Showing 21001 words to 24000 words out of 114964 words

Chapter 8 - MIJIN HANEEFA Complete Hausa Novel

15 Oct 2024

13134

feel humility. Pls dad I beg of you let's ends wnn zaman da muke 'din, muci gaba da zaman mu as daughter and father. Ka kyaleni naje nayi aurena. Ni banma san dalilin da yasa nake biyeka ba. Kwalla ya ciko idonta nan kuka ya kufce mata tana fa'din haba dad this is not fair, ko dan kaga mum dina ta mutu shine ka maye gurbinta dani, am pretty sure if mum was still alive bazaka yi haka ba...... kuka sosai ya kufce mata.
"Dad kuwa da tuni 'ya'yan cikinsa sun hau ka'dawa tsoronsa 'daya kardai asirin da yayiwa Latifa ya karye ne, toh idan kuwa hakane da sakel. Komawa Nigeria ta kamasa knn. Share mata hawayen ya shiga yi yana fa'din kar ki damu daughter zan barki kiyi aurenki kinji zanyi magana da Aliyu da zaran mun koma Nigeria I promise you that.
"'Dago ido tayi tana kallonsa tana murmishi, girgiza mata kai yayi alamun ta daina kuka, rungumesa ta sake yi tana jin farin ciki. Dad kuwa idonsa kyam yana tunanin lallai akwai babban aiki a gabansa. Knockn da akayi ne yasa shi tashi ya nufi parlor yace maza ta tashi ta shirya zaikaita shopping tayi tsaraba bari ya duba guests dinsa before she dress up. Da murnan ta tashi dan dama ta gaji da zaman _Las Vegas_.

"Naval chief of staff ya sauko kasa wajen ba'kinsa, wasu turawa ne guda biyu, da sauri suka mi'ke suka shiga sara masa.
"Have a seat please. Ya fadi yana nuna masu kujeru. Nan da nan ma'aikata suka shiga tambayansu me za'a kawo masu, gaba daya suka ce wine. Hakan kuwa akayi.
"Cikin harshen turanci suka shiga tattauna da su James gameda har'kan sayan 'danyan man petur da suke.

"Latifa ta gama shirinta ta nufo downstairs, daga staircase ta tsaya tana jiyo tattaunawan mahaifinta da wa'dann jajayen fatan. Gabanta ne yayi mugun fa'din jin irin ku'da'den da suke ambata. "Take ta soma zargin dad dinta. Tabbas zargin da Aliyu ke masa akwai 'kamshin gaskiya idan ba haka me zaiyi da ma'kudan ku'di da suka kai 200000 million dollars, a ina ya samesu. Da wann tunanin ta sauko 'kasa dad yayi introducing masu James suka gaisa. Latifa ta dubi dad tace I'l be outside. Kai yayi nodding kafin yace okay princess.
"Kwana biyu suka 'kara a America kafin suka dawo Nigeria.

*Nigeria*
_Lagos Apapa_
Tinkan island (Maritime)

