Showing 6001 words to 9000 words out of 114964 words
'dazu Haidar ya wuce.
"Eh mamy munyi waya dashi dama naje asibiti duba jikn Hanifa ne akace mun anyi discharging nata...
"Ayya sannu da 'ko'kari Saif Allah bar zumunci....
"Hira suke ta'bawa da mamy dan Saif akwai surutu ba kaman abokinsa Haidar ba shiyasa ma suka saba da mamy sosai, gaba 'daya hankalinsa naga Hanifa daketa cin abinci kaman mai tausayin abincin.....
๐ธ๐ปQueen Samy๐๐๐.......
[5/9, 6:10 AM] ๐น Muhammad๐บkabeer๐น: ๐น๐น๐น *Mijin Haneefah*๐น๐น๐น
09
"Tun bayan sallaman Hanifa a asibiti Saif kullum sai yazo gidan, sabo ne sosai ya shiga tsakaninsu dasu Shema amma Hanifa kam ko ka'dan ta'ki sakin jiki dashi tana ganin yazo ko suna zaune a parlor zata shige ciki abinta, har ranta ta tsane me tarraya da yaHaidar idan ka 'dauke 'yan gidansu.
*Lagos*......
_Maritime_.......
"Misalin karfe 5:30pm Haidar ne zaune a parlor dinshi bisa sofa, gabanshi laptop ne yana reserch gefe kuma kwalban wine 'dinshi ne yana danna laptop din yana sipping wine dinshi, a hankali ta turo 'kofan parlon ta shigo tana sanye cikin doguwar riga datake kamar a jikinta aka 'dinka dan yanda ya matseta, gashin kanta a bu'de as usual sai handbag dinta dake makale a hannunta na dama.
"Da mugun mamaki ya 'dago yana kallon Lateefa dake tsaye tana binsa da mayen kallon data saba, Sai sannan Haidar ya tuna ashe singlet da gajeren wando ne a jikinsa.... wani dogon tsaki yaja gamida mikewa ya nufi bedroom, idan da sabo Lateefa ta saba da halin Haidar na disgi dukda disgin da yake mata ko ka'dan bata jin sonshi na raguwa azuciyarta saima 'karuwa da yake yi after each and every second, tun ba yau ba ta sani Haidar is not womanizer ko ka'dan mata basa gabansa, dan kuwa tasha mi'ka masa kanta kyauta amma baya kulata saida ma suyi fa'da. Shi dai barshi da shan ruwan kwalba kawai, shima shan giya tafiyanshi navy ne ya soma sha dan acikin ko wani jirgin ruwa sunada bar dinsu mussaman na shan giya, wani 'kasar idan sukaje akwai sanyi sosai bararsar takan taimaka masu wajen warming temperature a cewarsu. tun bayaso har ya fara korawa daga haka ta zame masa jiki(Allah ka tsaremu ameen).
"Mintuna 'kadan Haidar ya fito cikin jallabiya fara kal sai ya koma tamkar balarabe, ya nemi waje ya zauna ba tare da yace da ita komai ba. Murmushi ta sakar masa gamida matsowa kusa dashi, dakatar da ita yayi ta hanya narka mata mugun kallo. Nan fa Latifa tasha jinin jikinta ta soma fa'din "haba Aliyu what have I done kuma, tun dawowanka fa bamu ha'duba nayi tafiya sai yau na dawo, and thi is how you welcome me. Haba Aliyu this is not fair fah...
"Cikin ko in kula yace "how many times do I have to tell you bana son ana zuwa mun gida without informing me, wama yace miki ki shigo min gida babu ko knocking in the first place hum.
"Ha'kuri Latifa ta shiga bashi gamida shagwa'be fuska, abun har yaso bawa Haidar dariya ganin yanda Latifa da suke kusan age mates amma sai wani masa shagwa'ba take _the thing no fit her at all ๐๐_.
