Showing 9001 words to 12000 words out of 114964 words

Chapter 4 - MIJIN HANEEFA Complete Hausa Novel

15 Oct 2024

13135

Abba, kaman bazai amsa ba sai kuma ya amsa masa murya a ciki.
"Haidar inason ganinka gobe goben nan duk abinda kake ka bari kazo. Abba ya fadi.
"Na'am Abba gobe kuma Abba em... em...... ya soma kame kame gamida ture Latifa dake kwance jikinsa.
"Ya isa ba shawarinka nake nema ba umarni nake baka a matsayina na mahaifinka. Idan kaga kana iya zuwa fine.... daga haka Abba bai kuma sauraren Haidar ba yayi hanging up.

"Tashin hankali gobaran gemu, gaba daya Haidar yama rasa wanne zaiyi. Latifa ta matso gamida kwanciya cikin jikinsa tace "what's going on dear, who just called you?...
"Mikewa yayi ya nufi wardrobe ya shiga fito da kaya ba tare da yace da ita komai ba, ta mike ta tsare shi da ido tace Aliyu tambayarka nake ina kuma zaka.
"Tsawa ya daka mata "Shut up, Shut the hell up!.. ke har kin isa ki tambaye ni ina zani how dear you, okay wato don baki room shine bari ki rainani ko.
"Nan da nan Latifa ta marairaice ta soma bashi hakuri... am sorry, I dont mean to upset you, am just asking ne because I do care about you that's all....
"A fusace yace hold your sorry with you, and get the hell out of my house.
"Mikewa Latifa tayi ta nufosa tana fadin haba Aliyu me yayi zaf..... "I Said Out.... ya daka mata tsawa gamida nuna mata 'kofa... jiki a sanyaye ta dauki jakarta ta fice...
"Hissing yayi gamida banging door din da karfi....
"Washi gari flight din 'karfe 11:00am yabi zuwa jihar ta dabo babban birni....

*Kano*
"Abba yayi shiru yna kallon Haidar da gaba 'daya ya susuce,.... muryan mamy ta katse shirun, "na fa'da maka idan kabi na yaron nan to sai a shekara yana cewa ka 'kara masa lokaci, Zakiya diyar hajiya Larai kawata kawai zaka aura masa tunda yarinyace niitsetsiya mai hankali.... A razane Haidar ya dago yana duban mamy...
"Mamy pls don't do this to me, I beg of you mamy I promise zan kawo matan in a couple of days pls mamy, gaba daya ya marairaice yana magiya...
"Rufewa mutane baki dalla waye zaka mayar mutanen banza tun yaushe ake binka dan ka raina mutane kullum kace a sake maka lokaci cewan mamy cikin hasala...
"Abba na tsananin son yaransa dan haka yace kyaleshi Mariya na bashi zuwa gobe ko naji batu me da'di ko na masa yanda kika ce... tashi kaje.
"A sanyaye ya mike ya nufi kofa gaba daya jikinsa babu kuzari...

"Sashensa ya nufa amma gaba daya ji yake baijin dadin kwanciyan da yayi ya dauki car key dinsa ya nufi gidansu Saif....

