Showing 69001 words to 72000 words out of 77635 words

Chapter 24 - WATA UWA

Unknown   

10 Nov 2024

3634

da nufin tabashi hak'uri itama....hakan yayi daidai da shigowar Aliyu aguje tsakar gidan yana fad'in ummi !ga Anty bilkisu nan itada mijinta sunzo cikin sabuwar mota me kyau"gaban jidda yayi wani irin mugun fad'uwa"Abba yayi murmushi yace"madalallah! kafin yadubi jidda yace"kin wofintar da zab'in dana miki"na kuma d'auka nabama bilkisu ta hak'ura ta amsa"gashi yazamar mata alkhairi"ko jiya yazo yasanarmun saura kwana3 su tashi su koma sabon gidansu ga aiki yasamu"ita duniya dakike gani fad'i ne da ita kuma bbu irin karatun dabata koyama mutum"indai kayi hak'uri kaine da riba"dududu yanzun shekara guda kenan da auren nasu"amma Allah yasauya komai"da kece Kika auresa kinyi hak'uri da yanzun komai ya sauya"saidai ance dana sani k'eya ce......jidda na girgiza kanta zatayi mgn tattausan muryar yah Abdul ta daki dodon kunnanta yana sallama cikin nutsuwa"ta juya da sauri tagansu shida bilkisu yana rik'e da hannun ta da akayima lalle"sunyi gwanin kyau shar dasu....atake yah Abdul yacanza fuska sbd ganinsu dayayi"wanda Abba da ummi na lura da yanayinsa"cika hannun billy yayi yaduk'a yace"Abba da ummi ina wuninku??"yafad'a danma kar yayi jam'i magajiya tasan harda ita yagaida" lfy qlau Abdul yawajen goggo da jiki?"Alhmdllh! yafad'a yana murmushi yakalli auta Aliyu yace"auta zo muje waje ka rakani"ummi na murmushi tace"anyi mota Abdul Allah yasa alkhairi yatsare "Ameen yah Allah ummi "my billy zamuje mudawo"bilkisu dake zaune tana kallon jidda ta amsa dato "yah Abdul beko kalli su jidda da magajiya ba wad'anda keta kallonsa"saima yayi k'asa da kansa aladabce yace Abba"inaso muje dg waje"to shikenan Abdul hakeem muje"yah Abdul na rik'e da hannun Aliyu yayima ummi sallama yafita"Abba yabi bayansa"sai asannan bilkisu ta gaishe da magajiya daketa kallonta kamar ta cinyeta"Anty jidda ya jiki kuma?da sauk'i bilkisu"dg haka shiru yabiyo baya"bilkisu ta matsa suna gaisawa da ummi suna firansu gwanin sha'awa "ummi na yaba kyawun lallen na bilkisu"ahaka Abba yadawo yana murmushi"Aliyu da wasu yara na biye dashi sunata shigowa da kayan abinci wanda Abdul ne da kansa yasiya yaraba biyu yakaiwa goggo rabi yakawo rabi anan gidan....bilkisu ta gaishe da Abba ya amsa cike da kulawa kafin yanufi d'aki "magajiya na kallon Abba dake k'ok'arin bud'e k'ofar d'akinsa tace"mlm kai nake jira fa"yanzun kuwa zan baki sak'onki yafad'a ko ajikinsa yana bud'e k'ofar d'akin ya wuce ciki"bbu jumawa yafito rik'e da takarda a hannunsa"magajiya ta zaro ido tana nuna kanta tana fad'in da gske ka sakeni?"ki duba mana sbd ki tabbatar"yafad'a yana jifarta da takardan yakoma d'aki"jidda kamar zuciyarta zata fashe dan gaba d'aya sabon son Abdul ne aranta"saidai aganinta yamata nisa fintin kau"tasan ko bilkisu mutuwa tayi bazai auretaba"magajiya tafashe da kuka tana rik'e da takardan ta kalli jidda tace"muje jidda"tafad'a tana turata kan wheelchair d'in datake azaune"wani irin tausayi suka bama bilkisu da ummi dake zaune"amma sun tabbatar koma miye yafaru laifinsune"suna fitowa suka hau adaidaita suka nufi gidan atine....