_2:53pm_
"Hanifa na zaune a dinning tana cin lunch taji nkcn a kofa, a zuciyanta tace tooh yau kuma knckn yayi niyyan yi knn, tab ai kuwa sede ya bushe a wajen dan wllhi bazan bu'de ba, ta mike rike da plate din abincinta ta nufi dki. Zama taayi taci gaba da cin abincinta. Can dai taji knckn ya'ki 'karewa. Gajeren tsaki tayi ta tashi ta nufi 'kofan.
"Saida tayi danasanin bu'dewa ganin wanda ke tsaye jikin 'kofan, Latifa kiwa gabanta ne yayi mugun fa'duwa ganin yarinyar da Aliyu yace mata 'yar aiki ce tayi masifan kyau, wnn ko a villa ba'a kirata 'yar aiki ba.
"Hanifa ta ta'be baki tana binta da kallo ganin ta mata 'kuri tana kallonta, data ga dai kallon bana 'kare ba tace "malama idan zaki shiga ki shiga idan bazaki shiga ba kuma ki sanar dani.
"Sai snn Latifa ta dawo daga duniyan tunanin data tafi ta ra'ba ta gefen Hanifa ta shige parlorn.
"Zama tayi bisa sofa ta dubi Hanifa tace serve me lunch.
"Hehe he su lunch manya, Hanifa ta fadi sanda take bin Latifa da kallo.
"Da mugun mamaki Latifa ke bin Hanifa da kallo tace "ke ma ni kike fa'dan haka.
"Eh an fa'da 'din waye zaiyi serving mistress, prostitute Allah ya sawa'ke. Ki jira karuwan naki yazonya zuba maki.... tan gam fa'din haka ta juya zata shige 'daki.
"Fizgota Latifa tayi tana huci take fa'din " lallai ma yarinya kin samu waje ni kike kira prostitute, koda shike ba laifinki bane laifin Aliyu ne, ni bam yarda dake bama anya baki seducing dinsa banda bana nan.
"Hanifa ta shiga kiciniyan kwace hannumta tana fadin " let gof me, let me go, me zanyi da mazinaci, kin dauka kowa mazinaci ne irinku da har kike tunanin zan yi seducing dinsa Allah ya sawake mun..... Latifa da ranta ya gama jagulewa batasan sanda ta kifa wa Hanifa mari ba. Hanifa ta dafe kuncinta tace "kut kika mare ni... eh an mareki din ko akwai abunda zakiyi.... Latifa bata gama rufe baki ba taji tass Hanifa ta dauketa da mari masu kyau har biyu. Snn ta ta wawushi dogon takalmin latifa ta zube 'kasa saida rabin attach din kanta ya tuge.
"Hanifa kuwa data ga haka wnn me 'kiran samudawan tasan tsaf zatq mata duka, a guje ta fice daga gidan ta nufi waje.

"Aisar da Haidar dawowansu knn suna tsaye a parking lot suna tattauna maganan tafiyan da zasuyi soon kawai sai ganin Hanifa sukayi ta fito a guje. Cikin ru'dani dukansu biyu sukayi kanta bata ankara ba tayi tuntu'be zata zube 'kasa Haidar yayi saurin tarota ta fa'do jikinsa shi kuma ya fa'din 'kasa gaba daya ya 'bata uniform 'dinsa. Aisar ya 'karaso yana fa'din, "lafia beautiful meke faruwa, ya mika hannu zai 'dagota Haidar yayi saurin mi'kar da ita tsaye yana mata mugun kallo na me ya fito dake.
"Daidai nan Latifa ta 'karaso tana huci ai kuwa da sauri Hanifa ta shige bayan Haidar ha'dida 'kan'kamesa. Kallon Latifa suke gaba daya da mamaki. Dariya sosai ta basu ganin yanda gashinta ya tuje takalmi daya a hannu daya tana dingisawa da kyar, Haidar ne yayi 'kakarin dakewa, Aisar kam sosai yaketa dariya abunshi wanda hakan ya da'da 'kular da Latifa.
"Wllhi yau saikin fa'da mun wacece karuwa sai kinsan kin mare ni shegiya er aikin banza..... enough! Haidar ya daka mata tsawa me ya ha'daki da ita. Kuka Hanifa ta soma tana fa'din nide yaHaidar wllhi ka maidani wajen mamy tunda wnn budurwar taka duka na take wai dan kawai banji tana knckn ba banzo na bude mata kofa da wuri ba shine tayita duka na saida na gudo waje.... baki sake Latifa ta tsaya tana bin Hanifa d kallo, cikin "kunan rai take fa'din lallae ma yarinyar nan marina fa tayi ta kadani a 'kasa..... shut up! Haidar ya daka mata tsawa. Latifa tabisa da kallo tana tunanin ko ba'a fada ba wnn kanwar Aliyu ce dan kuwa gashima taji tana fadin yaHaidar, toh ko meyasa yace mata 'yar aiki ne da oho, kai itama dai she was stupid da ta yarda 'yar aiki ne.
"Aisar kuwa me zaiyi banda dariya dama yana ji da haushin Latifa duk neman matansa bata kulasa sai Haidar dukda iyayensu aminan juna ne. Latifa ta da'da kulewa.
" Haidar harara ya watsa wa Latifa kafin yace kema rashin jin magann ki Hanifa oya wuce ki shige gida... Da sauri ta shige abinta tasan taci darajan Aisar ne da yau ta gaywa aya za'ki...
"Aisar na dariya ya juya ya nufi gidan shi yan fa'din toh navy sai kajini inaga yau zanje wajen su mum dina later, koma yaya ne dai I'll phone up you. Ya shige yana watsawa Latifa kallon 'keta.

