Showing 93001 words to 96000 words out of 114964 words

Chapter 32 - MIJIN HANEEFA Complete Hausa Novel

15 Oct 2024

13156

gobe insha Allah yaHaidar zai bar gidan yari, zai dawo mu ci gana da rayuwar mu tare, babu abunda zai kuma rabamu sai mutuwa, mutuwa ma rana 'daya zamuyi insha Allah.
"Inna ta murmusa tace" Oh yaran zamani baku kunyan nuna soyayya wa junanku, 'yar ba'do naga da ai cewa kikayi baki sonsa amma ni nasan kina sonsa dan jikan nawa 'daya ne tamkar ga dubu.
"Dariya Hanifa tayi tace kai Inna ai shima yana sona, a haka momma da Amal suka fito suka samesu aka ci gana da hira cikin jin da'di.
"A ranar Hanif kusan kwana tayi tana sallah tana ro'kon Allah ya wuce masu gaba cikin wnn shari'a, kai duk 'daukacin masoyan Haidar kusan hakan ne ta kasance dasu.
"A 'bangaren Sameer kuwa ya kira Aisar yafi abunda yafi amma Aisar bai daga ba, karshe ma kashe wayarsa yayi, sosai abun ya dami Sameer, Aisar kuwa ba ya'ki dagawa bane baisan abunda zaice wa Sameer ba.

"Washe gari da safe sun fito dan tafiya kotu sai ganin su Mamy dasu Sumy sukayi harda Abba a haraban gidan sunzo ashe tun jiya, da'di ne ya lullu'be su gaba daya, Hanifa ta 'karasa da gudu ta rungume mamy tace mamy dama zaku zo, mamy ta shafi duskanta tace " zamu zo daughter, Hanifa ta 'karasa wajen Abba tace "Abba ka yafe wa yaHaidar ne, Abba na murmushi ya shafi gefen fuskanta yace na yafe masa daughter na yafe masa duniya da lahira, rungume Abba tayi tana hawaye, kowa a wajen saida ya zubda 'kwalla. Gaisawa akayi gaba daya tare da addu'an samun nasara.
"Sameer ya dubi agogon hanunsa yace "let's get going kar muyi latti.
"Haka suka jera motocin gaba daya suka wuce kotu...

👸🏻Queen Samy😍💄💋...........
[5/21, 10:33 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
74

"Sameer ne tsaye a bakin kotu sai kai komo yake yana jiran isowan Aisar, amma shiru Aisar be iso ba, ya ciro wayansa yayi dialing no din Aisar yajita a kashe, a hankali ya furta "ya Allah gamu gareka, mutane kuwa sai kai komo suke ana jiran isowan Al'kali, motocin alfarma ne suka sako kai cikin kotun, " Chief of defense staff ne ya samu hallarowa, ( ni samy nace lallai yau shari'an ta manya ce) isowansa yayi daidai da isowan " Naval chief of staff tare da amininsa NNPC National Chairman. Gaba daya suka nufi Chief of Defense Staff. General LA Kaita dan mi'ka gaisuwansu. "Admiral ya sara ma Chief of Defense shima sara masa yayi nan yayi masa ta'aziya na rashin 'diyarsa da yayi, daga haka bai kuma cewa komai ba ya nufi cikin kotu tare da securities dinsa, nan suma suka rufa masa baya da nasu securities din.
"Sameer ya dafe kansa yana duba agogon hanunsa, har juya kawai zai shige kotu ya hangi motan Aisar, ai tun bai gama parking ba Sameer ya isa wajen yana tambayamsa lafiya.
"Aisar ya gama parking snn ya fito, kallonsa kawai Sameer keyi dan gaba daya he don't look him self, definitely something is wrong. Mi'ka masa hanu Sameer yayi bayan sun gaisa yace "haba Navy I've calling you tun jiya, baka dauka snn baka kirani daga baya ba, karshe ma wayar naka a kashe. Meke faruwa Aisar
"Aisar ya fuzar da iska yace "Barrister komai ma ya faru, I'm lost Sameer I don't what to do.
"Sameer yace " don't be panic navy, nasara na tare damu da izinin Allah, daga yau komai ya zama tarihi, yanzu ina laptop din naka ina fata kazo mana da information na CCTV camera din( security camera) na ranar da abun ya faru cikin maritime, dan hakan ne kawai zai tabbatar mana da wa'enda suka shiga gidan Haidar a daren, idan ma Latifa ne ta shiga da 'kafarta CCTV will show, hakan idan wasu ne suka shiga zai nuna.
"Aisar ya 'dago yana duban Sameer kafin yace " Sameer komai ya jagule batun CCTV anyi hiking 'dinsu gaba 'daya ranar sun daina aiki...... Ai bai 'karasa fa'da ba Sameer yace " What! Innalillahi wa inna'ilaihirra ji'un, this our last hope, haba Aisar meyasa baka kirani tun jiya ka sanar dani ba, bayan nayi statement a prosecution office kan cewa yau zamu kawo wnn video din, ya salam komai ya jagule.
"Aisar ya fuzar da iska sanda idanunsa suka ka'da sukayi ja mum 'dimsa kawai yake tunowa da 'kyar ya iya bu'de baki snn yace" that's why inaga bazan tsaya a shari'an nan ba, I won't show up kawai zan tafi....." Girgiza kai Sameer yayi kafin yace " no you don't have to that, zo muje Allah na tare damu, testimony dinka da na Hanifa zai mana amfani. Haka Aisar yabi bayan Sameer kaman ra'kumi da akala.

