Showing 66001 words to 69000 words out of 114964 words
kafin yace " waye kike masa tsaki, ni sa'anki ne, dan kinga ina biyeki koh, toh kici gaba, idan baki da kunya kije wajen 'dan iskan mutumin nan ki ga abumda zan maku ke da shi... oya get the heck out of here.... kaman zata tashi sam haka ta fice gamida banging kofar... tana tafe tana hawaye.
"Mamy ta fito sashen Abba knn suka hadu da Hanifah, baki sake mamy ke kallomta kafin tace " daughter ya da kuka this early morning, ko Innan koroki tayi ne.... rumgume mamy tayi tana share jawaye tace " mamy ba yaHaidar bane...nidai kice ya sake ni wllhi na tsanesa... ta soma kuka, "rarrashinta mamy ta shiga yi tana fadi ki kyaleni dashi zai fito ya sameni, dole ya baki takardan ki a yau, wuce mu shige ciki kiyi break.
"A dining ta samu Sumy na breakfast nan ta tsaya wajent bayan sumy sun gaisa da mamy ta haye sama, Sumy ta kalli Hanifa tace ke kuma jiya shiknn daga kawo wa bako ruwa kika kaiwa mijinki koh kika kyale bawan Allah.
"Tabe baki Hanifa tayi tace Silly, ke wllhi I was kidnapped ne..... dariya Sumy tayi tace I see, so are you guyz fixing..... bata gama rufe baki ba Hanifa tace never that will never happen, dariya Sumy tayi tace uhm kunfi kusa ance ba'a shiga fadan mata da miji kai zakaji kunya, ta mike ta dau mayafinta da handbag dinta dake bisa kujera a parlor tace toh am leaving, zan tafi sch, Hanifa tace morning class kike da, Sumy ta girgiza kai tace wllhi registration ne ban gama ba almost a week ina abu daya, abun ba sauki sai a hankali.
"Jinjina kai Hanifa tayi tace su student ba sai kin dawo ni barin shiga nayi wanka.
"Mamy ce ta sauko ta mika wa Sumy key tace ki duba ko Haruna ya iso yayi dropping dinki, ta karba tana fadin toh mamy.
"Yana zaune a garden da newspaper a hannunsa ya hangeta tsaye a parking lot tana gyara files. A ransa yaji dadin ganinta har ya rasa dalilin hakan, he just couldn't resist starring at her.
"Jikinta ne ya bata ana kallonta, ai kuwa tana daga kai sukayi ido hudu, murmushin sa mai tsada ya sakar mata, itama ta mayar masa da martani, ta shiga takawa a hankali ta isa zuwa garden din, yana sanye cikin faran jallabiya kanta a 'kasa ta gaishesa, ya amsa yana kallonta face dinsa dauke da smile, tayi masa kayu cikin atampa riga da skirt green me zanen ganyen rogo yellow, ta yafa yellow veil a taikaice dai tayi kyau sosai.
"Dama ka tashi shine ka zo nan ka zauna, dan Allah kayi hakuri wllhi bamusan ka tashi bane da an kawo maka break.... "no kar ki damu ba yanzu zanyi breakfast ba, har kinyi shirin sch dinne. "Kai tayi nodding ba tareda ta kallesa ba, yayi murmushi da gefen bakinsa tana tuno masa matarsa Fauziya they have something in common, ya dago yana kallonta har lokacin idonta na kasa kafin yace " Ok toh ya naga kin tsaya a parking lot what are you waiting for, sai snn ta dago ta dan kalli gefe tace wllhi driver nake jira kuma har yanzu bai iso ba.
"Sameer ya rufe newspaper din gabansa yace " Shall I, ta dago tana dubansa da mamaki, daga mata kai yayi yace" I can drive you idan bazaki damu ba...
"Da sauri ta shiga girgiza kanta tana fadin " aa haba dai you don't have do that, zai zo yanzu nan, mikewa Sameer yayi yace I insist, pls don't reject my offer.
"Murmushi tayi tace barin sanar da mamy first. Snn ta shige ciki.
"Mamy wllhi bani na sashi ba, shi yayi insisting, Sumy ta fadi a shagwabe, Ok fine kice masa yana dawo wa ya shigo har ciki yayi breakfast, kuje Allah tsare hanya. Fuska dauke da fari'a ta fice tana fadin toh mamy.
"Yana hangota ya kunna motan data basa key din ya fito da ita nan Sumy ta shige suka dau hanya, suna tafe yace " ina saurarenki ina muka nufa, nan ta shiga masa kwatance har suka isa Bayero University...
"Da sallama ya shigo parlorn Abba dukda tunanin yanda zai fuskanci iyayen nasa da yake, dan rabonsa dasu tun jiya isowansu Hanifa, sanin darajan Sallama ce kawai yasa su amsa masa.