"Haidar da ransa ya gama 'baci ko kallon Latifa beyi ba ya shige gida abinsa, babban abunda yafi basa haushi shine Aisar ya kalle masa Hanifa babu mayafi.... Latifa tabi bayansa tana kiransa....

👸🏻Queen Samy😍💄💋......
[5/9, 6:18 AM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
27

"Aliyu pls mana let me explain I beg u..... a hasale ya juyo yana mata mugun kallo kafin yace "don't provoke me am warning you, ki wuce ki bar mun gida tun kan ranki ya 'baci...
"Pls Aliyu I just want you to unders....... "are deaf! I said I don't need your explanation, leeeeeave now. Ya fadi yana daka mata tsawa.
"'Kwalla tab idanunta ta juya tana tafiya. Gajeren tsaki yayi kafin yayi banging door din da 'karfin gaske.

"Hanifa kam tana shiga ta kulle kanta a 'daki, kirjinta sai dukan tara tara yake musamman da taji 'karan rufe 'kofan yaHaidar.
"Da 'karfin gaske ya bu'de 'kofan 'dakin, a razane ta 'dago tana dubansa baki na 'bari ta soma basa ha'kuri..... " would you shut your trap! Ya daka mata tsawa. Zaki gaya mun uban waye yace ki mareta ko sai na karerayaki a wajenn.
"YaHaidar wllhi ita ta soma marina kuma ni ban yi niyyan ramawa ba kawai hanuna ne naji ya mareta...
"Kalamanta yaso bawa Haidar dariya, lalle ma yarinyar nan wato shi zata raina wa hankali. Ya da'da murtu'ke fuska kafin ya 'karaso kusa da ita yace" kina jina, ta gy'da kai da sauri kafin yaci gaba "idan kina son zaman lafiyan ki a gidan nan you should behave your self, how dear you har zaki mari macen da nake so nake son aura, ko dan kinga an li'ka mu ke shine kike zaton zan soki, toh bari kiji never. I will never ever fall for you, gashi kinsa princess 'dita tayi fushi ta tafi despite the fact I missed her awfully. Ya matso kusa da ita ta shiga matsawa da sauri..... hannu yasa ya cafkota ya matseta cikin jikinsa a kunnenta yake ra'da mata. Latifa taimakon ki take she's giving me what you cannot give me. She takes your responsibilities, now tell me kina son 'daukan gaba 'daya 'dawainiya ta...... zaro ido tayi waje tana dubansa. Mayaudarin murmushi ya sakar mata kafin yace " Afff ashe ma 'kwaila aka aura mun am pretty sure koda zan daura maki dawainiyata you can't handle have of it, inspired of maitan mazan dake azalzalanki, too bad for you haka zaki 'karace jarabar ki babu namijin da zai kusance ki, bani Aliyu ba kuma auren mu babu saki balle kiyi tunanin zan sake ki samu wani. Haka zan ta gana maki azaba har 'karshen rayuwarki, ya 'dan yatsina fuska kafin yace perhaps idan kika 'kara girma na iya taimaka maki na cire maki maitanki. Daga haka ya mi'ke ya barta nan zuciyanta kama ya fashe dan takaici.... saida yakai 'kofa ba tareda ya juyo ba yace ki shirya gobe zankai ki ki bata ha'kuri.... daga haka ya fice abunsa zuciyansa tass ya 'kuntata wa Hanifa.

