Showing 57001 words to 60000 words out of 114964 words
malam Habu ma ba gaisuwan da suka saba sukayi ba, a ransa yace lallai ba lafiya ba, dan ko bai taba ganin Soja( haka yake kiran Haidar) cikin wnn yani ba.
"Yana shiga gidan bugun zuciyansa ya 'karu sosai, kai tsaye sashen Inna ya wuce jiki babu laka hakan nan yake tafiyan.
"Inna na zaune saman kujeranta na gado lol, sauraren radio take filin za'ben yamma, gaba daya bata ji shigowan mutum ba sai ganinsa tayi 'ki'kam tsaye jikin 'kofa, baki ta sake tana kallonsa dan daba don ta masa faran sani ba da sai tace wnn ba Aliyu bane an canza sa ne tsaban rama da sauya kammani da yayi.
"lale lale da mijin ina ka baro mun kishiyar tawa , ya ka tsaya daga wajen, waima ya na ganka haka nn ciwo kayi ne, shiru Haidar bai ce mata 'kala ba, ta karkato da kyau tana dubansa kafin tace " wai ko ba Ali bane wnn, meye haka Zaki meke faruwa da kai, ta mike tana gyara daurin zani ta nufo Haidar, rungumeta Haidar yayi kuka mai 'karfi ya kufce masa..... " jikin Inna yayi sanyi da ganin wnn ba'kon lamari, dan kuwa rabonta da taga kukan Haidar tun yana 'karamin yaro, wnn juriya nasa ne ma yasa 'kanin mahaifinsa me rasuwa yake kiransa da Soja har Allah ya mashi bakinsa ya zama sojan.... "Ali lafiya wai meke faruwa ne. Sosai ya rungume Inna cikin kuka yake fa'din " I couldn't make it, I couldn't make it Inna, why did she disappeared, she's the love of my life, she's the one whom I wanna be with. I can't loose her.... kuka me 'karfi ya kuma kufce masa, " Inna dai taji yanata sunbatu amma bata gane me yake fada ba.
"Ali idan zaka bu'de baki kamun bayanin meke faruwa ka bu'de, kazo kanata mun sunbatu ni nasan me kake cewa..... kuka kawai Haidar keyi kaman 'karamin yaro. Tun tana masa sababi har ta koma rarrashi ganin abun yaci tura yasata yanke shawarin kiran malam Habu yazo ya tayata ganin wnn ikon Allah, dashike dama babu kowa a gidan su mamy Abba da Sumy sun raka Sady sch ABU, suka rakata gaba daya bayan Abba ya barta tayi ABU din.
"Yana zaune saman bencin sa ta iske sa, ganinta a rude yasa malam Habu mikewa yana fadin lafiya Hajiya, Inna tace inafa lafiya, ga Zaki can yana abunda ban ta'ba gani ba, kuka yake kaman karamin yaro na tambayesa meke faruwa yaki fada mun,
"Subhannallah, aiko kodaga yanda na gansa nasan ba lafiya, malam Habu ya fadi.
Babu yanda basuyi ba Haidar yaki magana sai kuka yake yi, fuskarsa tayi jajazur, nan fah Inna ma ta 'buge da kuka, malam Habu ya shiga basu baki gaba daya inaa babu me saurarensa cikinsu (niko samy nace wayaga sahoro da sahorama😂).
"Jin ana horn a gate yasa Malam Habu ya wuce da sauri yana fa'din a ransa Allah sa su Alhaji ne suka dawo.
"Abba yace malam Habu yay dai aka bar gate babu kowa, jiki a sanyaye malam Habu yace "wllhi Alhj gidan ne nake tunanin babu lafiya amma dai ku 'karasa ciki. Abba da mamy harma da Sumy duk sun rude..... Inna ce babu lafiya mamy ta tambaya... "a'a hajiya Soja ne ya dawo yanzu.... "Sumy kam tune ta shige ciki duba Inna. Nan Abba da Mamy suka rufa mata baya.
