musu ruwan d'auraya"dukda yanad'e k'afar wondonsa da hannun rigarsa"amma saida suka b'aci da ruwa sukayi squising"suna d'aurayar yah Abdul ya deb'o ruwa ahannunsa ya yarfomata a fuska"har taji tsoro ta d'an zaro ido"yakalleta yasaki murmushi mai sauti"wanda yafito masa da tsantsar kyawunsa yana fad'in kin yarda ke matsoraciya ko?"Allah nima zan rama"yaushe to?"wata ran mana"bece komaiba yafara shanya kayan"bilkisu na matsewa ta mik'a masa saiya amsa ya shanya"har suka idar"ta nufi kitchen ta d'akko kayan d'azun harda morning frash nayin wanke wanke"wanda dashi aka kawo cikin kayanta"yah Abdul na ganinta "yayi saurin zuba ruwa a sabuwar robarta da sukayi wanki atare"wajen magujin yazo yaka mata yaduk'a agefenta yana cewa"miye aikin mijin billy? d'auraya zaiyi ko wanke wanke?"yafad'a yana kallon ta"murmushi yasub'uce mata tace"ah ah zanyi da kaina"fitafa zakayi"bbu damuwa bilkisu kinga baida yawa"inaso dama na dinga tayaki aiki"hakan koyine da Annabi muhammad S A W"sbd yana taya matansa aiki"hakane kam"to kamun d'aurayan"ina kwandon to?"yana kitchen"bece komaiba yaje ya d'akko yana addu'ar Allah yasa kar goggo tasamesu har su gama"bayan ya ajiye yafara yi mata d'aurayan"yana bin duk wani motsinta da ido"yafahimci batada damuwa da d'aukar kanta ita watace"sab'anin jidda dayasan Inda itace abubuwan nan da goggo tayi wlh da tayi fushi dashi "k'ilan ma tace bazata zauna agidan ba"amma dubi ita bilkisu bbu ruwanta koma ajikinta da yadda halin goggo yake.....yarfo masa ruwan datayi yasakashi saurin dawowa tunaninsa"Lallai yarinya zamu koma d'aki nidai ko?"dan Allah kayi hak'uri dama na ramane fa"hmm yafad'a yana Ida tsame kayan dake cikin ruwan ya d'auki kwandon yanufi kitchen"ita kuma tafara k'ok'arin sharce wajen.....yah Abdul na fitowa dg cikin kitchen d'in goggo na fitowa dg parlourn ta"ta kallesa ta tab'e baki ta kalli kayan dake shanye"kafin ta kalli bilkisu tace"ke bilkisu da wane ruwan ne kike sharce sharce haka ?"a bayi ta d'ebo goggo dan akwai fanfo.....ba shakka! ta gidan ubanwa har aka jawo muku fanfo mu nan bbu??"wlh dg gidan Alh haruna ne"tsaki taja tana fad'in kace" rok'a kayi?"to ninafi k'arfin nema wajen wani shege"idan kabiru yadawo k'arshen sati za'a mana soma"kuma bazaku amfana dashiba"dan kai bakayin komai agidan nan saidai kai amaka"bece komaiba kansa ak'asa yana sauraronta"bilkisu kuma ta mayar da robar ta kitchen ta fito tashiga d'aki"aranta tausayin mijintane"tabbas ta fahimci yana cikin jarabawa"Allah yahad'ashi da WATA UWAH! bed room d'in ta shiga ta duba cikin kayansa"wani sabon yadi fari mai zanan bak'i ta fito masa dashi"dan dama kala 5 kaya yayi sabbi"tasan fita zaiyi,gashi kayan daya saka sunyi squising"shiyasa ta fito masa dashi"tana k'ok'arin rufe ward rope d'in yashigo d'akin"atsorace ta juyo suka had'a ido"kallon kayan hannunta yayi yace"sannu da k'ok'ari da kulawa bilkisu"dama kayan nazo na canza saina fita"kanta ak'asa tace"to gasunan"tafad'a tana ajiye masa gefen bed"tazo zata rab'a agefensa ta wuce yayi saurin tare bakin k'ofar"gabanta nata fad'uwa bata yarda ta kallesaba"kince keba matsoraciya bace yanzun tsoron miye nake hangowa a idonki??"ki saki jikinki kinjiko?"kanta ta gyad'a masa batayi mgn ba"ganin da gske kunya takeji yasaka kawai yamatsa dg bakin k'ofar yashigo ciki"ita kuma ta fita"bayan yagama saka kayan yafeshe jikinsa da turare yad'akko kud'in da suka rage masa yafito dg d'akin"bilkisu bata cikin parlourn"zama yayi kan kujera yana latsa waya"ahaka tayi sallama ta shigo tana rik'e da basket d'in"da wata leda ahannunta"k'asa gefen santala santalan k'afafuwan sa ta duk'a tana fad'in gashi abashi kayan nan mungode" wannan abama hafsat"sosai yatsareta da ido yana amsar ledar"wadda yafahimci"dubulan ne da cincin dasu alkaki"sosai ya yaba da wayonta da kirkinta"ta gode sosai"kin kyauta Allah yayi miki albarka"ta amsa da Ameen cikin jin dad'i"tsaye ya mik'e yana cewa taso kimun rakkiya zan fita"dato ta amsa ta mik'e tsaye"k'in fita yayi yamatso kusa da ita yakama hannun ta sannan suka fito"ita kuma meenah zata shigo d'akin sukayi cin karo

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login