Showing 51001 words to 54000 words out of 77635 words

Chapter 18 - WATA UWA

Unknown   

10 Nov 2024

3623

fuska.....kasa mgn tayi hawaye nata zuba a fuskarta"yaja doguwar tsuka yana fad'in 30 minit na baki kiyi abinda zakiyi ki fito ki koma part naki"sbd inada abinda zanyi anan"abinci na nan in bazaki iya ciba damuwarki ce"akwai kitchen saiki shiga ki girka abinda kikeso"gidana bbu masu aiki"dg masu gadi da bama flowers ruwa bbu wasu ma'aikata"dole ranar kwananki ki gyaramun part nawa kimun girki"ranar daba kwanankiba"zaki iyayin girkinki"gyara part naki wankinki da gugarki duk kece zakiyi"bbu zancen zuwa anguwa"sannan bana buk'atar bak'o agidana"wlh kika karyamun doka zan amshe shegiyar motarki dana sakq aka ajiyeta a compound"sannan lefe na kwashe manyan kaya na mayar anbar miki abinda ba'a rasaba ko akwati ban bar miki ba na mayar musu da kayansu... yana fad'in hakan yaja tsaki yabar d'akin"jidda ta fashe da kuka tana ganin abin kamar a mafarkine"zuciyarta na wani d'aci da k'una ta tashi dak'yar kamar y'ar kugunu tana tafiya k'afa wawware"kayanta ta kallah dasuka yaga"wanda sabon material ne me tsada"ta kauda kanta ta d'auki ledar kayan bbu komai ajikinta ta nufi bath room tana kuka mai cin rai"tafi minti 30 acikin bayin"kafin ta gama abinda takeyi ta shirya jikinta"tana d'ingishi ta bud'e k'ofar ta fito..... innalillahi wa inna ilaihir raju'un! Jidda ta fad'a with a very shock tana zaro ido"sakamakon ganin Alh duniya kwance zir da mata 2 kowace tana k'ok'arin janyo hankalin sa gareta"sai niahinsu ke tashi cikin d'akin"kauda kanta jidda tayi dan taga alamar basusan da ita bama"kanta dake juyawa ta dafe tana fatan ace mafarkine takeyi"wane irin tashin hankali ne wannan ni jidda?? tafad'a tana laluben hanya tabar d'akin da sauri"da k'yar ta gano part nata"ta tura k'ofar parlourn tashiga"wayarta da keys d'in part d'in nakan center table"ta d'auki key ta rufe k'ofar parlourn"ta dawo tana bin abincin da aka kawo d'azun da kallo"dab'as ta zauna kan kujera tana share hawayenta"gaba d'aya duniyar ta mata zafi"dana sanin auren Alh duniya ne kawai aranta"kuma aganinta be kamata tasanarwa Asee baby wani abuba ko umamanta dg zuwanta gidan yau"abinda yaka mata tayi yanzun shine ta gujewa wannan auren da wannan tantirin"dama haka mata keji idan suka kama mijinsu da karuwa?"bata tab'a jin ta tsani rayuwar datayi ta barikiba sai yanzun"musammun da Alh duniya ke kiranta da karuwa! kuma wai itaba y'ar asali bace"sannan yana kiran mahaifiyarta makwad'aiciya..... wani sabon kukan ta fashe dashi"tana fatan Allah yasa mazan da suka kwanta da ita basuda cuta"gashi kuma Alh duniya nacan na mu'amala da wasu matan.....ta jima tana tunani da kuka"ganin yunwa zata mata lahani yasaka ta zuba abincin taci ta k'oshi ta zauna bbu sallah balle salati"tana ganin kiran Asee ta mata banza"ita yanzun damuwarta shine ta rabu da Alh duniya"damm! k'irjin ta yabuga data tuna ai bilkisu ta auri yah Abdul"to inma bata aureshiba tanada tabbas zai sota har ya aureta??"ta tambayi kanta"gabanta yadinga fad'uwa data tuna har Allah ya isa yamata abaya"tunawa tayi da yadda yagaya mata mgn kwanaki dataje kaima bilkisu anko"yadda taga yana nunama bilkisu soyayya ta tabbatar wani irin mugun so suke yiwa juna shida bilkisu"gaba d'aya kan jidda ya k'ulle ayau duniya ta mata zafi.....koda ta koma bed room d'in ta"tasamu Alh duniya yabar mata kayanta saman bed na lefe"wad'anda ba'a d'inkaba basufi kala 10 ba"sai dubai abaya kala2 da kayan bacci dana shafa suma bamasu yawaba"wani bak'in ciki yakoma kamata"taji dama agida tabar lefen....