" Da kyar Latifa ta samu ta lalla'ba Haidar bai koreta ba nan ta sanar dashi Dad dinta nason ganin shi... ya dago yana dubanta kana yace shi ya gaya maki na son ganina, ta gya'da kai alamaun eh... shiru Haidar yayi yana tunanin toh meye Naval chief of staff yake nemansa, tun dawowansa ya'ki su ha'du dukda shine musabbabin dawowansa hutunsa bai 'kare ba...
"A ina yace na same shi ya jeho mata tambayan?
"Yace a gida zaka sameshi by 8:pm..
"Nodding kansa Haidar yayi gamida tunanin wann secret meeting da Naval chief of staff yake so suyi....
"Karfe 8 daidai Haidar da Latifa suka nufo gidansu Latifa, tun daga gate sojoji ke sarawa su Haidar har suka 'karasa ciki.
"A parlorn ba'ki ta masa mazauni kana ta wuce ciki sanar da Dad 'dinta Aliyu ya iso.
"Latifa ita da mahaifinta kawai suke rayuwa cikin gidansu saiko ma'aikata, dan kuwa tunda mahaifiyarta ta mutu dad dinta bai sake aure ba ya 'dauki son duniya ya 'dora ma 'diyarsa wanda soyayyan nasu ni kaina Samy ina zarginsa dan kuwa kaman ya zarce na 'diya da uba kawai....
"Kan kace me an cika gaban Haidar da wine iri da kala masu 'dan karen tsada, mintuna ka'dan Latifa ta dawo ta sauya shiga cikin kanan riga da skirt. Gogan naku ko ajikinsa kaman ba mace bane a gabansa haka ya 'dauki Latifa, ita kuwa sai karairaya take masa...
"Saukowan *Naval Chief of Staff Razaq Tanim* knn daga stirs, Haidar ya mi'ke gamida sara masa. Murmushi ya sakar masa gamida nuna masa kujera have a seat Captain. Aliyu ya zauna suka shiga gaisawa da Dad din Latifa, ita kuwa sai wani jin da'di take.
"Dad ya juyo ya kalleta ya shafa kanta yace "daughter go inside let us talk ok. Babu musu ta mike tana kashe wa Haidar ido sann ta haye sama.
"Captain AA ina so na turaka Nija Delta akwai aikin da nakeso ka mun dan naga you're so brave. Haidar ya 'dago yana dubansa kana yace Ok sir yaushene tafiyan.
"It should be any moment any time, kawai inaso ka zama rady ka gane.
"Haidar ya gya'da kai kana yace Ok Sir.
"Murmushi Naval Chief of Staff yayi kana ya mike, da sauri Haidar ma ya mike gamida sara masa, ya mika wa Haidar hannu suka sha hannu kana ya haye sama ya bar Haidar tsaye a wajen.
"Dad na hayewa Latifa ta sauko wajen Haidar cikin juya kwankwaso da salon tafiya....
*Kano*....
"Suna zazzune sun kewaye Abbansu dake cin lunch bisa darduma, Hany ta turo baki tace Abba yanzu boarding zamu tafi, nidai zanyi missin mamy.
"Abba ya shafa kanta yana murrmushi yace zaki saba Angel.
" 'yan uku ma sai shagwa'ba suke zubawa Abba nasu, 'Danmasani kuwa sai murna yake wai gwarama su tafi boarding ko gidan zaiyi da'di.
"Mamy dai mi'kewa tayi dan tasan tabbas zatayi kewan yaran nata itama.....
๐ธ๐ปQueen Samy๐๐๐.......
[5/9, 6:10 AM] ๐น Muhammad๐บkabeer๐น: ๐น๐น๐น *Mijin Haneefah*๐น๐น๐น
10
"Yau satinsu Haneefah guda da tafiya boarding school gaba 'daya gidan sai ya zame masu babu da'di, shi kansa 'Danmasani mai son tafiyan nasu duk yaji dama basu tafi ba sau'kin shi 'daya shima ya sami admission a 'kasar Switzerland zai tafi ya soma karatun degree dinsa, kewansu zai ragu masa idan ya tafi akan yana gidan shi kadai.