***********************
"Ta ko ta ina securities ne suka kewaye gidan, wnn duk aikin Cheif of Defense ne, yayi haka ba tare da sanin Naval cheif of staff ba, gaba daya asalin securities masu gadin gidan yasa aka bu'desu da hodan ibilis, snn yasa nashi securities din su saka uniform din securities din Admiral, dan haka koda Admiral ya fiti dan tafiya kotu bai fahimci komai ba,.
"A hankali suka sa kai cikin gidan suka shiga gudanar da bincike, 'kofa bayan 'kofa suke bincikensu, ma'aikatan gidan gaba 'daya suka kama suka kulle a store.
"Dakin da mum din Latifa take suka fara buga 'kofan, haba nan fah hankalin Lawo ya tashi, a sttin ya dauki mum din Latifa ya azata a kafa'da yana neman hanyan warewa😂.

*****************************
"Kotu ta cika ma'kil ana jiran shigowan Al'kali, Al'kali yana shigowa aka mi'ke tsaye gaba 'daya, bayan Al'kali ya zauna kowa ya koma ya zauna, nan Al'kali ya bu'ci a shigo da wanda ake tuhuma.
"Hannunsa daure cikin handcuffs ya tsaya cikin akulkin tuhuman, idanunsa yau sun gane masa mutane masu tarin yawa mutanen da beyi tsammanim ganinsu a shari'an ba, ciki kuwa harda mahaifinsa da Chief of Defense Staff, idanunsa suka kada sukayi ja sanda suka hada ido da Abba, girgiza masa kai yayi alamun be strong, haka mamy ma, haka cheif of defense ma jinjina ya masa daga yanda yake zaune kan don't give up. " yana sau'ke idonsa kan Hanifah 'kwalla yagani tab a idanun nata, girgiza mata kai yayi yana mirmushi, itama murmushin tayi ta kwantar da kanta bisa kafa'dun Inna.
"Aisar kuwa yana ganin Haidar bai bari sun ha'da ido ba yayi saurin sunkuyar da kansa 'kasa, kana ganin Aisar zaka iya gane he's in guilty conscious gaba daya ya kasa samun sukuni, ga zuciyansa dake bugawa da sauri da sauri.