yah Abdul kuwa be dawo gidan su billy ba saida marece sosai yamata waya ta fito"suka nufi wajen shak'atawa cike da farin ciki da k'aunar juna"sannan yakaita aka mata gyaran gashi"wanda tana acan magrib tayi"shi yayi sallarsa a masjeed"ita kuma batayiba"sai bayan angama suka tafi gida sannan tayi tata sallar....
washe gari misalin k'arfe 8:11 am"bilkisu ce da yah Abdul tsaye asoron gidansu" yana sanye da suit bak'ak'e"y'ar ciki red"nectie d'in yazauna sosai"yanata zabga k'amshi"billy na rik'e da jakarsa ta office"kanta bbu d'an kwali tana sanye da doguwar riga ta bacci iya gwiwa"lallen da aka mata yakomayin maroon"sai shagwab'a takeyi yana aikin kallonta"gaba d'aya kishine dank'are aranta"yana murmushi yace"my billy ki koma kiyi bacci anjima zan kiraki nabaki labarin yadda na fara aikin"shikenan Allah yakaimu"kayi addu'a idan zaka shiga office naka kuma kadinga d'aure fuska"yana dariya yaja hancinta yace"to shikenan ranki yadad'e"amun kiss saina wuce ko?"yafad'a yana matsowa da fuskarsa asaitin tata" ta sum baci lips nasa tana murmushi"my billy kamar karna tafi na barki nakeji"kuma fa saina biya gidan goggo"yanada kyau ka biya d'in gsky"to mezan fad'a mata?"kace ina gaisheta"Allah yatsaremun kai yabaka sa'a yah Abdul"tafad'a tana janye jikinta dg nasa suka had'a ido"yasakar mata tattausan murmushi yana amsawa da Ameen"ta d'aga masa hannu yafita cike da kewarta"ita kuma takoma cikin gidan tafara aikace aikace.....
kimanin kwana 3 kenan da fara aikin yah Abdul"kuma komai Alhmdllh"kabeer ma na part d'in dasu yah Abdul suka tashi agidan goggo" babu wata sana'a dayakeyi"anan gidan goggo ake cidashi"sannan yanzun goggo bata sake masa fuska kamar da"aiyuka da dama tana sashi bbu kuma damar yak'iyi koda baiso kuwa aransa sai yayi"yau tun bayan sallar la'asar meenah ta d'auki zazzafan wanka sbd zataje gidan yah Abdul amma sabon gidan"dan ayau zasu koma"kuma be sanarwa billy ba"kawai dai yace"ta shirya idan yadawo office zasuje anguwa"koda meenah ta fito cikin sabuwar shadda"d'inkin doguwar riga light blue" an mata aiki da bak'in zare"mayafi da hand bag duk bak'ak'e tasaka da plate shoes"tanata k'amshi tayi gwanin kyau da ita"goggo na kallonta tana murmushi tace"auta kin shirya?"eh goggo yaya kabeer yazauna dake harna dawo"kabeer dake parlourn yana kallo yafito fuska ad'aure yana fad'in ke k'arfe 5 kallon ball zanje fa"ke meenah wuce kije ki rabu dashi"kallon ball d'in yafiye maka ni?"kai bakaje kayi sana'a ba ka tare agida kana mana zancen kallon ball"cewar goggo tana tab'e baki"bece komaiba ya koma parlourn kamar yayi kuka sbd b'acin rai....meenah kuwa ficewa tayi ta hau adaidaita ta nufi gidan yaya Abdul...