***********************
beely na zaune bayan ta gama sallar la'asar yah Abdul yashigo da sallama cikin d'akin"fuskarsa cike da annuri"bilkisu ta d'ago kanta tana amsa sallamar tasa suka had'a ido"turo baki tayi"beely nah nayi laifine?"shiru tayi kawai tana murmushi"yamatso Inda take zaune yaduk'a agabanta yakama hannun ta ya sumbata"mrs Abdul ragguwace kusan 8 month da aurenmu amma kina mun kukan nidai zafi nakeji kaden....kukan shagwab'a tasaka yayi shiru yana dariya"ya d'auke ta gaba d'aya yanufi samqn bed d'in da ita yana fad'in my billy jibi zamu fara zuwa awo fa adubamin lafiyar baby nah"dama sunce 6month zamu fara zuwa awo ko?"kanta ta gyad'a masa"yacire mata hijab d'in jikinta yana shafa gashin kanta"ya aza kanta samqn cinyoyinsa"murya can k'asa yace"wajen yadena zafin ko?"uhmm! Allah my beely sai kin mun mgn"wannan shirun fa?"ashagwab'e tace"to miye zance maka yah Abdul?"yana k'ok'arin mgn sukaji sallama a parlourn"beely ta d'an ware ido tana fad'in kamar fa yaya Ana's ne?"shine ma ba kama ba"yafad'a yana cikata suka sakkowa dg kan bed d'in"tana k'ok'arin riganshi fita tana kuma amsa sallamar"yayi saurin rik'eta yayi hugging nata ta baya yana fad'in bbu Inda zakije yarinya"dan Allah kayi hak'uri nika k'yaleni naje"tafad'a tana turjewa ajikinsa tana shagwab'a"ya lumshe idanuwansa yana kissing gefen kumatunta"ta zuro hannunta ta baya ta masa rankwashi"Ana's d'in zai tafi yabarmu tare yarinya"yafad'a yana dariya yacikata"adaidai time d'in da yaya Ana's ke fad'in kodai na koma bilkisu??nina isa nace haka yah Anas"ta fad'a suna fitowa dg ciki"tun kafin su zauna yayi saurin cewa"yanzun na had'u da wata yarinya ta fita"Allah sarki billy ta fad'a suna zama kan carpet itada yah Abdul dayak'i cika mata hannu"sosai taji kunya"amma ta lura dg Ana's d'in har yah Abdul d'in ko ajikinsu"bayan sun gaisa yamusu jaje da sanar masa ummi da Abba na masa jaje"kan billy ak'asa tace"bara naka maka ruwa ko?"kiyi zamanki ni ak'oshe nake ai"zanma wuce gida "tun yanzun yah Anas?"Eh mana bilkisu dadai yarinyar dana gani yanzun tana nan dana zauna"billy da yah Abdul suka dinga dariya"shi kuma yafita yana murmushi"billy ta kalli yah Abdul tace"ko wace yarinya yake nufi?"to ni kuwa ina zan sani my billy?"k'ilan ko friends d'in meenah yagani"to may bee"tashi mu koma ciki"nidai mu zauna anan sbd masu shigowa ko"bece komaiba ya zame jikinsa ya kwantar da kansa samqn cinyar ta"tayi murmushi taja karan hancinsa tana shafa sumar samqn kansa Ahankali tace"wlh bakaji farin cikin danakeji ba na dawowarka yah Abdul"nima murnan kasancewa dake ne kawai nakeyi my sweet billy"wlh naji jiki da dare wajen bacci"harfa mafarkinki nakeyi saina farka na ganni ni d'aya"time d'in da musa yasanarmun kince kina neman izinin fita anguwa"wlh billy hankalina yatashi"har nace kodai billy nah baya zata juyamun"bana fatan Allah yakawo wannan ranar"bakama yarda da soyayyar dana ke maka ba ko?"ta fad'a tana b'ata fuska tana ture kansa dg samqn cinyarta.....
