Showing 75001 words to 77635 words out of 77635 words
aura yayi accident yarasu"anbinnesa amma k'asa tak'i karb'ansa! innalillahi wa inna ilaihir raju'un"wlh kuwa sau 10 ana canza masa kabari"sannan aka samu yazauna aciki"ita rayuwa ka shuka alkhairi shine yafi"ki rik'e mijinki bilkisu dan Allah"insha Allah Anty jidda muje karma yayita jira"cewar bilkisu tanayin gaba"suna fitowa dg cikin gidan"jidda ta zuba awara me yawa aleda bak'a ta bama bilkisu tanata mata godiya"tana kallo ta bud'e front sit ta shiga aka ja motar"taja ajiyar zuciya....kowa ta sallama ta kwashe komai ta koma cikin gidan"ta zauna tana bud'a ledar da bilkisu ta kamata"kayane kala 4"lace kala 2 atamfa kala2 duk masu kyau da tsada d'inkin dogayen riguna"wanda koda kayan sunga wanki be wuce sau 2 ba dan kamar sabbi suke"ga kayan shafa agefe ga kuma kud'i 20k cif"jidda ta girgiza kanta hawaye na wanke mata fuska"afili tace" duniya budurwa wawa! ada ina cewa" nice zan bama bilkisu kwancen kayana gashi itace ayau ta bani"wanda ayanzun kaf cikin kayana babu kamar wa'annan"yah Allah kasaka k'addarata ta tsaya iya haka"tafad'a tana d'aukar kud'in ta wuce d'aki dasu.....
bilkisu na shigowa motar ta zauna ta kalli yah Abdul tana fad'in sweet heart baka gaji da jiraba?"ah ah my billy"jikina yayi sanyi ne ina tuna yanayin rayuwa"ban mayi zaton kin jima sosai ba"gsky bilkisu rayuwa abin tsoro ce Allah yasa mudace"Ameen yah Allah"ni kaina wlh banji dad'in ganin Anty jidda haka ba"to amma sai hak'uri"dan Allah yaya Abdul kataimaka mata da jari mai tsoka ta dinga neman kud'i itama"in sha Allah idan mun dawo dg saudiyya za'a bata"yafad'a yana jan motar"bilkisu ta dinga masa godiya"yana murmushi yace"kefa Amarya ce yau"barama mu tsaya na siya miki kazar siyan baki"murmushi tasaki batace komaiba"dan itama harga Allah tana buk'atar mijin nata"ga kayan mata ummi ta d'irka mata gaba d'aya jikinta abuk'ace yake da yah Abdul"agefen hanya yayi parking yafita"bayan ya siyo kazar yadawo suka nufi gida yanata zolayarta da fad'in adaren yau za'a yiwa affan k'anwa ko k'ani"ita kuma tanata b'ata rai da wannan barkwancin suka iso gidan nasu"wanda meenah tun d'azun atare suka bar gidan da bilkisu sadda ta fita"yanzun su kadaine suci karonsu bbu babbaka.....awannan dare bilkisu taga surkulle kala kala awajen mijin nata"dan har kukan dad'i yah Abdul yamata....