Ahankali yah Abdul yayi parking k'ofar wani had'add'en gida me farin get"bilkisu dake zaune gefensa wacce gaba d'aya batama jin dad'in jikinta tunda ta tashi a yau"Ahankali tace"inane nan yah Abdul?"siyar dake nazo nayi my billy"d'an murmushi tayi tace"zolaya ko?"nidai ka fad'amun mana"tafad'a cikin shagwab'a"to gidanki ne nakawoki....wannan suprise haka yah Abdul"
?" tafad'a tana k'ok'arin fitowa dg cikin motar" farin cikin ta yak'i b'oyuwa"shima fitowa yayi yana murmushi yanufi gefenta Inda take a tsaye yabud'e k'ofar get d'in"tayi hanzarin shiga"shi kuma yazare key d'in yakoma cikin motar yashigo da ita cikin gidan"kafin yagama parking yarufe k'ofar get d'in"billy na tsaye tana k'arema haraban gidan kallo"madaidaici ne wanda zaici mota 2"ranta fari k'al tana yaba tsarin gidan"yah Abdul ya matso ya rungumeta ta baya yana fad'in gidan yayi ko my billy?"yafad'a yana mata rad'a agefen kunne" yayi kyau sosai yah Abdul"Allah yasa alkhairi yasa wajen zamanmune"Ameen yah Allah"muje dg ciki kiga ko ina"dan anan zamu kwana in sha Allah" yanzun meenah na hanya zamu koma idan tazo mu kwashe sauran kayanmu dake can"dato ta amsa suka zagaya hanyar shiga cikin gidan"wata k'ofa ce dg gefe da alama itace k'ofar main parlour"ita suka nufa suka taka step 2"yah Abdul yabud'e k'ofar parlourn suka shiga.....zaro ido bilkisu tayi sbd ganin kujeru na alfarma da center table"ga kayan kallo da dining table ,ga carpet da labulaye"kai parlour dai na y'an gayu wanda bilkisu bata tab'a zaton zata mallaka ba ko a mafarki"juyowa tayi suka had'a ido"yah Abdul ya gyad'a mata kansa yana murmushi had'e da cewa"k'warai my billy parlourn kine"idan Allah yabani ikoma zan miki finsa"furnitures naki zamu d'akko asaka a bed room guda"nan gaba gudan bed room d'in za'a zuba furnitures"ga kitchen kuma can muje ki gani"billy batasan time d'in data fad'a jikinsa ta rungumesa ba tana kukan farin ciki"sorry my billy"kin cancanci fin haka dg gareni"fatana Allah yak'ara bamu zaman lafiya nest 9month ki koma bani wani babyn ko?"yafad'a yana murmushi yad'ago kanta yana share mata hawayenta....ahaka wayarsa tayi ringing yaduba yana fad'in meenah ce"kinga musa da Ana's d'in ma basu isoba"k'ilan yana hanya ne"cewar billy"bara naje na bud'e mata get my billy"dato ta amsa shi kuma yafita"bilkisu ta nufi kitchen d'in"wow tafad'a sbd arba datayi da gas cooker an gama had'a ta"ga wasu sabbin warmers agefe a ajiye"kitchen cabinet d'in sosai suma suka burgeta"tana ahaka taji muryar meenah"fitowa dg cikin kitchen d'in tayi tana fad'in ga autan goggo"masha Allah Anty billy"gida yayi kyau"Allah yasa alkhairi"Ameen yah Allah meenah"kinsha kyau fa"yah Abdul yayi murmushi sbd burgesan da sukayi"beyi mgn ba yanufi k'ofa zai fita"ina zuwa sweet heart?"cewar billy tana k'ok'arin zama gefen meenah" Ana's zanje na shigo dashi"okay billy ta fad'a shi kuma yafita"meenah taji gabanta yafad'i dataji an anbaci sunan yah Ana's ! tadai dake kawai tana yiwa billy santin gidan"kije kiga kitchen d'in mana"ga kuma 2 bed room can"cewar bilkisu"meenah na k'ok'arin mgn yah Abdul da yah Anas sukayi sallama acikin parlourn...✍️

wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