"Haidar ya nemi can 'kasan carpet ya zauna, ya soma gaida Abba dake breakfast ga mamy a gefensa tana tayasa, saida Abba ya 'dibi kusan mintuna uku masu kyau snn ya amsa masa da kyar, dan Haidar har ya cire rai Abba bazai amsa sa ba, mamy ma da kyar ta amsa masa gaisuwan nasa a ciki ciki.
"Shiru ne ya biyo baya sai dirin ac da sautin tv ne kawai ke tashi, Haidar ya mike a hankali zai fice Abba yace zo nan Haidar, babu musu ya dawo ya zauna.
"Ina maganar da mukayi jiya na takardan sakin Hanifa, ka bani yanzun nan.... zaro ido waje Haidar yayi yace Abba..... Pls Abbba don't do this to me, wllhi bazan iya rayuwa babu ita ba.... "dalla rufewa mutane baki, kana tunanin zaka 'kara raina mana hankali ne, kana tunanin zaka kuma manipulating dinmu ne kaman yamda kayi da, tunkan ranka ya 'baci ka kawo takardan sakin nan, dan 'yata ta gama zama da kai. Cewan mamy.
"Abba yace nama riga na gama magana zaka bani takardan sakin Hanifa like it or not, dan I won't force her to be with you again, za'bi na gareta, a randa ta gama idda ta kawo mun wanda take so zan aura mata..... kaman daga sama sukaji murryan Inna tana fa'din " Yo wani idda kuke magana, ai babu iddansa akanta jikata sabuwa take fil a leda, a yau ya saketa gobe zata auri loyan nan..... "Dan'kari ma'kari.... wani kallo kawai Haidar kayiwa Inna yama rasa ta cewa.
"Abba da mamy kam mamaki ne ya kamasu da kuma kunya, amma basu ce komai ba, Inna ta watsawa Haidar harara tace 'karya na fa'da daka wani kafe ni da idanuwa, ka musa mana idan 'karya ne, dama jira nake gari ya waye ka bata takardanta ko na maka ka a kotu,.
"Abba nidai wllhi ina son matata dan Allah mamy kisa baki wllhi I love her, don't even listen to this woman she's saying things out of anger. Pls Abba don't separate us, we both love each other..... ka gama 'karyan turancinka da zakayi amma saki kam kaman anyi an gama.Inna ta fadi tana zama bisa sofa.
"Abba ya dubi Mamy yace kira mun Hanifa, mamy ta mike ta fice kiran Hanifa.
👸🏻Queen Samy😍💄💋......
[5/21, 5:35 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
58
" Abba ya dubi Hanifa dake zaune kasan carpet gaban inna sai faman wasa da 'yan yatsun hannunta take yace "Mamana kar ki damu I understand you, kar kiji nauyin fada mana abunda ke zuciyarki, babu wanda zai sake saka ki abunda baki so, idan kika ce baki son ci gaba da zama da Haidar, dole ya sawake maki, har kullum ke diyace me biyayya Allah ya maki albarka, hakika kin mana biyayya mun maki aure babu sanin ki, koda kika sani kikace kinji kin gani kinyi na'am da za'binmu, wann biyayya da kikayi Allah ya saka maki da alkhairi Allah kuma ya baki 'ya'ya wa'enda zasu maki fin haka. Gaba daya suka ce amin idan ka dauke Haidar da Hanifa wa'enda keta sake sake cikin zuciyoyinsu.
"Ke nake saurare Mamana kina son ci gaba da zama da Haidar a matsayin miji... "Dago kai tayi tana kallon Haidar shima ita yake kallo, gaba daya ya wani susuce kaman bashi ba,... da sauri Inna ta ture 'keyan Hanifa daga barin kallon Haidar.
"Girgiza kai Hanifa ta shiga yi ba tare da ta iya cewa komai ba, Abba ya dubeta duk ta basa tausayi kafin ya dubi Haidar yace " Aliyu, Haidar ya dago a zabure yana duban Abba jin ya kirasa da asalin sunan sa kafin Abba yaci gaba da fadin " inaso ka bani takardan sakin diyata yanzun nan..... kaman saukan aradu haka Haidar yaji saukan magana nan Abba, ya nemi yawun bakinsa ya rasa, duk da sanyin ac dake raysa cikin 'bargo da tsokarsa bai hanasa jin zufa ta karyo masa ba.
"Kai ake jira Zaki maza rubuto ka mi'ko mu fara shirshiryen biki... cewan Inna.
