Showing 39001 words to 42000 words out of 114964 words
ya kwanta ya rufa bargo. Tana nan a dur'kushe a wajen har bacci ya 'dauke ta.... can ya farka ya ganta a haka, gajeren tsaki yayi ya mi'ke ya fice.
"Bayan motansa yaje ya bude ya 'dauko T shirt na kakin soji sabo fil da shi snn ya dawo dakin, 'dagota yayi ya dawo da ita kan gado ya shiga 'ko'karin canza mata kayan, aiko nan ta bu'de ido, da sauri ta mi'ke tana kare 'kirjinta da hannunta.
"Hissing yayi yace " meye kike karewa a nan, me kike da shi, ki bar wahalar da kanki yarinya am not interested. Ya jefa mata rigar yace gashi idan kinga dama kisa ba don halinki ba. Daga haka ya koma yayi kwanciyarsa.
"Mi'kewa tayi tace a ranta " whatever kaikaji wajen, ni nace maka ka saka min wani kaya. 'Daukan rigar tayi ta shiga juyawa ta ta'be baki ta mi'ke ta nufi bathroom ta canza.
"Da san'da ta fito wai kar yaji motsinta ya kalleta, aiko duk bata sani ba idonsa kyam a kanta, rigar yayi mata kyau sosai, ya sau'ko mata har cinyanta snn ya 'dan kamata ta 'kasa kasancewar t shirt din kaman body hook na maza yake. Kalan kakin sosai ya mata kyau, ta ha'de gashinta tsakiyan kanta. Yanda take san'dan yaso basa dariya. Kwanciya tayi bisa rug ta ta'kure saida ya bari tayi nisa da bacci snn ya dauko ta ya azata bisa gadon ya eufa masu bargo. Rungumeta yayi sosai cikin 'kirjinsa, a haka suka samu bacci mai da'din gaske....
" 'karfe 10:13 am su Sady Sumy Lailo da Jesmy ne suka shigo gidan sun fito daga gidan amarya Shema dan a can suka kwana dashike yau ne wunin biki, sashen mamy suka nufa suka gaisheta, nan suka shiga tambayan Hanifa.
"Mamy tace ku dubata can sashen Inna mana, Sady tace bata can fa mamy, kila tana sashen yaHaidar pls ki dan kirasa a waya mamy, zamu koma gidan Shema ne an barta ita ka'dai kuma 11:00am za a fara bu'dan kai 'din.
"Anty Hiba ne ta shigo tana fa'din barin kira Haidar din.... ringing biyu ya 'daga lokacin ya tusa Hanifa a gaba sai taci breakfast.
"my Anty good morning.
"Morning 'dan gida na, ina kuka shiga ne kam su Sadiya nata jiran Hanifa su tafi bu'dan kai, kuma kaima you suppose to show up a bud'an kai 'din.
"Mugun kallo ya watsa wa Hanifa kafin yace "Anty nifa banson event me maza su tafi kawai ita bazata je ba.
"Haba Haidar kan me zaka hanata, pls ka kyaleta ta fito ta shirya.
"Shiru yayi kaman bazaice komai ba sai kuma yace "Ok fine shiknn Anty.
"Yawwa 'dan gidana Anty Hiba tace.
"Yana gama wayan ya watsa ma Hanifa mugun kallo ya mi'ke ya zari carkey yace tashi mu tafi, da sauri ta mi'ke harda 'dan murmushinta suka fice.
"Suna isowa gida ya ska lock ma motan ya kalleta yace, kina jina wllhi kika kuskura na sake ganin ki cikin maza saikinga abimda zan miki, kuma saura kar ki rufe jikinki kiga yanda zanyi dake. Ya bu'de lock din, har tasa kai ta fita yace zo nan, dawowa tayinta tsaya
"Kije ki shirya ki fito, kanta tayi nodding kananta wuce, side dinsa shima ya wuce dan shiryawa.
"Tana shiga ta shirya ta samu already su Sumy sun tafi, saida ya jima a wajen Abba kafin ya fito ya samu Hanifa a sashen mamy ta ha'de rai, aiko nan mamy ta shiga masa sababi kan me zai bar Hanifa tana ta jira.
"Mamy na tsaya magana da Abba ne kinsan jibi zamu wuce, kuma yace mun 'kila ya tafi Abuja gobe.
"Mamy tayi 'kwafa ta kalli Hanifa tace tashi ku tafi.
"Sai snn ya watsa wa Hanifa mugun kallo irin na _Zaki gane kuren ki_ kafin ya wuce waje abunsa.
