Showing 75001 words to 78000 words out of 114964 words

Chapter 26 - MIJIN HANEEFA Complete Hausa Novel

15 Oct 2024

13148

in kula yaci gaba da tadiyarsa sanda yake danna security lock daga jikin key dinsa ya bude motar, a haka ya karasa parking lot ya shige yayi tafiyarsa, masu gadi na faman gaishesa.

"Asubanci Anty Hiba tayi ta dira a garin KN, bata wani sha wahala ba wajen amimcewan su Abba, hasalima sunji dadin hakan, Hanifah ma hakan yafi mata sauki, tunda kullum ita kadai ke wuni Sumy na zuwa sch sai ko Inna, mamy kam tun bayan abunda ya shiga tsakaninta da yaHaidar wani irin kunyan mamy takeji, duk wani shwagwa'ba da take mata a da yanzu ta rage, sosai take jin nauyinta, ita kanta mamy ta gane hakan, kasancewar Kaduna da Kano ba wani tafiya me nisa bane yasa suka juya Kaduna a ranan, Hanifa sai dauki take Sumy ma ta waya sukayi bankwana.

" 'Karfe 4:00pm ya gama duk wani abumda zaiyi a Office ya tarkasa ya nufo downstairs, Captain Paul da Admiral ya hanga daga can suna tattaunawa, daga nesa Paul ya dago masa hannu yana sara masa, murmushi Haidar yayi ya jefa masa yarensu na sojoji, ko kallo Admiral bai ishe Haidar ba ya shige motarsa ya bar wajen, Paul ya sheke da wata dariya yace I pity your life navy.... Admiral yayi wata mirmushi kafin yace yanzu zai gane ba'a ja da babba a waje, Paul are you sure kunyi aikin nan da kyau, paul yace haba sir ko ka mance ni na halaka chief of staff balle wani Haidar karamin kwaro, ai kawai yana isa soldiers zasu bi bayansa a bincike sa,.
"Admiral yayi dariya yace" Captain AA this is your end. Paul ya sheke da dariya ya sara ma Admiral, daga na suka wuce paul na binsa a baya kafin cheif security dinsa ya karaso yana sara masa.

