Showing 78001 words to 81000 words out of 114964 words
Sumy, abun sai ya dawo masu sabo.
"Abba da kanshi ya shigo har dakin mamy yanda Hanifa ke kwance, zama yayi gefenta da sauri ta tashi tana share ragowar hawayen dake idanunta, Abba yace daughter banson ganin hawayen nan, ki tashi kici abinci, snn ki cire magann Haidar gaba daya daga zuciyanki, he got what he deserves, daya daga cikin 'yan matansa da yake cin amanarki dasu ita ya kashe kinga babu abunda zamu iya yi. Tunda rayuwar da ya za'ba wa kansa knn.
"Murya na rawa take fadin" Abba wllhi sharri ne, wllhi 'karya ake masa, ni bazan ta'ba yarda yayi haka ba Abba, dan Allah Abba kasa baki a sakar mun miji..... " Enough Abba ya daka mata tsawa, abunda bai ta'ba mata ba, "koda wasa kar na kuma jin kin kira Haidar mijinki, he don't deserve you, he don't deserve any of us here, he's a murder kar ki mance he confenced it, ya aikata laifin, kafin a yanke masa hukuncin sa zai ruboto maki takardan sakin ki dan bazakiyi takaban sa ba.... daga haka Abba yasa kai ya fice...
"Kwanciya tayi bisa gadon taci gaba da rusa kuka mai tsuma rai.....
*****************************
"Babu yanda Aisar baiyi ba Haidar ya daina jinhina ma kansa laifi amma Haidar ya'ki, karshe ma idan Aisar yazo wajensa baya ko fitowa.
"A 'bangaren Hanifa ma abun yayi affecting dinta sosai, idan ka ganta yanzu sai ta baka tausayi, ita kanta bata san tana son yaHaidar har haka ba, yau tana kwance dakin Inna bayan ta gama lalla'bata ta 'dan saka wani abu a cikinta, sip dinta ta bude ta ciro ledan da kwanaki Haidar ya bata, wani kwali ta ciro a ciki, ta shiga juya kwalin, ta bude ta ciro wayace me dankaran kyau da tsada da gani yaji kudi, ta ciro cahajan ta jona a socket, gani tayi har ya kirata bata dauka ba kwanaki, alamun a kunne ya bar wayan knn, wallpaper din kan screen din kuwa hotonsa ne a jiki da kakinksa yasha bakar glasses yayi kyau sosai, tayi murmushi tana shafa kan screen din da hanunta bata san sanda bakinta ya furta I love you so much yaHaidar. Ta runtse idanunta siraran hawaue suka sauko, haka ta rungume wayan cikin 'kirjinta tana tuna ranar da suka rabu da daddare ranar dayiyata riritata yana rokonta gafara.... kuka sosai ta shiga yi tana fadin na yafe maka yaHaidar na yafe maka duniya da lahira, Allah ya toni asirin duk wanda ya 'kulla maka wnn ba'kin sharri.
👸🏻Queen Samy😍💄💋......
[5/21, 5:49 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
64
"A kwana a tashi babu wuya yau watan Haidar daya da sati daya gidan tasko, idan ka ganksa ya rame hakan nan ya 'danyi ba'ki alamunnba zaman jin da'di yake ba knn. Babu yanda Aisar beyiba akan yayi hiring good lawyer wa Haidar for their coming trial, amma fir Haidar ya'ki musamman dayaga babu wanda yazo wajensa, sai Saif shima din Abba baisan yaje ba a sace yaje. Koda Saif ya fada masa irin damuwar da Hanifa tayi be wani damu ba, abun na Haidar dai sai Addu'a kaman wanda aka sa masa hanu.
"Yana zaune yana jiran a fito da Haidar, duba agogon hanunsa yayi yaga time ya soma tafiya, ganduroba daya ya fito ya sara wa Aisar kafin yace "sir lokacin da aka ware dan ganawa da prisoners ya kusa tafiya, snn shi Captain AA yace baison ganinka. "A hasale Aisar ya mi'ke yana kallon ganduroban nan kafin yace " what the heck are you talking about, look am not leaving here until I talk to him, bazan tafi ba sai munyi magana is better idan ya fito. Now go in an tell him bazan bar nan ba sai ya fito munyi magana.
"Sara masa gandiroban yayi ya juya yana fadin yes sir, right the way sir. "Rai 'bace kaman baisan kalman dariya ba ya fito, Aisar yabisa da kallo shima rai 'bace. Daga nesa Haidar ya tsaya yana watswa Aisar mugun kallo, Aisar ya taso ya 'karaso gabansa ya dan sassauta murya yace" how you doing, ko kallo bai ishe Haidar ba yace " as you can see. "Aisar ya fuzar da iskan bakinsa kafin yace zan tafi Kano gibe.... " da mugun mamaki Haidar ke kallonsa kafin yace " what for?, me zaikaika Kano kuma.