"Har suka isa gidan baice mata komai ba, safe din jikin motan ya bu'de ya ciro bunch din 'yan dari biyu ya jefa mata kan cinyarta. Fita shim yayi ya isa wajen sai kirari kuwa maroka ke masa nan yayi 'barin ku'di wa amarya da ango.
"Su Sady Jesmy sai zolayanta suke wai isowan mr mrs daban ne, wai kalannnasu soyayyan daban ne. Lailo tace kai friend mijin nan naki akwai kishi, daga dita filin rawa sai ya suri matarsa ya gudu.
"Ta'be baki Hany tayi tace kwaji dashi dai ni mu 'karasa naga Shema ta.... nan suka 'karasa filin suna dariyan Hanifa.
"Washi garin gama biki su Jesmin suka wuce KT bayan mamy ta cikasu da kayan arziki da tsaraban biki iri da kala. Randa su Hanifa zasu tafi kuka tayi tayi wai ita bazata tafi ba. Wnn karan kam ko mamyn nata bata bi bayanta ba, haka suka rabu da 'yan uwanta suna kewan juna, har airport su mamy dasu Sady suka rakata harda Inna, bayan Inna ta ha'da mata shirgin su kuka garin kunu da sauransu, haka jirgin su ta daga zuwa birnin ikko, tan cike da kewan 'yan uwanta masu 'kaunanta....
👸🏻Queen Samy😍💄💋.......
[5/21, 2:01 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
40
"Da yamma lis suka isa garin Apapa, kai tsaye Tinkan island suka wuce yanda suka yada zango a gidansu dake Maritime. Sosai ta gaji saikace wacce tayi tafia by road, shima Haidar a gajiye ya shige yayi wanka.
"Kitchen ta wuce ta zazzage kayan da inna ta bata, kallon shirgin tayi ta 'dn ta'be baki, a fili tace ko Inna ta 'dauka girki nake a nan gidan da zata hada mun wanga shirgi tab ina zan iya wnn aikin wahalan dan cikina ni ka'dai.
"Fridge ta bu'de ta sami bread ta shafa butter ta dan soya kwai scotch, ta yanka veges ta zuba bisa bread din bayan ta saka scotch egg din snn ta zuba ketchup akai, wow yummy😋, parlour ta dawo ta zauna tana cin sandwich dinta tana sipping chill drink dinta. Saida tayi nak kafin Haidar ya fito, as usual sai wani 'daure fuska yake ya dubeta da gefen ido baice mata ci kanki ba itama bata tankasa ba.
" 'kanshi duk ya cika masa ciki, tana mi'kewa ya bita da kallon mamaki, shida gidansa amma ayi girki a hanasa. Wata zuciya tace yanzu 'yar wnn yarinyar ma har ta iya dafa abincin da mutum zaici, sai jagwalgwalo. Ta'be baki yayi a fili ya furta "irritating. Mi'kewa yayi ya fice ya nufi eatery dake cikin maritime. Yaci abincinsa dukda ba wani cin kirki ne dashi ba tun asali haka nan yake bai faye cin abinci ba, tun yana yaro ya'kinsa da mamy knn. Yana gama ci ya mi'ke yana 'ko'karin neman layin Aisar, ya kira yafi sau biyar be 'daga ba.
"Yana gama parking motarsa a parking lot kurtayen da suke 'karamin gate dinsu suka shiga zuwa kwasan gaisuwa. Nan Haidar ya tambayesu ko Aisar na nan, dan yaga gadai motarsa but baya daga waya.
" daya daga cikin masu gadin yace, Captain the truth is that we were worried too, tun safe Captain Aisar bai fito ba.ko office beje ba.
"Haidar ya gyada kai yace, and what time did he came back last night?,
"Very late, and drunk.
"Haidar yayi nodding kansa kana yace, it's Ok I'll check on him right the way.
"Sara masa suka yi kafin suka koma bakin aikinsu. Sandarewa yayi ya furta " Carry on....
"Ya jima yana knocking a door step din Aisar amma shiru ba'a bu'de ba, har zai juya sai kuma wata zuciya tace ka murda handle din kaji ko a bude ne, aiko yana murdawa 'kofa ta budu.
"Da gudu ya 'karasa ganin Aisar kwance cikin kwalaben giya kaman baya numfashi." A saba'in ya fito yana ma securities din magana " call an ambulance, hurryyyyy...., komawa yayi ya shiga danna 'kirjin Aisar, yana kiran sunansa, amma shiru. Haidar ya 'daukosa a kafa'da suka sau'ko 'kasa, daidai nan ambulance ta iso, suka saka Aisar a baya aka daura masa na'urori dan ceto rayuwansa.