"Saida ya biya wani store ya danyi minor shopping dangin su coffee da sauransu kafinnya nufo gida.... " Tun daga Main gate yaga navys kota ina an kewaye, fannin en securities, sosai abun ya basa mamaki kafin kaga haka sai wani gagarumin abu ya faru, bai gama shan mamaki ba saida ya iso cikin building dinsu dan ko ina securities ne ana bincike, yana gama parking ya fito.... " Daga nesa Admiral ya fara nunasa cikin zafin rai ga hawaye na bin kuncinsa yake fadin, there he is, arrest him, arrest him he's a murder, he killed her he killed my only daughter..... gaba daya Haidar be fahimci abunda Admiral ke fada ba, ganin Admiral gadan gadan ya nufosa yasa akayi arresting Haidar " you're under arrest sir..... " da mamaki Haidar ke binsu da kallo kafin yace, what do you mean I'm under arrest, this is ridiculous, out of my way. 'Kin matsawa sukayi saima dada arresting dinsa da sukayi daya daga ciki yace " muna zarginka da kisan 'yar Admiral ta baro hida jiya da daddare ta taho gidanka kwana, " tsaki Haidar ya buga snn yace thus is nonsense, will stop this stupid acquisition, "bindiga ya daura a 'keyar Haidar yace "am sorry Sir, but we need to check in your house..... " securitin ya shiga dagawa sauran hannu yana fadin " let's ho in... Haidar baice komai ba ya hangi Admiral yana tsaye can gefe an daddafesa, girgiza kai yayi yasaka key ya bude gidansa, nan aka shiga bincike ta ko ina, har sun fito suna girgiza kai ba komai, dayan yace " are you sure you search everywhere, no Sir except the bathroom, oya go in and serch.... bathroom din dakin Hanifa suka fara dubawa babu komai, suka duba na daya dakin ma babu, ana shiga na Haidar aka ga gawan Latifa cikin bathtub an cika da ruwa, har ta soma kumbura.... da sauri suka fiyo suna fadin " we found her death body in there...... " A zabure Haidar ya mike ya nufi cikin bathroom din, ji yayi 'kafarsa ta kasa daukarsa, innalillahi wa inna'ilaihirra ji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifli khairan min ha.... abunda Haidar ya iya fadi knn, Admiral kuwa wani 'kara ya sake yana fa'din a barsa yazo ya sha'ke Haidar....
" Handcuffs aka saka wa Haidar wanda ya koma tamkar mutum mutumi, meyake shirin faruwa dashi, meyasa baya kyutawa mutanen da suke kyauta masa, meyasa haka, Allah sarki Latifa wa ya mata wnn kisan gillan, tana da matsayi a raywarsa, ko babu komai ta nuna masa 'kauna, daya sani da ya saurareta a daren jiya.... sisiriyan hawaye ya sauko daga idonsa, ha'kika yaji zafin mutuwan Latifa..... " You have the right to remain silent, duk abunda ka fada zai iya zama hujja a gaban al'kali, cewan daya security din... " Admiral ya shako wuyan Haidar yana fadin " tell me me ta maka me ta maka ka kasheta, koda yake kayi furucin sai ka kasheta a gaban kowa last week, saboda kawai tace ta daina sonka ta daina kwana da kai shine ka za'bi rabani da gudan jini na, you won't escape the law Captain,.... "Haidar kam baisan sanda ya soma fa'din yes " ni na kasheta I killed her I'm a murder..... "Admiral ya juyo yana fadin kunji ko kunajinsa ko shine... take him away... nan aka dauki Haidar aka tafi dashi....

"A gajiye suka iso garin Kaduna, ta rasa dalilin dayasa gabanta keta fa'duwa, koda Ajmal ya dawo daga islamiya ma ba kaman yanda suka saba wasa ta masa ba, haka uncle Faruq, uncle Faruq yafi ala'kanta hakan da matsalolin da take fuskanta, dan haka ya gargadi Anty Hiba kar ta takurata da wani maganganun da zai rinka sata damuwa, haka a ranar dai Hanifa tankwana duk bata jin da'di, ga wani mummunan mafarkin da tayi da yaHaidar, haka tayita farkwa cikin dare, karshe dai mi'kewa tayi ta shiga jero nafilfili...

"Fitowansa knn daga wanka yana shiryawa wayarsa ta shiga ringing, gajeran ysaki yayi kafin ya 'karasa ya daga wayan, yana fadin navy ya akayi.. daga daya bangaren me maganan yace " sir kaji abumda ya faru da friend dinka kuwa, Aisar yace which of my friends, Captain AA mana he was arrested yesterday, an kamasa da laifin kisan 'yar Admiral..... " Aisar bai gama jin abunda yake cewa ba dan ji yayi kaman wasan yara, wait navy are you sure of what you saying,
"Am very sure sir, ka kalli news anjima ko ka saya news paper zaka gani.... salati kawai Aisar yake baisan sanda yayi jifa da wayan ba ya shiga 'kwala kirawa mum dinsa..

"Mum na zaune a parlor Aisar ya diro mata ka daga shi sai towel, gaba daya mum ta razana ta mike tana fadin lafiya kai kuma Aisar what's all this, yaushe zaka girma ka daina yawi da towel cikin gida.... " hanunta Aisar ya rike yana girgiza kai yake fadin mum " we need to leave, we need to go back to lag.... " har hutun naka ya kare I thought 1 week ka dauka, noo mum mu tafi babu lafiya... wai meke fatuwa ne Aisar, Mum sunyi sharri wa abokina sun kulla masa... Aisar will you put your self together and spell it out, Mum wai Haidar ya kashe Latifa, amma nasan wnn 'karya ne, Aliyu will never do that, kawai anaso ayi Framing dinsa ne.
"Salati mum ta hauyi tana fadin " ko ni nan bazan ta'ba yarda ba wnn yari mai hankali wanda yayi sanadiyan shirya tsakanin ka da dad dinka, kai wnn sharri ne aka 'kulla masa, maza saka kaya ka tafi ka sayo mana tickets. Aisar yace yeah mum right the way.... a sittin Aisar ya gama komai ya fice daga gudan...