"Nan fah aka soma gudanar da shari'a, Al'kali ya bu'kaci Barr Ridwan ya gabatar da shaidansa da yayi furucin zai gabatar, banda lugude babu abunda 'kirjin Sameer keyi, addu'an dake ta nanatawa cikin zuciyansa shi ya taimaka masa ya 'dan sami strength.
"Sameer ya fito gaban kotu gamida mi'ka godiya wa me shari'a, snn ya soma magana" ya me shari'a, gameda video na CCTV da nayi furuncin zai gabata a gaban kotu an samu akasin haka, CCTV cameras dasuke cikin Maritime gaba 'daya a wnn rana anyi hiking dinsu ma'ana an rufesu gaba daya sun daina aiki a wnn rana.
"Al'kali ya sunkuya yayi wasu rubutu, kafin ya 'dago ya duni Sameer yace " Barr Ridwan konada hujja ko shaida na cewa wnn cameras din a wnn rana basa aiki.
"Eh ya me shari'a inada shaidan da zai tabbatar da haka. Akwai Captain Aisar Hashim wanda shima daya ne daga cikin sojin ruwa shi zai tabbatar wa kotu haka.
"Al'kali yace idan Captain Hashim yana cikin wnn kotu, kotu tana bu'katan ganinsa.
"Da 'kyar Aisar ya mike ya nufi akulkin bada shaida, har lokacin ya kasa dago kai ya hada idi da Haidar. Ya dago ido da kyar sukayi ido hudu da Admiral, hannu Admiral yasa a wuyansa alamun idan yayi wani abu stupid a bakin ran mahaifiyarsa.
"Kaine Captain Aisar Hashim, muryan Al'kali ya dawo da Aisar.
" Eh nine ya me shari'a.
"Ko meye ala'kan ka da Wanda ake tuhuma.
"Abokina ne, kuma abokin aikina.
"Kaji abunda lawyern wand ake 'kara ya fadi akan ka kome zaka ce.
"Shiru Aisar yayi kaman bazaice komai ba..... ya dago yana duban Haidar cikin zuciyansa yake furta am sorry friend I never want it to be like this, but I have do this for my mum....... "kai muke saurare Captain miryan Al'kali ya dawo dashi daga duniyan tunani da ya tafi....." A'a ya me shari'a bani da tabbaci gameda abunda lawyern wanda ake 'kara yake fa'di....... "Innalillahi wa inna laihirra'ji'un Sameer mutuwan tsaye yayi yana kallon Aisar haka Haidar ma, they couldn't just believe it..... a guje Hanifa ta fito gaban kotu tana kuka take fa'din" Noooo no that's not true,. Pls Aisar don't do this, dan Allah ka fa'dawa kotu gaskiya.... "Al'kali ya buga desk yana fa'din" Silence, behave your self woman this is a court.... ina ko kula al'kali Hanifa batayi ba nan securities suka nufota inaaa ro'kon Aisar kawai take tana fadin ya fada gaskiya...... kannkace me ta fadi luuu a wajen... " wani wawan tsalle Haidar ya buga daga yanda yake yana fa'din " Haneeeeefahhhh, no no Haneeefah... nan securities suka 'karaso suka rirri'ke Haidar, mamy dasu Abba a tamanin suka nufota,...."Ran Al'kali idan yayi dubu...." tell your client to behave him self Barr Ridwan, this is court...."Sameer ya soma fadin am sorry your honor... Haidar kuwa cewa yake let me go and see my wife she's pregnant, let go of meee.." Sameer yayi saurin jan Haidar ya koma cikin akulikin tuhuma. Ya ha'da hannayensa biyu yana bawa Al'kali ha'kuri,
"Am sorry your honor, we didn't mean it, his wife is pregnant that's why she fainted.
"If his wife is pregnant she shouldn't have come here in the first place, you perfectly know the consequences Barrister.
"Sameer yace" I do apologies Your Honor....
"Al'kali ya buga benchi snn yace shari'a zata ci gaba daga yanda aka tsaya.
"Haidar gaba daya jijiyoyin jikimsa sun tashi idanuwanshi sunyi jazur fatan jikimsa kuwa ta koma jajazur, shi a halin yanzu ba takansa yake ba, no damuwan shi yasan wani hali Hanifa ke ciki.
"Admiral banda murmushi babu abunda yake, Aisar kuwa wani mugun kallo ya watsa wa Admiral zuciyansa naji kaman zata fashe.

"Suna fita asibiti madi kusa suka nufa da ita hankali a tashe, nan da nan likita ya kar'beta, mamy banda kuka babu abunda take yi, Abba na faman rarrashinsu ita da Inna dan gaba daya sun kasa ta'buka komai sai kuka.