"Dr ya fito ya samu Haidar yace "you can go in now.. da sauri Haidar ya mi'ke ya nufi 'dakin, kwance yaga Aisar bisa gadon hawaye na bin 'kuncinsa, Haidar ya 'karasa gamida ri'ke hannun Aisar yace" how you feeling now.
"Murmushi Aisar yayi yace " feeling better.
"Haidar, Aisar ya kira sunansa, dago kai Haidar yayi yana kallonsa.
"Thank you, Aisar ya fadi, thank you for saving my life Captain.
"Murmushi Haidar yayi yace, this is our duty captain mu tsare al'umma da dukiyansu, I suppose you know that. So pls stop thinking me you making feel nervous. The important thing is that you're alive. Dan haka dukkan godiya ma Allah zamuyi shi.
"Nodding kansa Aisar yayi yace" haka ne Captain, Allah shine abun godiya, dan da na mutu a daren jiya da bansan ina ne makomata ba.
"Cikin rashin gane last statement din Aisar na karshe Haidar yace, "Aisar duk abinda ya samemu tawakkali shine first, shan giya ba komai zai mana ba ha'ki'ka turawan yamma sun cuce mu, ta hanyar sabar mana da shan giya da sukayi.
"Idan rai ya 'baci memakon mu kai kukan mu ga Allah sai mu rungumi giya muna sha, a tunanin mu shine zai calming temper dinmu, which not. Na sani nima drunker ne, but ever since danayi realizing giya bata da wani alfanu na daina sha.
"Ya ri'ke hannun Aisar sosai kafin yaci gaba da fa'din, " it's obvious yanayin aikinmu shi yayi influencing most of our Colliques suka zama mashaya giya including me. So pls ka nutsu ka daina making life dinka so miserable.
"Aisar ya gyada kansa yace " you're right Haidar, shan giyan da nayi jiya it was never my intention, I was so depressed that I couldn't help it, shiyasa na sha giyan da yafi 'karfin tunanin mutum.
"Haidar ya ri'ke hannayen Aisar yace, am like your bro, when ever you need someone to talk to , don't hesitate to talk to me, just feel free with me, I promise I'll listen to you and i'll share my advice with you.
"Thank you Haidar, I suppose you need know what am really going through. "Ya dan ja fasali kafin ya soma fadin, " am having a hard time with my dad, he never understood me. Burin shi a kullum ta ina zai sami haram kota halin 'ka'ka ne, Haidar is my duty to protect dukiyan 'kasar nan, I can't say back watching him tempering da dukiyan al'ummah. Matsalan 'daya shine mum 'dina tana matu'kar sonsa, I always want to be by her side ko ka'dan banson barinta da mutumin nan, dan kuwa tun ina yaro nake ganinsa always yelling at her, always mistreating her like piece of trash, it hurts me a lot and makes me furious. Ita kuma mum bata son ina medling in to their marital problems, inayi dan ita ne but ko kadan bata so. And idan nayi reporting dinsa ko nayi arresting dinsa zan iya samu matsala da ita.. wann shine dalilin da yasa nake kau da idona... precisely I can't deny that he's my father, though he always neglected me. but I still want to fix my relationship with him ko dan mahaifiya ta.
"Sau'ke ajiyan zuciya Haidar yayi kafin yace " I do understand you friend, ka kwantar da hankalinka everything is gonna be alright, ka ci gaba da masa addu'a komai zai zama normal.... daidai nan Dr ya shigo, kallonsu yayi da murmushi saman fuskansa ya sara masu, murmushi suma sukayi kafin Dr yace, " Captain how you feeling now, murmushi Aisar yayi yace " I fine now, I suppose I'll be discharge.
"Don't rush Navy, Haidar ya fa'di yana kallon Aisar. Dubashi Dr yayi snn yayi discharging dinsa, hadi da basa shawarwari.
"Motan Haidar suka shiga ya soma driving, duk a tunanin Aisar gida suka nufa amma sai yaga Haidar ya dauki hanyar gidansu, da mamaki Aisar ke kallonsa kafin yace ina kuma zamuje.
"Just wait n see, Haidar ya fadi sanda ya karyi kwanan street din gidansu Aisar.
"Tun daga gate suke ganin masu irin uniform dinsu, da alama securities din Naval chief of Staff ne, Aisar ya 'bata fuska yace you see the big devil is here. Tare suke satan man petur suke fitarwa 'kasashen waje.