"Sai na tsaye field din gidansu yana buga Snooker Haidar ya iso, Saif ya karasa ya tarbesa yana masa zolayan da suka saba "a a kaga mazaje sojan Sea saukan yaushe... Haidar ya mika masa hannu sukayi handshake kana yace saukan yau din nan, gaisawa suka danyi kana ya karbi cue din hannun Saif yana zungurin ball din dashi... Saif ya tsare Haidar da ido gaba daya gani yayi bashida walwala, "mutumina lafia kuwa Saif ya tambaya.
"Lafiya mana me ka gani
"You don't seem well, meke faruwa.
"Haidar ya sauke ajiyan zuciya kana yace "Friend I don't know how to explain but am having a hard time.
"Pls talk to me Haidar maybe I can help.
"Haidar ya zunguri ball din ta shige rami ya danyi murmushi kana yace "wai aure su Abba suke so nayi, and dateline din ya bani na kawo masa wacce zan aura gobe ne if not zai aura mun koma wacece, and worse part of it naji mamy tayi mentioning wata 'yar kawarta idan ban kawo mata zuwa gobe ba ita za'a aura mun.
"Saif yayi shiru yana bin Haidar da kallo kana yace "toh kai Haidar ka zaba mana cikin 'yammatan da suke sonka, ko abu mai sauki ka auri Latif.... bai 'karasa Haidar ya katse sa "wayo zai auri Latifa ni Haidar Allah forbid.
"Saif ya sauke ajiyan zuciya kana yace toh baka da wani choice saidai kuma idan zaka bari su aura maka wancan yarinyar din..
"Murmushi Haidar yayi gamida ajiye sandan hanunsa kana yace " the whole Aliyu Haidar ne za'a masa arrange marriage kaima kasan bazai yuwuba I wll find a way out....
"Saif ya girgiza kai yace toh Allah za'bar da abinda yafi zama alkhairi... nan suka ci gaba da game dinsu har lokacin sallahn magrib tayi suka nufi masallaci. Bai bar gidan ba sai bayan isha prayer...

"Kai tsaye sashensa ya wuce ko dinner beyi ba ya kunna series dinsa yana kalla har dare taja, mamy kam abin duk ya dameta amma haka ta daure taki bin takan Haidar.
"Kaman daga sama yaji ana buga masa kofa, a hankali ya karasa muryan Inna yaji tana fadin Zaki ka bude kofan ga abincinka na kawo maka kaman bazai kulata ba sai kuma ya karasa ya bude, dan mugun haushin inna yake ji duk ita tasa sa cikin wannan damuwa.
"Inna ta dire tray kan center table ta juyo tana dubans gani tayi ya murtuke fuska, ta murmusa tace haba dan Inna haba autan Maza, haba shalelen sojoji ina ka taba jin anyi fushi abinci. Maza zauna na baka a baki.
"Abin yaso basa dariya amma ya dake yana yamutsa fuska yace na koshi banjin yunwa.
"Inna bata fasa zuba abincinba tace Ali baka so naga jininka a duniya ne kafin nawa rayuwar ta kare haba Zakin sojoji, soyayyar kenan dazamu nuna maka a duniya. Haidar yayi shiru yana saurarenta, haka Inna tayita lallabasa har ya yarda ya danci abinci kafin ta bar dakin bayan ta gama masa barkwanci wanda har ya sanyasa nishadi....

_Washi gari_
*at Abba's palour*
"Kai nake sauraro Haidar Abba ya fadi cikin dakewa.
"Abba.... sai kuma yayi shiru......
"Hm dama na gaya maka ai cewan mamy, Abba yayi gyaran murya yace yanda kikace din hakan za'ayi mariya.... daidai nan Inna tayi sallama ta shigo...
"Dama akwai maganan da nake son yi maku gameda auren Ali... da sauri Haidar ya dago yana duban Inna suAbba ma duk duban nata suke.
"Inna ta dake ta ci gaba da cewa na riga nayima Ali mata,
"Da mugun mamaki Haidar ke duban Inna..... tunaninsa ya katse sanda yaji tana fadin Ali *Mijin Haneefah* ne tun ba yau ba nakeda wann buri na bari ta karasa karatunta ne na fada maku..... Haidar kam bai gama jin kalaman Inna ba ji yake kaman film ne ba zahiri ba, me wannan tsohuwa take nufi dashi ne, Hanifa kuma ta rasa wa zata ce ya aura sai Hanifa, yarinyar da yafi tsana a duniya yarinyar da kwatakwata bata da kunya, waima yaushe Hanifa tayi girman da shi Haidar za'ace ya aureta, shi bazai iya tuna when last ma ya ganta ba. Tab lallai za'a yita shi kuwa da ya zama *Mijin Hanifa* gwara ya mutu babu aure.....

