Showing 42001 words to 45000 words out of 114964 words

Chapter 15 - MIJIN HANEEFA Complete Hausa Novel

15 Oct 2024

13161

kaman daga sama taji 'karan rufe 'kofan 'dakin sa, 'dago kai tayi dan tabbatarwa, ai kuwa shine yana sanye cikin kayan training yayi kyau sosai, kaman bazata gaishesa ba sai kuma wata zuciya tace ki gaishesi.
"Da kyar cikin tunanin kar ya yafarta tace, " ina kwana yaHaidar.
"Murmushi ya sakar mata wanda yasata sake baki tana kallon ikon Allah, muryan shi ya dawo da ita daga duniyan tunani.
"Lafia, ya 'karaso yana fa'din how was your night?
"Cikin yanayin tsoro dan tasan 'kila wani abun yake shirya mata tace " it it was fine.
"Dafa kujeran dake saitin nata yayi yana kallonta with a smile on his face yace " babu tayi ne?
"Surprisingly ta dago tana kallonsa, "Farr ya mata da ido kafin yace " uhum, can I have some.
"Sure have a seat, ta fadi tana gyara masa kujera, murmushi yayi yace "thanks.
"What would you like to eat, ta fadi tana dan satan kallon sa.
"Le'ka plate dinta yayi ya jawo shi gabansa yace " wannan ma is Ok, kallomsa ta tsaya yi da mamaki dan chips din dake ciki basu wuce a 'kirga ba, yana ci da kidney sauce yana mamakin ashe dama ta iya abinci.
"Ita kama banbara'kwai abun ya mata wai namiji da suna Hajara, she just couldn't believe it, wai yaHaidar ne wnn, mutum me girman kan nan shine ke treatin 'dinta nicely haka, kai there most be something, she wonder what he's capable of...... hannunsa dataji kan nata ne ya dawo da ita daga duniyan tunanin da ta tafi, tayi saurin 'dago ido tana dubansa kaman wacce aka zabura, murmushi ya sakar mata yace " I never knew you can cook delicious food like this, ai da ban 'bata lokaci na ina ci a restaurant ba, anyway abinci yayi da'di sis, may Allah bless your hand. Ya karashe maganr yana murmushi.
"Murmushi itama tayi me kama da ya'ke, mi'kewa yayi bayan ya kur'bi tea 'din dake gabanta yace " I gotta get going, if their is anything you need just let me know ok.
"Nodding kanta tayi tace babu komai, a dawo lafiya. Sake hannunta yayi ya 'dauki wayansa da car keys ya nufi 'kofa.... har ya kai 'kofa ya juyo yana kallonta akayi sa'a kuwa itama shi take kallo, murmushi ya sakar mata kafin ya fice...

"Sau'ke ajiyan zuciya tayi kafin tace " what's really going on, ohhh I don't understand, why is he acting strange, why the sudden change. Wata zuciya tace let him be, ki bisa a haka ki gano me yake shirin 'kulla miki... da wnn tunani tayi murmushi tace "yes I need to find out what he's up to.

"Koda ya dawo ita tayi serving dinsa lunch, yaci kuwa sai zuba santi yake, da yamma misalin karfe biyar yace da ita ta shirya su fita, nan ne fa ta soma tunanin to ko zai kaita wani wajen ne. Kaman ya gane me take tunani yayi murmushi ya matso kusa da ita ya ri'ko hannunta yace" don't be nervous, just feel free, remember you're with your bro.... kallonsa kawai take, ta maimaita a zuciyanta "bro, lallai yaHaidar, wato he will never accept the fact that she's his wife. Wata zuciya tace "and what would make you worry about that, kema ai ba sonsa kike, ki tsaida hankalinki kiga gudun ruwansa.
"Murmushi ta sakar masa, ya gyada mata kai kafin yace" shall we. Ta gyada kai tana murmushi... "After you ya fadi yana nuna mata hanya.

"Daidai wani makeken mall yayi parking, tankallesa tace yaHaidar me zamuyi a nan, baice komai ba ya fito ya zagayo ya bude mata ya ri'ko hannunta ba musu tabi bayansa, dukansu sunyi kyau sosai gwanin sha'awa.
"Suna shiga yace ki za'ba abubuwan da kike bu'kata, and kar kiji nauyin za'ban koma meye, remember am your brother ok. Gyada kai tayi ba tare da tace komai ba, I'll pay the reservation at the restaurant. Maybe we'll have dinner together ok. Ya fa'di yana shafa kanta. Irin yanda ake ma yaran nan
"Kallonsa kawai tayi kafin tayi nodding kanta tana murmushin ya'ke.