"Haidar ya jinjina kai yace let's get in. Suna fitowa Sojojin suka shiga sara masu su kuwa suna sandarewa. (Wow gaskiya soji sun ha'du inji Samy😜)
"Suna 'karasawa 'kofan parlourn NNPC chairman da Naval chief of staff suna fitowa, da mamaki dad din Latifa ke binsu da kallo, sara masa sukayi shima ya sara masu yana wata mayaudariyan murmushi, dad din Aisar kuwa ko kallo basu ishesa ba, ciga da tafiya sukayi haraban gidan saida sukayi nisa kafin Dad din Aisar ya dubi Dad din Latifa yace " kaga wnn tsinannen yaro am sure shi yake influencing Aisar ya rin'ka sa'ba umarnina, wata silent dariya dad din Latifa yayi kafin yace " 'kwarai kuwa dan kuwa yaron ni kaina ya tsaya mun a ma'koshi ya hanani ha'diyan ruwa yanda nake so, I really wan to get rid of him, he's beyond your imagination. Amma kar kaji komai da sannu zamu 'batar dashi shi 'din banza har nawa yake da zai hana mu sakata, mun gama da wa'enda suka fishi balle shi..... " dariya Dad din Aisar yayi yace shiyasa nake 'kara sonka abokina yanzu dai sai munyi waya.... nan suka yi sallama dad din Latifa ya tafi.
"Dad din Aisar na shigowa yaga sai hira Haidar da mum din Aisar suke, koda ya shigo Haidar ya gaishesa a da'kile ya amsa, ya juya yana ma Aisar kallon "what the heck brought you here.....
👸🏻Queen Samy😍💄💋......[5/21, 2:01 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
41
"Kallon Aisar Haidar yayi alamun ya gaida mahaifinsa, kafin Aisar yayi magana sukaji muryan dad dinsa yana fad'in "what the heck you think you'er doing here? I thought I've already made this clear to you, I don't want to see you in my house. Now leave before I go out of control.
"Mi'kewa Haidar yayi ya 'karasa gaban dad snn ya mi'ka masa takardan asibiti, kallon hadarin kaji dad yake ma Haidar wanda yayi matu'kar tunzurasa dan babu abunda soja ya tsana kaman raini musamman daga civilian, dabadon yana ganin kiman Aisar ba da kuma yana girmama duk wanda ya fisa a haife da yau mutumin nan ya gane kuransa ba tare da la'akari da mu'kaminsa a gwamnati ba.
"Haidar ya ha'de hannayensa ta bayan hanunsa kafin yace " take a look of it pls sir, yana fa'di yana masa nuni da takardan hanunsa da 'kwayan idonsa.
"Gizo da Haidar ke dashi yasa jikin dad yayi sanyi ya kuma kasa masa musu, kallon takardan yayi ta'be baki kana ya nemi waje ya zauna.
"Haidar ya zauna snn ya soma magana cikin sigan yanda 'da ke magana da ubansa, " please sir you need to fix your relationship with your son, look how he became miserable, this is all because you neglected him, kar ka manta dad akwai ranan da zaka nemi 'danka dan kuwa ko wani mutum yanada rana ballantana 'dan da ka haifa. Wani yana neman ya samu amma be samu ba kai Allah ya baka is that how thank your lord, he lost your compassion and affection ever since he wsa a child, kayi forcing nasa ya zama soja even though beso hakan ba, and kar ka mance ko kaine doka ya hau kanka yanada right da zai hukunta ka, so pls sir I beg of try to fix your relationship with your son before it's too late for you.
"Shiru dad yayi dan Haidar gaba daya ya gana daure sa da kalamansa, mi'kewa Haidar yayi ya ta'ba kafa'dun Aisar yace "I'll take my leave friend, ka zauna ka kwana a gida for today, gya'da masa kai Aisar yayi kafin yayi sallama da mum ta bisa har waje tana sa masa albarka tana godiya.
"Yana dawowa gida a parlor ya zauna yana tunanin rayuwa, ha'ki'ka idan ka samu iyaye masu tsoron Allah wa'enda they're presentable wa'enda baka kyaman nunasu ma duniya kace mahaifanka ne abin godiya ne ma Allah, ha'ki'ka ya tausayawa Aisar da yanayin mahaifinsa.
"Haidar ya kwantar da kansa yana tunanin yanda ya nunawa iyayensa yayi biyayya na auren Hanifa zai ri'keta bisa gaskiya da amana, shin ya kyauta ma kansa knn by manipulating his parents, they all believed that zaman tsakani da Allah yake da Hanifa babu cutarwa, dafe kansa yayi ya furta " oh my Allah what have I done, am I doing the right thing? Oh what should I do, I don't love her, I don't even know if I can live with her like a husband and wife. Gajeren tsaki yayi ya mi'ke ya shige 'dakinsa.
"Washi gari tana zaune bisa dinning tana breakfast duk a tunaninta ya jima da fita office,