"Sa'daf sa'daf ya fito ya hangi wata 'kofa a bu'de, a saba'in yasa kai zai wuce, sai ji yayi anyi pointing bindiga akansa ana fa'din surrender or I'll shoot, ai a tamanin Lawo yayi jifa da mum din Latifa zai arce " daya daga cikin sojojin yana fadin " freeze stop inaaa Lawo yasa kai... ji kake pammm an fasa kan Lawo. Da sauri suka karasa wajen aka dagasa,
"Mum din Latifa kuwa juyi ta soma yi kaman wata guguwa, can ta fadi gefe guda, su kansu sojojin nan saida abun ya razana su, wa'enda suka santa da farko arcewa sukayi niyyan yi dan a ganinsu fatalwa ce ta dawo, a iya saninsu ance masu ta jima da mutuwa sai gashi yau sun ganta da 'kafafunta, babban abun da yafi razanasu shine yanayinta ya canza gaba 'daya, gashin kanta duk ya damfare kaman dada, snn wasu jajayen kaya ne a jikinta, fatan jikinta kuwa duk ya tattare ya jeme.
"Securities suka rikota suka zaunar da ita, da farko ihu ta soma masu can sai ta soma fadin, ina Tanim kunkaini wajen sa na ro'keku.....

👸🏻Queen Samy😍💄💋.......
[5/21, 10:33 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
75

"A hankali komai yake dawowa mum din Latifa sanda suke tafe cikin mota, kuka take kaman ranta zai fita dan agabanta Tanimu ya kashe diyarasu, "Drivern mota gudu kawai yake shararawa dan akwai tazara sosai tsakanin gidan zuwa kotu.