"Haka suka iske Inna da Haidar, Inna na matse hawaye Haidar na ta'kure can gafe ya manne jikin garu bakace shi bane. Gaba daya jikinsu yayi sanyi.
"Inna tana ganinsu ta mike tana gyara daurin kwali tace " yawwa ai gwara da Allah yasa kuka dawo yanzu sai kayi masu bayani, idan turancin zaka masu ma ai su suna ji, tunda ni ka'ki fa'da mun meke damunka.
"Kallonsu Haidar yayi da idanunsa da suka koma jajzur, a dur'kushe ya matso gabansu, mamy jikinta duk yayi sanyi da ganin yanayinsa, dukansu ma dan kuwa ba'kon lamari ne basu ta'ba ganin Haidar a irin wnn yanayi ba.... hannun Abba ya kama yana daga dur'kushe yake fadin " Abba ku yafe mun, mamy ku yafe mun,.... mamy tayi karfin halin cewa Aliyu meke faruwa, me kamana kake neman gafara irin haka. Abba kam totally speechless yake bin Haidar da kallo.
"Mamy it's Hanifa.... 'kirjin mamy ne ya yanke ya fadi, take hawaye suka shiga zirya a fuskanta, haka Sumy da inna, salatai inna ta hau yi tana fadin me ya sameta Ali, ina Hanifar..... cikin tashin hankali mamy ke fadin ina Hanifa Haidar, where is my daughter. ? Where is she Haidar, what happened to her.
"Haidar na kuka yake fadin, "mun samu sa'bani da Hanifa mamy ta tafi ban ganta yau kwana biyar...... bai gama rufe baki ba Abba ya su'ke masa wata mari, ya kuma 'kara masa wata marin, ganin Abba bazai daina marinsa ba yasa inna tayi saurin shiga tsakaninsu, ta riko Haidar. Abba na huci yake kallonsa... " are you idiot, are you stupid, shine zaka zo mun gida kana fa'din baka ganta ba, na 'dauki amana na damka maka, abunda zaka saka mun dashi kenn Haidar. Now get out of here, get out of my house, na baka 24hrs ka nemo mun 'yata yanda ta shiga ta fita.... daga haka Abba ya fice zuciyansa na tafarfasa....
*manage this ba yawa, idan nasamu time zaku jini later. Love you all😍*
👸🏻Queen Samy😍💄💋......
[5/21, 5:35 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
52
"Mamy mutuwan zaune tayi a wajen ta kasa 'daga koda 'dan yatsan 'kafarta banda hawaye babu abunda ke bin 'kuncinta, Sumy jiki a sanyaye ta wuce 'kuryan 'dakin Inna ta kwanta bisa gado ta shiga aikin kuka, Inna banda salatai babu abunda take yi.
"Jiki a sanyaye mamy ta mike ta nufi 'kofa, 'kafarta Haidar ya ri'ke yana fa'din mamy pls..... bai gama rufe baki ba, ta fizge zaninta tana masa wani mugun kallo, kuka ya hanata furta koda kalma 'daya. Wucewa tayi sahenta tana matsan hawaye.
" Yafi minti goma na dur'kushe a wajen yana aikin abu 'daya, Inna ma 'daki ta wuce aka barsa shi 'daya a wajen. Saida yayi mai isarsa kafin ya mi'ke ya nufi sashensa, kulle kansa yayi bai kuma le'kowa ba.
