Showing 33001 words to 36000 words out of 114964 words
tauna take tana kallo dan dama bakinta ba'a rabasa da tauna. A hankali ta shigo sa'daf sa'daf Inna kam hankalinta gaba daya na kan kallo saiji tayi an 'dale kanta ana fa'din " kakuuuus, juyowa Inna tayi tana kallonta baki sake kafin tace " wa nake gani kamar Hanifa, Hanifa tamsaketa tana dariya tace nice mana Inna ko rashin ganin naki ya 'karu ne baki gane mutane. Inna ta kai mata duka tace ja'ira kina nan da halin naki ko, " aushhh Hanifa ta saki 'dan 'kara baki a ture tace wato tarban da zaki min knn ko shiknn barin ma na juya, jawota inna tayi ta rungume tana fa'din haba 'yar jikalle na zauna mana mu gaisa, 'daram Inna ta 'daura Hanifa a cinya suka shiga gaisawa tana zolayanta ta 'boye mata miji.... dai dai nan Haidar yayi sallama ya shigo, ya sauya shiga cikin 'kanan kaya "maroon shirt da brown chinos, sai yayi kyau sosai. Ganin Hanifa zaune cinyar Inna yasa sa jan tsaki a hankali. "Lale lale da sojin ruwa, inna ta fa'di tana washe baki, mi'kewa Hanifa tayi tana fa'din Inna ina Shema... tana can 'kuryan 'daki tana sana'an waya mana... da gudu Hanifa ta nufi 'dakin, Inna tace ki tafi a hankali kar ki wahalar mun da tatta'ba kunne na, Hanifa ta juyo tace ina tatta'ba kunnen naki, Inna tace gashi kuwa a cikin ki.... da sauri ta juyo tana kallon yaHaidar shima ita yake kallo, ta'be baki tayi tace nidai babu komai cikina... bata jira cewan Inna ba ta shige corridor. Ta'be baki Haidar yayi yace a ransa " ina 'yar wnn yarinyar zata wani iya 'daukan ciki. "Nan suka gaisa da Inna tako shiga zolayansa.
"Shema na kwance kan gado tana waya Hanifa ta turo 'kofan ta shigo, aiko da gudu Shema ta tafi ta rungume Hanifa tana fa'din babyyy sis, rungumeta Hanifa ma tayi suka shiga tsallen murna, gaba daya Shema ta mance da waya take. " Saif kuwa nata sauraren su ta cikin waya nan ya gane su Haidar sun iso knn. Sai snn ta tuna da wayan ta dauka tace masa, " su Hany sun iso wll talk later, Saif yace a mi'ka masa gaisuwa kafin sukayi sallama.
"Hanifa tace ke wai keda waye kike waya,
"My ango to be, ta bata ansa kai tsaye. Sai yanzu maganan mamy ya dawo mata da tace " su Sady sunje wajen tela dubo ankonsu.
"Ke wai auren waye za'ayi ne? Hanifa ta tambaya. "Da mamaki Shema ke kallonta kafin tace yaHaidar be gaya maki ba, ta'be baki Hanifa tayi tace 'kila ya mance.
"Shema ta kwashe komai gameda soyayyanta da Saif ta fa'dawa Hanifa.
"Sosai Hanifa taji da'di tace " yaSaif akwai kirki ai na tuna sanda na kwanta asibiti kullum sai yazo, gaskiya kinyindacen miji Shema Allah ya baku zaman lafia. Ameen cewan Shema.
"Oya yimin lectures gameda aure tough you're my baby sis but nasan kin fini samun experience, oya zayyano mun me dame dame ake yi a ri'ke miji.
"Galala Hanifa ta kalleta kafin tace "kinga ni ba wnn ba tashi muje ki nuna mun kalan ankon da nasan irin shigar da zanyi. Mi'kewa sukayi Shema tana fa'din kiyita dogging wollah sai kinmin lecture. " su lecture manya cewan Hanifa, Da haka suka 'karasa sashen mamy.....