"Misalin 9:am, Sumy ta shigo parlorn Abba nan ta tarae da iyayen nata suna breakfast kaman yanda suka saba snn ta gaishesu, Abba na murmushi yace my princess come and have some, murmushi tayi irin yanzu an girman nan an daina shagwa 'ba wa Abba, ta dan lagabe kai tace yanzu na gama ci Abba, sch zani inda 10 to 12, Abba yace toh my princess Harunan yazo, daga masa kai tayi tace eh Abba, Abba yace you sound sad my princess, akwai wani abu ne, " ta langabe kai tace no Abba, Abba yace tell me idan akwai kinsan yanzu dole na baki spcl kulawa dan hidan an watse an barmun ke, murmushi tayi tace Abba is just that am missing Hany so much, murmushi Abba yayi yace that's natural dear ai ba jimawa zagayi ba, just two weeks kawai zatayi.... mamy dai sai murmushi kawai take.... " News din da aka soma ne na labarun karfe taran safiya a AIT yasa gaba daya suka maida hankali can.... innalillahi wa inna lilaihirraji'un... mene wnn ake fada, wani kara Sumy ta sake ta zube kasa, mamy kam sumewa itama tayi a wajen.... Abba ne kawai me kardin hali ya shiga neman ruwa yana yayyafa masu, ihun da Sumy tayi yasa Inna fitowa babu shiri.... har lokacin ba'a daina nuno news din ba, ganin Haidar an daure hanunsa yasa Inna ta soma fahimtan meke faruwa dan ba turanci take fahimta ba....
"Habubakar meke faruwa, menene wnn suke fada, me ya kawo Ali cikin tv... Abba ya share kwallan da ya zubo masa ya rike Inna ya zaunar da ita saman kujera, yayinda Sumy ta rungume mamy tana ci gaba da kuka take fadin, " mamy wllhi wnn karya ne, Abba karya suke wllhi, yaHaidar bazai iya kashe muyum haka ba da zalunci, Abba kar kabari su kashesa.... nan fah inna ta fahimce komai.... haba basai ta mike ta hau zagagye parlorn tana salati tana kuka, hankalin Abba ya kuma tashi shi ka'dai ysakanin mata uku, haka aka wuni a hidan jigum jigum kaman gidan makoki, wasu daga cikin relatives dinsu da sukaji abunda ya auku a news nan fa aka soma yururwan zuwa jaje wasu suna waya, mamy kam ko iya daga waya batayi...

" Tunda wuri sukaji labarin amma suka kasa sanar da ita, gaba daya Hanifa ta rasa gane Anty Hiba da uncle faruq, wata zuciya taxe 'kila tausayinki suke, haka suka wuni basu bari taji labarin ba, koda Anty Hiba tayi waya da mamy, mamyn ma cewa tayi karta fa'dawa Hanifa tukunna

👸🏻Queen Samy😍💄💋........
[5/21, 5:49 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
63

"Isowarsu garin Apapa knn kai tsaye ya wuce ofishinsu, koda ya bu'kaci ganin Haidar sai ce masa akayi an tafi dashi prison sakamakon amsa laifinsa da yayi, Alkali ya yanke masa watanni uku a gidan yari kafin a shiga kotu a gabatar da shari'a, sosai hankalin Aisar ya tashi, yana fita bai zarce ko ina ba sai prison, nan aka shiga aka sanarwa Haidar yana da visitor....