"am gonna confront them, zan samu iyayenka Haidar zan fada masu komai everything, duk abunda ya faru it was my fault, inaga idan iyayenka sun yafe maka suka taho lag su zasu saka kayi magana tunda ni ka'ki jin nawa.
"No Aisar, don't even start, you will make them more furious, I've suffered a lot, pls ka kyaleni haka..... " no Haidar bazan kyaleka ba, on the contrary kai ka za'bi hakan ma kanka. who do you think you are hum Haidar, what you're do I is awful, don't be so maniac Haidar. I can't let you do that.
"Na fada maka don't you dear meddle, babu ruwanka da tsakani na da family na.
"Cikin daga murya Aisar yace you can't prevent me, I've already made up my mind, zan samesu maybe su zaka jimaganar su ka bari a daukar maka lawyer, have a good day.... daga haka Aisar ya juya ya bar Haidar tsaye yana kallonsa, kafin aka zo aka shige dashi.
"Aisar yana komawa gida ya tarar da mum zaune a parlor, karasowa yayi ya gaisheta kafin ya zauna gefenta so tired and exhausted, nan da nan wata made ta jere gabansu da kayan sha, mum ta kallesa tace yaya dai son, any improvement. "Aisar da kwalla suka ciko idanunsa ya goge kafi ya soma fadin" no mum, he refused to cooperate, he already give up, I cannot loose him mum, I've to confront his family, they shouldn't abandoned him just like that, wllhi mum zan iya rantsuwa Haidar was innocent, daidai lokacin da Dad yake saukowa daga stirs, Aisar ya mike yana fadin wllhi mum who ever did this to my friend, he's not goin to get away with it, he'll pay dearly. Juyawan da zaiyi sukayi ido hu'du da dad, sa kai Aisar yayi zai wuce dad yace" naji kana ce zaka je Kano, barin fa'da mak babu hanuna idan ka jawo ma kanka wani abun, am warning you ka cire kanka daga hidiman yaron nan, he's a murder, kasan halin Admiral wllhi Aisar kaja ma kanka wni abun babu ruwana.
"A hasale Aisar yake fa'din" kana nufin na bari a yanke wa Haidae hukuncin kisa, kana nufin na bari ya amsa laifin da bashi ya aikata ba... " So what! Dad ya katsesa, ko ya samesa ba shi yaja wa kansa ba... " Dad don't tell me you've something to do with that, Aisar ya fa'di idon kyam kan mahaifin sa.." What the heck are you talking about Aisar, this is ridiculous, don't be so stupid, nidai na fada maka ka cire kanka daga hidiman yaron nan.
"Girgiza kai Aisar yayi kafin yace" I swear I will never rest until the truth finally came out... daga haka Aisar yasa kai ya nufi stirs.... Dad nankiransa ko juyowa beyi ba balle ya tsaya, " ya juyo da dubansa ga mum kafin yace" kina jina better stop your crazy son, before he does something stupid, something that I cannot deal with.
"Mikewa mum tayi tana masa mugun kallo kafin tace" Ina bayan 'dana 'dari bisa 'dari, and I'll give him my complete support na ceto rayuwan innocent Aliyu, the guy doesn't deserve that, kar ka mance irin 'ko'karin da yayi wajen taimakawa har Aisar ya nutsu har kaima..... "Enough Hannatu, dad ya daka mata tsawa, kuje kuyi duk abunda kuka dama amma wllhi kunji na rantse kome kuka jawo keda 'danki babu hanuna ciki... "kallon takaici mum ta bisa dashi kafin ta girgiza kai kawai ta wuce, tana mamakin hali irin na mijinta, he will never change.
*************************************
" Saukansa knn a garin Kano, hotel ya nema ya kama daki kasancewar already yamma tayi, washe gari da safe misalin 'karfe 9:am ya fita neman gidansu Haidar, kasancewar Abba ba 'boyeyyen mutum bane a garin yasa bai wani sha wahaln samun gidan ba.
"Mamy na daurawa Abba agogo yayinda yaketa bin fuskanta da kallo, sosai zaka gano ramar da tayi, Abba yasa hanu ya dago fuskanta yace " Mariya ta look up pls, kasa 'dago idonta tayi ta kalli Abba, ya da'da tallafo fuskanta sai hawaye yaga yana zauka sirara a fuskan nata, rungumeta tsam yayi cikin jikinsa ya shiga lallashinta. Suna a haka Sumy tayi knocking, da sauri mamy ta saita kanta gamida bata izinin shigowa, gaishe da iyayen nata tayi kafin tace Abba somebody is waiting for you down stirs, Abba yace wanene?
"I don't know him Abba, yaxe dai daga lagos yake, daga Abba har mamy saida suka sha jinin jikinsu, Abba ya gya'a kai yace ki shigo dashi parlor, toh Abba ta fadi sanda ta dubi mamy tace" mamy na wuce sch.