👸🏻Queen Samy😍💄💋.......
[5/9, 6:18 AM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
13

"Gaba daya Abba da Mamy sun rasa bakin magana sai bin Inna suke da kallo, they were all shocked da jin zancen Inna. Take Mamy taji 'kirjinta na dukan uku uku da sauri... Hanifa kuma ta ina hakan zata kasance yarinyar da sukayi alkawarin rufe mata sirrin da ya jima a binne ta ina za'a soma wannan 'danyen aiki.... tunaninta ya katse sanda taji muryan Haidar na fadin "haba Inna a ina kika ta'ba jin wa ya auri 'kanwarsa ai Hanifa 'kanwatace.... "Rufe mun baki Inna ta katse sa "Sai ka fada mun idan Habubakr da Mariya ne suka haifi Hanifa, ta nunasu duka uku kana taci gaba da cewa "dukanku kuna sane akwai aure tsakanin Ali da Hanifa dan haka na gama magana... Haidar da yayi mutuwan tsaye ganin babu alamun wasa a tattare da Inna yace "amma ai ita Hanifa yaya ta 'dauke ni Inn... "Ko ka aureta ma kanan nan a yayan nata ai kai Ali baka isa ba fa sai ka auri Hanifa wannan al'kawari ne dana 'dauka wa Ummaru kuma babu wanda ya isa goge wannan al'kawari daga kai har iyayen naka... shiru Haidar yayi yana binsu da kallo daya bayan 'daya.
"Abba yace toh Inna naji zanyi shawari akai..... "Salati Inna ta shiga yi tana tafe hannu "yanzu Habubakar har ni zan fadi magana kace zakayi shawari akai ta shiga matse hawaye tana fadin "shikenan kayi yanda kace amma wllhi idan ba'a daura auren Ali da Hanifa gobe ba babu ni babu kai.... daga haka ta fice tana matse kwalla.
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un abinda Haidar ke iya fa'di kenan shikam shikeanan Inna ta gama dashi. Bai kuma cewa komai ba ya mike ya fice daga parlorn.

"Abba yayi shiru yana nazarin kalaman Inna, tabbas Hanifa amanace a garshi sannan yayi alkawarin riketa amana har iya numfashin shi, yayi alkawarin riketa amana tamkar 'yar da ya Haifa. Ya tabbata Haidar zai kula masa da Hanifa tunda dukansu abu daya ne......
"A bangaren mamy ma tunanin da take kenan, Hanifa diyarta ce har abada wannan alkawari ne datayi wa 'yar uwarta zata rike diyarta da amana bazata ta'ba nuna mata ba ita ta haifeta ba, saidai tana tunanin irin wannan rana ranar da Hanifa zata sn cewa ba itace ta haifeta ba. Da wannan tunani mamy ta mike ta fice ta bar Abba ma na kan tunanin lamarin....

"Mamy tana fita ta shiga neman layin 'yar uwarta Hiba, bugu biyu Hiba ta dauka bayan sun gaisa ne Hiba ta gane 'yar uwartata na cikin damuwa.
"Nan ta shiga tambayan mamy meke faruwa.
"Mamy 'boye mata komai ba ta zayyane mata duk abinda ke faruwa. Ga mamakin mamy Anty Hiba kam murna tayi sosai.
"Hiba ban gane kina murna ba kinaga wannan hukunci yayi daidai kenan.
"Eh mana mamy this is the best wllhi beside yanda Haidar baison aure yanzu ko wacece aka aura masa bazai kula da ita ba, amma kinga Hanifa jininsa ne bazai ta'ba cutar da ita ba, kuma kinga wannan shine an rike amanar Anty Deena da Ya Umar.
"Mamy ta sauke ajiyan zuciya kana tace haka ne Allah tabbatar da abinda yafi zama alkhair.