"Kallo daya Haidar ya masa ya watsar, ko zama beyi ba yace " what are you doing here?, Aisar ya kallesa cike da tausayi kafin yace ka zauna pls Haidar, saida ya 'dau lokaci kaman bazai zauna ba sai kuma ya zauna a kujera me fuskantan na Aisar gamida kauda kai gefe, shiru ne ya biyo baya kaman babu wanda zaiyi magana cikinsu, Aisar dai gaba daya kallon Haidar yake da mugun mamaki he just couldn't believe it wai Captain AA ne sanye da uniform din prisoners instead of uniform din Nigerian Navy,...... " Would you mind telling me what the heck brought you here, muryan Haidar ya dawo dashi daga duniyan tunanin da ya tafi.
"Aliyu me kake tunanin kayi for goodness sake, how could you so stupid, meyasa zaka amsa laifin daba kai kayi, haba Haidar after all kasan hukuncin wanda yayi kisa bisa ganganci da son rai cikinmu, you perfectly know that Sentence din death ne, why Haidar why..... " Enough! Haidar ya dakatar dashi, " don't you believe it, ni na kasheta I killed her, this is obvious, ko ka mance nayi wnn furucin a kofar office dinmu, in front of everyone. And her body was found in my house right.
"No Haidar koda zaka shekara kana fada mun haka I'll never believe that, wllhi ba kai ka kasheta ba, somebody frame you I knw that.
"Well believe it or not, I'm guilty. Ya yun'kura zai mi'ke Aisar ya riko hanunsa yana girgiza kai, no Haidar pls tell wa kake tunanin yayi framing dinka pls Haidar ka fada mun, don't ruin your own life just like this,
"Murmushin takaici Haidar yayi kafin yace" which life are you talking about dude, remember I have nothing left in this miserable life of mine, I lost everything, my parents and the love of my life Haneefah, so ina me shawartakan don't waste your sympathy on me, I got what I deserve. Daga haka ya mi'ke wani ganduroba yazo ya wuce dashi cikin cell.
"Mutuwan zaune Aisar yayi a wajen ya jima yana zaune kafin ya tashi ya tafi jiki a mace.

*********************************************
"Abban Haidar dan Allah kasa baki a magana nan, ya kamata musan wani hali Haidar ke ciki, mamy ta fadi hankali tashe.
"Abba ya ajiye spoon din hanunsa yace" tuni na cire Haidar cikin iyalaina ko kin mance ne, babu wanda zai taka wajensa cikin iyalai na, ai gashi kina ji a news yayi confessing yace shi yayi laifin, dama budurwasa ce ta saba kwana a gidansa, itama ta gaji dashi ta daina kwana shine ya kasheta sabida son zuciya, toh akan me ni kuma zan saka baki na, itama yarinyar tanada iyaye dole suso kar'ba mata hakkinta, ni ba hanuna cikin wnn al'amari yaje can ya 'karata." Mamy tace nifa gaskiya ban yarda Haidar zai aikata haka ba ya kamata a bincik a duba lamarin. Abba baice komai ba sai mikewa da yayi ya haye samansa, nan hawaye ya shiga sau'ka daga idanun mamy.
"Yau kusan sati guda knn da faruwan wnn al'amari, Abba ya hana kowa zuwa lag duba Haidar, harta Saif Abba ya hanasa zuwa, gaba daya family din sun shiga wani irin yanayi na 'kuncin rayuwa.