"Abubuwa masu kyau da tsada ta 'dauka, nan ta ha'du da wata yarinya ta dinga binta 'yar 'karamar yarinyar da bazata wuce shekara biyar ba.... Hanifa kuwa saekin son yara nan ta shiga mata wasa, can saiga wata 'yar dattijiwan mata ta iso tana fa'din "Amal wai ina kika shiga... ganinta da hanifa yasa matar ta sakar ma Hanifa murmushi, murmushi itama tayi ta gaida matan matan ta amsa cikin sakin fuska, matan ta dubi Amal tace Daddyn ki nata neman ki kin fara san'an yawon naki a kanti ko, "cikin magananta da bai gama "kwari ba tace
"Ba na samu mummy na a nan bane, matar ta dago tana duban Hanifa, ta dubi Amal tace ina mummyn naki, Amal ta nuna Hanifa tace "there she's"
"Daga matan har Hanifa saida sukayi murmushi. Matan tace baiwar Allah kiyi ha'kuri wllhi hakan nan Amal take,
"Ayya ai babu komai Hajiya mun zama friends nida Amal, right Amal ta fadi tana duban Amal, gyada kai Amal tayi daidai nan " Barrister Sameer Ridwan ya 'karaso wajen yana fadin " Momma kin sameta kuw..... muryansa ya sar'ke sanda ya sau'ke idonsa kan Hanifa dake ta faman dariya tana wasa da Amal, da gudu Amal ta 'karasa wajensa tana fa'din " hey daddy meet my new mummy.... sai snn ya saita kansa, hadadden matashi meji da kyau da class, murmushi yayi sanda Hanifa take gaishesa, ya amsa duk jikinsa a mace, daga haka ya juya yana fadin momma barinyi settling bill, gyada masa kai momma tayi , suka ci gaba da ta'di da Hanifa....

👸🏻Queen Samy😍💄💋......
[5/21, 2:01 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
42

"Daidai nan Haidar ya dawo ya tadda Hanifa dasu momma da Amal sai labari suke kaman sunsan juna, mi'kewa Hanifa tayi sanda yake 'karasowa, ta dubi Amal tace toh Amaly zan tafi my brother is here, Amal ta turo baki tace "No pls don't leave, momma tari'ko hanun Amal tana murmushi tace, toh mummyn Amal a huta gajiya sai mun sake haduwa, Hanifa na masu waving har suka wuce suka daina kallonsu, zuciyanta cike da kewan Amal suka bar Mall din.

"Barr Sameer ne ya 'karaso da sauri dan burinsa bai wuce ya sake ganin Hanifa ba, be ganta ba sai momma da Amal, Amal na ganinsa ta 'karasa da gudu ta rungumw shi cikin shagwa'ba take fa'din daddy why is she left, I want her, pls daddy.... kallon momma yayi ta girgiza masa kai kawai alamun fitinan Amal, momma tace yau akwai rigima knn..
"Sameer yace " ta tafi ne?
"Eh ta tafi yanzun nan, gashi ko lambar wayanta bamu ansa ba. Saidai idan Allah ya sake ha'damu. "Kai nima dai Hafsatu da shirirta nake aiko ko sunanta bansani ba.
"Sau'ke ajiyan zuciya Sameer yayi ya 'dauki Amal ya azata bisa kafa'da sai faman rarrashinta yake " it's okay sweedy, ya dubi momma yace " muje momma...

"Suna tafe a mota kowa da abunda ya'ke sa'kawa cikin ransa, daidai wani makeken restaurant yayi parking, ya juyo yana dubanta yace" shall we, murmushi tayi gamida nodding kanta.
"Suna shigowa akayi directing dinsu to private section yanda ya masu bucking dan bazai iya barinta taci abinci in public ba, gani yake kaman zasu zuba mata ido.
"Yaja mata kujera ta zauna, kafin shima ya zauna. Menu card ya 'dauka ya mi'ka mata ta zaba dishes din da zata ci. Light food suka za'ba gaba 'dayansu.
"A hankali take cakalan abinci kaman wacce kwai ya fashe mata a ciki, murmushi Haidar yayi kafin yace " don't you like the food, ko restaurant din ne be maki ba, idan baki so sai mu canza wani.
"Girgiza kai tayi tace " no it's okay, and the food test good too. Ta'dan yatsina fuska tace " am getting a little nervous, you know it's my first time in a place like this.