"Yana fita bai zarce ko ina ba sai wani hotel yanda ake saida wine, ko ka'dan baishan wine a Kn amma yau kam dole ya nema yasha ko zai rage masa tension din dake kansa. Haka ya rinka Odern wine yana sha har ya soma ganin duniyar na juya masa ya fara jin kansa can sararin samaniya, da kyar ya iya daukan wayansa ya kira Saif ya fada masa yazo ya driving nasa zuwa gida.
"Ko kadan Saif baiji dadin yanda yazo ya tarar da abokin nasa ba, da taimakon Saif Haidar ya shiga mota nan Saif yayi driving nashi har gida, kai tsaye ya wuce dashi sashensa ba tareda kowa ya gansu ba...

"Abba kam lalla'ba Inna yayi yace ta bari ayi auren asabar me zuwa. Da kyar Inna ta amince juma'a me zuwa za'a daura auren idan ba haka ba ta bar gidan kuma babu ita babu Abba.

"Tunda Saif ya ajiye shi yake barci bashi ya farka ba sai wajajen magrib, a hankali ya soma recalling abinda ya faru, gajeren tsaki yayi ya mike ya nufi bathroom gamida sakar ma kansa shower, bayan ya fito ya shirya cikin light kaya sann ya tada sallah saida yi duk sallolin da ake binsa snan ya bude fridge ya dauko ruwa me sanyi yasha, yana zaune yana nazarin abubuwan da suke faruwa Saif yayi knckn da kyar ya karasa ya bude masa suka shigo a tare.
"Saif ya tsaresa da ido kaman bashine ya shogo dashi dazu na maye ba."ka tashi a barcin ya tambaya idonsa na kallon Haidar.
"As you can see, Haidar ya bashi amsa a takaice.
"Wai meke faruwa ne Haidar... shiru Haidar yayi ba tare da yace dashi komai ba, am asking man ka fada mun pls... nan ma shiru baice komai ba sai danna wayan da ya soma yi...
"Saif ya tsaresa da ido kana yace "perhaps it had to do with magan nan auren naka ko.
"Haidar ya dago ido yana duban Saif kana yace" it's obvious ai so no need to ask, ka gane I don't wanna talk about it am sick of it. Ya zuri car yana fadin tashi muje.
"Ina kuma Saif ya tambaya.
"Let's have some fresh air, koma inane muje kawai.... ya karasa collection din takalmansa ya zabi na sawa kana ya nufi parlor.
"Saif dai mikewa yayi yabi bayansa suka fice...

"Suna zaune a wani joint yana wasa da car keys dinsa on the other hand kuma yana tunanin yanda zai bullo wa lamarin waiter yazo ya tambayesu order, Chapman kawai sukayi ordering dan Haidar kam kwatakwata bashi da appetite he can't eat any solid abu.
"Saif ya katse shirun nasu da cewa "zanso sanin meke damunka friend dukda kace baka son maganan, anyway kayita addu'a shine solution to our problems.
"Kai kawai Haidar yayi nodding kana yace na gode friend, haka dai har suka tashi suka nufi gida gaba daya Saif bai gane ma abokin nasa ba......

👸🏻Queen Samy😍💄💋.......
[5/9, 6:18 AM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
14

"Washe gari da safe ya fito judging yana sanye cikin armless shirt blue da farar three quarter kunnensa manne da headphones da alama waya yake, ya zauna bisa resting chair dake garden kana yaci gaba da amsa wayanshi. Bayan ya gama wayan ne tunanin auren da ake shirin mashi ya fado mashi, wani murmushin mugunta yayi sanda ya tuna kalan rashin kunyan Hanifa.
"The best way da zai gyarata kenan ya nuna wasu Abba ya amince zai aureta, sannan zai kula da ita, he will take this advantage to teach her a great lesson ta yanda zata nutsu bakin tsaurin idon da rashin kunyan sai yayi maganinsa.
"Yayi wata murmushi gamida shafa ha'barsa ya mike ya nufi cikin gida...