Acc n 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki ta what's app n d'ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika fitarmun Allah ya isa ban yafeba

........tunda yah Anas yashigo idanuwansa k'yam akan meenah datak'i kallon gefen da suke tsaye shida yah Abdul"yah Anas yasha gayunsa cikin k'ananun kaya yanata k'amshi"siririn sajensa yak'ara k'awata fuskarsa"bilkisu cike da fara'a ta tarbesa ya zauna suka gaisa yana yaba tsarin gidan da musu fatan alkhairi"yah Abdul na zaune gefen billy yana lura da meenah batayi mgn ba"yana k'ok'arin yi mata mgn ta gaishe da Ana's"sai shi Ana's d'in yarigashi da fad'in meenah ina wuni?"yafad'a yana tsareta da ido"gaba d'aya duk ta tsure takasa amsawa sbd kunya ta kamata"yah Abdul yatab'e baki yana fad'in gulman banza ki amsa mana tunda ke baki gaisheshi ba"yah Abdul naga mgn kukeyi fa"wai dama kasan sunanta yah Anas?"cewar billy"harara yagallah mata yana fad'in gata nan ki yambayeta mana"bata gaisheni ba nina gaisheta tak'i kuma ta amsamun"murmushi meenah tayi tace"ina wuni yasu ummi?"lafiya qlau Alhamdllh"ya goggo da jiki?"da sauk'i sosai"masha Allah"my billy bara naje nasamu musa azo da sauran kayan dake gida"bandamu zakaje yah Abdul?"Eh ayanzun sai komawa ta biyu zamuje dake da wannan magulmaciyar"yafad'a yana kallon meenah yatashi tsaye"waini yaya gulmar menayi ne?"nima dai abinda nakeso naji kenan"cewar yah Anas yana murmushi"yah Abdul beyi mgn ba yaja hannun bilkisu suka fita dg cikin parlourn"cikin rashin sa'a meenah ta d'ago kanta.....caraf idanuwanta suka sark'e dana shi"tayi saurin janye idanuwanta kamar ta tashi tabar wajen haka taji"meenah idan bbu damuwa pls samin contact naki mana "yafad'a yana tasowa yamik'a mata wayar sa"bbu musu ta amsa ta saka masa yanata kallonta ya amshi wayar yakoma yazauna"yana k'ok'arin mgn bilkisu ta shigo cikin parlourn"d'an murmushi tayi ta zauna tana fad'in yah Anas firan me akeyi?"yana murmushi yace"ta soyayya mana"irin wacce kikayi keda yah Abdul"ni zan wuce gida"sai nazo na kamiki auta"tana murmushi tace"ummi bazata zoba?"kema ai kinsan bazata zoba"yafad'a yana mik'ewa tsaye yasaci kallon meenah yana murmushi kanta ak'asa"meenah na wuce gida"sai anjima agaisheda ummi tafad'a batare data kallesaba"yafita yana murmushi"bilkisu na kallonta tace"kai meenah kodai bakyason yaya na nah?"meenah ta d'ago kanta da nufin tayi mgn taji k'arar shigowar text message awayarta"tana dubawa taga bak'uwar number anturo kalmar I LOVE U*murmushi tasaki dan ranta yabata yah Anas ne"billy dai na kallonta"meenah ta d'ago kanta suka had'a ido tayi dariya tana fad'in wlh tako ina yayanki ya had'u Anty billy"ina son namiji kyakykyawa kuma d'an gayu"wlh idan naga kuna soyayya da yaya mugun burgeni kukeyi"billy na dariya tace"aikuwa indai shine zaki aura tokin samu baban soyayya....duk suka saki murmushin atare"sunata firansu har yah Abdul da musa da wani suka dawo da furnitures"meenah da billy suka k'afa gadon aka shiryashi"sannan gaba d'aya suka tafi tsohon gidan su duka amotar yah Abdul suka kwaso sauran kayan"wanda koda suka dawo billy da meenah suka shirya komai tsab"atake gida yayi kyau gwanin sha'awa"suna zaune gab da magrib a parlourn"sai santin gidan meenah keyi tana tuna rayuwar yah Abdul ta baya shida billy"afili tace"ikon Allah kenan ! na yarda rayuwa tana