Showing 3001 words to 6000 words out of 114964 words
kuka tsaya.
"Ya 'danmasani meke faruwa pls me ka shirya mana cewan hany.
"Ok nayi maku 'karyan dana saba ko, shikenan fine kar kuzo.
"Pls tell us you're not tricking us.
"Mtsw shikenan Sadiya kuzo muje, ganin yaci serious yasa su binshi gaba 'daya suna addu'an Allah sa ps zai barsu su buga... hanyan da sukaga ya nufa ne yasu tsayawa suna kallon kallon. Ya juyo yana murmushin mugunta yace muje mana.
"Tab wllhi na yafe cewan Hanifa.... Haidar dake tsaye ta window na kallomsu ya gama 'kuluwa cikin tsawa yace "kuzo nan dukanku ya nuna harda 'danmasni....
"Hanifa kam sida tayi kusan sakin fitsari a jikinta dan tsoro, shikenan ta shiga uku ya gane an 'bata masa key point dinsa....
"Go on your kneels ya fadi a dake, gaba daya suka tsuguna suna muzurai.
"Cikinku wani shafeffe da man ne ya 'bata mun motata, shiru sukayi babu wanda ya iya cewa komai.
"Are you deaf! Ya daka masu tsawa.
"Wllhi yaya bani bane nikam bana gidan yanzu na dawo, 'danmasani ya fadi,
"Ba da kai nake ba su sunsan kansu wa'enda nakeda su, kai naka punishment din na late 'din aikan da kayi ne.
"Am talking to you you idiots ya sake daka masu tsawa, who among you touched my car.
"Ya dubi 'danmasani yace oya start frog jump sannan ya shiga zuge belt din jikinsa, nan su shema suka shiga kuka suna rokonsa. Pls yaHaidar we're sorry pls, ko ajikinsa haka ya shiga zuga masu belt suna ihu suna basa ha'kuri, saida sukayi laushi ya tsagaita Sadiya dataji azaba nan tace wllhi yaya Hanifa ce dama cewa tayi sai ta rama abinda ka mata wai.
"WHAT! Ya furta awkwardly. Lallaima raini ya shiga tsakaninsa da wann yarinyar, ya dubesu yace suje and duk wanda tace Hanifa na side dinsa sai ya karya yarinya. Simsim suka wuce suna goge hawayen idanunsu.....
"Ya maida dubansa ga Hanifa wacce 'yan hanjin cikinta suke kan 'kugi, shikenan yau itakam ta mutu, juyawa cikin 'dakinsa yayi yace biyoni babu musu tabi bayansa gabanta na fa'duwa, ruwan sanyi mai 'kan'kara ya shiga cirowa daga fridge, tana kallonsa sida ya ciro gora biyar, ( ni kaina Nazee I wonder me zaiyi da goran ruwan sanyi har biyar🙄).
"Gaba daya ya bude bottles din ya 'dauko belt ya nannade a hanunsa ya kura mata ido, wani mugun tsananta yakeji.
KE! ya daka mata tsawa, a razane ta 'dago idonta da sukayi raurau tana dubansa.
"Na miki kama da wanda zaki raina?
"Kasa cewa komai tayi sai 'barin da jikinta keyi.
"Am asking you, you piece of trash.
"A hankali ta soma girgiza kai,
"Murmushi yayi gamida 'dauko goran ruwan sanyi ya shiga juye mata a jikinta ga shi dama lokacin sanyi ake, take ta shiga 'bari ha'de da kwalla ihu, wani wawan mari ya 'daura mata yace "shut up! Idan kika sake kuka plus goran ruwan sanyi daya dan haka gwarama kiyi shiru.
"Kuka take tana 'barin sanyi amma Haidar ko a jikinsa babu alamun tausayi a tare da shi. Bayan wann azaba da ya gama yima Hanifa yana ji yana gani tana rawan 'dari yace oya tidy this mess. Haka ta dauko mopa ta shiga goge wajen ga sanyin ac gana gari ga kuma na ruwan jikinta. Ta gama gyara wajen tsaf sann ya fito da kayan wardrobe dinsa yace she should tidy it. Tana gani ya dauki car key ya fice gamida kulleta cikin 'dakin....