"Anty Hiba da Uncle Faruq ne zaune a dan madaidaicin parlorn su suna tattauna lamarin, Ajmal da Hanifa basa nan Hanifa ta kaisa islamiya dashike kisa dasu ne babu nisa.
"Uncle Faruq yace nifa inaga gwara a fa'da wa Hanifa halin da ake ciki kinsan eventually zata sani dole, Anty Hiba ta sau'ke ajiyan zuciya tace gaskiya ne nima tunanin da nake knn, tunda dai dole zata sani yafi a gaya mata, ku, a maybe idan ita Hanfar ta yafewa Haidar kila a samu Abba ya sau'ko.... sallaman Hanifa ne ya dakatar dasu, ta karaso ta gaishesu tana zama bisa sofa me zaman muyum 'daya. Uncle Faruq ya mike yana mata wasa da zolaya *Matar Navy* sunan da yake kiranta knn) kai uncle wllhi ko dadi fa sunan nan babu, Uncle Faruq ya fice yana mirmushi.
"Anty Hiba tace Hanifa akwai maganar da nake so muyi, " Hanifa ta gyara zama gamida cire hijabin jikinta dan taji Antyn nata sounds serious.
"Hanifa kina son Haidar pls just tell me truth, kar ki 'boye mun komai, be honest with me knji.
"Shiru Hanifa tayi sai bugawa da 'kirjinta keyi da sauri da sauri, kallon 'kasa kawai take tama kasa 'dago idanunta, nan da nan hawaye suka cika idanunta..
"Anty Hiba ta taso daga kijeran da take ta dawo kusa da Hanifa ta ri'ko 'yan ytsun hanunta tace " I know exactly how you're feeling right now, na sani this is hard for you, but I just wanna know if you really love him,
"Girgiza kai Hanifa ta shiga yi tana fa'din, " Anty I never loved him, I don't love yaHaidar, bana sonsa ko ka'dan Anty.
"Anty Hiba ta gyada kai tace shiknn ki daina kuka pls, na yarda baki sonsa,
"Ta goge hawayen idanunta kafin tace Anty meyasa kika tambaya.
"Anty Hiba tace" Hanifa the truth is that Haidar ya fa'da cikin mummunan jarabawa, gaban Hanifa ya fadi rass tana sauraren me Anty Hiba zata ce. Anty Hiba taci gaba da fadin, "Haidar was arrested last week, ana zarginsa da kisan wata budurwa. In ta'kaice maki zance Haidar ya amsa laifinsa, amma dukanmu bamu yarda zai aikata haka ba, snn Abba yace bashi ba Haidar tun kan abunda yayi maki, pls ki yafewa Haidar ko Abba zai yafe masa la'alla Haidar ya sami sau'ki cikin lamuransa....... "Tashin hankali gobaran gemu, innalillahi wa inna ilaihirraji'un..... gaba daya Hanifa tama rasa me take saurare da bakin Anty Hiba... kaman wacce aka zabura haka ta mi'ke, Anty Hiba ta ri'kota tana fadin ina zaki Hanifa.... " take hawaye suka shiga ambaliya a fuskanta tana fadin, " wajen yaHaidar zanje Anty, I really want to see him, wllhi 'karya ake masa Anty, wllhi bazai yi kisa haka kawai ba..... rungumeta Anty Hiba tayi tana fadin" calm down Hanifa, ya isa ki tsai da hankalinki waje guda.... kuka sosai Hanifa keyi tana fadin" dan Allah ki kaini na gansa inason sanin wani hali yake ciki, dan Allah ki kaini Anty kar ku kashesa nima mutuwa zanyi..... "Sosai hankalin Anty Hiba ya tashi har tayi da ta sanin sanarwa Hanifa, dan wuni tayi tana kuka ta'ki cin komai sai kuka kawai take yi, babu ywnda uncle faruq da Anty Hiba basuyi ba sun kwantarwa Hanifa hankali abu ya'kici ya'ki tura, a ranar haka tayi kwana zaune tana abu daya kuka tana tuno Haidar.
"Washe gari suka zo Kano, mamy ce suka soma haduwa da ita, mamy tana ganin yanayin Hanifa da ita kanta Anty Hiban harma da Uncle Faruq din ta gane akwai matsala.... da gudu Hanifa ta haye jikin mamy tana kuka me tsuma zuciya, itama mamyn kuka ne ya kifce mata.
"Haka illahirin mutan gidan suketa faman kuka harda inna da

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login