"Murmushi yayi sanda ya maida dubansa cikin plate din kafin yace " that's normal, just feel free and eat as much as you can, dan naji ance mata ci ne dasu.
"Dariya tayi saida dimples dinta suka lotsa tace " kai yaHaidar maza fa sunfi mata cin abinci, saidai ko kaine baka da ci, but most of them sunada ci.
"Murmushi yayi a ranshi yace "tafi kyau idan tana dariya.

" daga bakin titi ya hango mota kaman na Haidar pake cikin restaurant din, kwana yayi ya shigo gamida parking motarsa, yana sanye cikin 'kann kaya, yayi kyau abunsa, ya rufe motan yana 'ko'karin shiga restaurant din ya hangosu suna 'ko'karin fitowa, idonsa 'kyam kan Hanifa.
" 'karasa ciki yayi yana magana wa Haidar, juyowa Haidar yayi yace, Navy gamida mika ma Aisar hannu suka gaisa, Hanifa ta gaishesa ya amsa da sakin fuska, yayi saurin 'dauke idonsa daga dubanta sabida Haidar.
"kasan kuwa daga nan gidanka na nufa.
"Allah ya hutace ka knn tumda gashi ka sameni.
"Indeed, Aisar ya fadi yana satan kallon Hanifa. Dama akwai little talk da nake so muyi, kar ka damu it won't take long.
"Ok fine, Haidar ya fadi gamida duban Hanifa ya mi'ka mata car key, yace jirani a mota inazuwa, kar'ba tayi tace toh kafin ta soma tafiya, Aisar ya bita da kallo ha'di da yin wata murmushi maras sauti, a ransa yace " She belongs to me, I will never give up on her.

"Muryan Haidae ya dawo dashi sanda yake fadin let's seat and talk. Zama sukayi bisa kujeru kafin Aisar ya soma fad'in....

*Sa'kon gaisuwanku ya iso gareni 'dinbin masoyana Allah ya bar 'kauna, nima ina sonku baki 'daya, #1Luv*

👸🏻Queen Samy😍💄💋.....
[5/21, 2:03 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
43

"So how are things going between you and your dad? Haidar ya tambaya yaana kallon Aisar.
"That's precisely what I want us to talk about, first I wanna thank you for what you did Haidar, you're just an incredible. You've no idea how pleased I'm, at last my dad and I started to get to know each other, he's willing to fix his relationship with me, and that's all because of you. Na gode Haidar bansan da wane irin kalma zan nuna maka godiya na ba...... " no haba Aisar dan Allah ka daina yimin godiya haka, na fada maka we're brothers, ciwonka ciwona ne, Alhamdulillah Allah ya 'kara ha'da kanku, murmushi Aisar yayi yace ameen.
"Mi'kewa sukayi suka nufi waje, har sun fito Aisar yace aff yaushene tafiya Sudan din nan, Haidar ya 'dan ta'be baki yace " tafiyan da ya kamata ayi shi lat week gashi ba'ayi ba.
"Dariya Aisar yayi yace " com'on Soldier you perfectly know anyi postponding tafiyan nan ne saboda kai, it's obvious we can't make it without you.
"Murmushi kawai Haidar yayi yace " Sounds ridiculous, akan ni ba mutum bane ko me, we're all the same, anyway Allah ya kaimu jibinnda rai da lafia ya kuma bamu sa'a akan abunda mukasa gaba.
"Ameen Aisar ya fadi. Nan sukayi sallama da juna kowa ya nufi motarsa...

"Suna a mota wayansa ta soma ringing, ganin lamban Latifa ne yaji kawai baison 'dauka, saida ta kira sau uku, kafin ya'daga murya a dake, " what is it. Abinda ya fadi knn kawai.
"Da mamaki tace " I don't get you Aliyu, m kake nufi.nayi mka wani laifi ne.
"No bakimun komai, driving nake . I'll call you later.
"Har zaiyi hanging tace, I think we need to talk it's urgent.
"What for? Ya tambaya yana satan kallon Hanifa da ta ha'de rai,
"Gaskiya Aliyu if possible mu ha'du later kawai dan maganan bata waya bace.
"Gajere tsaki yayi yace " there you go again, just give me a hint mana.
"Ok fine, wasu documents na samu so suspicious.
"Da sauri yace Ok ok fine, we will talk later.
"Tace, should I come to your place.
"Da sauri yace no no don't border zan kira ki na fa'da miki location.
"Ok fine, see you then.... daga haka yayi hanging up. Ya juyo yana kallon Hanifa gani yayi ta juya gaba 'daya tana kallon Window, ta'be baki yayi a ransa yace " I wonder if she's jealous of me.