"Inna kam banbami ta ri'kayi wai ita gida babu kowa babu yara, gida duk ya mace sabida rashin yara aciki.
*Niger Delta*
_Rivers_
"Cikin 'kwarewa sojojin ke gudanar da ya'kin ta saman ruwa har Allah ya basu ikon fasa jiragen ruwa na bogi wanda aka sha'kesu da albarkatun man petur na 'kasan nan dan fita dasu kasashen waje.
"Captain Aliyu wanda shine in charge gaba 'daya na sojin ya umarce su su tsagaita da wuta wato su daina harbi. Binciken jiragen aka soma yi amma cikin rashin sa'a babu wanda yayi rai cikin theorists din duk sun mace....
"Captain Paul ya dubi abokin aikinsa Captain Aliyu ya sara masa gamida fa'din congratulations Captain, Sara masa Aliyu ma yayi gamida saukowa daga cikin jirgin ya nufi camp....
"Captain Paul ne yaja gefe ya kira ogansu Naval chief of staff, bugu biyu chief of staff ya daga dan jin rahoton da Paul zai basa.
"Bayan Paul ya sarama chief of staff ta cikin wayan kaman wani yana ganinsa kana yace "Sir unfortunately an 'kona jiragenka da suka sha'ko crude oil har guda biyu sann an 'kona na tsagerun Niger Delta guda 'daya sann an 'kona wani guda 'daya wanda nake zaton na wasu ministers ne.
"What! Naval chief of staff ya fa'di gamida mikewa tsaye, garin yaya ba'a gama dashi wann shegen yaro Aliyu ba. What are you busy doing there paul har ka bari hakan ta kasance, kasan musabbabin tura Aliyu wajen nan shine a gama da shi.
"I apologies sir, but it wasn't my fault. Captain AA ba kaman kowa bane ya zarce tunanin mutum sir.
"Cikin 'kunan rai Dad din Latifa ya zube bisa kujeran office dinsa ya kwantar da kai bisa kujeran gamida lumshe idonsa ya shiga juya kujeran a hankali. A fili ya furta Captain Aliyu....
"Wannan ya'ki da Aliyu ya jagoranta ba 'karamin girma ya 'kara masa ba, satinsu guda a camp suka dawo lagos.
"Koda ya ha'du da dad din Latifa a fili ya nuna masa yayi murna a cikin ransa kuwa ba haka bane, ya 'dau alwashin sai yaga bayan Aliyu.
"Mai girma shugaban 'kasa yaji da'din aikin da Aliyu yayi ya zamana duk wanitura navy da za'ayi nija delta toh Aliyu ke jagoranta sojojin. Girma da dukiya ya 'karu sosai wajen Haidar, saidai rashin zaman shi ya 'karu sosai. Kusan kullum yana can Rivers. Idan ka ganshi a Kano toh hutun annual leave ne.
"Kwanci tashi babu wuya wajen Allah su Hanifa sun kammala ss2 sun dawo gida hutu ,suna shirin shiga ss2, duk hutun da suke dawowa basu ta'ba ha'duwa da yaHaidar ba hakan sai yafi masu da'dima, saidai sunyi kewan 'Danmasani abokin fa'dansu dake can 'kasar Switzerland.
"Idan ka gansu yanzu bazaka zata su bane sun girma sun zama 'yan mata sosai kyaunsu sai ya 'kara fitowa mussaman Hanifa da take tamkar wata fure, kowa yasan su a sch da suna Pretties hakan nan ake kiran su. Idan za'a ware Hanifa kuma sai kaji ana cewa Queen of the pretties. Da wann suna suka yi tashe a makaranta ta fanni karatuma ba'a barsu a baya ba suna 'ko'kari sosai hakan sai ya 'kara 'daga martabansu a wajen students da kuma teachers.
"suna zaune can 'dakinsu suna ha'da kayansu lokaci guda kuma suna zuba surutu wanda rabin surutun gameda sch dinsu suke, aka turo 'kofan dakin gamida sallama.