"Tsugunawa tayi a wajen tana rera kuka, wani mugun tsanan yaHaidar na dada fizganta.
"Koda mamy ta tambayi su Shema Hanifa sai ce mata sukayi tana sashen inna dan haka mamy bata kuma bin ta kansu ba dan tasan wataran sukan kwana wajen kakar tasu mussaman Hanifa yar lele....
👸🏻Queen Samy😍💄💋......
[5/9, 6:10 AM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah* 🌹🌹🌹
07
Yana fita bai zarce ko ina ba sai gidan abokinsa Saif,,
" Haidar sojan ruwa yau 'batan kai kayi naganka a gidanmu, cewan Saif matashi kyakyawa maiji da ku'di da class.
"Ka fara halin naka ko wllhi kasa tsiya zan juya. Haidar ya fadi sanda yake kokarin zama bisa sofa.
"Hannu Saif ya mika masa suka gaisa kafin yace "mutumina nasanka ne ba'a ganinka saida dalili idan ba new series nace maka na samu ba bazan ganka ba, anyway yaushe kazo.
"Last week and gobe zan wuce insha Allah.
"Haba dai so soon.
"Wllhi nayi receiving urgent call frm my boss 'dazun nan.....
"Dariya Saif ya kyalkyale kana yace kace in law dinka mana....
"Mtsw don't even start ko na rasa mata ai bazan auri Lateefa ba kawai dai tana 'bata lokacinta ne. Toh wai ni yaushema nakeda lokacin wasu mata, I don't think suna agenda dina. Kawai so nake nayi kusa da Dad dinta coz am spying on him.
"Saif ya tsare Haidar da ido sann yace " kasan Allah zai tambayeka idan ka yaudari yarinyar nan ka duba ka gani fa how she's dying for you.
"So! Ni nace mata ta soni, beside ni ban ta'ba ce mata ina sonta ba in the first place kawai dai tana shirmenta ne.... Saif zaiyi magana Haidar ya dakatar dashi ta hanyar 'daga masa hannu yace " kaga malam let's change the subject if not nayi tafiyata...
"Murmushi Saif yayi gamida 'dauko masu ta'din series din da suke bi *24*.
hira sosai suka sha da Saif har sukayi sallahn magrib. 'Karfe 7:00pm on the dot Haidar ya mi'ke dan tafiya gida tare suka fito da Saif suka nufi gidansu Haidar...
"Tun bayan fitan Haidar Haneefah keta cin aikin gyara masa wardrobe, saida ta shirya komai ta maidasu mazauninsu. Ga wani irin zazza'bi da ya sau'ko mata lokaci guda, karkarwa take tana numfashi da kyar abu kaman wasa nan fa taji bata iya 'daga koda 'dan yatsanta ne. A haka ta zube a wajen kaman sumemmiya.....
" yana zura key jikin 'kofa gaban shi yayi mugun fa'duwa sai yanzu ya tuna da Hanifa, yayi saurin 'karasa bu'de 'kofan gamida shigewa bedroom. Kwance ya ganta a 'kasa kaman bata numfashi, gaba daya ya kidime ya 'karasa ya shiga jijjigata yana ambato sunanta amma shiru.
"Saif dake zaune a parlor yaji shirun Haidar yayi yawa ya mike ya nufi 'dakin, da sauri ya 'karasa ganin Haidar na shafa ruwa ma Hanifa....
"Lafia friend meya sameta,
"Dauko car key na mu kaita asibiti pls Saif she's running out of conscious...
"Saif kam tuni yayi mutuwan tsaye yana bin Haneefa da kallo... _tunda yake bai ta'ba ganin kyakyawa kamar Haneefa ba_......." a fili ya furta "GOD HAVE MERCY"....
"cikin 'kuluwa Haidar yace dan Allah ka wuce muje kar ta mace mun a nan.... da sauri Haidar ya azata bisa kafa'da suka nufi asibiti....