*****************
Ayau bilkisu da Abdul da goggo cikin farin ciki suke"sbd isowar su gida nigeria"sun kammala aikin hajjinsu lafiya"suna fitowa dg jirgi"suka sami kabeer da meenah sunzo daukarsu"bilkisu ta had'e cikin tsadaddar jallabiya bak'a ta yane kanta da mayafin tana sab'e da affan d'an 5month"yyinda yah Abdul ke sanye da suit bak'ak'e yayi kyau masha Allah"goggo na gefensa cikin shigar atamfa super da hijab iya gwiwa ajikinta"tanata washe hak'ora hakorin makkanta guda biyu sunata bayyana"meenah ta rungume goggo tana ihun murna"goggo na murmushi tace"nidai yi a hankali auta"kin san k'afar nan har yanzun sai a hankali"fama nakeyi da ita idan ta motsamun"meenah ta cikata ta rungume bilkisu ta amshi baby affan"kabeer kuwa rungume juna da yah Abdul sukayi"kabeer d'in yayi wata uwar rama kamar wanda ya kwanta jinya"bayan sun gama murna"suka kwashe kayansu gaba d'aya suka shige mota"yah Abdul aransa yana mamakin yadda kabeer yayi rama"kai tsaye gidan goggo suka nufa"wanda angyara gidan sadda suna saudiyya"dan harda get yanzun"wanda yah Abdul ne yasaka Ayi aikin harda gidansu billy"su kuma shida bilkisu yafara gidana babban sabon gida Inda zasu koma"dan yanzun bayan aikinsa harda kasuwanci yakeyi.....sosai goggo da bilkisu keta santin gidan da aka gyara"kasancewar dama meenah saida tayi musu girki tun d'azun"komai ta ajiye musu aka zauna a parlourn goggo sukayiwa cikinsu k'at"sannan bilkisu ta wuce d'aki danyin sallar azahar sai su tafi gidan ummi ta ganota"yah Abdul yaja kabeer su tafi masjeed dg nan yaji miye damuwarsa?yyinda jama'a nata shigowa yiwa hjy goggo sannu da zuwa.....suna fitowa bakin get yah Abdul yace"wai kabeer meke damunka kayi rama haka??kansa ak'asa yace"wlh yaya Abdul aure nakeso"ina gudun kar shed'an yaci galaba akaina"tunda dai nasamu aikin gidan yafi rabi daya kammala"zan siyar da motata tunda inada mashin sainayi auren"bbu damuwa Ayi haka in sha Allah nan gaba kad'an zan canza maka mota"itama billy inaso zan siya mata"to muna saka ran wasu kud'ad'e nan gaba in sha Allah"Allah ya Ida nufi yaya Abdul"nagode sosai Allah yabarmun kai"yah Abdul na murmushi ya amsa da Ameen suna yin gaba......bayan bilkisu ta gama sallah tafara k'ok'arin canzawa affan kaya"dan komai na tsarabarsu da kayan sawarsu na motar kabeer sai zasu tafi gida zasu tafi dasu "bilkisu na d'akin tana shirya affan tana dariya sbd jin goggo nabama wasu labarin saudiyya"gaba d'aya bilkisu rayuwarsu ta baya kawai take tunawa....tana wannan murmushin yah Abdul yashigo d'akin"amaryata kina nan dama?"haba yah Abdul wane irin amaryakuma? kusan 3 yrs da aure"amaryace ke mana my billy! tunda kullum zam zam nake jinki"yafad'a yana k'ok'arin zama gefen bed d'in goggo"tana murmushi tace"pls mud'an lek'a gidan hafsat da gidan ummi"eh wlh dan hafsat batama jin dad'i laulayi takeyi haka yafad'amun"dan in bacin bata lafiya ai dayama zo"hakane kam Allah yabata lafiya"Ameen yah Allah"yafad'a yana amsar affan suka fito dg cikin d'akin"tafiya gida zakuyi?"cewar goggo"Eh amma gidan ummi zamu fara zuwa"eh hakan nada kyau kice ina gaisheta bilkisu"to zataji goggo"meenah babu rakkiya"taff kunya nakeji"to shikenan zan sanarwa ummi kunyarta kikeji"duk sukayi dariya gaba d'aya"kasancewar tsaraban da akayiwa ummi daban take"suma ta gidan musa daban take"hakan yasa suka fidda su agefe suka tafi da motar yah Abdul dake ajiye agidan...gidan musa suka fara zuwa kafin suje gidan ummi"wanda bilkisu har kukan farin ciki tayi sbd yadda taga mijinta ya gyare gidansu abin shar sai son barka"anan wajen ummi billy kejin yah Abdul yabama yah Anas 5Ok yakaiwa jidda taja jari"sosai sukayi murna dan jiddan abin tausayi ce yanzun....su billy sai marece suka koma gidansu"acanma mutane nata zuwa yimusu sannu da zuwa.....