"Kodasu Sady da Sumy suka dawo ma ba 'karamin murna sukayi ba na ganin Hanifa, 'Danmasani ya 'karasa da mota parking lot kafin ya 'karaso yanda suke shima, zolayan Hanifa ya shiga yi " ah ashe de ashe de.... " ta kuwa 'bata fuska tace zaka fara ko? wallhi kaga ka daina... " toh ni me nace kawai fa cewa nayi ashede fa'dan soyayya ake ya 'karashe maganar ta sigan ra'da. Duka Hanifa ta kai mai ya kauce yana dariya..... daidai nan Haidar ya fito haraban gidan, kallon da ya watsa mata yasata nutsuwa. Gaba 'dya suka 'karasa suna masa sannu da zuwa banda Hanifa. Ya dubi 'Danmasani yace "yaushe kazo, 'Danmasani yace last week nazo mun samu hutu. "Haidar ya gua'da kai yace ka kawo mun results dinka anjima. Kai 'danmasani ya gya'da yace toh yaya sanda Haidar ke 'karasa parking lot, 'Danmasani yace a dawo lafia.... su Hanifa kuwa tuni sun shige gida su Shema sai zolayanta suke " wai kallon soyayya suke ma juna....
"Yana fita be zarce ko ina ba sai gidan su Saif, a parlor ya sami Hajiyan Saif. Da mirnanta ta tarbe Haidar, ya 'karasa ya dur'kusa ya gaida Hajiya. Nan ta tambaheshi ha ya da Hanifa, ya amsa da lafiya lou Hajiya yaya muka sameku. Lafia lou Aliyu. Mutumin naka ma bai jima da shigowa ba ka isa sashensa. Haidar ya mike yana fa'din toh Hajiya kafin ya wuce sashen Saif...
"Saif na zaune a parlorn shi yana rubuta cards Haidar ya shigo, da mamaki Saif ke bin Haidar da kallo, sau'kan yaushe navy?
"Ta'be baki Haidar yayi yace "is non of your business, tinda kai baka iya neman mutum ba. "Ikon Allah haka Saif yace a zuciyansa, shi Haidar wato saidai ka nemesa idan baka nemesa ba yaji haushi shi kuwa baya neman mutum saida dalili.
"Saif yace kaga malam nifa ka mun laifi ma fita ban son ganinka.
"A da'kile Haidar ke kallon Saif ba tareda yace komai ba ya mi'ke dan duba cards din dake gaban Saif, da sauri Saif ya tattara yace nace ka tafi Haidar we're no more friends. Dariya Haidar yayi maras sauti da gefen bakinsa kafin yace " ok fine naji zan tafi amma ka fa'da mun wani laifi na maka.
"Saif yace " Oh wato ma baka sani ba.
"I wouldn't have asked idan nasani, ya basa kai tsaye.
"Hidar kayi aure cikin garin nan "amma ko na sani for goodness sake.
"Dariya sosai Haidar yayi kafin yace "dama wai kan wnn ne yasa kake fushi dani, mysw yayi gajeren tsaki kafin yace 'su Abba dai suka yi aure, kaima kasan idan aurena yazo you'll first person to know.
"Saif ya bisa da kallo kafin yace "don't tell me har yanzu kana nan da halinka. Haidar hope dai baka ta'kura 'yar mutane.
"Kaga let's not talk about this pls. Meye kake 'boyewa ne kam naga kaman invitation cards.
"Sai sann Saif yayi murmushi yace yess IV ne, gashi ma ka gani kasan mu bikin mu bana rowa bane everybody is invited. Haidar ya kar'ba yana fa'din aure babu labari wazaka aura. a iya sani na baka da budurwa..... ganin suna Shema ne yasa yin tsit tsaf ya karance kafin yace, wato dama da biyu kake zuwa wajena knn.
"Dariya Saif yayi yana kashe ido 'daya yace sorry big bro,
"Ta'be baki Haidar ba tare da yace komai ba.... " toh yanzu dai babban aboki tunda ya iso sai kayi scheduling yanda abubuwa zasu kasance...