"Gaba 'daya sunyi jigum suna tunanin baby sis dinsu har yanzu bata dawo daga wajen yaHaidar ba gashi sunji fitar motarsa ko wani irin azaba yake mata sai Allah.... suna a haka mamy ta turo 'kofan 'dakin ganinsu tayi gab 'daya kaman marassa lafia..
"Ku kuma lafia meye kuka zauna haka.
"Ba komai mamy Shema tayi 'karfin halin fa'din haka....
"Har yanzu Hanifar tana sashen inna ne..... mamy ta tambaya
"Kame kame suka soma daidai nan wayan mamy ya 'dau ruri...
"Daga 'daya 'bangaren Haidar yace "mamy dama muna asibiti ne.. na kawo Haneefa batada lafia...
"Haneef kuma ta fa'di sanda take fita daka 'dakin.... su Shema kuwa kallon kallo suka shigayi wa junansu.
"Sady tace bakuji wayan da mamy keyi ba da yaHaidar take waya kardai yaji ciwo wa Hany ce.
"Haba dai saidai bata da lafia amma bazai mata dukan kisa ba Shema ta fadi.
"Hm shiasa nake kwa'ban ta ai, kwatakwata hany bata jin magana ta faye tsaurin ido yanzu ga irinta nan, su sojoji basuda imani ko ka'dan inagama idan zaka shiga soja sai an maka alluran zalunci. Sumy ta fa'di sanda take kokarin daura dan kwalinta. Muje muji mene ne. Gaba daya suka fice sukabi bayan mamy...
"Salati inna ta soma yi " toh meyasameta harda bada gado a asibiti.
"Mamy ta 'dauko mayafin inna gamida rufa mata tace muje asibitin mu gani Sale dreba na jiranmu. Har suka isa mota inna bata daina zuba salati ba.....
"Bayan an daura mata ruwa Dr ya bu'kaci ganin Haidar dan haka ya rage daga Hanifa sai Saif a 'dakin, Saif ya 'kura mata ido yana kallon tsantsan kyaunta da kuma kammaninta da Haidar. A ranshi yake raya anya ba dukan yarinyar nan Haidar yayi ya kulleta ba, dan yasan irin tsoransa da kannensa keji, ya matso kusa da ita yana kallon kyakyawar fuskarta a hankali ya furta "Allah ka nufeni da zama *mijin Haneefah* daidai nan ta soma hattishawa.... da sauri Saif ya matso yana mata sannu 'ko'karin tashi ta shiga yi Saif ya ri'keta dan kuka kawai takeyi.
"Sorry Hanifa kina son wani abu ne.
"Dagowa tayi tana kallon Saif ta ganeshi abokin yaHaidar ne kana tace "inane nan ni ka kyaleni wajen mamy zanje ta sake masa wani sabon kuka... daidai nan aka turo 'kofan 'dakin Inna ne da mamy, gaba 'daya suka karasa kan Hanifa basu ko kula da Saif dake zaune gafe ba... Inna tarungume Haanifa tana fadin meyasameki 'yar jikalle.. sai sann mamy ta kula da Saif nan suka shiga gaisawa yace bari ya kira Haidar yana office din Dr...
"Kasa ce masu komai Hanifa tayi sai kwanciya jikin Inna da tayi.... suna ahaka Haidar suka shigi 'dakin ya nemi waje ya tsaya yanama su Mamy sannu da zuwa.
"Suna ha'da ido da Hanifa kuwa wani mugun kallo ya watsa mata ba tare da yace da ita ko sannu ba. Har cikin jini datsokanta ta tsane yaHaidar ta tsaneshi like hell.
"Magunguna Haidar ya ajiye saman drawer ya kalli mamy yace ga prescriptions din mamy inaga gobe zasu discharging dinta...
"Mamy ta amsa da toh kana tace wai me ya sameta ne Haidar.
"Ya 'dago ido gamida narka mata harara yayi sa'a itama shi take kallo, take ta kuda kanta gefe va tare da tace komai ba..
"Its just a cold mamy, wasan da suka saba na shiga ruwa da shan ice cream without a limit shi yasa mata cold 'din. Ya karashe yana hararanta...