Ayau da dare misalin k'arfe 11:5 pm"bilkisu na bacci ajikin yah Abdul"shima baccin yakeyi"wayarsa sai ringing takeyi tana verbration"yah Abdul yabud'e idonsa cike da bacci yaduba wayar"tsaki yaja iya labb'ansa sbd ganin wata yarinya ce mai suna *suhaima* awajen aikinsu yasanta kuma budurwace"daya san zata damesa da yawan kira daba zai bata n nashiba"shima yabata number ne sbd wasu da lilai akan aikinsu"janye bilkisu yayi dg jikinsa ya sauka dg kan bed d'in yafita yana rik'e da wayar"bilkisu ta bud'e idanuwanta gabanta nata fad'uwa ta mik'e tsaye itama ta bishi"yah Abdul kuwa a gudan bed room d'in yashiga yafara k'ok'arin kiran suhaima"bugu 2 ta d'aga wayar tana wani kashe murya....yah Abdul yayi saurin dakatar da ita gun cewa"gsky banji dad'in irin wannan kiran da kika mun ba"kusan 3 miss call kika mun da dare haka"me kikeso matata ta zata?"haba Abdul dan nadamu dakai zaka gayamun mgn?"look suhaima"yanzun lokacin iyalinane banida time d'in kowa"koma miye ki dena kirana ki bari mu had'u wajen aiki mana sai muyi mgn"yana fad'in hakan yakashe wayar"yana juyowa suka had'a ido da bilkisu dake tsaye bakin k'ofar d'akin tana jifarta da wani irin kallo na tuhuma"gabansa yabuga! sbd yadda yaga fuskarta"yana k'ok'arin mgn ta juya tabar d'akin da sauri"tana shiga bed room d'in su ta rufe k'ofar da key"tafad'a samqn bed tana fashewa da wani irin kuka"bbu irin bugun k'ofar da yah Abdul beyiba amma ta masa banza"yafi awa 1 yana kiran sunanta da mata magiyar ta bud'e yamata bayani amma ta masa banza"azuciye yakira suhaima yaci mata mutunci yagoge number nata bayan yayi blocking....sannan yakoma waccan d'akin ya kwanta zuciyarsa bbu dad'i"yasan halin bilkisu idan zafin kishinta yamotsa bata iya ba......
Bilkisu kuwa shed'an yaci galabar hura wutar kishi aranta"tana tuna yana fad'in koma miye tadena kiransa idan yaje office sayi mgn"dama idan yaje office mata yake kulawa kenan?"ta tambayi kanta zuciyarta acunkushe"tasha kuka sosai har kanta yafara ciwo sai gab da asuba tasamu bacci b'arawo yasaceta"wajen k'arfe 7:am kukan affan ne yatasheta dg bacci"tayi saurin bud'e idanuwanta tana hamma had'e da salati"ta dubi affan d'in daketa rarume rarume"wani irin mugun haushi taji yabata sbd laifin babansa"balle yadda taga suna kama"azuciye ta tashi ta d'akko affan d'in dg saman bed d'in ta bud'e k'ofar bed room d'in ta fito parlourn dashi a hannunta"yah Abdul na zaune da jallabiya ajikinsa idanuwansa jajir sbd damuwa da rashin bacci"fuskarta ad'aure batayi mgn ba yanadai ta kallonta"aza affan d'in tayi kan kujera ta juya zata tafi"bilkisu ina zakije kuma yana kuka?"idan laifina ne yashafesa ki mana afuwa kiji uzurina kar shed'an yaci galabar shiga.....bana son jin komai dg bakin ka"cewar billy ta juyo a harzuk'e tana balla masa harara"kafin tace"dama amanata kake ci idan kaje office d'in ko?"to yanzunma kaje wajenta mana"d'a kuma gashi nan ka rik'e abinka" kai dashi duk na tsaneku....tana fad'in hakan tayi gaba"yah Abdul tagumi yayi yanata kallonta harta b'acewa ganinsa"ransa yab'aci sosai"saidai yadda yakeson bilkisu da irin karamcinta agaresa bazai iya wulak'antata ba"balle yasan duk akan sonshi tayi haka"d'aukar affan d'in yayi yaje wancen bed room d'in dashi yacire masa parmpers yabashi ruwa"shi kuma yanata kuka harda shashsheka da ajiyar zuciya"gaba d'aya yaron yabashi tausayi yama rasa yazaiyi dashi"ga anata kiransa office"amma bazai iya tafiyaba billy tama zargi ko wajen yarinyar yaje"wata iriyar muguwar tsanar suhaima yaji aransa"sbd itace silar komai"asaman kafad'a yasaka affan"yana rirriga"saiga fitsari yamasa"yazuba ruwa gashi bbu kayan dazai canza masa da parmpers duk suna a wancan d'akin da bilkisu ta rufe..."parlourn yafito yana rirrigarsa yakira musa ta waya yasanar masa abinda yafaru"musa yace"gashinan zuwa gidan"yah Abdul na gama wayar yanufi d'akin yasaka wani key sai gashi yabud'e"bilkisu na zaune kan bed tana kuka da hijab d'in datayi sallah ajikinta"tana ganinsa ta wuce toilet da sauri ta banko k'ofar"girgiza kansa kawai yayi yanufi Inda kayan yaron suke da parmpers yad'auka ya fito dg cikin d'akin"da k'yar