"Haidar kam baima gane me ake cewa, he's completely lost, ..... tswan da Abba ya daka masa ya dawo dashi daga duniyan da ya tafi.. na'am Abba, rai bace Abba yace am pretty sure kaji abunda nace, ka bani takardan sakin 'diyata.
"Abba pls don't do this, I beg you Abba don't let this happen, Abba Allah mafa baya son saki, Abba ina son matata I can't do without her.
"Abba yace au sai yanzu kasan da wnn, na sani Allah baya son saki amma shi ya halatta saki, duk auren da akwai cutarwa a ciki saki ya halatta, ka zalunci 'yar marainyan Allah, ka salwantar da rayuwarta and now you're expecting me na sake damka maka ita ka kasheta, you must be stupid comon rubuta mata sakinta yanzu nan ka bata let her be free.
"Girgiza kai Haidar ya soma yana fadin " Abba no, pls no, mamy say something pls... haba mamy na kema kin bar sona ne, pls don't this... mikewa Inna tayi ta riko hanun Hanifa ta dubi Haidar tace " idan ka gama dogon tirancin naka ka aiko mana takardan mu ko kaji sammaci a kotu, snn suka fice...
"Mamy kam 'kwllan da suka ciko idanunta ta shiga kokarin mayarwa, she never want this to happen, taso Haidar da Hanifa suyi rayuwa ta har abada a maysayin ma'aurata.
"Bazaka kuma maidani mutumin banza ba kaji na fada maka, na baka nan da gobe ka gama jimaminka snn ka kawo mun takardan idan baka rubuta takardan nan ba ni da kai ne, daga haka Abba ya mike ya nufi sama, mamy ma tabi bayansa suka bar Haidar kaman an dasa dutse. Innalillahi wa inna ilaihirraji'un kawai yake iya ambato, " a fili ya firta kai, inaa no no way, that can't happen, I can't loose her, she's my whole life. Mikewa yayi ya fice dama already car key dinsa na aljuhun sa ya nufi parking lot.
"Daidai nan ya hadu da Sameer yana parking ya dawo daga kai Sumy sch, kallo daya Haidar ya masa ya watsar wani muhun haushinsa yake ji, ji yake kaman ya kai mai naushi,
"Sarai Sameer ya gane Haidae shine jiya ya punching dinsa a hanci, ya dake dan Sumy ta sanar dashi ysakanin Haidar da Hanifa, karasawa Sameer yayi ya mikawa Haidar hanu alamun suyi musabaha, " wani mugun kallo Haidar ya watsa masa kafin yace " let me make this clear to you, Hanifa is my wife, don't you dear think of getting her, idan kuma taimako kayi an gode pls ka koma yanda ka fito we don't need you here, she's already happy with her husband. Wllhi kayi gigin shiga between us sai na kashe ka. Mark my word. Daga haka Haidar ya fincike motarsa ya fice a guje kaman zai tashi sama.
"Kallo Sameer yabi motan dashi har ya fice kafin yayi mirmushi yace " Allah sarki luv is given this guy a tuff time, tabe baki yayi ya girgiza kai kawai ya wuce.
"Yana fita ya shiga neman layin Saif, Saif ya dauka yana fadin Sojan Sea how fa, Haidar yace so far kaidai, where are you. Saif yace gani nan ina fitowa daga BUK, just dropped my wife, daga nan Office na nufa is anything the matter, Haidar yace ok mu hadu a office din, Saif yace alright see you then snn yayi hanging.
"Saif yana shigowa ya hangi motar Haidar a farfajiyan office din, karasawa yayi da motarsa yanda staff ke ajiye nasu motocin snn ya nufo wajen Haidar, gaisawa sukayi ta hanya musabaha kafin suka soma tafiya suka nufi building din.
"Saif ya bude fridge ya ciro drink mai sanyi ya ajiye gaban Haidar dake zaune kujeran hefen na Saif, gani yayi Haidar ya dafe kansa baiko ansa masa maganar da yake masa ba.
"Haidar where are you? Saif ya fadi yana ta'ba table din gabansa. Ajiyan zuciya Haidar ya sau'ke kafin yace " what if I lost her, kai no no that can't be.
"Saif baki sake yace ka soma magana kai kadai ne, wcece zaka rasan. "Galala Haidar ya dago yana kallonsa kafin yace " no bazan rasata ba, she and I are meant for each other, we gonna fix this insha Allah. "Saif ya cire hulan kansa ya ajiye bisa table ya soma dariya wa Haidar kafin yace " what's all this navy, haba kaikuwa kar mace tasa ka zare, nasan bazai wuce akan Hanifa ba. " gajeren tsaki Haidar yayi yace " this is not funny, yeah its obvious is about her, could you just imagine su Abba are asking me to get her divorce,.