"Da gudu suka tafi suka rungumeta suna fadin oyoyo Anty Hiba.
"Murmushi Anty Hiba keyi kana ta samu ta zame jikinta da 'kayr daga rikon da suka mata. "'Yan matan mamy kar ku 'karasani dan Allah ta fa'di tana 'ko'karin zama bisa sofa. Anty ina my Ajmal? Hanifa ta tambaya.
"Anty shine zaki zo bayan yau zamu wuce sch Shema ta fadi baki a ture.
"Hoh Hany lets greet her first mana , cewan Sadiya dake saka kaya cikin trolly.
" bayan sun gaisa ne suka shiga zuba mata surutu nan ta sanar dasu Ajmal na downstairs tareda mamy. Nan suka fice suna rige rigen ganin Ajmal.
"Anty Hiba sistern mamy ce kuma autan su koda yake su biyu suka rage 'yan uwan juna. Anti Hiba tana aure a Kaduna tazo kwana biyu ne ma yayan nata wato mamy.
"Tunda suka fito zasu tafi Inna ke kuka wai ita kam wallhi karatun ba dole bane, idan bazasu yi shi kusa da ita ba, Anty Hiba da mamy ne suka ta bawa Inna baki har su Hanifa suka dau hanya.
"Nan fa bayan tafiyansu Inna ta rinka sababi wai sai Aliyu ya dawo gida yayi aure ta rinka ganin 'ya'yansa. Abba kam gaba 'daya ya rasa yanda zaiyi da Inna haka dole ya 'dau waya ya kira Haidar ya sanar dashi yazo gida as soon as possible.
"Dole Haidar ya bar tulin aikin dake gabansa dan yaji Abba sounds serious sosai ya nufo gida Kano....
๐ธ๐ปQueen Samy๐๐๐........
๐น๐น๐น *Mijin Haneefah*๐น๐น๐น
11
"Zaune suke shida Anti Hiba a parlorn mamy gaba 'daya jin Anty Hiba yake amma to be sincere bashida niyyan aure a yanzu.
"Kai nake sauraro Haidar kayi shiru baka ce komai ba, Anty Hiba ta fa'di sanda take duban Haidar.
"Aunty you know am always been honest with you, wallahi ba aure a agenda na beside ni 'din nawa nake for Allah's sake da har za'a matsa min da wani maganan aure, am just 27 ne fa kawai shi Abba komai Inna ta fa'di biyeta yake despite the fact ta tsufa yanzu, ba komai zai na biyeta ba wani abin sai ana dan 'daga wa mutum 'kafa.
"Anty tayi shiru tana duban Haidar kana tace "toh yanzu wacece dama budurwan taka?
"Ya 'dago kai gamida nuna kansa yace" ni Haidar budurwa kana yayi wani 'kasaitaccen murmushi snn yace "haba Anty ni Aliyu banga yarinyar da zanyi confronting dinta and propose to her that I do love her, wllhi babu ita.
"Anty Hiba ta ri'ke baki tana duban Haidar kana tace ai maganinka sai Innan wllhi gwarama a aura maka koma wacece. Zan fa'dawa Abba ya rage lokacin da ya 'diba maka dan ba kawo masa mata zaka yi ba. Haba Haidar is high time mana ya kamata ka san me kake ciki kaine fa babba duk gidan nan ko so kake har sai 'Danmasani yazo yayi auren ya barka hum.
"Ya mi'ke yana murmushi yake fa'din haba my cute Anty nasan bama haka da ke ki 'kyale Abba kawai akan haka. Sooner or later nasan zai sake tambayana. But for now kam aiki ya min yawa kinga in a couple of days zamu tafi Russia and inagaa zan kai four months ban dawo ba.
"Anty Hiba ta ta'be baki tace sai ina kuma?
"Zan le'ka tsohuwan nan ne kafin tazo ta isheni...