"Dawowan Abba knn daga masallaci sallahn isha, nan ya tsaya tambayan malam Habu ko Haidar ya fice masa daga gida, malam Habu yace baiga fitansa ba dai, Abba ya 'daga kai snn ya shige cikin gida, kai tsaye sashen mamy ya wuce ya samu ta idar da sallah knn tana faman ci gaba da kuka. Zama yayi bakin gado yana tunanin lamarin. Juyowa mamy tayi tana kallon Abba sanda ta jiyo sautin kukasa. Tabbas ba 'karamin abu ke sa Abba kuka ba. Hankali a tashe mamy ta shiga basa baki. Ya dago yana dubanta kafin yace " Mariya na kasa ri'ke amanar da 'dan uwa na ya bar mun, na kasa kula masa da tilon 'diyarsa, na dauka Haidar zaifi kowa iya ri'kemun amanarta ashe ba haka bane. it's all my fault da ban aura wa Haidar Hanifa ba da hakan bata kasance ba.... "mamy ta rungumeshi tana fadin " haba Abba dan Allah ka daina fadin haka, stop blaming your self for what happened, wnn kaddara ce daga Allah, addu'a zamuyi har Allah ya bayyana mana ita. Abba ya da'da matse ta cikin jikinsa kafin yace "haka ne Mariya, Allah baya bacci yana kallon mu yana sauraren mu Allah ya bayyanr da ita. Murya na rawa Mamy ta amsa da Ameen.
"A ranar dai gidan Alhaji Abubakar Aliyu ma iya cewa kwana zaune akayi, kowa na cikin tashin hankali da tsananin damuwa.
"Har rana ta fito Haidar bai bu'de sashen sa be fito ba, banda nadama babu abunda yake yi, baisan yana son Hanifa har haka ba yana sonta so me tsanani. Inna ce keta faman buga masa 'kofa tana 'dauke da tren abinci, tayi tayi ta gaji 'karshe haka dole ta ha'kura ta koma, ita ka'dai sai sababi take, " kar Allah sa kaci abincin ni nace ku samu sa'bani da matarka, gwara ka bu'de 'kofan nan ka tafi ka nemo mun jikata dan wllhi baka isa ba, ba kai soja ba Allah sa bindiga ne kai..... da haka har inna ta koma sashenta bata bar sababin da take ba.
"Hanifa da Amal zauna a parlor suna kallon animation momma ta 'karaso ta zauna tana zolayansau, Hanifa tace momma dama so nake na tafi gida tunda naji sau'ki sosai.jikin momma yayi sanyi ko ka'dan bata 'kaunar taji Hanifa tayi magann tafiya gida, musamman yanzu da suka saba, momma tace haka ne Hanifa bari Sameer ya shigo sai muji yanda tafiyan naki zai kasance, momma ta matso kusa da ita ta rungumeta tace "Hanifa zamuyi kewarki, jiki a sanyaye Hanifa ma tace nima zanyi kewarku momma ta shafi kan Amal tace "banson rabuwa da Amal dina. Sai snn Amal tace mummy wai ina zaki je. Hanifa tayi murmushi tace gidan mu zan tafi Amali na... kukan shagwa'ba Amal ta soma tana fadin" no nidai a nan zaki zauna, pls don't leave. Rungumeta Hanifa tayi tace ai mun zama 'daya Amali na zan rika zuwa wajenki da momma kema watarana zaki je wajena kiyi hutu. "Amal ta ma'ke kafa'da tace I want us to together forever pls pls pls.... haka ta rin'ka fadi wanda saida ta saka su Hanifa da momma dariya.
"Sameer ne ya shigo ya taddasu suna hiran tafiyan, yafi kowa son Hanifa ta kasance uwa ta har abada wa Amal, zama yayi yana taya su dariyan draman Amal, nan Hanifa ta dauketa suka nufi garden.