"Da mugun mamaki Hanifa ta 'dago tana dubansa.. ya galla mata harara take ta sunkuyar da nata idon 'kasa.... itakam anya yaHaidar yayanta ne kai kodai ita 'din ba 'yar gidan bace.... take taji 'kirjinta na bugawa da sauri da sauri....
"Karfe 8:32 Haidar da Saif harna da mamy suka nufi gida bayan sun bar inna wajen Haneefa.....
👸🏻Queen Samy😍💄💋......
[5/9, 6:10 AM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
08
"Misalin 'karfe 10:12am Haidar ne ke shirya tsaf cikin kakinsa na Navy, yayi matu'kar kyau kayan ba 'karamin kar'bansa suke ba. Ya gama 'daura belt sann ya 'dauko cap dinsa ya sakata ta zauna 'das a kasansa. Wayyo come see handsome😍.
"Mamy na zaune bisa darduma ta ida sallahn walha Haidar yayi Sallama, da murmushi saman face 'dinta ta amsa masa. Ya 'karaso gamida zama bisa stool.
"An fito baban Abba, ta tambaya sanda take dubansa cike da so da 'kauna.
"Eh mamy na fito flight din 11:00am.
"Toh kunyi waya da Abbanka ne?
"No na kira bai 'daga ba but zan sake kira before na tashi.
"Ok toh... ko zaka ci wani abu ne? Kaga fa just coffee kasha.
"No mamy am Ok bana jin yunwa.
"Shikenan Son Allah ya maka albarka ya kuma tsare hanya..
"Ameen mamy na gode...
"Tare suka fito har bakin parking lot, sale dreba na ganinsu ya taso da sauri yana fa'din hajiya ina kwana. Mamy ta amsa snn sale suka gaisa da Haidar ya kar'bi luggage 'dinsa gamida sawa cikin boot.
"Har ya shige mota mamy ta juyo tace karfa ka mance kubi asibitin ka duba Hanifa snn kayi sllama da Inna.
"A ta'kaice yace toh mamy insha Allah.... sann malam habu ya hangame masu gate suka fice...
"Tun shigowan Haidar cikin asibitin mata nurses ke binsa da kallo kakin nan ba 'karamin kar'bansa tayi kaman dominsa aka 'kera. Shi kuwa gogan yasan suna kallonsa dan haka ya 'daure fuskan nan tamau kaman baisan kalman dariya ba, hakan sai ya zame masa fashion, yana tafiya kana jin sautin tafiyan nasa irin ta mazaje cikakkun sojoji takalmin 'kafarsa ya 'kara ma tafiyan nasa sauti mai da'di da kuma kyau. Wani hanya Captain AA ya nufa ba mata kawai ba harta maza sai sunbi shi da kallo dan kuwa kwarjininsa da kyaunsa ya zarce bayani....
"Tana zaune tana shan lipton ya turo 'kofan gamida shigowa, bata 'dago kai ba dan azatonta nurse ne ko Dr. 'Kamshin turarensa ya tabbatar mata shine dan kuwa wann kamshin shine tamau a wardrobe dinsa jiya da take gyarawa, da sauri ta 'dago dan tabbatr ma idonta shi'dinne kuwa yana tsaye ya ha'de rai kaman baisn kalman dariya ba.
"Baki a cure tace inakwana yaHaidar sanda yake shigowa cikin 'dakin.
"Kaman bazai amsa sai kuma ya amsa a ta'kaice, gaban gadon da take kai ya 'karaso 'kirjinta sai dukan uku uku yake, a ranta take addu'an Allah sa ba kasheta yazo yi.
"Hannu yasa ya 'dago ha'banta yana mata mugun kallo. Ita kam kasa kallonsa tayi dan kuwa sosai yayan nata ke mata 'kwarjini snann ta tsane koda ganin fuskansa ne.
"Jin yanda jikinta ke karkarwa ya tabbatarwa Haidar Hanifa ta shiga makarantar ta nutsu, yayi wani murmushin mugunta kana yace" next time don't try to mess with me, wann ka'dan ne daga cikin irin horon dana tanadar wa marassa kunya irinki useless kawai me kamada mayu. Ta 'dago ido tana kallonsa ya daka mata tsawa "bar kallona da ido kaman na mujiya.