"Kai tsaye sashen mamy ya nufa.
"Mamy na kitchen suna hada breakfast ya karasa face dinsa dauke da murmushi kana ya gaisheta sann suka gaisa da me aikinsu....
"Mamy kam mamaki ne ya isheta, she wasn't expecting to see him this early morning dan tasan jiya gaba daya ransa a 'bace yake. Haidar ya gane haka dan haka ya 'karasa ya dauki chips ya hau ci...
"Mamy tace yunwa kake ji ne, kai yayi nodding kana yace terribly ma kuwa mamy.
"Ok bari Delu ta kai maka dinning kana son coffee ne?
"Toh mamy no abar coffee din zan sha fresh pineapple kawai..
"Murmushi mamy tayi tace toh baban Abba... shima murmushin yayi yace "I'll take the shower first. Kana ya fice....

"Mamy ta dubi Delu tace kiga yaron nan kama bashine jiya yakicin komai a gidan nan ba.
"Delu tayi murmushi tace sojan kenan hajiya komai nasu ai daban...

"Abba na zaune yana kallon program din good morning Nigeria a NTA Haidar yayi sallama ya shigo, Abba ya amsa gamida maida dubansa ga Haidar...
"Gefen Abba ya zauna a 'kasa kana ya gaisheshi....
"Har an gama fushin ne? Abba ya tambaya..
"Murmushi Haidar yayi gamida shafa sumansa kana yace" a'a Abba ai dama ba fushi nake ba, hukunci da kuka yanke yayi daidai Abba inshaa Allah zaku sameni ina maiyi maku biyayya....
"Wani sanyi ne ya ziyarci zuciyan Abba kana ya shafa kan Haidar yace" Allah yayi maka albarka Aliyu yanda kayi mana biyayya Allah ya baka yaran da zasu maka kaima..
"Ameen Abba " ya fa'di a ta'kaice....
"Nan Abba ya fada masa duk yanda tsarin abin yake Haidar ya nuna yayi na'am.
"Ya btun aikin naka yaushe ne dama zaka koma...
"Gobe nake son komawa dan munada tafiya a satinnan.

"Shiru Abba yayi kaman mai nazari kana yace toh ya batun daurin auren naka bazaka samu halarta ba kenan ko 'ka'aka...
"Eh Abba ai babu matsala za'a iya daura auren ko bananan.... zan turawa Anty Hiba kudi ta account dinta saita saya lefen...
"Abba yayi murmushi kana yace Allah maka albarka... toh ya batun tafiya da matar taka kaga next week zasu rubuta final examz dinsu...
"Saida Haidar yaji wani dumm da Abba ya ambaci Hanifa da matarsa, ya dan sosa kai kana yace babu matsala Abba sati uku kawai zanyi na dawo idan na dawo sai muga yanda abin zai kasance....
"Sosai Abba yaji dadin yanda Haidar ya kwantar da hankalinsa ya nuna masa ya isa dashi, haka suka dan ta'ba hira kafin Haidar ya mike ya fice zuciyarsa cike da tsanar Hanifa, ya dau awashin sai ya saitata bisa hanya....
"Washe gari Haidar ya 'daga zuwa Lag....

"Su mamy kam shiryeshirye suke kan yi Anty Hiba kuw abun ba'a cewa komi, bata sama bata 'kasa tuni ta iso kano kullum tana kasuwa ana sayayya.
"Yau suna zaune ita da mamy hira suke wanda ya shafi bikin.
"Nifa sai inaga kaman bamuyi ma Hanifa adalci ba ya kamata mujira muji ta bakinta dan ballaline wannan hukunci ya mata, sannan ko kadan dama jinin Hanifa da Haidar kwatakwata bai jutuwa, beside sai inaga tayi karama ma aure gaba daya tausayinta nake.... mamy ta fadi sanda take duban Hiba.
"Anty Hiba tayi shiru kana tace "mamy ki rika kyautata zato inshaAllah wann aure zai

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login