"Sameer yabisu da kallo har suka shige, ya juyo da dubansa ga momma dake kallonsa cike da kulawa, murmushi yayi ya shafa kansa, momma tace I know you're deeply in love with her son, " shafa kansa yayi yace yeah I do love her momma, ina sonta kaman yanda nake son Fauziya ina so ta maye gurbin Fauziya. Amma ban sani ba gaskiya ina tsoron sanar da ita... momma ta ri'ke hannayensa tace a hankali zak nuna mata irin son da kake mata, amma yanzu ka maidata wa iyayenta first sai abi komai in order, gya'da kansa yayi yace haka ne momma Allah ya shige mana gaba, momma ta amsa da Ameen. Ya mi'ke yana fa'din barin yi wanka naje sayo mana tickets, zuwa gobe sai mu tafi kanon insha Allah. Momma tace yawwa hakan yayi. Kan ya wuce saida yabi wajen su Hanifa da Amal a garden ya gansu sai wasa suke gwanin sha'awa, a ransa yake addu'an zama *Mijin Haneefah*.
"Bayan ya dawo ne Hanifa ta bada numbern mamy momma ta kira, sosai mamy taji dadin jin Hanifa na safe hand, saida tayi kukan murna, Hanifa tace su kwantar da hankalinsu zuwa gobe zata dawo da izinin Allah, da wnn labari me da'di yasa hankulan mutan gidan ya kwanta idan ka 'dauke Haidar da baisan me ake ciki ba, da wnn dadda'dan labari Abba ya samu strength na fita Office.
" 'karfe biyar da mintoci ya fito ya nufi sashen mamy, ko kallo bai isheta ba balle ta amsa masa gaisuwansa, karshe mi'kewa tayi tana masa mugun kallo kafin tace " gwara ka fice masa daga gida kafin yazo ya sameka.... daga haka ta wuce upstairs.
"Mikewa Haidar yayi jiki a mace ya suri motarsa ya fita, bai zarce ko ina ba sai gidan Hajiyan Saif. Zaune ya sameta a parlor, Hajiya ta razana da ganin Haidar kaman wanda ya jima yana jinya, yayi ba'ki ya rame, zama yayi dirshan a 'kasa ya kasa ce mata komai, hankali a atashe take tambayansa lafiya.... kasa furta koda kalma 'daya yayi, kukan da bai son ya fito ya shiga zarya a fuskarsa, ya kasa ce mata komai sai kuka.... sosai hankalin Hajiyan Saif ya tashi, Haidar yafi mintuna takwas a wajen ya kasa ce mata komai sai kuka.... 'karshe dai ta yanke shawarin kiran Saif a waya ta sanr dashi.... mintuna ka'dan Saif ya 'dauka ya iso....
👸🏻Queen Samy😍💄💋......
[5/21, 5:35 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
53
*This page is for all the members of Queen Samy Novels, thanks for your luv and support. I lUv YoU sO mUcH❤*
"Da mugun mamaki Saif ke bin aminin nasa da kallo, abune me kaman wuya kaga Haidar na zubda hawaye, bai gama karaya ba saida yaga irin ramar da Haidar yayi, ya 'karaso gamida kallon Hajiya alamun "meke faruwa".
"Girgiza masa kai tayi alamun "no idea, ta masa alama da kai akan su tafi sashensa... Riko Haidar Saif yayi suka nufi sashensa sanda yake samartaka, a parlor Saif ya zaunar da Haidar bisa sofa kafin ya fice ya nufi sashen Hajiya, ba'a jima ba ya dawo da bottle water, ya tsiyaya a cup ya mi'kawa Haidar, ba musu ya kar'ba ya kur'ba.
"Friend what's all this, what's going on. Why are you shading tears?. Ban ta'ba ganinka in this condition ba, pls talk to me Haidar meke faruwa.
"Haidar ya dago jajayen idanunsa yana kallon Saif kafin yace " I failed my parents, I failed my self...... I can't help it Saif, I can't loose her, meyasa ta 'bace mun, why things had to happens this way, I love her with all of my heart. I love her ever since she was born...... ya ri'ke hanun Saif sosai yake kuka... Saif ya shiga basa baki duk da ba wai ya fahimci asalin abumda Haidar ke nufi bane.. Saida yayi mai isansa kafin Saif yace " I don't get you Haidar pls spell it out, meke faruwa.