"Saif ya kuma sa dariya snn yace " So isn't that what you want, ka mance kasha fada mun you never loved her, you'll never fall for her this and that bla bla bal..... "Enough dalla malam, Haidar ya katse sa, kafin yaci gaba da fadin " you never take things serious, idan bazaka tayani neman way out ba then fine, sai nayi tafiyata.
"Saif ya dan daina dariyan kafin yace " Haidar gaskiya this is pretty complicated, dama Hanifa tana sonka ne da... " And who told you bata sona, stop talking silly. Ya mike gamida daukan phone dinsa yana fadin" I must find a way out, I cannot loose her, she's mine. Saifa dai kallonsa kawai yake kafin yace "har zaka tafi. Ba tareda ya kallesa ba yace yeah zan barka kayi aikinka..... 'karan da wayansa tayi ne yasa yin shiru... Aisar ne me kiransa, ya danyi tsaki kafin ya daga.
"Har yanzu dai basu koma normal da Haidar ba, a dan takaice suka gaisa kafin Aisar ya tambayesa Hanifa, nan Haidar ya sanar dashi an sameta tana gida, hamdalah Aisar yayi snn ya sanar da Haidar ya dauki leave na sati daya, yanzu haka yana Zariya shida mum dinsa sunje ganin Family. Haidar yace good for you, Haidar be bari sunja hiran ba yayi masa sallama.
"Ya kalli Saif dake fito da files yace toh civilian ni na wuce sai kajini, Saif ya mike yana saka hulansa har waje ya rako Haidar bayan ya basa baki kan cewa komai zai zama normal inshaAllah.
"Yana gama parking a haraban gidan kai tsaye dakinsa ya wuce ya kulle kansa yana tunanin solution.
*Ahmadu Bello University Zariya*
"Horn yaketa ma 'yan matan dake tsaye bakin titi gefen wani business center yanda masu saida recharge cards suke amma ko ajikinsu, yanda kasannba mota bace ke masu horn haka sukayi, waya na manne a kunnensa yana fa'din, gani cikin sch din but bansan ta yanda zan sameka ba, daga daya bangaren mutumin yace, just keep going slowly yanzu zan fito.
"Daya daga cikin 'yan matan tace Kunaji ana maku horn kuna tsaye.... da sauri Sady ta katseta ta hanyar fadin, kefa Rashida wllhi haka kike, to meye laifin idan mun tsaya a shoulder naga dai ba kan titi muke tsaye ba ko, idan hanyan ta masa kadan ya tashi sama mana, wllhi bamu barin wajen nn sai mun gama loda katinmu.
"Aisar cikin kuluwa ya fito da kansa ta glass din window yana kara danna masu horn da iya karfinsa, take biyu daga cikin 'yan matan nan suka juyo suma a hasale, banda Sady wacce take faman saka kati a wayanta Rashida da Fadila har suna hada baki wajen cewa woow, me motan da motar ya burgesu.
"Ganin sunyi tsaye suna kallomsa yasa jan tsaki kafin yace " are you guys deaf,ko baku gane horn ne. Sosai abun yabawa Sady haushin jin mutumin nan yana masu Fadila masifa su kuma suna tsaye sunyi shiru. "Aiko a hasale ta juyo sukayi ido hudu kallon kallo sukeyi, cikin masifa ta karaso gabansa tana fadin " idan mu kurame ne kai kuma mene ne? Kana driving tsaban bakasan dokan tuki ba amma kana making call, ko kuma cewa akayi har kan shoulder na tukin motana ne, daka bi takanmu da kafi burgeni..... "Da mugun mamaki Aisar ke kallon yanda take masifa, murmushi yayi ya fito daga cikin motan ya 'karaso gabanta, yana sanye da shirt na kakin land army da bakar three quarter, duk suka bisa da kallo banda Sady da ta wani hade rai ta rike 'kugunta kai kace dukan tsiya zatayi wa mutumin nan, har gabanta Aisar ya tsaya kafin yace" kikace dana fi burgeki, yayi wata murmishi kafin yace so you have a crush.... " What ni Allah ya kiyaye ni wllhi, I've never seen a disgusting mutum kaman kai ba a rayuwata, taja dogon tsaki zata wuce ya riko gyalenta, fizgewa tayi tace dalla malam karka sake ri'ke mun mayafi, ya mayso da fuskansa kusa da nata yace ko kuma me? Me zaki iya mun, nan fah su Fadila suka matso suka shiga basa hakuri, suna jan Sadiya. Murmushi yayi yace kinci darajan 'kawayenki da yau kin gane kurenki yarinya, da kinyi frog jump yanzun nan.... dogon tsaki taja tana fizge hanunta daga rikon dasu Rashida suka mata tace," kai kana tunanin zaka iya sani