"Mugun kallo ya watsawa Saif kafin yace " wa ni Haidar, ni kake tunanin zan shiga cikin yaran nan, ai ka cire ni cikin hidiman bikin ka kaima kasan bazan shiga cikin yaran nan ba. Dariya Saif yayi yace whatever kaime de babban aboki kuma dole kayi participating ba. T'be baki Haidar yayi yace this is your business not mine..... hira suka ci gaba dayi har kusan magrib kafin Haidar ya mi'ke dan tafiya gida, yasan by this time Abba ya dawo....
👸🏻Queen Samy😍💄💋........
[5/21, 1:55 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
36
"Da dare misalin 'karfe 10:12pm su Shema Sady Sumy da kuma 'Danmasani ne zaune a parlor mamy, Shema da Sady kallon wani series suke a zee world me suna "King of hearts" 'Danmasani yasasu gaba sai sun canza masu wann Dramatics din dan shi ko ka'dan baison kallon indian, su kuwa ko kulasa basuyi ba sai kallonsu suke, Sumy dai dariyan draman 'Danmasani dasu Shema take kullum suka ha'du abun ba sau'ki (yaran mamy knn😂😜)... shigowan Haidar ne yasaka su nutsuwa dan sunsan yanzu sai yasa su baccin dole. Gaba daya suka shiga gaishesa, ya wani amsa a dake yabisu da kallo baiga Hanifa ba hakan yasa sa 'karasaw stirs ya nufi 'dakin mamy.
"Anty Hiba na zaune saman darduma da alama salla ta idar, Hanifa nata 'ko'karin shirya Ajmal tayi masa wankan dare tana samasa pyjamas Haidar ya turo 'kofan ha'di da sallama, Anty Hiba ce ta amsa tana fa'din ah a Soldier anshigo.... Ajmal ya 'karasa da gudu ya 'dale wuyan Haidar yana fa'din uncle navy nima soja fa zan zama I rin'ka gusha gusha..... gaba daya suka saka dariya idan ka 'dauke Hanifa da ta 'daure fuska kaman taga dodo.
"Haidar ya tsuguna ya shiga ha'da wa Ajmal battens rigarshi yana fa'din, are you not afraid of soldiers? Yana maga nan yana satan kallon Hanifa dake 'ko'karin saka hijabi. Ajmal yace noo am not afraid of them, I want hold their guns...... dariya anty Hiba da Haidar sukayi... Anty Hiba tace toh maza aje a kwanta koh little soldier.... duk saida Ajmal ya bisu da good night kisses sann ya wuce ya haye gado.
"So take ta sau'ka 'kasa parlor amma yaHaidar ya tsare 'kofan, Anty Hiba ta mi'ke tana linke Hijabn'dinta tace soldier kaci dinner kuwa? Ta'be baki yayi yace na 'koshi Anty da yamman nan Inna ta cika mun ciki da fura.
"Still ya kamata dai ka saka wani abu a cikinka, no Anty ban cin solid abu idan dare yaja haka inaga dai coffee kawai zan sha. " Toh shiknn Hanifa ta shigo maka da shi.... da sauri Hanifa ta juyo tana kallon Anty Hiba. Kallonta yayi bece komai snn yanjuya ya kalli Anty Hiba yace "have a good night Anty... daga haka ya juya ya fice,.,, Anty Hiba tace a huta gajjiya....
"Anty nifa dan Allah meyasa kika ce zan kai masa coffee ni dai a nan zan kwana tate dasu Shema... galala Anty Hiba ke kallonta kafin tace "ni kike gaywa a nan zaki kwana common dalla wuce kitchen ki ha'da wa mijinki abunda yake so dama kulle 'kofa zamuyi is already late. " marairaice fuska tayi tace pls mana Anty.... "mugun kallo Anty Hiba ta watsa mata tace "kinsan Allah you're spending your night with your husband, oya ki wuce tunkan ranki ya 'baci, kuma gida 'daya da mijinki kice zaki barshi yayi kwanan gauranci, maza fice kafin na sa'ba miki.... turo baki tayi ta nufi 'kfa rai 'bace.... su Shema ta samu a parlor ta 'karasa ta zauna suka hau zuba surutu.... Anty ce ta sau'ko da mugun mamaki take kallon Hanifa, aiko Hanifa tana ganin Anty Hiba na sau'kowa ta mi'ke a guje ta wuce kitchen.... Anty Hiba ta 'karaso tana fa'din dama kin bari nazo wajen na sameki.... "dariya su Shema suke yi dukda basu san musabbabin fa'dan nasu ba, Sady tace Anty yau ke da 'yar gidan naki munjiku a rana, Anty Hiba tace wnn 'yar gidan nawa mun 'bata ai dama 'yar gidan mamy ce ni Fan 'din Haidar ce (kaman Feesaty knn #fan 'din Haidar😉).... sukayi dariya gaba 'daya... zama Anty tayi har Hanifa ta gama ha'da coffee din ta fito... baki a ture bata ce ma kowa 'kala ba ta wuce.