"Mamy tace Allah bada sa'a dear.
"Kallon Sumy Aisar yake tayi ta masa kama da wata but ya rasa a ina yasanta, haka dai har ta fice Aisar na kallonta na son tuno yanda yasan face din.
"Alhaji pls dan Allah ku taimaka nasan idan ku kukayi wa Haidar magana he'll cooperate, dan Allah kar ku bari a yabke masa hukuncin da babu laifinsa.
"Abba yayi gyaran murya yace "young man da ka tashi ka tafi da yafi maka sau'ki, ta yaya zamu kare mutumin da ya amsa laifinsa da kansa. "Alhaji a duba lamarin dan Allah... Abba ya mi'ke yana duba agogon hanunsa yace" ina abunyi idan bazaka damu ba ni zan fita... Aisar ya dubi mamy yace "Hajiya pls say something, Mamy ta dan kalli mijin nata taga babu alaman wasa a tare dashi... har Abba yakai 'kofa Aisar yace ok fine" a 'kara minti biyu dan Allah, abunda zan fa'da yanzu is very important...... " Haidar bai aikata laifin da kuke tunanin yayi ba da ganganci, he was trying to save a life, shiyasa ya aikata haka, I was the guilty one, laifina ne, ni nace masa idan bai bari na fita da Hanifa ba bazan basa map din ba, kuskurensa daya da bai fada mun Hanifa matarsa bace, amma wllhi believe me ko a da can I've no bad intentions for her.... cikin rashin gane ina Aisar ya dosa Abba ya juyo yana masa mugun kallo, mamy is confused, gaba daya kallon Aisar suke kafin Abba yace" Spell it out, yi mun bayani me kake cewa.
" nan Aisar ya kwashe komai ya fada masu.... wani sabon tashin hankali ne ya ziyarci Abba da mamy, knn Hanifa bata fada masu gaskiyan abunda ya faru ba, lallai Haidar baiga komai a rayuwa ba.... A fusace Abba ya mike ya nufi sashen Inna, Hanifa na zaune kan darduma da idar da sallan walha, Na tare da Abba yace da ita 'kala ba ya ri'ko hanunta suka nufo waje, Inna data ga haka dan bata ta'ba ganin hakan ba nan ta shiga bin bayansu tana tambayansa lafiya, Hanifa kam tama rasa ta cewa sai bin Abba da kallo kawai take yanda taga fuskansa babu alman walwala, ga ' kirjinta da yake faman lugude...
"Abba bai tsaya ko ina ba sai cikin parlorn sa, Aisar ya shiga nuna mata yana tambayanta kinsan wnn.... ai kan Abba ya gama rufe baki, ta shiga 'buya a bayan Abba tana fa'din " it was him Abba, shine Abba shine mutumin da ya rabani da mijina farin cikim rayuwata, tunaninta 'daya kar dai Aisar ya fadi abunda Haidar ya mata, nan ta shiga fadin Abba kar ku yarda da abumda yake fada 'karya ya shirya maku, " tsawan da Abba ya daka mata yasata nutsuwa, ta shige bayan mamy da gudu tana maysan hawaye. Inna dai sai kallonnikon Allah take, ta kalli wnn ta kalli wancan.
"Abba ya dubi Aisar yace maimaita abunda ka fa'di yanzun nan, Aisae bai canja komai ba ya fadi, snn yace Amma wllhi banyi niyan cutar da ita ba yun acan, kuma wllhi Haidar beyi haka da wata mummunan nufi ba, dan Allah ku yake masa Hanifa nima ki yafe mun dan Allah ku tausayawa Haidar kodan halin da yake ciki, na tabbata hakkinku shike bibiyan Haidar,
"Banda kuka babu abunda Hanifa keyi, Inna kuwa sai rafka salati take, mamy kam kwantar da Hanifa tayi kan cinyarta tana rarrashinta.
"Cikin tsan tsan 'bacin rai Abba yace tashi ka fice mun a gida you coward, get out before I lost control. Jiki a sanyaye Aisar ya mike.
"Hanifa ta sauko kasa ta kama kafar Abba tana fadin "Abba dan Allah ka ceci rayuwata ka amince mun naje naga yaHaidar dan Allaj Abba, Abba kar ka bari su rabani dashi,...... pls Abba... kuka mai tsuma rai ya kuma kufce mata, fitan da Abba beyi ba knn ya juya ya haye samansa.
"A sittin Hanifa ta mike ta bi bayan Aisar, har ya fice haraban gidan ta kwala masa kira, juyowa yayi yaga tana faman kuka sharshar, cikinnkuka take fa'din" kafada mun wani hali yaHaidar keciki, ka fad mun pls Aisar...