"A ranta tace ai naga da kai da Abba muke kama kaima kana kama da mayun kenan...
"Inna ce ta turo 'kofan bayin tana fa'din likitan ne ya shigo.... murmushi Haidar ya sakar mata sanda take goge fuska yana fa'din tsohuwa ko nazo na ri'keki ne kinsan jikinki babu laka yanzu kin tafi.
"Kaci gidanku Ali wannan 'kafa tawa da kake gani ras take gudun da zanyi ma bazakayi ba... Haidar sai dariya yake.. Hanifa kuwa cewa tayi a ranta mugu kawai ji kaman ba shi bane ya gama 'daure fuska yanzu...
" Inna taga yanda jikan nata yasha kyau cikin uniform dinsa ta wage baki tana fa'din "A a a kaga soji marmari daga nesa ta fa'di sanda take zama bisa sofa.
"Murmushi Haidar yayi ya 'karaso gamida gaida Inna.
"Badai yau zaka tafi ba dan nasan kana saka wannan inifom 'din naka toh tafiya ne zakayi ko zaka wani taro....
"Ya 'dan dara kana yace tshohuwa kenan kice baki son tafiyan nawa..
"Toh ai kaine idan ka tafi sai ka shafe rabin shekara mutum kullum a saman ruwa kaman kifi....
"Ya 'karaso gaamida ri'ke hannayen Inna yace ba jimawa zanyi ba tsohuwa wata shida kawai zanyi..
"Hanifa a ranta tace Allah sama karka dawo kayi zaman ka a can mugu kawai...
"hira sosai suka sha da Inna 'karfe 10:35 ya mike yana fadin to tsohuwa zan wuce kada na makara.
"Inna ta mike tana fadin toh bazaka ci wani abu ba... girgiza kai yayi yace "noo bazan iya cin abinci a nan ba it will irritate me beside am Ok ma...
"Baki inna ta hangame tana dubansa kana tace kaji dashi muje ni na raka ka.
"Ya murmusa yana wani ksahe ido yace "baki so wata ta kwace maki nine gashi tun shigowana 'yan matan ke bina da kallo.
"Dariya Inna tayita jawoshi jikinta tasan zatayi kewan jikan nata sosai da sosai.
"Suna ficewa Hanifa taja tsaki a hankali sann tace " harda wani wai bazai iya cin abincin asibiti ba hmm mtsw, ta kwai kwayi yamda yayi magana "no its irritating. Taja dogon tsaki kana tace Allah raka taki gona azzalumi kawai...
"Fitan Haidar da 'kadan su Shema suka shigo da uniform dinsu a jikinsu daga sch suke dashike friday ne...
"Gaba daya sukayi kanta suka ru gume Inna tace dan Allah kad ku 'karasata mana.
"Sumy baki a ture tace kai kakus we missed her a lot nefa.
"Sady ta riko hanunta tace baby sis how feeling now.
"Am fine now, Dr muke jira ya iso yayi discharging namu...., 'Danmasani ne y shigo yana 'ko'karin maida dariyansa ciki. Nan fahh Hanifa ta 'kule.
" kunnenta ya 'karaso yana ra'da mata "wayace miki a raina soja, gashi kinji a jikinki..
"A kufule ta ture shi tana fa'din eh 'din ina ruwanka.....
"Yana dariya yake fa'din um um yanzu zanyi waya na gayawa ya Haidardan yace komawa kikayi tsaurin ido a fa'da masa, jirginsu batayi landing ba yanzu zai juyo...
"Karki kula shi baby sis cewan Shema dake zaune gefenta....
"Sai bayan juma'a aka sallameta, suna zaune gaba 'daya a parlor Saif yayi sallama ya shigo...
"Wani 'katutun ba'kin ciki Hanifa tayi dn ba yaHaidar kawai ba harta abokansa ta tsanesu... bayan sun gaisa mamy take ce masa