"Kwanciya tayi gijif kan gadon ta shiga rera kukan takaici, kukan da babu wanda yasan tana yi balle ya lallasheta. Haka taci kukanta har barcii yayinawon gaba da ita, tsanan Haidar kuwa ya da'da tsamari cikin zuciyanta. Da addu'an Allah ya kawo mata 'karshen zaman gidan yaHaidar tayi bacci....
"Ba ita ta farka ba sai wajejen biyar, da sauri ta mike ta nufi bayi ta 'dauro alwala tazo ta tada sallan la'asar.

*******************************************
" Tun daga 'kofan gidn yake tunanin shiga tunaninsa 'daya kardai daddynsa na gida dan kuwa gwara ya koma da ya ha'du dashi. Cikin dakewa ya mur'da handle din kofan ya shiga. Momy ya hango zaune bisa sofa cikin makeken parlon tana kallon wani animation, murmushi yayi yace a ransa momy dai bazata daina son kallon cartoons ba kama wata yarinya, wata zuciyan tace kil dan babu yara a gidan ne. Motsin da ta jiyo yasata juyawa babu shiri.... baki sake ta mike da sauri ta 'karasa ta rungumesa tana fa'din son, Aisar my son, I missd you so badly son.... hugging dinta yayi very tied kafin yace momy I miss you too mom, zama sukayi kan sofa hannumsu na ri'ke dana juna ya gaisheta kafin yace "I hope daddy baya nan...... shiru tayi ta kasa basa amsa ganin mijinta tsaye saman stairs yana kallonsu fuska atamke.... ganin ta tsaida idonta tana kallon stirs yasa daga ido sama sukayi ido hu'du da sauri ya mi'ke da niyyan juyawa, ri'kosa mom tayi tace no son dan Allah kar ka tafi Aisar.
"Daga yanda daddy ke tsaye yace "let him go, girgiza kai mom tayi tace no Hashim ka barni naji 'dumin 'dana.
"Dady ya 'karaso 'kasa kafin yace me zakiyi da 'danda yayi abandoning iyayensa me zakiyi da 'danda baya fatan samun farin cikin iyayensa ki fada mun hannatu... kuka kawai mom keyi ta kasa cewa komai....
"Dady yaci gaba da fa'din Aisar ba 'dana bane bani da 'da na goge shi tuntuni, now get the hell out of my house...
"Mom ta rikesa tana kuka tace wllhi bazai fita ba saidai mu fita tare... cikin hasa NNPC chairman Hashim Husain yace wa matarsa Hannatuuu ni kike fadawa haka, ya karaso zai kai mata mari sai ji yayai an ri'ke hannunsa....
"To his greatest surprised Aisar ya gani ri'ke da hannunsa ran maza ya 'baci abunka da soja. Cikin 'kunan rai Aisar yake fa'din " duk abunda zakayi kayi dani dan na'ki amincewa wa wani b'katarka na zaluntan al'umma but the moment you intend to hurt my mother I'll make you regret. And zan fita daga Dammn house dinka, snn kar kace banyi warning dinka ba dont mess with my mom, am just warning you. Duk abunda ya sameta you'll pay the price. Mark my words. Daga haka Aisar yayi jifa da hannun mahaifinsa ya dubi mom dinsa yace " we'll keep in touch mother, ya riko hannunta yayi kissing kafin yace I love you ya fice... mom tabi bayansa tana kiransa innaaa ya fice......