yasamu ya shirya yaron dan kuka kawai yakeyi yanata rarume rarume....kamar yayiwa yaron kuka"sai rirrigarsa yakeyi"yasamu baccin wahala yad'auki yaron"yasaki ajiyar zuciya"gaba d'aya damuwarsa"bilkisu yasamu ta hak'ura da wannan fushin datakeyi dashi"yana ahaka musa yayi knocking"yaje ya bud'e masa k'ofar"musabuha sukayi"musa cike da tsokana yace"abokina anata baka punishment ko?"mai hak'uri bai iya fushiba"kusan 3 yrs kenan da aurenku amma ban tab'a jin kunyi fad'a ba"to an fad'a maka yanzun laifinane?"kawai takasa fahimtane"gashi shima affan abin yashafesa yanata kukan yunwa harma yayi bacci"yanzun jekamun mgn da ita"Abdul beyi mgn ba yaje k'ofar d'akin yasaka key amma yak'i bud'uwa alamar tabar key ajiki"knocking yakamayi yana fad'in kizo ki bud'e musa keson mgn dake"nan ma banza ta masa"yafi 10 minit yana mgn"ransa yakai k'arshe gun b'aci"yabaro wajen yana fad'in musa kaje kawai"tayi duk abinda ta gadama dan taga ina lallab'ata"ko agabanta zan iya mgn da mace meta isa tamun??"calm down abokina idan rai yab'aci hankali bazai gusheba kamata uzuri ta huce"matsalar kawai da aka saka affan a case d'in"amma bara naje na amso priso abashi idan yatashi"yah Abdul beyi mgn ba ya zauna kawai yana furzan da zazzafan huci dg bakinsa.....yana anan zaune musa yadawo yakamasa"atare suka had'a aka tashi affan aka bashi"yasha amma ba sosai ba"gashi yak'i dena kukan"sai rirrigarsa Abdul keyi har yasamu yayi shiru"duk yayi wuri wuri dashi"jallabiyan jikinsa duk ta b'aci"Ahankali musa yace"zanje anjima saina dawo nasan lokacin ta huce"karka dawo musa kar Allah yasa ta huce tayita fushin nata mana"musa bece komaiba yafita"yana fita kai tsaye gidansu bilkisu yaje"anutse yayiwa ummi bayanin komai"yamata rantsuwar Inda suhaima budurwar Abdul ce bazaima shiga case d'in ba"ummi ta dinga fad'a tana fad'in koma budurwarsa ce ta isa ta hanashi yayi inyaga dama"musa dai na bada hak'uri yatafi"ummi ta kira Abba tasanar masa zataje gidan bilkisu sun sami matsala da mijinta"bayan yabata izinin zuwa ta nufo gidan bilkisu....
Bayan tafiyar musa yah Abdul yabar parlourn yakoma wancan d'akin ya kwantar da affan daketa bacci"yayi tagumi yanata tunanin bilkisu...."bilkisu kuwa dataji ta dena jin motsin kowa, saita fito ta nufi kitchen ta had'o tea sbd yunwar dake damunta"fitowa tayi dg kitchen ta zauna parlourn tanata cin magani"ahaka yah Abdul yasameta zaune tana shan tea"tausayin kansa dana d'an sa yaji"su basuci komai ba"amma ita datake fushin tazo tanashan tea"bilkisu! yakirata cikin tattausan muryanshi yana tsareta da ido"ta turo baki tana d'aure fuska tak'i mgn"irin wannan rayuwar kikaga yadace muyi?"kin wofintar dani da yarona"bayan kinsan muna buk'atar kulawar ki"ina yardar dake tsakaninmu dake billy?"wlh tallahi bilkisu bbu soyayyar wata mace araina saike! suhaima awajen aikinmu na santa"kuma na zageta tun jiya na goge number nata danayi blocking"gashima ki duba ki gani"yafad'a yana nufar gabanta da wayar ahannunsa"ummi da taji duk kalaman yah Abdul ta shigo parlourn bbu ko sallama ranta ab'ace tana fad'in dan ubanki irin tarbiyyar dana baki kenan?"tafad'a tana nufo bilkisu da niyar ta deketa"aikuwa bilkisu tasaki k'ara ta mak'alk'ale yah Abdul dake tsaye agaban ta"dan Allah ummi kiyi hak'uri"wanene yaje yasanar miki?" ai mun shirya ma"cewar yah Abdul"musa ne yasanarmun Abdul"meyasa baka mammari marar kunyar banza ba?zaki cikasa ki duk'a ki bashi hak'uri kosai na takaki?"ke yanzun sbd kina sakara sbd wata zaki sab'a da mijinki"da sauri bilkisu ta cika yah Abdul ta duk'a tana bashi hak'uri"shima duk'awa agabanta yayi yana fad'in komai ya wuce awajensa"ummi na hararar ta tace"wlh muddin nakoma jin makamancin haka zaki gane kuranki"tana fad'in hakan ta juya tayi ficewarta"yah Abdul yayi saurin janyo bilkisu jikinsa ya rungumeta yana fad'in kinga my billy zaki saka ummi ta dokarmun ke ko?"shiru tayi tak'i mgn"ko baki hak'ura ba?"nafa hak'ura ai"ta fad'a tana turo baki"yyi murmushi yana kissin d'in lips nasa yace"to nima muje ciki kafin affan yatashi abani hak'uri"yafad'a yana d'aukarta yaje yarufe k'ofar suka wuce d'akin baccinsu....