"Sosai Aisar ya tausaya mata" girgiza kai yayi kafin yace " ki kwantar da hankalinki Hanifa, everything is gonna be alright insha Allah, ni na sani wani ne ya 'kulla wann sharri wa Haidar, amma insha Allah he won't get away with it who ever he is. Hanifa ta share hawayen idonta tace yaushene shari'an, Aisar yace saura wata daya da sati uku, kuma idan har Haidar bai bada hadin kai ya bari aka dauka masa lawyer ba komai na iya faruwa, idan ya kuma amsa laifin a gaban al'kali there is nothing we can do.... " toshe bakinta tayi sanda wani sabon kukan ya kufce mata, sosai tabawa Aisar tausayi, yace ni zan wuce amma insha Allah bazan ta'ba gajiyawa ba wajen ganin Haidar zama free, daga haka Aisar ya nufi gate ya fice daga gidan,
"Hanifa kam dirshan ta zauna a wajen taci gaba da rusa kuka.
"Tun daga wnn rana kullum tana rubuta sauran kwanakinnda suka rage a shiga kotu, hankalinta kullumm'kara tashi yake, gaba 'daya sun du'kufa wajen addu'a.
"Yau ta kama sauran sati uku cif a shiga kotu, idan kaga Hanifa zaka zata itace za'a yanke mata wnn hukunci, tana zaune tana kallon hotonsa Sumy ta turo 'kofa ta shigo, dawowanta knn daga examz, ta tarar Hany na aikin abu daya kuka
"Ajiye jakanta tayi bisa hanun kujera ta 'karaso gamida dafata, ta soma fadin" kiyi ha'kuri Hanifa duk tsanani na tare da sau'ki, Allah zai kawo mana 'dauki, Hanifa ta 'dago idanunta da suka ji'ke da hawaye ta soma fadin" why Sumy, why all this, ina son shi Sumy, with all my heart and all my soul, wllhi ina son yaHaidar, bazan iya jure rashinsa ba.... kuka mai 'karfi ya kufce mata, rungumeta Sumy tayi suka shiga rera kukansu a tare, " together we will go through this horror tragedy, am here for you sis Sumy ta fadi cikin kuka.
"Inna ce ta shigo ta gansu sun rungume juna suna kuka, sosai ta tausaya masu, rai 'bace ta mike ta nufi sashen Abba, yana zaune a parlor yana kallon BBC World inna ta shigo da sallama, fuska babu walwala, Abba na gaisheta tayi banza dashi. Ta soma fadin " inace ni nasa Ali ya auri Hanifa, toh wllhi babu abunda zai rabasu, akan me zaka dage sai an rabasu, yara suna son junansu, idan kai baka sonshi saboda kanada wasu 'ya'yan mu muna sonsa, idan kai bazaka je dubasa ba mu zamuje, zan dauki Hanifa mu tafi, tunda baka son farin cikin mu, kuka ya kufce wa Inna taci gaba da fa'din wllhi zamu je mu duba zaki ko kana so ka baka so, koma shi yayi laifin mu muna sonsa dan hanunka bazai ru'be ka yanke ka yar ba.... Inna dan Allah kimdaina kuka ki saurare ni..... kana jina idan ba baki kake so na maka ba, hwara tun wuri ka sayo mana tikitin jirgi nida Hanifa muje muga zaki.... Abba cikin 'kan'kan da murya yace Inna kiyi ha'kuri zan sayo maku yanzun nan, idan kunje muma zamu zo, dan Allah ki daina kuka haka saboda ni.... sai snn Inna ta fice zuciyanta cike da tausayin Haidar.
" Washe gari Inna da Hanifa suka daga zuwa jihar lagos,Mamy harda later ta bayar akai wa Haidar, Sumy taso binsu saboda examz da bata gama yasa bata bisu ba, suna isa already dama sunyi waya dasu Sameer, dan haka suna isa Sameer ya dauko su a airport, tun daga isan su Hanifa ta maysa itafa saidai akaita taga Haidar, momma tayita faman rarrashinta tac ta bari gari ya waye tukunna, dan yanzu yamma ta riga tayi, lokacin visiting ma ya wuce. Sosai Sameer da momma suka tausayawa Hanifa ganin halin da take ciki.
"Tarba me kyau momma tayi wa Inna da Hanifa, Inna nata faman godiya, momma tace haba ai nan gida ne, da daddare Amal nata faman surutu wa Hanifa, saida Sameer ya maya dabara ya dauketa ta bar Hanifa ta dan samu bacci, momma da Inna kam ai ranan sosai suka jima a parlor suna ta'ba labarai kaman tun can dama sun san juna....
👸🏻Queen Samy😍💄💋........
[5/21, 5:49 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
65 to 66
" 'Karfin hali tayi ta shirya da sassafe dan kuwa kwana biyun nan daurewa kawai