yah Anas kuwa yana fitowa asoro zai fita sukayi clashing da meenah zata koma cikin gidan"had'a ido sukayi, anan ya hango kamannin ta da yah Abdul na jini"ita kuwa gabanta taji yafad'i"dama d'azun ma ta ganshi"ayanzun ma haka saidai yamata kama da Anty billy"rab'awa gefensa tayi ta wuce ciki"shi kuma yayi gaba yana jin gaba d'aya yarinyar ta tafi da imaninsa.....meenah parlourn su billy ta nufa"da sallama ta shigo"saidai taji kunyar yadda tasamesu"dan bilkisu na zaune kan cinyarsa yanata rarrashinta sbd fushin datayi yanzun"yazuro kansa agefen kunnanta yana mata rad'a ta turo baki tana saurarensa... yarik'e hannayenta"saidai tana ganin meenah tafara kiciniyar k'wacewa"yarik'e gam"meenah duk ta daburce tace"yaya sannunku da hutawa"yauwa dg ina kike?"goggo dama ta aikeni na kira sadeeq"okay time d'in dazaki fita kin had'u da Ana's?"waye haka yaya?"ina tambayarki kina tambayata"yafad'a yana matse bilkisu ajikinsa"yaya nidai na had'u da wani zai shigo"sai yanzun kuma dazan fita nakoma ganinsa"naga kamar ma suna kama da Anty billy"yaya Ana's nefa meenah"shima yace yaga wata ashe kece?"murmushi meenah tayi tabar parlourn cike da kunya"tana fita billy ta cijesa ayatsa tace"me kenan kayi agaban meenah?"bakajin kunyarta?nifa ko agaban ummi zan iya zama dake ahaka"ina sonki billy zan kuma nuna ko agaban waye"murmushi tayi ta juyo ta kwantar da kanta akirjinsa ta masa zobe da hannayenta"murya can k'asa yace"kin hak'ura?"uhmm!yauwa tawan kinsan kowa yana kuskure arayuwa my billy"Allah yabarmu tare"fad'amun me akayi dabana nan? babu komai"nidai nashiga damuwar rashinka yah Abdul"amma kaga Alhamdllh tunda kadawo ko?"hakane my billy yanzun damuwata nasamu wata sana'aryi kar na zauna a haka"ga cikin mu kusan 6 month billy dole nadamu"babu komai ni a wajena yah Abdul"Allah yasan damu"munada kayan abinci ayanzun wanda zamuyi kusan 2weeks dashi"sannan akwai cikon 10k da kuma 2600 naka dana gani a aljihun rigarka dazanyi wanki.nasan ka mantasu"10k na meye kuma?"sanar masa yadda sukayi da musa tayi"yana murmushi yace"my billy ai kud'inki ne banawa ba...batayi mgn ba tafara k'ok'arin barin jikinsa"yarik'e ta yana murmushi yace"bana son wannan saurin fushin naji nawane shikenan?"kanta ta gyad'a masa"yaja kumatunta yana fad'in banida bakin gode miki sai addu'a da fatan alkhairi"kinyi kota ina bilkisu"ada ina yiwa mata kallon mayaudarane amma billy kin ciremun wannan shakkun"kullum ina godema Allah daya bani ke amatsayin mata"Allah yasa karki canza kyawawan halayen ki"wanki kuma dg yau na sokeshi nizan dinga mana ina yi mana guga"sbd me to?"sbd ina sonki billy nah"murmushi tayi cike da shauk'i....sun jima anan suna firansu da wasansu na soyayya"sai ana kiran magrib yafita be dawo ba sai isha'i"yasamu ta gama dafa musu jallof d'in taliya dataji curry da kifi tanata k'amshi"ya zauna sukaci atare..... awannan dare billy tasha kalaman k'auna gun yah Abdul"be kuma yi mata komaiba sbd beson tasha wahala"badan kuma beda buk'ata ba....awashe gari ma bayan sun gama sallar asuba"ta fahimci yanada buk'atar amma yabarta sbd ta huta"hakan yasa da kanta tafara masa wasu salo masu wuyar fad'i"besan time d'in daya biye mata suka lula wata duniyar ba....