faruwa wucewa take kamar ba'a yiba"kuma duk abinda kayi hak'uri dashi insha Allah wata ran zai wuce"Anty billy Allah yasa alkhairi yak'ara baku zaman lafiya da yaya"dan Allah ki k'ara rik'e yaya Abdul gam"musammun sbd yanzun kun samu hutu zai k'ara kyau da gogewa"billy fuskarta bbu walwala tace"wlh kuwa meenah"matan yanzun wasu sai addu'a"basujin kunyar su furta suna son namiji"shi kuma namiji baka shedarsa"ina kishin mijina sosai"karki damu Anty billy insha Allah yaya bazai kasance mai cin amanarkiba"ki dinga kulawa da abinki kamar da kina mamuke dashi bbu shegiyar da zatayi gigin kusantoshi"Allah yasa meenah"Ameen yah Allah"kinga an kusa magrib bara na tafi gida dama yaya kabeer ne kawai na bari wajen goggo"Eh gsky da har zance ki bari sai yah Abdul yadawo"nika d'ai za'a barni kenan?"billy bata rufe bakiba yah Abdul da musa suka shigo da kaya nik'i nik'i ahannunsu suka nufi kitchen"billy na musu sannu"suna fitowa yah Abdul yace"abokina ka wuce da meenah gida"okay bbu damuwa"hjy billy Allah yasa alkhairi, baby nah itama tana nan tafe"Ameen yah Allah"gsky kamata yayi gobe ka kamun ita yini"saidai Friday"week end ina gida bancika barinta fitaba aranar"yah Abdul na murmushi yayi shiru kawai dandai agaban meenah ne"bilkisu dai y'ar dariya tayi batace komaiba"atare musa da meenah suka fita"yah Abdul yabisu yarufe get d'in gidan"bilkisu na tsaye aparlourn yashigo"rungumota ajikinsa ta baya yayi yana maida numfashi"ka gaji ko yah Abdul?"wlh kuwa my billy"muje kitchen kiduba kayan can ko kafin akira sallah"dato ta amsa yacikata suka nufi kitchen d'in atare"sosai ta dinga kallon kayan tana murmushi tana mamakin wai itace ayau zatasha ruwan roba"dan ruwa katan 3 ne, lemo na roba katan biyu"ga shinkafa , super getting,macaroni, indomie,dankali ,cefane, fruits"kayan vegetables,mai ,maggi da sauransu"yah Abdul meyasa baka Adana wasu kud'in ba?"naga duk kasiyo abubuwa masu tsada"tafad'a tana maida kallonta garesa"my billy kenan! "ai amfanin nema samu"amfanin samu kuma huce takaicin duniya"kaf kud'in nan sun k'are duka"100k ne sukayi saura yanzun"kuma na bama musa su"wanda acikin kud'in nace ya ibi konawa yakeso"yak'iya yace"nabashi 10k sun ishesa"na nuna masa b'acin raina shine ya amshi 100k"wlh banji dad'i ba yanunamun babu komai ai hidima mukeyi"amma albashin farko zai amshi wani abu da yawa"hakane kam tarenku dashi yaci konawane ya iba"wlh bilkisu ko duka kud'in zan iya rabawa dashi"sai yanuna bema san haka"aishi abotarmu dashi ta Allah ce ba biyansa zanyi abinda yamun abaya ba"wannan gsky ne kuma Allah yabarku tare"ina taya su ummi godiyar kay.....bana son wata godiya my billy"su ummi nima iyayena ne"wai kinsan ashe Ana's son meenah yakeyi?"haka nima nagani"amma beda wata rik'akkiyar sana'a zai kama soyayya?"Allah zai dafa masa my billy ai yagama karatu ko?"service yakeyi yanzun"in sha Allah za'a dara nan gaba"kuma nabashi meenah sbd babban wa ubah" kaida bakaji ta bakin taba? cewar billy tana tuna Inda goggo bata canza Hali ba bazata bari yah Anas yafara soyayya da meenah ba"ai Ana's irinsu ba'a cewa ba'a so my billy"yafad'a yana tayata suka jera komai Inda yadace"sannan suka wuce bed room d'in su"atare suka shiga bayi"yayi alwalah yafito yabarta ciki sbd yatafi masjeed...