"Ajmal ne ya shigo a guje ya haye jikin Haidar yana fa'din Uncle my ice cream,
"Haidar ya dagasa sama yana fadin Ok my boy muje mu gaida Inna sai muje nasaya maka..., a haka suka fice Anty Hiba ma ta mike ta nufi sama.
"Kwana biyu Haidar yayi bayan yayi alkawari wa Abba zaizo masa da magana mai da'di idan ya dawo daga Russia, gaba 'daya Haidar ya rasa goyon bayan kowa. Yanzu kam harta mamy ma ta 'kagu Haidar 'din yayi aure hankalinta zaifi kwanciya a cewarta dan bata san me yake aikatawa a can kudun ba. Yaro da ku'di a hannunsa sai a hankali a cewarta.....
_Three months later_...
"Su Hanifa sai shirin rubuta waec suke gaba 'daya yanzu karatu suke babu 'ka'kautawa, yau sun dawo daga prep suna zaune a room dinsu 'kawarsu Laila ta shigo da gudu tana fa'din Hany albishirinki. Hanifa dake zaune saman bed dinta tana shan cornflakes ta mike tana fadin lailoo me kika jiyo mana. Shema tace bbc ba me kuma kika jiyo mana.
"Laila ta zauna tana fa'din kece kikazo highest a mock examz. Hany ta mike tana fadin dan Allah laila, gaba daya suka mike suna murna. Laila ta fice tana fa'din barin kwaso books dina ina zuwa. Nan ta barsu sai faman murna suke....
Lagos.....
"Yana zaune yana tunanin maganganun Abba ya sha kwalban wine kusan kala uku, gaba daya ji yake sama ta koma masa 'kasa. wannan karan kan da gaske Abba yake masa mamy ma babu alamun wasa a tattare da ita toh shi yaya zaiyi ne... a haka Latifa ta shigo ta samesa..
"Yana tangadi ya mike yana fadin "what brought you here... ganin yana buge yasa tayi using wann opportunity ta samu kan Haidar, nan da nan ya biyeta bayan ta tallafo kansa ta fara kissing nasa babu kakkautawa, cak Haidar ya dagata dukda irin tangadin da yake ya nufi bedroom da ita..... for the first time in his life da ya ta'ba kusantar wata mace......
"Bacci me nauyi ne ya daukesa ya kifa kansa da pillow yayi rubda ciki, Latifa ya shifi farin fatan bayansa wanda yake lawai lawai kaman jikin mace wani da'di takeji maras misaltuwa, ita kam bata taba samun peace of mind irin na yau ba. Ta rungumesa gamida manna masa kiss a bayansa. A fili ta furta "you are now mine Aliyu.. me alone...
"Tun daga wannan rana mummunan ala'ka ta kullu tsakanin Haidar da Latifa, kullum tana ma'kale dashi suna aikata masha'a... wa iyazu billah wannan shine sharrin giya gashi tasa shi aikata wani babban fasadi. 'Yan uwa muyi hattara..
๐ธ๐ปQueen Samy๐๐๐........
[5/9, 6:18 AM] ๐น Muhammad๐บkabeer๐น: ๐น๐น๐น *Mijin Haneefah*๐น๐น๐น
12
"Tun bayan komawarsa Lag tunanin maganganun Abba ya dameshi, shi yanzu yaya zaiyi mezece wa Abba idan ya kuma tambayarsa harga Allah shi har yau bai macen da yake so ba as a matter of fact basa gabansa. Latifa de ya 'dauketa abokiyar hole rayuwarsa ce amma ko ka'dan baya sonta baijin zai iya aurenta ya zauna da ita for the rest of his life, yana using wannan opportunity ya samu information masu gamsarwa gameda Dad dinta da zaran ya gama bincikensa he'll get rid of her.
"As usual yauma tana kwance kan 'kirjinsa wayansa dake bedside ta soma ringing, ganin Abba ne yasa gabansa mugun faduwa. Da kyar ya daga wayan cikin kasaliyan murya yayi sallama.
"Daga daya bangaren Abba ya amsa masa a dake, da kyar Haidar ya iya bude baki ya gaida