"Barr Barnabas yaci gaba ds fa'din" ya me shari'a da wnn hujjoji da suka gabata a gaban kotu nake ro'kon wnn kotu me alfarma da ta yankewa captain AA irin hukumcin data dace dashi na gode ya me shari'a, daga haka ya koma ya zauna, Admiral kaman ya zuba ruwa a 'kasa yasha dan murna.
"Al'kali ya sunkuya yayi rubutu kafin ya 'dago kai ya soma fa'din" bisa ga hujjoji da suka gabata agaban kotu, da rashin ta'kamemmen hujja wanda zai tabbatar Captain AA bashi ya aikata laifin ba, snn a ranar 21 ga watan January captain AA ya amasa laifinsa cewa shi da kansa ya kashe marigayiya Latifa snn an samu gawanta a cikin gidan Captain Abubakar, dan haka wnn kotu me alfarma ta yanke wa Captain AA hukuncin 'daurin rai da rai ta hanyar rataya kaman yanda yazo a 'kundin tsarin mulki 1999........Admiral baisan sanda ya shiga sarawa barr Barnabas ba " inna lillahimwa inna'laihirra'jiun Sameer cire malfar kansa na lauyoyi kawai yayi Sady da Sumy rungume juna kawai sukayi suna kuka."Al'kali na shirin mikewa kawai sai ji sukayi an bu'de 'kofan kotu......" Jikin Admiral ya 'dauki karkarwa haka su Dad din Aisar da duk wanda yasan mum din Latifa...." jiki na 'bari Admiral ya isa gabanta yana fadin "ke wayace ki fito waya dawo dake wnn duniyan..." Aifa kallo ya koma kansu," mum din Latifa tace" Allah mahallici na mahallicinka wanda ya haramta zalumci shi ya dawo dani wnn rayuwa, Allah bazai barka kaci gaba da aikata zalunci ba yau 'karshen zaluncinka ya zo," ta shiga nuna sa da yatsa tana fa'din ka cuce ni Tanimu ka kashe 'yarka ta cikinka a gabana ka mallakani wa bokanka...." Malikaaaaa me kike cewa "ya me shari'a kark yarda da wnn matan fatalwa ce ta jima da mutuwa wllhi fatalwa ce...
"Al'kali ya buga benchi silence..... kowa ya koma wajen zamansa ya zauna, haba nan fah Admiral zufa ta shiga ysatsafo masa hakama dad din Aisar, Admiral yana 'ko'karin mikewa Chief of defense ya narka masa wata kallo kawai a saba'in ya koma ya zauna. Da yawan mutanen dake cikin kotun sun razana da ganin mahaifiyar latifa gaba daya suffanta ya canza kamar wata hallita.
"Mum din Latifa ta 'karaso gaban Haidar hawaye na bin kuncinta ta soma fa'din ko bansani ba kaine Haidar, kaine mutumin da matarka ta ceco 'diyata daga halaka na wnn azzalumin mutumin, matarka ta fito da latifa daga duhu zuwa haske, snn kaine Tanimu ya la'kaba maka sharrin ka kasheta saboda tsoron kaine zaka fasa abunda yayi shekara da shekaru. Hawayene kawai kebin kumatun Haidar..
"Ta juyo tana kallon me shari'a kafin tace ya me shari'a a yau zan bayyana mummunan aiki na wnn azzalumin bawa, " ta juya tana nuna Admiral da tuni ya soma sakin fitsari a jikinsa kafin tace" Wnn mutumi ya aurani wa bokansa shekara da shekaru, bana cewa um bana cewa um um amma kuma ina sane da duk abunda ke faruwa, wnn mutumi ya mayar da 'diyarsa Latifa tamkar matarsa ya lalata mata rayuwarta wnn mutumi shi ya kashe tsohon kwamandan rundunar sojan ruwa dan ya maye gurbinsa wnn mutumi shi ya kashe mun 'diyata a gabana...... kuka ya kufce mata. " Dan'kari ma'kari, kotu tayi tsit sai sautin kukan mum din Latifa kawai kakeji, da yawan mutane mamakin irin laifukan Admiral da aka zayyano suke, anya wnn mutum ne lallai wnn shime babban shedan.
"Al'kali ya 'dago cike da 'dunbin al'ajabi kafin ya furta " kotu tana bu'katan Naval Chief Of Staff da ya shigo cikin Akulkin tuhuma...." Admiral ya soma 'bari yana fa'din ya me shari'a kar ku yarda da wnn matan ta jima da mutuwa fatalwa ce kawai ta fito... tsawan da aka daka masa yasa yin tsit jiki a mace ya nufi gefen Haidar..." wata mirmushi kawai Haidar ya sakar masa sanda ya tsaya a gefensa.
"Alkali ya soma fa'din" Admiral kaji abubjwan da iyalinka ta zayyano akanka, shin ka yarda ka amsa laifinka kokuwa....
"Admiral kam ganin ta tashi masa yasa duk ya susuce, bai ankaraba ya hango dad din Aisar na 'ko'karin warewa. Da sauri ya nunasa yana fadin ga dayan can zai gudu, Dad din Aisar ya soma fadin" ni kuma me ya hada ni da kai ni babu hannuna cikin mutuwan 'yarka nida ka kamamun mata kasa 'dana bada shaidan 'karya dan kar..... Admiral ya soma fadin karya kake kai ka kawo wnn shawara dan kar asirinka ya tonu abunda kayi shekaru talatin baya kisan Barrister Ridwan Marafa da kayi...... "Ai bai gama rufe baki ba Aisar yayi wata tsalle ya dun'kule hannunsa bai tsaya ko ina ba sai fuskan Dad dinsa ya kai masa wani wawan naushi naushi duk tarin mutanen da suka taru suna ri'ke Aisar ina bai ko sairaresu ba dukan Dad kawai yake da iya 'karfinsa yana fa'din " you blackmail me you monster.... "Dad ya dago kai yana fadin" Aisar kar ka yarda dashi 'karya yake maka... inaaaa Aisar baiji bai gani dukan Dad dinsa kawai yake ya cukume wuyansa yana fa'din am gonna kill you invincible ina ka kai mun mum dina ina mum takeee..." fuskan dad duk jini yake fa'din tana guest house dinshi tana guest house din Admiral..... " A tamanin Aisar ya fice daga kotun..."( jama'a gaba 'daya kotu ta rikice😳) dole Al'kali ya bada hutun rabin lokaci abubuwa su daidaita tare da

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login