##########
kimanin wata d'aya da sati 2 kenan da faruwar haka ga yah Abdul"wanda kwanansa 4 da dawowa akasha bikin kabeer suka tare da amaryarsa laurat a anguwar *sama road*.....billy da Abdul sunsha mita wajen goggo sbd bema bilkisu anko ba"dan ita bilkisun ma ranar yinin bikin tun wajen 10 am tabar gidan"sai wajen isha'i yah Abdul yaje yasameta agidansj suka dawo tare....ahaka suka cigaba da zama agidan yah Abdul beda aikinyi"y'an kud'in billy na ribar sana'rta dasu suke yin komai"kullum sai goggo ta masa gori"dukda haka sunyi kyau abinsu abin shawa'a"billy nata hak'uri da juriya da yanayin bukatarsa"time d'in da yah Abdul yaga cikin billy yayi 7 month yadamu sosai"hakan yasa bayaji baya gani yana neman ko wane aiki ne yayi sbd yasamu abinda zai rufawa kansu asiri dashi"atare da musa sukayi nassarar samun aikin gini wanda duka befi sati 2 da samun saba"kuma Alhmdllh arana yasamu 3k nashi na kanshi bayan anbashi 1k yayi cefane"to hakan yasa yarage zaman gidan sosai"tunda kabeer yayi aure sai yayi sati ko 10days bezo gidan ba"goggo nasan masa mgn amma tana gudun kar abinda yakeyi mata yafasa"gashi yanzun yadawo nan da aiki an masa transfer"meenah kuwa harta shiga aji na biyu"tanata karatunta amma zuciyarta dank'are da soyayyar yaya Ana's"wanda har yanzun bata koma zancensa da billy ba"to shima yah Anas d'in a b'angaren nasa yanajin soyayyar yarinyar a kullum amma yabasar...
Ayau da marece misalin k'arfe 5:11 pm"billy ce duk'e da tulelen cikinta tana share soro Inda duk yaran dake shigowa siyan k'ank'ara suka b'ata da ledoji"dan tasan idan bata shareba tashiga ukku da masifar goggo"dan dama ta gama cin kasuwarta harma takai kular da kud'in d'aki"tana k'ok'arin kwashe sharan taji wani k'amshin turare mai dad'i"sai kuma taji motsin mutum"da sauri ta juya bayanta suka had'a ido da kabeer"yatsareta da ido yanata kallonta yayi tsaye"d'auke kanta tayi da sauri tana jin fad'uwar gaba"Ahankali tace"ina wuni?"lafiya qlau big madam"dama inaso nayi wata mgn dake tuni ban sami iko ko dama ba"wata mgn kuma?"ta tambaya tana mik'ewa tsaye"yana d'age gira yace"Eh kuma harkan samuce in ba zaki iyaba wlh zan baki mamaki"subahanallahi! ta fad'a tana k'ok'arin tafiya"yayi saurin shan gabanta da sauri"tayi baya sbd ganin yana gab da ita"mlm lafiya wai?"miye haka?"ta tambaya fuska ad'aure"ba wani abu bane kud'i zan baki indai zaki amince dani mu dinga hud'da"dan kinada wannan cikin be dameniba"nasan dai yah Abdul beda kud'in dazai dinga baki kina kashewa"amma ni nan komai kike so zan baki"kawai anguwa zaki tambayesa"saiki kirani nasanar miki inda mai nafef zakice yakaiki saimu had'u.....cak yah Abdul da zuciyarsa ke bugawa ya tsaya dg wajen k'ofar gidan yana hangensu ta k'afar k'ofar sbd yaji wace irin amsa billy zata bawa kabeer??

wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
Acc n 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki ta what's app n d'ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika fitarmun Allah ya isa ban yafeba

..........bilkisu na girgiza kanta cikin yanayi na tashin hankali da b'acin rai tace"innalillahi wa inna ilaihir raju'un!! tir da mugun halin ka"Allah ya shiryeka"niba fasik'a bace komai zakayi kayi Allah yafika"in bacin kana bunsuru matar yayanka zaka yiwa wannan maganar banzan?"an fad'a maka talauci hauka ne?"miyasa bama tunanin me gaba zata haifar son zuciya shine muke bi??"kowa dai kud'i kowa dai kudiiiiiiii! ke dakata kin isa kig....shigowar yah Abdul soron kamar anjehosa yana huci shine yasaka kabeer ya had'iye sauran maganarsa "gabansa na fad'uwa yakalli yah Abdul daya nufosa idanuwansa jajir"yaya Abdul! cewar bilkisu"banza yamata cikin hanzari ya damk'o kabeer dake k'ok'arin shiga ciki"arikice kabeer yajuyo yana fad'in mlm lafiya?"amma be yadda ya kalli cikin idonsa ba"wani zazzafan huci yafurzar dg bakinsa yana bin kabeer da wani irin mugun kallo yace"iskancin naka ya wuce kayi awaje harma cikin gida yazo"kuma akan matata ta sunna"zan iya kasheka akan bilkisu! zan iya rasa raina sbd mutuncin matata"natsaneka kabeer! kaiba d'an uwane nagari ba... sharri zakamun kenan?"cewar kabeer cikin borin kunya yana k'ok'arin k'wace jikinsa"yyinda bilkisu ke tsaye tana kallonsu gabanta nata fad'uwa.....yah Abdul yamakasa jikin bango kansa yabugu"yasaki ihun azaba mai k'arfi"yafara dukansa ahaukace yana fad'in zaka koma kallon mun mata dan ubanka??"arikice bilkisu dake tsaye tace"dan Allah yaya Abdul karabu dashi kar goggo tazo"bata rufe bakiba taji muryar goggo na fad'in ihun menakeji haka?"shiru kawai bilkisu tayi gabanta nata fad'uwa musammun dataga itace silar komai.... innalillahi wa inna ilaihir raju'un me zan gani ni fatima??"bakada hankali Abdul?"meya maka kake dukansa?"bazaka dena ba?"goggo tafad'a atsawace tana matsowa gabansu"Abdul na huci yana dukan kabeer yana koma maimaita zaka koma kallon Inda matata take??"ohho sbd ita bilkisun kake neman rabashi da ransa?"kana bak'in ciki yafika samu"wlh idan baka dena dukansaba zan tsine maka albarka"kaji mugun yaro azzalimi"kai bakamun uban komai shida yakemun zakaga bayansa.....cak yah Abdul yacika kabeer yana huci"kabeer yafad'i hancinsa da bakinsa na fitar da jini"arikice goggo ta nufesa tana k'undumama yah Abdul zagi"billy tafashe da kuka tazo tafad'a jikinsa"yarungumeta yana sakin ajiyar zuciya"goggo ta d'ago kanta ta kallesu"cikin tsananin b'acin rai tace"ayau zakubar gidan nan bama sai an kwana ba"ko kuwa wlh na tsine maka! arikice yah Abdul ke kallonta yace"tsinuwa goggo sbd na hukunta kabeer dake k'ok'arin neman ya aikata bad'ala da matata?"karkamun maganar banza dan ubanka"kaje kaga ga matar nan nabar mata kai"dama kun isheni agidan nan"sai kasan yadda zakayi da ita"amma wlh zamanku yak'are agidan nan"karma kusake ku kwanarmun agida"in kuwa kak'i ji ba kak'i ganiba"mutumin banza wanda yazab'i mace akan d'an uwansa"ke kuma munafukar Allah zakisan kin had'a tsakanin d'an uwa da d'an uwa"saiki koma gidan ku ki haife wannan cikin"goggo nakai aya azancen ta takama hannun kabeer suka wuce ciki tana fad'in dg nan zuwa isha'i muddin basubar gidan ba zasuga abinda zai biyo baya"bayan barinsu soron"bilkisu ta fashe da kuka tana turashi dg jikinta tana fad'in kaga abinda wannan zuciyar taka tajawo mana ko yaya Abdul??"koma miye yaso yamun Allah yafisa"gashi yanuna