👸🏻Queen Samy😍💄💋.......
[5/9, 6:18 AM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
28

"Da 'karfin gaske ya fizge motan shi ya fice daga layin, mom tana jin 'karan motan kaman zai tashu sama, ta juyo da dubanta ga mijinta dake tsaye har yanzu cikin tsan tsan shock yake he couldn't believe it, his very own son wai yake fa'da masa magana son ransa har yana kafa masa warning.
"Cikin 'kunan rai mom take dubansa kafin tace" wllhi duk abunda ya sami 'dana bazan yafe maka ba, daga haka ta wuce sama tana sharen hawaye.
"Murmushin takaici dady yayi yace a fili "zan saita ka kan hanya Aisar, ba kana ganin kai soldier ba Allah yasa bakin bindiga ne kai amma sai na saita ka. Daga haka dady ya fice gaba daya daga cikin gidan ya nufi garden.

"Tunda Aisar ya fita yake gudu da mota kaman zai tashi sama, yana isowa gida 'daki ya shiga ya kwanta rub da ciki yana tunanin wnn mummunan hali irin na mahaifinsa, quite alright yasani he's a spoiled child, amma ko ka'dan bazai iya zaluntan al'umma ba, beside hakkinsa ne ya tsare al'umma da dukiyansu, baiga abunda zaisa shi on earth yaci dukiyan wani ba this is the last thing da zai iya yi a rayuwarsa. ya sani yana shan giya which is haramun ne yana neman mata duka manyan laifuka ne amma ko ka'dan basu kai kaci hakkin wani ba, su tsakaninka da Allahn ka ne ko yaushe kayi tsarkakken tuba Allah zai yafe maka ,hakkin wani kuwa sai ka neme mutumin ya gafarta maka, idan kuwa hakane ta ina zaka fara samun 'dunbin jama'an dake 'kasann kace su yafe maka. Dadyn shi na cikin bala'i nason dukiya da duniya.
"Da wnn tunani ya mike ya nufi bar dinsu dake cikin barrack din, zama yayi gaban bar yace a hada masa double whisky...... haka Aisar yayita kwankwadn giyan nan kaman babu gobe. Har dare ta soma ja yana nan yana kwankwadn giya.

"Haidar ya dawo daga sallan isha knn yace kai bari ya ta'bo mutuminsa dannyaji shi shiru, waya ya ciro ya shiga neman layin Aisar, da kyar cikin tsantsan maye Aaisar ya iya 'daga wayan....
"Cikin yanayin maye da kuka yake fadin" Cappptaiin I can't take it anymore, I don't want to live annny moooore...... "cikin rashin gane kalaman Aisar Haidar yace "Aisar are alright, what's wrong with you, where are you now?...
"Cikin yanayin maye Aisar yake fa'din " don't mind me friend am in the hell right now..... a zabure Haidar ya mike ya 'dauki car keys yana tambayan Aisar yana inane. Aisar yace pls don't trouble your self Haidar I already told I don't wanna live anymore. "Enough Aisar tsawan da Haidar ya daka masa knn wanda yasa sa yin shiru... Haidar yace now tell where you are, I'll be there right the way.
"Hehehe okay juuust because yoou insisted, I'm at the bar fresshinng uuup.
"Cikin sauri Haidar yayi hanging up ya fice daga gidan ya dauki mota ya wuce bar dinsu....

"Hanifa kam tana jin fitansa amma ko ajikinta dan wani azabebben ciwon mara ne ke damunta, gaba daya kwanciya tayi tana mur'kusoso a wajen, kuka take tana kiran mamynta jefijefi....

"Ganin tulin kwalaben whisky da Aisar ya 'karar yasa gaban Haidar mugun fa'duwa, toh meke damun Aisar yaga dai 'dazu suka rabu lafia lafia... ya 'karasa ya ri'kosa suka nufo waje, waya yayi wa driver dinsa yazo ya maida masa motansa shi kuma suka shiga na Aisar ya nufi gida dashi sai sun batu yake masa...
"Mazauni ya masa a parlor ya kawo gkass of cup na ruwa ya bashi, girgiza kai Aisar yayi ya soma fadin "meyasa ka dawo dani gida Aliyu na fada maka ka barni na mutu... I just couldn't believe it my very own father throw me out of his house, he threw me out

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login