"Knckn tayi a 'kafar 'dakin, sarai yasan itace saida ya 'diba kusan mintuna biyar kafin ya mi'ke ya bu'de 'kofan, kallo 'daya ta masa ta sunkuyar da kanta 'kasa, yana sanye ne cikin singlet da gajeren wando. Baice mata komai ba ya juya yayi shihewarsa 'dakin, " 'kun'kuni ta soma yi ciki kafin ta 'karaso, gefen bedside ta ajiye masa coffee din ta koma ta zauna can kan sofa. Ko kallo bata ishe Haidar ba. Shi kuwa zama yayi yaci gaba da danne dannen da yake a system. Kwanciya Hanifa tayi bisa sofa ta gudundune cikin hijabinta.... kallonta yayi ta gefen ido yayi wata shu'umin murmushi da gefen bakinsa.
"Ke me kike yi a nan! Ya fa'di cikin dakewa.... " ba Anty bace tace wai sai nazo. Ta bashi amsa.
"Tace sai kinzo kokuma kika nuna mata halinki na jaraba ba, ke tsaban jaraba a gidan inlaws dinki ma sai kin nuna ke mayyar maza ce, tashi ki bar mun 'daki I don't need you here.
"Cikin jin zafin kalamansa ta mi'ke ta nufi 'kofa..... sai jiyo muryansa tayi yana fa'din, zo dawo ba dan halinki ba ..... ba tare da ta jiyo ba ta karas jikin 'kofan, ta mur'da da iya 'karfinta ya'ki bu'duwa, yana kallonta baice komai ba gashi ita gaba 'daya ta kasa kallonsa sabida ba kaya jikimsa sai singlet da boccers, dawowa tayi ta kwanta bisa sofan.... saida ya gama shan cofde din kafin ya juyo ya watsa mata mugun kallo yace " are you deaf! thought I said you should leave, " baki a ture ta mi'ke tana fa'din ba 'kofar bane a kulle.... ta'be baki yayi yace " mayya ai nasan bazaki fita dan jaraba, sai ki kwanta a wajen kuma first thing tomorrow morning zaki bar min 'daki, kuma saura ki 'kura min ido ki hanani barci da jarabanki.... yana gama fadin haka ya 'kure sanyin ac snn yaja bargo ya rufa yayi kwanciyarsa, sai murmushi yake ya 'kuntata mata.
"Kaman wacce aka dasa haka ta tsaya a wajen, tafi mintuna biyar tana tsaye a wajen " wnn shine a dake ka a hanaka kuka, gaba 'daya ta nemi kukan ma ta rasa, ga sanyi da yake ka'data kaman me, ji take kaman ta 'balle 'kofan ta fice daga 'dakin, haka dole ta dawo kan sofan ta kwanta amma me mugun sanyi ne ke ka'da ta gashi kujeran saitin ac din yake, ta du'kunkune cikin hijabinta, "dago kansa yayi yaganta dukunkune cikin hijabi, " murmushi yayi ya kashe bedside lamp din ya maida kansa ya kwanta.
"Can dare sanyinya dameta ga remote din ac din na wajen yaHaidar amma da tayi kasadan ragewa. "Mi'kewa tayi a hankali tana san'da kaman munafuka ta 'karasa ta kwanta can gefen 'kafarsa ta 'dan ja bargon ta rufa. Duk a tunaninta bacci yake.