ikonsa daya kawoka..... rik'eta yayi gam yana saka k'wayar idanuwansa acikin nata"fuskarsa ad'aure yace"bilkisu koda goggo bata kore muba dole agobe mubar wannan gidan"akan mutuncinki zan iya komai"inada zafin kishi akanki bilkisu"tayaya bazan hukunta kabeer ba bayan yaso yatab'a k'imarki?tun farkon fara maganarsa na iso wajen"na lab'e har yakai aya azancen banzansa"indai bilkisu wahala ko dad'i zaki kasance atare dani bbu komai"adaren yau zamubar gidan nan kamar yadda goggo ta buk'ata"in sha Allah barinmu gidan nan alkhairi ne! kuka kawai bilkisu taci gaba dayi"yah Abdul yajata suka shigo cikin gidan"meenah na tsakar gidan tana kuka"sbd dama bacci takeyi haka yafaru"shine taji fad'an goggo a parlour ta farka"ta tambayi meke faruwa"?goggo tasanar mata yadda kabeer yafad'a mata"kai tsaye meenah tace"ba haka akayiba"kuma wlh ta koresu zata sanarwa baffa Aminu"shine goggo ta mammareta ta koreta dg cikin parlourn"tana nan tana kuka tabi su yah Abdul da kallon tausayi har suka shige d'aki"suna shiga bilkisu ta fisge hannunta ta wuce ciki ta haye saman bed d'in tana kuka"beyi fushi ba yabi bayan ta"ya kwanta agefenta yakamo hannunta guda ya had'a da nasa"murya na rawa yace"billy bana son kukanki kin sani yana d'agamun hankali"ki dena wannan kukan ba'a so mai juna biyu na shiga damuwa"zamu bar gidan kamar yadda goggo ta buk'ata"bazata tsinemun ba"nasan sbd haka kike kuka ko?"yafad'a yana shafo cikinta"hannunta take murzawa cikin nasa tayi shiru tana sakin ajiyar zuciya"my billy nah! Uhmm"kin hak'ura ko?"kanta ta gyad'a masa"tana k'ara matsowa jikinsa tana shige masa"shima matseta ajikinsa yayi yana sinsinarta yana sakin ajiyar zuciya"wayarsa dake gaban aljihu ya d'auka yafara k'ok'arin kiran layin musa"bubu 2 musan ya d'auka"ko gaisawa basuyi ba"yasanar masa komai....salati kawai musan keyi"dg k'arshe yace"bbu matsala akwai gidan babban yayansa da matarsa ta rasu da yaransu 3"to yaran na wajen iyayen matar"zai kirashi yanzun yaji idan ya aramusu kona wata 6 haka kafin susan yadda zasuyi"godiya Abdul yamasa yakashe wayar"yad'ago fuskar billy suka had'a ido"langab'e mata kansa yyi yace"in sha Allah ba anan zamu kwana ba"komai zamu kwashe mu koma can"da safe saimu jera komai ko"kanta kawai ta gyad'a masa"ya matso da fuskarsa asaitin tata tayi saurin manna bakinsa cikin nata tana shafa kansa"sunjima suna kissing juna"ganin zai saki layi yasaka ta janye bakinta"yakama hannun ta suka sauka dg kan bed d'in"acikin akwatinanta na lefe suka kwashe kayan sawarsu suka saka"sannan yah Abdul yakwance gadon"yacire labulaye da carpet"sai ana gab da kiran magrib yasanar mata zaije masjeed"bayan yafita meenah ta shigo"rarrashin bilkisu tayi tanuna mata garama su tashi indai akwai Inda zasu zauna sunfi walawa"ta jima tana rarrashinta"kafin da kanta taje ta kamata buhunna sukayi parking d'in kayan kitchen aciki"zuwa bayan sallar isha'i duk sun gama parking d'in komai"bilkisu na zaune da hijab ajikinta bisa abin sallah tanata lazimi a parlourn"ahaka taji muryar yah Abdul da musa"billy mu shigo"sosai taji wani irin tausayinsa"murya akare tace"Eh ku shigo"da sallama musa ya shigo ta gaishesa"yah Abdul na murmushi yamatso yakama hannun ta yana fad'in kaga abokina dukta damu"bayan tasan damuwarta nad'agamun hankali"hakane kam"amma ke hjy billy yaka mata ki kwantar da hankalinki bbu wata matsala in sha Allah"fatanmu Allah yasa tashin naku shine yafi alkhairi"kanta ak'asa tace"Ameen yah Allah"ta kalli yah Abdul

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login