washe gari da safe yakama week end"tun bayan sun gama sallar asuba billy ta gudo dg wajen oganta"sbd tasan muddin yafarka dg bacci zai nemi kar'i dan jiya sosai da dare yagajiyar da ita"kitchen ta nufa tafara k'ok'arin had'a musu break fast......chips ne da ruwan zafi ta dafa"saita soya bread da k'wai"tana jera komai acikin tray taji motsin shigowar mutum"juyowa tayi suka had'a ido"yatsareta da fararen manyan idanuwansa yanata aikin kallo"cike da burgewa da tsantsar so"yana sanye da jallabiya blue colour"yayi tsaye"yah Abdul ka tashi?"b'ata fuska yayi kamar wani d'an yaro yace"meyasa kika gudo nan my billy?"bayan kinsan idan nashafa naji bbuke akusa dani bana samun nutsuwa"oh my God yah Abdul break fast nazo na had'a maka"banaso katashi kaji yunwa fa"ni babu wani nan"yafad'a yana fita dg cikin kitchen d'in"bilkisu tayi murmushi"sbd ta fahimci yau rigima yakeji"babban tray d'in ta d'auka tanufi parlourn"yana zaune kan kujera yana kallo"kan dining table ta ajiye komai ta nufo wajen yah Abdul"agefensa ta zauna ya kauda kansa"murmushi tasaki tana rik'e hannun sa guda tana kallon sa tace"haba habeebi nah!katashi na maka wanka kazo kayi break fast"sai kaje ka gaishe da goggo"idan kadawo zan baka wani labari....duk tana maganar ne cikin rarrashi kamar tanayi da k'aramin yaro"dariya yakamayi ya rungumeta k'yam ajikinsa yana fad'in ilove you my billy! Allah yadauwamar damu cikin farin ciki na har abada"itama shigewa jikinsa tayi tana murmushi tace" ilove you too! yad'ago kanta ya manna bakinsa cikin nata yana tsotsa tamkar zai cinye bakin"itama ta lumshe idanuwanta tana tayashi"ganin zai saki layi yasaka tayi saurin yanke abin"yad'auketa suna dariya suka nufi d'akin baccinsu....."agurguje ita dashi sukayi wanka suka shirya"ita k'ananun kaya shima haka"yakama hannun ta suka nufi dining area d'in suka fara break fast d'in anutse cikin farin ciki....gaba d'aya yah Abdul na lura da billy bata wani cin abincin sosai sai ruwan tea kawai taketa sha"yah Abdul kuwa sai loda masa abinci takeyi"can ya ajiye spoon d'in hannunsa yace"my billy wai meyasa sai tea kawai kike sha?"dama jiya da muna bacci naji jikinki da zafi"kasa mgn tayi aguje ta nufi wajen sink tafara kwara amai"da sauri yabiyota yarik'eta cikin damuwa yana tambayarta dama bata lafiya?"kasa mgn tayi tanata Aman"bayan ta gama yataimaka mata ta wanke bakinta"yakama hannun ta suka nufi bed room d'in su"Ahankali tace"yah Abdul karka damu zazzab'i ne nakeji sama sama"kabani magani kawai"ah ah my billy asibiti zamuje gsky"indai akan lafiya ne ba'a so Ayi wasa da ita ko?"yafad'a yana zaunar da ita kan bed yanufi gefen ward rope yabud'e"gogaggun kaya yafito mata dasu"riga da siket na atamfa"da mayafi colour d'in kayan"batayi musuba tasaka da taimakonsa"wanda mayafin bada son ranta ta yafa ba"sai dan bin umarninsa"yana rik'e da hannun ta suka fito yarufe k'ofar main parlour suka nufi parking lot suka shige mota"yana driving d'in billy na kwance ajikinsa"sai gudu yakeyi dan su iso asibitin da sauri"nidai yah Abdul karka kayar damu pls"to nadena my honey"sonake adubamin ke naji meke damunki?"batace komai ba tayi shiru"da haka suka iso asibitin"yana rik'e da hand bag nata"yasaka hannunsa agefen k'ugunta yarungumota ajikinsa suka wuce reception"sai kallonsu akeyi"dan ba k'aramin kyau sukayi ba"shi kuma yatamke fuska sbd ganin k'ananun nurses mata nata kai da komo suna kallon su"zaunar da billy yayi kan kujerun dake a nan reception"ta rik'e hannunsa tana
b'ata rai"murya can k'asa mai cike da nuna kulawa yace"sorry zanje nayi cuku cukun ganin likita ne"nidai Allah ban yarda kaje kabarni ba zan bika ne"my billy kefa bakya lafiya amma kike wata rigima?"ture hannunsa tayi tak'i mgn"yana murmushi yatayar da ita tsaye "sai turo d'an bakinta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login