"Haidar na jinta yayi silent smile yace a ransa mission perfect, dan dama da biyu ya mata haka. Mirginowa yayi yanda take ya rungumota, aiko nan da nan ta razana ashe dama beyi bacci ba, ta mi'ke tana 'ko'karin sau'ka daga gadon. A kunnenta yake ra'da mata ina kuma zakije, dan tsaban jaraba na barki ki kwana a 'dakin ma na maki alfarma shine sai kin biyoni har gadona,..... "ni dai wllhi sanyi nake ji shiyasa na dawo nan dan Allah yaHaidar ka bu'de mun 'kofan na fita... cire hijabin jikinta yayi ya matseta cikin jikinsa yace " ai kin riga kin gwada kanki yarinya, zan taimaka maki na baki abinda kike so.... 'bari jikinta ya shiga yi tana kuka ta shiga magiya tana ro'konsa yayi ha'kuri.......
👸🏻Queen Samy😍💄💋.......
[5/21, 2:01 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
37
"Sosai take kuka wa Haidar duk jikinta ya gama macewa, kunna bedside lamp yayi ya 'kuarawa face dinta ido, har lokacin idonta na kulle tana kuka. "Zaki min shiru kose na fasa baki, ya fa'di yana watsa mata mugun kallo, shiru tayi kaman an 'dauke ruwa ta shiga shan zuciya.
"Jawota yayi cikin jikinsa ya rungumeta gamida kwanciya, har lokacin shan zuciya take ta razana sosai da hidiman yaHaidar. A haka barcci mai nayi yayi awon gaba da ita.
"Kurawa fuksanta ido yayi tana barcin, a fili ya furt sleeping Beauty. Kwanciya yayi gamida mannata sosai cikin jikinsa yana sha'kan dadda'dan kamshinta, a haka shima barci barawo ya sace shi, bacci mai da'di wanda ya jima beyi irinsa ba.
"Tana jin fitansa sallan asuba, bayan ya fita ta mi'ke da niyyan fita amma taji 'dakin a kulle alamun kulleta knn yayai. Tsaki taja tace mugu kawai Allah ya isa na wllhi, bathroom dinsa ta wuce tayi alwala tazo ta tada sallah. Bayan ta idar nan kan sallaya bacci ya kuma 'dauketa. "Koda Haidar ya shigo ya ganta be tasheta ba saima daurata bisa gado da yayi. Kwanciya yayi gefenta bacci yayi gaba dashi shima.
" 'karfe 7:12am ta farka ta ganta rungume cikin 'kirjin yaHaidar, ta 'dan juyo tana duban fuskansa, hankali kwance yake barcinsa, kyakyawan fuskansa sai haske yake ta sau'ke idonta kan gashin giransa wanda yake kaman an zana yayi kyau da kyawawan idanunsa dukda a rufe suke. Ta'be baki tayi sanda idonta ya sau'ko kan pink lips 'dinsa a ranta tace "ga mutum har mutum fuska fari tas zuciya ba'kikirin. A hankali ta zare jikinta ta fice daga 'dakin.
_10:00am_
"Tun daga waje kake jiyo hayaniyansu suna murna results din waec dinsu dan masani ke duba masu a computer. Dukansu sun fita da grades masu kyau sai murna suke. "Yana jiyo hayaniyansu yayi tsaki yace a ransa idiots, fasa shiga sashen mamy yayi ya wuce sashen Abba nan ya tarar da mamyn ma, Abba na breakfast mamy na gefe tana hada masa shayi Haidar yayi sallama ya shigo...
"Da murmushi saman fuskokin iyayen nasa ya gaisa dasu. Sai nan nan suke dashi ya jima suna hira nan shima yayi breakfast kafin ya fice yana fa'din bari ya gaisa da Anty Hiba. Mamy tace afff ai bata nan tayi tafiya 'dazun nan.... "Tafiya kuma babu sallama ya fadi yana uban mamy. Mamy tace a a bawai ta tafi ba knn, sun kirata ne daga can kadunan magan NYSC dinsu zasu shiga