*bayan shekara ukku*
tsaye bilkisu da Abdul suke awani katafaren parlou na alfarma"bilkisu na murmushi tace"sweet heart irin wannan suprise haka?"to tsohon gidan wa za'a barmawa?"na abokina ne"amma sai ammasa gyara"idan sun dawo saudiyya dashi da baffa Aminu dasu ummi saisu koma aciji"hakane yah Abdul kaida musa ba'a shiga tsakaninku"Allah yasa amincinku har tsufa"Ameen my billy"tana k'ok'arin mgn meenah da affan da wata baby girl me kama da bilkisu na hannunta suka shigo cikin parlourn"oh mamaa(sahura)ashe tana wajenki meenah?"eh wajen goggo na amsota danace nan zamuzo muga sabon gida"sai tace azo harda affan d'in dayaje week end"cewar meenah tana mik'awa billy mamaa"kafin ta gaishe da yah Abdul da masa fatan alkhairi na sabon gida"ya amsa cike da kulawa yana tambayarta babynta dake bayanta yana bacci"dan Anyi bikinsu da Ana's last 2yrs"itama jidda tayi aure shekara 1 data wuce"ta auri wani shima k'afarsa yana d'an jefata"matarsa ta rasu wajen haihuwa"da yaransa biyu"kuma bbu laifi tana d'an hutawa"dan yanada abin hannunsa"saidai beson laifin yaran"hak'uri kawai jidda keyi"ayanzun haka laulayi takeyi"ghalima yadawo dg sudan yayi aure" kabeer ma yayi aure har matar ta haihu"goggo kuma an sake girma amma jiki yau lafiya gobe sai hak'uri.....magajiya kuwa na gidanta tana y'ar sana'arta.....meenah ta zauna a parlourn da yaran"yah Abdul yaja bilkisu dan taga ko ina na gidan"sbd dg su sai kayan sawarsu suka dawo"komai sabo aka canza"master bedroom d'in su suka fara nufa wanda ke upstairs"furnitures ne na y'an dubai masu masifar kyau da tsada"yah Abdul ya finciki billy suka fad'a samqn bed d'in yana fad'in Alhamdllh!
nima dai mom fareesa Alhamdllh nace🙏🏻🙏🏻 tamat bi hamdilillahi tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabammu annabi muhammad S A W
duka duka anan nakawo k'arshen wannan littafi mai taken WATAH UWA! kuskuren danayi aciki yah Allah kayafemun dani da makaranta baki d'aya"yah Allah yabamu ladar abinda ke daidai yasa mu amfana da abubuwan alkhairi dake cikin wannan book.....
Har gobe ina alfahari daku masoyana na gsky makaranta littattafaina"Allah yasaka muku da alkhairi yabaku zaman lafiya da mazajenku😍😘love you all guys🥰🥰 Allah yabar tare....sai mun had'e a sabon book d'ina kafin zuwan azumi in sha Allah
Ina mik'a godiya da jinjina ga fans d'ina mutanan sokoto😍
Dg k'arshe na sadaukar da wannan littafin ga wacce keda suna Aysha💃💃
kamar yadda kuka sani wannan book d'in nakudine idan kin karanta baki biyaba kema kinsan me Kika karanta"duk wacce ta karanta bata biyaba nabarki da Allah bazan tab'a yafewa ba.....