"Haidar be 'boue wa Saif komai ba tun daga farkon zamansu da Hanifa har I zuwa abunda yayi sanadiyan rba su.
" Kallon mamaki kawai Saif ke bin Haidar dashi kafin yace " why why Haidar, what on earth could possibly make you do that, it just doesn't fit in my head, haba Haidar haba that was so awful. You shouldn't have done that, you've made a huge mistake,
"I don't know Saif, I was stupid,
"Saif ya fuzar da iska, kallon Haidar kawai yake cike da tausayawa, rawan 'dari Haidar ya soma, ya ta'kure cikin kujera yana rwan sanyi. Kallon sa Saif yayi kadin yace " are you sick?, bai iya basa amsa ba sai daga masa kai da yayi. Saif ya taba goshin Haidar yaji zafi ra'dau" O gosh you having a fever, tashi muje asibit, girgiza kai Haidar yayi yace " no need, I'll be fine, just help me with panadol.
"Saif ya girgiza kai kawai ya fice ya nufi sashen Hajiya, zaune ya sameta a parlor ta rafka tagumi bayan ta gama waya da 'kawarta mamy ta sanar da ita komai, Saif yana shirin mata magana tace " Hajiya Mariya ta kirani ta sanar dani komai, oh my Allah give me some strength, ta fa'di gamida sauke numfashi.
"Saif yace Hajiya first aid yana ina, " me zaka yi dashi. "Haidar ne ba lafiya yanada fever. Hajiya tace "kuma" aida asibiti kuka tafi Saifu, Saif yace ya'ki yarda Hajiya.
"Ok ka duba 'dakin Jamila yana ciki idan jikin nasa baiyi sauki ba sai mu tafi asibiti, toh Hajiya Saif ya fadi gamida shigewa, Hajiya ta mike tana fadin barin hada masa ruwan shayi.
"Kwance Saif ya samu Haidar ya du'kun'kune cikin bargo, da 'kyar ya mi'ke yasha maganin nan bacci ya 'daukesa, koda Hajiya ta samu na bacci bata 'daga sa ba. Saif ya isa sashen Hajiya suna tattauna lamarin. Har kusan magrib Haidar be farka ba, Saif ya dawo daga sallah ya le'ka sa, ya samu ya tashi yana sallah, Hajiya da kanta ta shigo tasa Haidar ya saka wani abu a cikinsa,
"Saif ya kallesa bayan Hajiya ta fita yace I'll drive you home, girgiza kai Haidar yayi yace " no am staying here, I can't go there Saif, no one is willing to listen to me. "Saif ya fuzar da iska yace shikenn, idan Allah ya kaimu gobe sai muje mu sami Abba dga nan musake komawa can Lag din. 'Daga kai kawai Haidar yayi ya koma ya kwanta, kana ganinsa kasan 'karfin hali kawai yake amma baya jin da'di.
"Koda Saif ya samu Hajiya da batun taji da'din hakan, tace he needs your company, yanzu ka dauko Shema'u mu kwana da ita, Saif ya mi'ke yana fadin toh Hajiua sai na dawo.
"A parlor ya samu Shema tana kallo, yana shigowa ta 'dale wuyansa tana faman shagwa'ban ya barta ita ka'dai, zama yayi ya daurata bisa cinya gamida dafe kansa. Shema ta kallesa cike da kulawa, " Ya dai Sweet, is all well? Sauke ajiyan zuciya yayi kafin ya gyada mata kai kawai yana shafa gashinta, toh why the long face ta fadi fuskanta dauke da damuwa. Murmushi Saif yayi kafin yaja hancinta yace " tashi ki shirya mu tafi gidan Hajiya. Shema ta kafesa da ido kadin tace " wai meke faruwa ne, pls ka fada mun you making me nervous.
"Rungumeta yayi tsam cikin jikinsa kafin yace " I love you Shema, I love you so much, promise me you won't leave me, we'll always be together for the rest of our life. "Jiki a sanyaye Shema