" Amal rikici sosai ta shiga yi sai ankaita wajen mummynta da suka hadu a mall, Barr Sameer ya tsuguna gamida dafe kansa yace " Oh Amal for Allah's sake will you stop, I've told you zan nemo maki ita, but for now you need to go to sleep, you see is already late. Kinaso kiyi lattin sch ne, ta girgiza kai a shagwa6e alamun a'a, murmushi yayi yace " yawwa that's my girl, rungumesa tayi tace I love you daddy, yace I love you more my Angel. Shinfi'da ta yayi ya kunna mata ayatul kirsiyu a MP4 dinta ya manna mata kiss a goshi ya fice.
"Zaune ya samu momma a parlor tana kallo, ta dube shi tace ina er rigimar tayi baccin kokuwa, a kasalce ya gyada kansa alamun eh, ba tare da ya kalleta ba yace " momma zan kwanta zan fita da sassfe gobe insha Allah. Ya fadi yana ficewa daga parlorn.... Sameer momma ta kira sunansa, dawowa yayi yace na'am. Zo ka zauna magana nake son maka, langa'be kai yayi kaman 'karamin yaro yace "oh pls momma does it really has to be now, bacci nakeji sosai.
"It won't take long zo ka zauna, momma ta fadi tana dubansa.
"Zama yayi gamida nutsuwa a gaban mahaifiyar tasa.

"Sameer is high time, you can't go on like this, ya kamata kasan me kake ciki, Fauziya ta rasu and she will never come back, don't ruin your present by thinking of the past. Think about this pls, ko dan marainiyan yarinyar nan me kukan samun uwa a koda yaushe ya kamata kayi aure yanzu kam, am tired of this, am sick of it, yarinya kullum taga matashiyar mace sai ta ma'kale tace ga mumminta, kaida anyi magana kace baka son kowa dukda tulin 'yan mata da zaurawan da suke sonka. This is not fair, don't make your life so miserable, so as your daughter's, ni dai na fa'da maka na gaji gwara tu wuri kasan me kake ciki.

"Murmushi yayi ya mike daga kujeran da yake ya 'kara ya ri'ke hannun momma yace " momma na mafarkin ku keda Amal ya kusa tabbata, naganta naga wacce zata maye gurbin Fauziya, momma na murmushi me bayyana ha'kwara tace, "and where is, a ina take son,
"Annurin fuskansa ne ta 'dan 'dauke kafin yace, I don't know, I don't know ko zan sake ganinta, so 'daya tak na ganta and she just disappears. Momma pls ki taya ni addu'an Allah ya sake ha'dani da ita. Ya kwantar da kansa kan cinyar momma, cike da tausaywa 'dan nata take shafa bayansa tace " kullum ina maka addu'a son kuma bazan ta'ba gajiyawa ba, Allah ya za'ba maka abunda yafi zama alkhair, maza tashi kaje ka kwanta Allah ya maka albarka.
"Mi'kew yayi yana furta "ameen momma na.... itama ta mi'ke tana fa'din barin duba 'yar rigiman nan...

👸🏻Queen Samy😍💄💋......
.[5/21, 5:35 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
44

"Tana zaune a 'daki tana duba kayayyakin da suka sayo ya turo 'kofan ya shigo, ya dubi kayan data jido, kayan za'ki ne suka fi yawa, 'bata fuska ya 'danyi kafin yace, kimsan dai wata yazo tsakiya ko, saura kizo kina mun kuka ciwon ciki... ta 'dan turo baki tace "kai yaHaidar dubafa babu yawa fah kuma ai a fridge ma zan zuba su ba shanyewa zanyi yanzu ba, 'daga kafa'dunsa yayi gamida ta'be baki, a ransa yace yaro dai ma yaro ne, musamman akaika shopping ka tsaya 'diban unnecessary abu irin kayan za'ki.
"Juyawa yayi ya nufi 'kofa yana fa'din am going out, ko zaki raka ni ne? Girgiza kai tayi ta ta'be baki tace "a 'a bazan je ba, sai ka dawo.
"Murmushi yayi da gefen bakins yace " akwai wani abunda kike so.
"Girgiza kai tayi tace a'a.
"Ok kizo parlor kiyi kallo it will keep you company. Daga ya fice... Hanifa ta bisa da kallo a ranta tace muje zuwa yaHaidar, da sannu zan gano plans dinka akaina, hm mtsw harda wani ko zan raksa ne, bayan na san wajen karuwarsa zaije, yanzu an daina yi a gida ana fita waje, hakan ma yafi mum banji ba ban gani ba.

"A wani joint suka hadu da Latifa, ta jima tana jiransa kafin ya iso, tana hangosa ta mike da gudu da zummar rungumarsa, matsawa baya yayi

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login